Showing 27001 words to 30000 words out of 186776 words
Chapter 10 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
nake yi ko?"
Ta ƙare maganan cikin low voice,manyan idanunta akan Maryama da ta saki murmushi me faɗi,kafin ta furta "Wallahi ni haka na ke gani TAIMIYYAH,gaskiya kina da ƙoƙari sosai kam da son aiki."
Daga haka suka kamo hiran Skull,Maryam ɗin na mitan yadda har yanzu babu wani labari game da janye yajin aiki,bare su samu su amsa Result ma susan madafa.Daga hiran Skull aka koma na auren Murja wacce aka sanyawa ranan aure watanni uku masu zuwa.TAIMIYYAH ce ta dubi Maryam tana dariyan tsokana take faɗin "Mu na gama shan bikin Murja sai kuma naki Besty,ni ba ki gaya min yanzu waye gwanin ba,tunda kin rabu da Sudais."
Harara Maryama ta zuba mata tana faɗin "Ko kuma sai ke ba,wai TAIMIYYAH ba za ki fito da miji mu aurar da ke ba,duk irin samarin da ke tare ki a hanya,ba ki sauraransu kar dai kice har yanzu baki kula kowa?"
"Bana kula su ɗin,kuma ban jin zan ma fara kula sun ba,samarin da ke tare ka a titi dama na arziƙi ne Maryam? Ai duk me son ka ya biyoka gidan ubanka ne ya gabatar da kansa,ke ni fa babu wani maganan aure a lassafina,inba gurgu iri na zan samu ba babu wani Namijin da zai ce yana so na in yarda da shi,ku dai lafiyayyu wanda ba ku da Nakasan da za'a goranta muku don Allah kuyi ku fito da Mazajen mu sha biki."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana dariyan hararan da Maryam ke faman zabga mata,kafin Maryam ɗin ta furta "Okey! Za ki ja da ikon Allah kenan?Don ya jarabceki a hakan shine zaki ce ke ce za ki zaɓi abinda zai dace da ke ba shi zai miki zaɓin abinda yafi dacewa bako?Kina bani mamaki TAIMIYYAH don waɗancan shashashan suna miki gori shine ki ke ganin kowa ma goranta miki zaiyi?To bari ki ji tun wuri ki cire wannan shirmen a ranki,Allah na tuba ke har wani Nakasa ma ki kai,ga guragu nan da ko tafiya ba sa yi sun kuma yi aure sun haihu.Kuma duk acikin wanda na sani kar ki ɗauka guragu suka aura,wallahi lafiyayyun maza suka aura don haka kar ki ja da Allah,ke dai ki bar masa zaɓi shi kaɗai yasan wanda zai zaɓa miki in lokaci yayi,mu dai kawai muyi addu'a Allah yai mana zaɓi mafi alkhairy,Ke ɗin ma da akaiwa baiwan da mu masu ƙafafun qalau ma bamu sama ba,ko a kyawunki da cikar halitta aka tsaya TAIMIYYAH ke ɗin matar manya ce sosai a hakan wallahi,bare azo ɓangaren karatu wannan Brain ɗin naki ba dama ne,wallahi ki godewa Allah."
Maryam ta ƙare maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ke sakin murmushi,kafin TAIMIYYAN ta amsa da"Nagode masa Maryama ina kuma ƙara gode masa,Allah yai mana zaɓi ni bawai ina ja da Allah bane,bazaki gane me nake ji bane araina a duk sanda aka min gori ko aka kirani da kalmar gurguwa,amma bakomi a rufe wannan babin a ɗakko wani kawai."
Yadda tayi maganan cikin wani narke murya,yasa Maryama dubanta wani abu na motsa zuciyanta,tana mamakin yadda TAIMIYYAH ta iya shagwaɓa me motsa zuciyan har mata ƴan uwanta,bare kuma namiji idan tana masa wannan narkewan ai tuni zata gama da shi,ta murmusa tana duban TAIMIYYAN cikin ido take faɗin "Na ji an bari gimbiyar Yah Deeku wai ina kuka kwana ne ko auren Zumuncin za'ai ne?"
