Showing 126001 words to 129000 words out of 186776 words

Chapter 43 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6629

ma me zance ba."


TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Haka nake so dama." Daga haka ta ɗakko wani zancen na daban suka ɗaura, duk yadda Yasmeen ta so TAIMIYYAH ta bata haɗin kai su tinkari Basmah da magana akan aurenta da Nass da za a ƙulla,TAIMIYYAH taƙi ba Yasmeen ɗin haɗin kai,ta kuma roƙeta akan cewa don girman Allah ko a fuska bata son Basmah ta ga canji daga Yasmeen ɗin.


Washegary ƙarfe bakwai da rabi na safe TAIMIYYAH suka fita xuwa makarantar Haddar tasu.Su Basmah ne dai da ba za a samu yaye su a wannan shekarar ba sabida sun sanya wasa,basu fita gidan zuwa makarantar ba sai takwas da rabi.


Kafatanin ƴan gidan tun daga kan Iyah har zuwa su Babah Ladi duk sun halarci wajen bikin yayen Mahaddatan.
Daga Ummie sai Umma da tace babu inda zata su kaɗai aka bari a gidan.Amma hatta Yah Sadeeq daya shigo weekend don kawai ya halarci taron,duk sun je tare da wasu daga cikin ƴan Rimi can Fam house ɗin su TAIMIYYAH,duk sun sama halartan taron.


Ƙarfe sha biyu na rana aka fara watsewa daga wajen taron, ɗalibai masu hazaƙa da suka fi sauran ƴan uwansu Mahaddata ƙwazo sun kwashi uban kyatuttuka daga manyan baƙi mahalarta taron.


Cikin wanda suka samu manyan kyautuka TAIMIYYAH na sahun farko,don ta amsa manyan kyautuka tun daga kan kuɗaɗe da suturu haɗi Qur'anai. Yah Sadeeq shine ya isa wajen bada kyaututtukan ya taya TAIMIYYAH amsa,zuciyarsa cike da tarin farin cikin da bazai misaltuba.


Iyah ta kai bakin Hijab ɗinta ta goge hawayen farin cik lokacin da ta ga yadda ake baiwa TAIMIYYAH kyatuka,tare da kwarzanta kwazonta na zamowarta cikin ɗalibar da ta fi sauran ƴan uwanta ƙarfin hadda,tare da fitar da Tajweed a cikin ƙira'arta.


TAIMIYYAH sun dawo gida jikinta a matuƙar sanyaye yake,duk wannan tarin ƙaunar da aka nuna mata,duk irin kara da bajintar da su Baba Sani suka nuna mata na son ganin sun faranta zuciyarta,ji take yi akwai sauran wani gurbi me girman gaske da suka kasa cike mata shi. Ba kuma kowane irin gurbi bane sai na kewan Abie da take ji me girma a wannan rana.


Zuciyarta cike take da farin ciki da bazai misaltu ba sabida wannan ranar yana ɗaya daga cikin ranakun da ba za ta iya daina alfahari da su cikin rayuwarta na duniya ba. Amma tun daga sanda ta ga Iyayen ƴan uwanta Mahaddata na cike da tarin farin ciki, taji cewa sun yi mata wani fami me tsanani a cikin zuciyarta.
Kewan Abie me tsanani ya taso ya danne dukkanin tarin farin cikin da take ji a wannan rana,hakan ya haifar mata da mutuwar jiki da wani irin rauni a zuciya har suka iso gida.


Ta nufi ɗakinta tana shigewa toilet ta rufo,ta jingin da bangon bayin hawaye na zubowa daga idanunta masu tsananin zafi.
Muryar Abie ɗinta take son ji kamar tayi hauka,amma ta san babu halin hakan don ya riga yayi mata nisan da ba za ta tadda shi ba sai a kiyama.
Ta sulale daga tsaye ta tsugumna tana kuka sosai,har sai da ta gaji ta rarrashi kanta ta share hawayen, tare da gabatar da uzurinta ta ɗauro alwalar sallar azuhur ta fito.


Da Idanun su Maryam Sunusi da Zee ta fara cin karo, wanɗanda suka iso kusan a tare da juna.
TAIMIYYAH sai ta saki murmushi tana takowa zuwa cikin ɗakin take cewa, "Welcome my friends ashe dai da gaske zaku samu zuwa ɗin."


Maryama ta dubi TAIMIYYAH wacce kallo ɗaya za kaiwa face ɗinta kasan ta sha kuka ta furta, "Haba Besty me zai hanani zuwa ni kam,inba wani babbar uzuri ne ya taso min ba,me kuma ya sanyaki kuka idanu suka kumbura haka?"


