Showing 117001 words to 120000 words out of 186776 words
Chapter 40 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
duba jikinta.
TAIMIYYAH jin Iyah kawai take yi amma sam bata yi magana ba,sai ma wani baccin da taji yana fisgar idanunta ba a jima ba kuwa ta ɓingire ta bar Iyah na ta surutunta ita kaɗai.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*49*
Washegari ƙarfe takwas da rabi na safe Baba Sani ya taso su Zuhura da Basmah ɗauke da kayan breakfast suka iso asibitin.Sun kuma tadda TAIMIYYAH ta taahi daga bacci,kuma ikon Allah garas ta tashi babu inda tace yana mata ciwo. Zuhurah suka gaida Iyah tare da tambayarta me jiki ta basu amsa da cewa, "Alhamdullillah! Ta samu sauƙi zuwa anjima kaɗan ma sai gida Insha Allah."
Baba Sani da ya isa gaban gadon da TAIMIYYAH ke kwance idanunta a buɗe tana jin duk abinda ake faɗi,isowan Baba Sani wajenta yana mata sannu yasa ta yinƙurawa ta tashi zaune,Baba Sani ya kama hannunta ɗaya yana ɗagota sosai ta zauna yana tambayarta ya jikin nata? Ta ɗaga manyan idanunta ta dubesa da ɗan guntun murmushi saman face ɗinta take gaida shi tare da bashi tabbacin ta samu sauƙi, ya shafa kanta yana faɗin, "Masha Allah Zaynab Allah tsare sai a dinga kulawa da kyau kinji ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a hankali tana faɗin, "Insha Allah Baba." Ƙarisowan su Zuhura suna mata sannu yasa ta dubansu tana amsawa,idanunta akan Basmah wacce rabon da TAIMIYYAH ta sanya ta a ido tun randa suka haɗu ta ganta tare da Nass.
TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai daga duban face ɗin Basmah tana jin can ƙasan zuciyarta wani abu na motsawa.
Iyah ce tace wa TAIMIYYAH ta tashi ta je tayo brush don ta samu ta karya ta sha magunguna.Babu musu TAIMIYYAN ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet,tana jiyo su Baba Sani na ma Iyah sallama zasu wuce,Iyah ta raka su bakin ƙofa tana sanar da Zuhurah cewa da sun isa gidan, ta shiga Sasanta ta sanar da Babah Ladi kar tayi wahalan yin abin karyawa tunda ga shi sun kawo.
TAIMIYYAH bata wani jima sosai ba cikin toilet ɗin ta fito,idanunta akan Iyah da ke zuba abinda zata ci cikin plate.Ta ƙariso bakin gadon tana gaida Iyah,Iyah ta amsa tana cewa, "Sannu ya jikin naki kan dai ya daina ciwon ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana cewa, "Eh babu inda ke min ciwo sai wajen da akai ɗinki a gefen wuyarnan ne kawai ke ɗan damuna."
Iyah ta dubeta da kulawa tana cewa, "Ayyah! shi ma ɗin zai bari kin san abu a maƙarfafa dole kiji ya dameki,da zaran zaren ɗinkin ya fita shikenan zaki samu sauƙi, sannu bari in zuba miki abincin ki ci, zaki sha tea ɗin ne in haɗa miki babu madara ko kunun zaki sha gashi nan sun haɗo da kunu?"
TAIMIYYAH ta ɗan ɓata face kaɗan cike da ƴar shagwaɓa take cewa, "A'a Iyah ni ba zan sha kununsu ba haɗa min tea ɗin kawai,amma zallah milo zaki samin ko sugar kar kisa inba haka ba zan ji ina jin amai ne da xaran na sha."
Iyah ta jinjina kai tana yin duk yadda TAIMIYYAH ta buƙata.Bayan duk ta kammala zuba mata soyayyen dankali da egg ɗin ne, ta haɗa mata tea ɗin tana ɗaukan plate da kofin tea ɗin ta kai mata kan gadon ta aje.
TAIMIYYAH ta fara cin abincin a hankali tana ji gaba ɗaya bakinta babu ɗanɗano sabida muran da ke son kamata.Dama ta san tunda ruwa ya doke ta sai tayi wannan muran, zazzaɓin ma don ta amsa allura da magungunan da take sha ne da yanzu ta san tana kwance sosai.