Maryama ta tsokani TAIMIYYAH tana sakin dariyan taɓara,sabida sun san da labarin Son da Yah Sadeeq ɗin ke wa TAIMIYYAN,da irin tsanan da su Zuhurah sukai mata,don zuwan Maryam na farko gidan a gaban idonta Zuhura taci fuskan TAIMIYYAH,wani harara TAIMIYYAH ta watsa mata kafin ta sanar da ita duk yadda suka kwashe da shi,da umurnin da Baba Sani yai musu akan fito da miji,ta ƙare maganan tana cewa "Ni kin ga Maryam tunda ba wani nake kulawa ba wallahi nafi so abar ni nayi karatu na."
Maryam ta taɓe baki tana faɗin "Ke dai kika sani idan Allah ya kawo mijin nan kusa sai mu gani ko zaki hana mu sha bikin."
TAIMIYYAH ta saki dariya tana taɓe baki itama take faɗin "Oho dai ni dai barni da karanta littafan Soyayyan muna course,wallahi kuma idan mutum yana karanta littafan sai yayi ta imagining ina ma kaine star ɗin,ko baki jin hakan Tawan?"
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana sakin dariyan shaƙiyanci,hakan yasa Maryam itama sakin dariyan tana faɗin "Munafuka mu je dai zuwa,dama irin ku masu gudun faɗawa tarkon luv ai baku iya kamuwa ba,idan lokaci yazo ni ina matuƙar son in ga wani me sa'an ne zai ɗauke ki."
Itama tayi maganan cike da shaƙiyanci daga haka suka cigaba da hiransu suna baiwa juna nishaɗi,har zuwa lokacin da sukai Lunch,TAIMIYYAH na jin kaman kada Maryam ta tafi,sai da Maryama tayi sallan la'asar sannan tayi shirin tafiya,TAIMIYYAH ta yo mata rakiya bayan Maryam ɗin tayi ma Iya sallama,Iyan har da bada wani haɗaɗɗen turare cikin wanda su Abie ke yawan kawo mata tsaraban su idan yayi tafiya ko yai mata siyayya a manyan wajeje,sosai Maryama tayi godia TAIMIYYAH ta rako ta har bakin gate,suna cigaba da hiran da bai ƙarewa indai an haɗu har a rabu baki bai iya shiru,sallama sukai da Maryam ɗin TAIMIYYAH na bata tabbacin zata je gidan nasu insha Allah,sai dai kawai taji ta kirata tace gata nan,lokacin da Maryam ɗin ta fara takawa don barin layin,sai TAIMIYYAH ta juyo tana takawa don komawa cikin gida,zuciyanta fes da jin daɗin ziyaran da qawar nata ta kawo mata.
________
Tunda suka fito daga gida gabanta ke cigaba da faɗuwa,ta kai dubanta kan A.Maleek ɗin wanda yake gefenta,ya bala'in haɗe face yana faman danna wayansa,sai ta sake manne masa tana me ɗaura kanta bisa kafaɗansa,abinda ya janyo hankalinsa har ya ɗago daga latsa wayan nasa yana sauke manyan idanunsa akanta,yana son jin tausayinta amma yana hana kansa hakan,don yana lura tun safe da ya tabbatar mata zasu je wajen wani Babban likitan mata,take faman kuka amma sai bai nuna damuwansa akan kukan nata ba,ya ɗauke kai a yanzu ɗin ma yana sake mayar da hankalinsa akan Chart da yake da wani manager ɗinsa me kula masa da harkan gidajen gonansa dake Kaduna,Yusuf Driver ɗinsa ne ke tuƙa su shi da Suhailah suna baya,har suka iso gidan Doctor Saiff Suhailah bata da wani nutsuwa,kallo ɗaya zakaiwa face ɗinta kasan a ruɗe take,waya Maleek Ado ya ɗaga ya shiga kiran layin Dr.Saiff ɗin,bugu biyu ya ɗaga Maleek ɗin ya furta "Ga mu daga bakin gate ɗin mun iso."
Ko mintu biyu baiyi da sauke wayan daga kunni ba,megadin gidan ya buɗe musu gate suka danna hancin motan ciki,daga can tsaye suka hangi Doctor Saiff ɗin yana jiran shigowansu,ya nufo motan cikin sauri yana kai hannu ya ƙarisa buɗewa Maleek murfin motan,yana faɗin "Ran Chairman ya daɗe,barka da ƙarisowa Bismillah mu shiga daga ciki."