TAIMIYYAH ta sake narke fuska tana baiwa Maryama amsa da cewa, "Maryam na tuna Abie ne kawai ina hasashen da yana raye wani irin farin ciki zai yi shi ma? Shiyasa na kasa daurewa sai da nayi kukan na samu sauƙin ciwan da zuciyata ke min,sai yanzu ne nake gane cewa shi mutuwar iyaye wata babbar jinyace da ba a warkewa sai dai aji sauƙi,Allah ya ƙara mana juriya da haƙury kawai,su kuma Allah yasa suna Jannatul Firdaus."


Zee da Maryama suka haɗa baki wajen amsawa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum." Zee ta ɗaura da faɗin,


"Sai haƙuri TAIMIYYAH amma tabbas rashin iyaye na da zafi duk da mu bamu san pain ɗin ba,Mama tace tana gaisheki kuma tana taya ki murna, ga saƙonan ma tace akawo miki babu yawa."


Zee ta kai ƙarshen maganar tana nunawa TAIMIYYAH ledar da ta aje akan gado.
TAIMIYYAH ta iso bakin gadon ta zauna kusa da Maryama tana cewa, "Allah sarki na gode ƙwarai,dama ba tayi ɗawainiyar kawo komi ba Zee haba." Tayi maganar hannunta na buɗe ledar,manyan idanunta suka sauka akan kyakykyawar atamfar da ke ciki.Ta dubi Zee da sauri tana faɗin, "Kai Zee wannan ɗawainiya ai yayi yawa,an gode Allah saka ya bar zumunci."


Zee ta amsa da cewa, "Ameen qawata ni ma kuma ga nawa babu yawa." Zee tayi maganar tana ciro wani ƙaramin kwali da akai raping wasu kyawawan Mug guda huɗu,an rubuta sunan TAIMIYYAH a ciki ana wishing ɗinta Happy Qur'anic Graduation.


Wani irin farin ciki ne ya tsarga a zuciyar TAIMIYYAH sabida sun mata kyau Mugs ɗin,kuma kana gani zaka san cewa wanda yayi aikin ƙwararrene.
Ta dubi Zee da tarin farin ciki akan fuskarta tana dinga zuba mata godia,Maryama itama tana taya ta godian kafin ita ma ta ciro envilop daga cikin jaka ta ajewa TAIMIYYAH a jiki tana cewa, "Ga namu gift ɗinnan babu yawa,ki sai duk abinda kike so inji Mummy. Ni kuma ga wasu fashion nan kya yi kwalliya,Allah ya sanya albarka yasa anyi na tsoran Allah ne Besty."


Maryama ta ƙare maganr tana ajewa TAIMIYYAH fashions ɗin da ke cikin box ɗinsu.TAIMIYYAH sai taji gaba ɗaya har ta rasa bakin magana, sabida irin yadda qawayen nata ke faman nuna mata ƙauna,ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Maryam tana mata godia har hawaye na cika idanunta.
Daga haka ta tashi ta gabatar da sallah,ita ma Zee sallar ta gabatar kasancewar da alwalarta ta iso gidan.
Maryam da ke off ne tayi kwance abinta tana danna wayarta, har zuwa lokacin da Yasmeen ta shigo ɗakin dai-dai da idarwar TAIMIYYAH daga sallah.
Ta waiwaya ta dubi Yasmeen da ke gaisawa da Maryam tana cewa, "Yasmeen tunda muka dawo kika ɓace a gidannan ina kuma kika kurɗa?"


Yasmeen ta saki dariya tana duban TAIMIYYAH take cewa, "Ina can sasan Ummie tana nuna min kayan snacks da ta saka a aiko ta tasha tun daga Kaduna,ba kiji yadda cupcakes ɗin su kai daɗi ba wallahi,an gode da ƙauna ƙwarai babu abinda zaki ce sai godia,domin an nuna miki ƙauna da kara me tarin yawa."


TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Gaskiya an nuna min ƙauna Allah kuma ya fini yabawa,kin ga abubuwan arziƙin da su Zee ma suka kawo min gasu nan akan gado,ki ɗauka ki kaiwa Iyah ta gani kafin in fito yanzu,sai akawo musu abinci please Yasmeen."


Yasmeen ta taya TAIMIYYAH godia tana kwasan kayan da kuɗin, wanda basu ma buɗe sun ga ko nawa bane ta nufi ɗakin Iyah.
Daga Iyah sai Mamienta ne a ɗakin, Yasmeen ta zube kayan bisa bed ɗin Iyah,tana sanar mata wanɗanda suka kawo wa TAIMIYYAH.