Suna tsaka da karyawa daga ita har Iyah dake zaune daga ƙasa saman babbar dadduma, suka jiyo sallama daga bakin ƙofan shigowa ɗakin.
Iyah ce ta amsa tana bada izinin shigowa don taso ta gane muryan kamar na Hajiyar jiya ce wacce suka kaɗe TAIMIYYAH.
Hajiya Aysha da Dattijiyar me aikinta Babah Rabi suka turo ƙofar suka shigo bayan Iyah ta amsa sallamr tasu da basu izinin shigowa,Babah Rabi hannunta riƙe da ƙaton kwandon ɗaukan abinci.
Cikin fara'a Iyah ke musu barka da zuwa tana me nunawa Hajiya kujera ta zauna,ita kuma Babah Rabi ta samu saman daddumar da Iyah ke kai ta zauna.
Hajiya Aysha memakon ta zauna sai ta nufi bakin gado kai tsaye wajen TAIMIYYAH,wacce tun shigowansu ta tsaida cin abincin da take yi.
"Sannu Zainab ya jikin naki,ina fata dai babu wata matsala ko?"
Hajiya Aysha tayi tambayar idanunta akan TAIMIYYAH data ɗan sadda kanta ƙasa,kafin ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan fuskar Hajiya Aysha da ke jifanta da murmushi.
TAIMIYYAH tayi ƙasa da muryarta tana gaida Hajiya Aysha tare da bata tabbacin taji sauƙi babu wani matsala.
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Masha Allah,Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba kyakykyawar ɗiyata."
Yadda tayi maganan cike da kulawa yasa TAIMIYYAH dubanta da murmushi tana amsawa da cewa, "Ameen Hajiya na gode."
Daga haka Hajiya Aysha ta koma wajen Iyah suna sake gaisawa, ita kuma Babah Rabi ta isa wajen TAIMIYYAH tana mata sannu.Iyah ta dubi uban kayan da suka kawo tana cewa, "Haba Hajiya ya da wannan ɗawainiya haka mu da za a sallama nan bada jimawa ba,wallahi da baku yi wahalan kawo komi ba, an gode ƙwarai Allah ya fi mu yabawa ya saka da alkhairy sannu da ƙoƙari."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana duban Iyah da murmushi take cewa, "Haba Hajiya babu komi ai abinda duk ya dace ne ayi ake yin,Allah dai ya ƙara mata lafia ai na ga jikin nata Alhamdulillah."
Iyah da fara'a take baiwa Hajiyar tabbacin jiki fa Alhamdulillah! Kafin ta miƙe ɗauke da flask ɗin ruwan xafi ta nufi toilet don haɗawa TAIMIYYAH ruwan wanka.
"TAIMIYYAH ta shi ki je ki watsa ruwan ɗumi a jikinki ko kya sake jin daɗin jikin,kafin mu koma gida kiyi wankan me sosai."
Iyah ce tayi maganar lokacin da ta fito daga banɗakin idanunta akan TAIMIYYAH, wacce zuwa lokacin ta zame ta kwanta lamo kamar ta koma bacci.
Jin maganar da Iyah tayi yasa ta tashi tana ɗan zumbure baki alamun bata son yin wankan,uwa uba su Hajiya da ke zaune a ɗakin wanda haka kawai take jin nauyin matar.Amma babu yadda ta iya haka ta sakko daga kan gadon idanunta a ƙasa,sam bata yadda ta dubi inda suke zaune ba amma tana jin idanunsu ya yawo akanta.
A hankali ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta tana tafiya zuwa hanyar banɗakin ta shige,Hajiya Aysha da me aikinta Babah Rabi suka bi TAIMIYYAH da kallo Hajiya Aysha na jin wani abu na ratsa zuciyarta akan Yarinyar.
Ta maida dubanta kan Iyah lokacin da TAIMIYYAH ta ɓacewa ganinta tana cewa, "Hajiya wannan Auta taki ba dai kyau ba,gata komi nata cikin sanyi da nutsuwa take yinsa,amma wannan laluran ƙafar a haka kika haifeta da shi ne?"