A.Maleek ya miƙama Dr.Saiff hannu sukai musabaha,dai-dai lokacin da Suhailah ta fito,Dr.Saiff ya dubeta yana faɗin "Ran Madam ya daɗe Bismillah mu je daga ciki." Daga haka yai musu jagora zuwa babban falon gidan nasa,ya ɗaga waya yai kiran matansa me suna Sumayyah ta fito,cikin sakin fuska takewa Suhailah barka da zuwa don ya sanar mata da zuwan su,ta risina kaɗan tana gaida A.Maleek ya amsa a taƙaice lokacin da yake zama cikin kujera,daga haka ta janye Suhailah zuwa ɗaya falon,tana komawa ta haɗo lemu da ruwa ta kawo mata,suka sake gaisawa cikin rashin sabo da sanin juna,shiyasa daga gaisuwan sai shiru ya ratsa,bada jimawa ba sai wayan Sumayyan ya sake ɗaukan kiɗa,ta ɗaga wayan tare da yin shiru kafin ta furta "Okey tuh." Ta sauke wayan tana duban Suhailah da sam bata da walwala ta sanar mata Daktan na jiran ta a falon da suka baro,cikin mutuwan jiki Suhailah ta nufi falon,tana samun kusa da Maleek ɗin ta zauna,tambayoyi Doctor Saiff yai mata ta sanar dashi komi tun daga lokacin da ta fara shan Pills na planing ɗin har zuwa lokacin da ta daina,shekara ɗaya kenan ya tsura mata ido kawai yana jinjina hauka da shirme irin na wasu matan,don shi baisan wani irin wauta ne zai kai mace fara yin planing alhali bata taɓa ko haihuwan fari ba,sai dai laifinta kaɗan ya gani akan na daƙiƙin likitan da ya bata go ahead ɗin fara tafka kuskuren da tayin,ya kai dubansa kan Maleek Ibrahim Ado wanda ya ɗauke kai tamkar baisan me suke tattaunawa ba,sai dai yana sauraran komi da suke yi,takaici da haushin Suhailah kuma na sake kama shi. "Ranka ya daɗe naji duk bayananta sai dai kafin komi dole sai nayi mata wasu gwaje-gwaje,don haka zuwa gobe zata sameni a asibitin ABU Shika,sakamakon result ɗin gwaje-gwajen shi zai bamu daman sanin meke faruwa,amma dai Madam kinyi kuskure sosan gaske."
Doctor Saiff ɗin ya ƙare maganan da maida dubansa kan Suhailah,wacce ita kuma idanunta nakan rabin ranta Maleek,daga haka A.Maleek ya miƙe yana sake miƙawa Daktan hannu,cikin muryansa me cike da ƙasaita yake faɗin "Thank u Dakta,ina ga zamu wuce goben zata sameka a can ɗin,yadda kuka yi kai tsaye ka nemeni kai min bayanin komi."
"An gama ranka ya daɗe,godia nake zaka jini insha Allah " Cewan Doctor Saiff yana rufawa A.Maleek ɗin baya wanda tuni ya nufi ƙofan fita falon,Suhailah ta rufa musu baya itama ba tare da ta tsaya sunyi sallama da matar gidan ba.
Har wajen mota Dr.Saiff yai musu rakiya,shi ne da kansa ya buɗewa A.Maleek murfin motan ya shiga ya mayar ya kulle yana ɗaga musu hannu,lokacin da Yusuf Driver ya ja motar,Suhailah ta ɗaga idonta ta dubi A.Maleek,ya balla mata harara lokacin da take matsowa jikinsa,ta haɗe gaf ɗin da ke tsakaninsu cikin shagwaɓe murya take faɗin "Sweet please mu wuce gidan Hajiya kaina ciwo yake."
Tayi maganan cike da narke masa face,yai mata kallo ɗaya yana ɗauke kai daga gareta ya mayar ya saci duban Yusuf Driver,da ya maida hankalinsa kan tuƙin da yake,sannan ya maido da dubansa kan Suhailah yayi magana cikin wannan dai ƙasaitan nasa "No gida zamu koma i think ina da Visitors za ku shirya abinci na kaman mutum goma."
"What! Baby mutum goma meyasa ba zaka sa ai order kawai daga Restaurant ba?" Suhailah ta jefa masa tambayan tana sake narke fuska,sam bata ji zata iya wannan wahalan duk da cewa akwai Ameena,sannan jiya ma an sake kawo mata wata sabuwar me aikin me suna Salima,yai mata wani kallo da ita kaɗai tasan ma'anansa kafin yayi magana cikin kausasa murya yana faɗin "Ai baki fini sanin da Restaurant ɗin ba,idan bazaki shiga ke da masu aiki ku shirya komi ba,sai na sauke su gidan Hajiya inyi waya ita sai su haɗu da masu aiki suyi komi,tunda ke ba'a isa ace kiyi abu ki amsa kai tsaye baki gardama ba."
Duk wannan maganan yana yinsa ne can ƙasa-ƙasa,babu ta yadda za'ayi Yusuf Driver yaji me yake faɗi illa Suhailan kaɗai da ke raɓe da jikinsa,ta ko zunɓure baki gaba tana kwantar da kanta bisa kafaɗansa,tana faɗin "Allah ya baka haƙury Sweet,abun bai kai Hajia ta ji ba."
Yai mata banza bai kuma sake magana ba har suka isa gidan,ta riga shi fita fuu!...Tana wani irin cika da batsewa,ta cika tayi fam cike da jin haushin yadda sam Maleek ɗin baya son ta da hutu,irin ita yadda take so ya kasance tana daga kwance za'a dinga mata komi,sai dai kawai ta dinga bada umurni,ita sam matan aure masu zagewa suna hana kansu sukuni wajen bautawa miji da ayyuka,a wahalallu take kallon su sai dai duk yadda ta so burinta ya kasance,indai Maleek ɗin na gari to fa duk yadda ta kai ga son hutu sai ta zage tayi hidimansa ko bata so,indai tana son ganin farin cikinsa yadda ya kamata.
Ɗakinsa ya wuce kai tsaye shi ma da ya shigo,yana aje wayoyinsa ya rage kayan jikinsa yana maida ƙananun kaya,zama yayi yana ɗaukan wayansa yai kira,ya daɗe yana magana kafin ya aje wayan yana tashi ya fito ya nufi ɗakin Suhailah,tsaye ya sameta tana cire kayan jikinta,idanunsa ya sauka akan Milk Push-up Bra da ke sanye a jikinta,ya ɗauke kai yana takawa zuwa gare ta,idanunsa cikin nata yake faɗin "Duk wannan cika da batsewan sabida nace muna da baƙi zakiyi aikin tarban su?"
Suhailah ta ɗaga ido tana kallonsa itama,lokacin da ya ƙarisa haɗe gaf ɗin dake tsakaninsu yana kai hannu ya mannata da jikinsa,ta sauke ajiyan zuciya lokacin da hannunsa ya ratsa ta jikinta zuwa bayanta yana ɓalle maɓallin Bra ɗin ya sake shi zuwa ƙasa,murya can ƙasa cikin marairaita Suhailah ke faɗin "Ni fa ba fishi nake ba Baby,kawai dai aikin girke-girken nan ne ban faye so ba."
Memakon yayi magana sai kawai ya ɗauke ta cak! ya aza bisa Bed,yana yin abinda zai fisshesa don a matuƙar matse yake da ita ɗin,cikin disasshiyar murya yake faɗin "Kinyi wanka ne?"
Suhailah da tai luff tana amsan zafafan saƙonninsa ta gyaɗa kai tana faɗin "Yanzu ne zan yi wankan."