Iyah ta saki murmushi me faɗi tana duban Hajiya Aysha take faɗin, "Ko ɗaya Hajiya wallahi bada shi aka haifeta ba daga baya ne Ubangiji ya aiko da lalurar,ta fara tafiyarta tana yawo ko'ina sai zazzaɓi dare ɗaya, washegari daga yin allura ƙafa ya saki shikenan mafarin sanadin ƙaddaran shanyewan ƙafar da akai ma allurar,mun sha fama sosai kafin ma asamu ta fara takawa da taimakon dafa guiwar ƙafar...."
Iyah ta cigaba da bayyanawa Hajiya Aysha yadda suka ci wuya akan laluran ƙafar TAIMIYYAH,kafin a samu ta fara takawa da ƙafar a haka yadda take tafiya.Ta cigaba da faɗin,
"Amma kin ga cikin ikon Allah da taimakon dafa guiwar nan da take tana takawa babu abinda bata iya yiwa kanta,tana harkokinta komi babu abinda ke gagararta sai kaɗan daga manyan abubuwan da dole sai an taimaka mata,amma tana da ƙoƙarin ayyuka da son yin komi da kanta bata ma so ace za a yi mata abu inba gagararta yayi ba."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Allah sarki haka Ubangiji ke ikonsa nata ma da sauƙi ai tunda tana yawonta ko'ina da ƙafar a haka,wasu a keken guragu ake turasu,wasu basa ma jirgawa ko'ina sai da taimakon jan gindi,sai a godewa Allah bakomi nakasa so da yawa wani baiwar ne,mutane ne kawai ke nasu shirmen ki ga ana nuna musu bambamci da kyaran su a wasu lokutan,ita dai Zainab gashi an mata baiwar kyau da nutsuwa ,lokaci ɗaya na ji ta shiga zuciyata Hajiya,ina fata dai tayi karatu ba a tauyeta ba an ƙi sakata a makaranta?"
Hajiya Aysha tayi magana idanunta akan Iyah da ke faman murmushi,kafin ta fara faɗin, "Aiko dai Hajiya tayi karatunta sosai don ma wannan yajin aikin da malaman makarantun jami'a suka tafi ne yasa bata cigaba daga NCE da ta kammala ba,amma yanzu haka ma wani makarantar Computer take zuwa,a islamiya ma tayi sauka ta sauke har da manyan littafai,sai makarantar haddah da ake daf da yayesu sun kusa kammala haddar Qur'ani baki ɗaya,ina ga bazai ma wuce nan da sati uku ba za a yaye su."
Iyah ta kai ƙarshen maganar dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin,tana ɗaure da zani a jikinta ta yafo rigar data cire akan kafaɗunta. Hajiya Aysha ta bita da ido tana cewa, "Kai Masha Allah,Allah yayi wa rayuwarta albarka ya bata mijin aure na gari wanda zai riƙe ta da amana."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Ita dai TAIMIYYAH tuni ta isa bakin gado ta zauna duk kunya ya isheta tunda ta fahimci hiranta suke yi,cikin sanyin murya ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah kayan fa baki ciro min ba."
Iyah sai ta tashi ta isa wajen jakan da ta sanyo musu kaya ta cirowa TAIMIYYAH doguwar rigar atamfa,ta haɗa da man shafawarta da ta zo mata dashi ta kai mata bakin gadon ta aje.
TAIMIYYAH sai ta ɗauka kayan da man ta koma banɗakin don shiryawa,sabida ba za ta iya shiryawa akan idanun su Hajiya Aysha wacce bata iya ɗauke ido daga duban TAIMIYYAN.
Komawar TAIMIYYAH xuwa banɗakin ya saka Hajiya Aysha cigaba da hiran su da Iyah akan masu lalura iri-iri,cikin hiran ne Hajiya Aysha ke tambayar Iyah bayan TAIMIYYAH tana da wasu yaran ne? Iyah tayi murmushi tana cewa, "Hajiya kenan wannan ɗin ma ba ni ce na haifa ba jikata ce ƴar wajen ɗana,mahaifiyarta ta rasu tun tana cimman goyo ni na raineta har kawo yanzu,kuma cikin hukuncin Ubangiji wata ɗaya da wasu kwanaki kenan da rasuwan mahaifinta da ƙanninta su biyu duka rana ɗaya ajalinsu ya sauka...