Bai iya cewa komi ba ya kai bakinsa kan ƙirjinta yana sake mannata da jikinsa sosai,ya shiga birkita duk wani lissafinta sai daya gama jagulata son ransa kafin ya zare ta daga jikinsa yana faɗin "Oya jeki ki wankan ki je ku fara aikin ayi komi me kyau please,na saka Fahad ayi ordering Snack's daga Apple white zai kawo nan ba da jimawa ba." Daga haka ya juya ya bar ɗakin ba tare da yaji me Suhailan ta faɗi ba......✍🏻
_Salamu alaikum! My luvly fans,kaman yadda na ji ƙorafin ku akan cewa Free Pages da na bayar 1to11 an ce yayi kaɗan,to na duba zan ƙara mu ku yakai zuwa iya 20 Pages for Free daga nan sai ko wacce ta biya ta shiga Payment Group,don jin cikakken labarin da ya zo da Zazzafan salo.Kada ku bari a yi ba bu ku Readers._ 😍
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 14 to15*
________A washegary kaman yadda A.Maleek suka rabu da Doctor Saiff cewa Suhailah zata same sa a Hospital,hakance ta kasance ƙarfe takwas da rabi ta gama shiryawa,cikin wani tsadadden lace Cream Colour da akai masa adon zane da golden ɗin zare,sai touch ɗin Mint Green wanda ya ƙawata kyawun lace ɗin,ya kuma yiwa lafiyayyen fatanta kyau sosai,da ƙyar ta iya tashi daga jikin Maleek tai wannan shirin,don a cike take da fargaban me zai je ya dawo,domin a fuskansa kawai take ganin yadda ya ɗauki lamarin da mugun girma,ɗan kunnaye ta saka ta zuba zabban Gold guda biyu hagu da dama,kyawun da tayi kai kace wani wajen zata ba Asibiti ganin Likita ba,gyale ta ɗauka irin wanda ake yayi na zamani me sharan-sharan da baida maraba da babu,kalan da zai shiga da kayan jikinta ta fesa turarukanta na MISS DIOR haɗe da COROLINA HERRERA,ɗakin ya buɗe da wani irin qamshi me ratsa zuciya,ƙaramin Hand Bag ta ɗauka ta jefa wayoyinta a ciki,ta fito kai tsaye ta nufi ɗakin A.Maleek ɗin wanda ta same sa naɗe cikin Duvet,ta saki wani irin murmushi tana takawa zuwa bakin gadon,tare da ɗosana mazaunanta daga bakin gadon,ta kai hannu ta ɗan janye Duvet ɗin,kyakykyawan fuskansa ya bayyana idanunsa arufe da alamun bacci yake sosai,hannu takai tana shafa fuskan a hankali tare da manna masa kiss a saman goshi, ya buɗe idanunsa daddaɗan qamshinta na gama cika hancinsa,ya sauke ganinsa akan fuskanta da taiwa kwalliya matsakaici,sai dai lips ɗinnan sun sha janbaki raɗau me asalin tsada,sai ƙyalli lips ɗin suke yakai hannu zuwa kan lips ɗin ya shafa,yana me yinƙurawa ya tashi zaune sosai,manyan idanunsa zube akanta babu ko ƙiftawa,cikin wani irin murya na wanda ya taso a bacci yake faɗin "Suhailah biki zaki ko suna ki kai irin wannan kwalliyan?Sannan sabida kin raina ni kuma shine zaki fita da wannan abun abakin ki,sau nawa zan sanar da ke bana so,wai ke bakya kishina ne bare guje ma ɓacin raina? Look at dis Veil da kika sanyo sai kace wata budurwa me tallan kanta,oya tun raina bai gama ɓaci ba kije ki goge wannan abin da ke bakinki,ki kuma sanyo Hijab ko Abaya akan wannan shigan okey!"
Yadda yai maganan kawai da yadda idanunsa ke jifanta da wani kallo,yasa ta fahimci ransa ya gama ɓaci,ta marairaice fuska tana shirin buɗe baki tai magana,ya ɗaga mata hannu cikin kaushin muryansa me zurfi da ke fita a ƙasaice tamkar basarake yake faɗin "Bana son jin komi getout please!" Hakan yasa Suhailah cuskule fuska tana barin ɗakin ranta a ɓace,kaman yadda ya buƙata haka tayi lokacin da ta koma ɗakin yana Toilet,tana shirin fita yana fitowa ya bita da kallo yana kallon inda tsayin Hijab ɗin da ta sanya ya tsaya,da kaɗan ya wuce cinyoyinta ya ɗauke kai yana takowa cikin ɗakin,murya a dake yake faɗin "Yusuf na jiranki a waje,kafin ku wuce ki sanar da masu aiki a shirya abin Breakfast a babban dining dake down stairs ina da baƙi da zamu karya tare,sannan a ƙara yawan lunch daga nan har zuwa jibi sabida zamuyi ta samun baƙi ƴan taya murna."
Subailah ta dube sa tana wani ɗan turo baki,cike da takaicin yadda ake so lallai a maidata Busy a gidanta,sabida yawan baƙi ƴan taya Maleek murnan muƙamin da aka bashi na Chairman na Shiffing Board na ƙasa baki ɗaya,shi yasa yake ta samun baƙi ƴan taya murna kama daga