Iyah ta baiwa Hajiya Aysha labarin yadda mutuwarsu Abie ɗin ya kasance,ta ƙare maganan da cewa, "Yanzu bata da uwa bata da uba sai ni da ƙanin mahaifinta kawai mu ne gatanta, ko fuskar uwarta bata sani ba sai a hoto, yadda kika ganta haka uwar take har kyawun duk na uwarce ta ɗakko,da sanyin halin da komi babu inda tabar marigayiya Zainab TAIMIYYAH.Dama kuma sunan uwar aka saka mata shiyasa muka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH yadda ake kiran marigayiyan."
Hajiya Aysha ta jinjina kai wasu hawaye na taruwa a idanunta,na tsananin tausayin TAIMIYYAH da taji ya cika zuciyarta.Shiyasa lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin Hajiya Aysha ta zuba mata ido,tana sake gano kyawun TAIMIYYAN tare da jin wani ƙaunarta me tsanani na ratsa zuciyarta,tana cigaba da jinjina ƙudiran Ubangiji me yin yadda ya so a kuma lokacin daya ga dama.
TAIMIYYAH ta wuce su a kunyace zuwa kan gado ta zauna,bayan ta aje kayan data fito da su a ninke daga bakin gadon.Ta warware ɗankwalin kayan tana rufe kanta zuwa ƙirjinta da shi,tana me zamewa ta kwanta ta juya musu baya sabida yadda take jinta a takure musamman kallon da Hajiya Aysha ke bin ta da shi.
Shigowar Likitan ɗakin yasa TAIMIYYAH sauke ajiyar zuciya tana fata ya kasance sallamace,aiko cikin sa'a yana sake duba jikinta yayi mata ƴan tambayoyi ta bashi tabbacin babu wani damuwa,sai ya juya yana wa Hajiya Aysha da Iyah magana akan cewa shikenan yanzu zasu iya tafiya gida.
Dama already an riga anyi clearing bill tun jiya,sai kawai Iyah ta ɗaga waya ta kira Sani akan ya zo su wuce zuwa gida an sallame su.
Bayan ta kira Sani driver sai ta kira Baba Sani shi ma ta sanar da shi,ita dai TAIMIYYAH na daga kwance har lokacin tana sauraran Iyah.
Hajiya Aysha ta dubi Iyah tana cewa, "To Hajiya bari mu amsa lambar wayan juna ko a dinga zumunci,kuma Insha Allah zan zo har gida idan an kwana biyu in sake duba jikinta,don gaskiya wannan ɗiya ta shiga raina matuƙa da gaske."
Iyah ta saki murmushi cike da jin daɗin kalaman Hajiyan tace, "Aiko ya kamata kam mu amsa lambar juna Insha Allah za a riƙa gaisawa akai-akai,idan bikin walimar gama haddarsu ya tashi ma, kin ga saina sanar miki ki zo mana bikin walimar,ga wayata sai ki sanya taki lambar idan kika kira sai duk mu yi saving."
Hajiya Aysha ta amsa wayar Iyah ta sanya lambar ta kira, kiran na shigowa ta kashe tayi saving number ɗin tayi ma Iyah itama saving nata numbar.
Ta miƙawa Iyah wayarta tana takawa zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance,ta tsaya kusa da ita sosai tana cewa, "Ɗiyata tashi zaune muyi magana kinji, ki bar jin kunya ta ni yanzu zumunci nake so mu ƙulla nima ki ɗaukeni kamar Iyar taki kinji ko?"
TAIMIYYAH ta tashi a kunyace tana murmushi kafin ta buɗe baki cikin sanyin murya take cewa, "To Hajiya nagode da kulawa Allah saka da alkhairy."
Hajiya Aysha ta amsa da, "Ameen Zainab Allah ƙara miki lafiya,yanzu ga wayata nan saka min number ɗinki zan dinga kiran ki,ke ma kuma sai ki dinga nemana a waya muna gaisawa."
Tayi maganar tana miƙawa TAIMIYYAH wayarta me nauyin kuɗi tamkar ba Dattijiya ba,inji TAIMIYYAH cikin zuciyarta lokacin da wayar ya je hannunta.
Ta loda lambobinta tana miƙawa Hajiyar wayar don tayi saving da sunan da take so.
Hajiya Aysha ta amsa wayar ta yi saving sukai sallama da TAIMIYYAH akan cewa sai ta ji kira,daga haka ta juya zuwa wajen Iyah suna magana.
Babah Rabi kuma ta miƙe don ɗaukar kwandon abincin da suka zo da shi wanda ba a taɓa komi ciki ba,sai Hajiya Aysha ta hanata tana cewa, "Babah Rabi aje kawai su tafi da shi gida,tunda har mun zo da shi ba za mu koma da abinci gida alhali wacce aka shirya domin ta bata ci ba,gwara su je dashi duk randa Allah ya nufa na samu lokaci na je gida sake duba ta sai na amsa kulolina."
Iyah dake saurarensu tana jinjina karamci da mutuncin wannan Hajiya sai ta riƙe haɓa tana cewa, "Ayi haka Hajiya ai ɗawainiyar tayi yawa,da kun koma da shi bakomi wallahi mun gode matuƙa."
Hajiya Aysha ta girgiza kai tana cewa, "Gaskiya Hajiya ba za a koma da abinci TAIMIYYAH da aka yi dominta bata ci ba."
Hakanan Iyah ta haƙura suka bar kwandon abincin,ta tafi yi musu rakiya zuwa bakin mota.
Ita dai TAIMIYYAH iyakarta bakin ƙofa Hajiya Aysha tace ta koma ta gode da rakiyan ta yafe,Iyah dai sai da ta ga tafiyarsu sannan ta juya zuciyarta na jinjina kirki da karamcin wannan Hajiyar, wacce basu san hakiƙanin wacece ita ba.
Amma dai daga yanayin shigar da ke jikinta zuwa ƙatuwar motar da ake janta aciki ya tabbatarwa Iyah cewa akwai masu gidan rana a tattare da Hajiyar wato (Kuɗi).
Tafiyar su Hajiyar bada jimawa ba Sani ya iso shi ma,suka tattara yanasu-yanasu Sani ya kwashi kaya da basket ɗin abinci zuwa mota.
TAIMIYYAH ta sakko tana zura hijab ɗin da Iyah ta aje mata suka fito tana takawa a hankali har zuwa wajen mota.
Iyah sai da ta tabbatar basu manta komi ba sannan ta fito daga ɗakin ta nufo wajen motar,tana shiga Sani ya tada motar suka baro asibitin zuwa gida..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*50*
Motar Sani na shigowa cikin gidan ita kuma Umma na fitowa daga Sasan su, hakan yasa ta nufi wajen motar Sanin kai tsaye don gaida Iyah da yiwa TAIMIYYAH sannu da jiki kada tayi laifi wajen Iyah.
Bayan sun gaisa da Iyan ne ta dubi TAIMIYYAH wacce ta fito daga cikin motar ta furta, "Sannu Zainab Allah ƙara lafiya,sai ki dinga kula tunda kinsan kina da matsala ki daina abu irin na masu lafiyan ƙafafu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai kawai ba tare da tace komi ba tayi gaba abinta,Umma ta bi bayan TAIMIYYAH da harara tana taɓe baki.Iyah ita gaba ɗaya hankalinta ma na kan Sani da ke sauke kayan da suka dawo da shi ne,sai daga baya ta dubi Umma lokacin da Sani ya aje kwandon abincin da su Zuhurah suka kai asibiti tana cewa, "Yauwa Zuwaira sai ki wuce da ragowar abincin aba masu ci,kin ga wani nan ma ko taɓawa ba a yi ba Hajiyar da suka kaɗe TAIMIYYAH ce ta kawo asibitin."
Umma ta dubi tsadaddun kulolin da ke cikin basket ɗin zuwa shi kansa basket ɗin da ke ɗauke da kulolin abincin,wanda kana kallo kasan ba ƙananun kuɗi ne suka saye shi ba, ta wani taɓe baki tana cewa, "Allah sarki ashe dai mutanen kirki ne da wasu ne fa guduwa za su yi Iyah."
Iyah ta tamke face tana faɗin, "To su