Iyah da Guggo Bilki suka duba tare da sanya albarka,Yasmeen ta bar kayan anan ɗakin Iyah,ta wuce zuwa kitchen don kawai su Maryam abinci da lemu,haɗe da snacks ɗin da akayi don rabawa mutane.


Misalin ƙarfe biyu kira ya shigo wayar TAIMIYYAH, ganin lambar Hajiya Aysha da tayi saving da suna Hajiyar GG (Hajiyar Gonar Ganye) yasa ta ɗaga wayar ta kai kunni.


Maganan seconds tayi ta sauke wayar daga kunni, ta dubi Yasmeen da suke ta hira dasu Zee tace, "Yasmeen wannan Hajiyar da nake baki labari wacce suka kaɗeni kwanaki,itace suka ƙariso bakin layin shigowa nan,don Allah tashi ki rakani mu taho dasu,Allah sa dai kan layin shigowa nan ɗin suka tsaya kamar yadda na basu address."


Yasmeen sai ta tashi tana zura Hijab akan kayan jikinta,ko wanka basu yi ba sai zuwa la'asar, sabida ƙarfe huɗu akace za a fara gabatar da walimar.


Cikin sa a suna isa bakin layin TAIMIYYAH ta hango ƙatuwar motar da ta faka daga gefen hanya.Ta nunawa Yasmeen motar tana cewa, "Yasmeen ga motarsu can mu ƙarisa."


Suka ƙarisa wajen motar lokacin da Shehu driver ya zuge glass ɗin ɓangarensa, yana wa TAIMIYYAH magana akan cewa su shiga cikin motar kawai su ƙarisa.


Suka buɗe back seat inda Hajiya Aysha ke kame a ciki,TAIMIYYAH fuskarta ɗauke da murmushi take gaida Hajiya Aysha.Yasmeen ma ta gaisheta ta amsa cike da fara'a idanunta akan TAIMIYYAH dake kusa da ita take faɗin, "Daughter kice gidan naku ma babu wuyar ganewa,sannu da ƙoƙari an taso ki ai da kin turo wani yazo ya taho damu kawai."


TAIMIYYAH ita dai sai faman blushing take yi har suka isa bakin gate ɗin gidan.
Yasmeen ce ta cewa Shehu ya tsaida motar sun ƙariso.
Ya tsaida motar duk suka yo waje har Hajiya Ayshan,wacce tace wa Shehu ya wuce da motar zuwa ƙarfe biyar sai ya dawo ya ɗauke ta.


Suka rankaya zuwa cikin gidan nasu TAIMIYYAH, Hajiya Aysha nata faman bin ko'ina da kallo,tana yaba tsarin ginin da ganin kyawunsa.Sabida gini ne standard irin na da me inganci,wanda kuma yake samun kula da gyara akai-akai.
Ta cigaba da bin ƙaton compound ɗin da kallo, wanda ake ta faman arranging fararen kujerun da mutane za su zauna akai.
Tana biye da bayan su TAIMIYYAH har zuwa ɓangaren Iyah, Yasmeen ce ta amshi jakar hannun Hajiyar ta riƙe mata sabida nuna girmamawa.


Lokacin da suka dangana zuwa cikin falon Iyah,da tsananin murna ta ƙariso ta tarbi Hajiyar suka ƙarisa cikin falon.
Iyah da farin cikinta ya kasa ɓoyuwa ta dinga jin ƙaunar Hajiyar da ganin ƙimarta, tare da yaba karamci da ƙaunar da take nunawa akan TAIMIYYAH.


Su TAIMIYYAH bayan sun sake gaida Hajiyar sai suka shige zuwa ciki,suka barta da Iyah da Guggo Bilki wacce itama ta fito tana wa Hajiyar barka da isowa.
Kanka ce kwabo an cika gaban Hajiya Aysha da kayan cima kala-kala, cikin abubuwan da aka shirya don ciyar da mutanen da za a tara.


Iyah ta zauna suka fara hira kai kace sun shekara da sanin juna ne,sabida daga ita har Hajiyar ma'abota son jama'a ne da faran-faran dasu.
Suna nan zaune suna hira baƙi suka fara zuwa ƴan Rimi da jama'an gari,tare da abokanan arziƙi da Iyah ta gayyata,ganin hakan yasa Iyah janye Hajiya Aysha zuwa ɗakin baccinta tace tayi zamanta anan.


"Bilkisu je ki Sasan Sani kice Zuwairah da yaranta su zo,idan kin fito daga nan kije itama Ummie kice ta zo duk su gaisa da Hajiya Aisha."


Iyah ce ke maganar tana tsaye daga cikin kitchen ita da Guggo Bilki.Guggo Bilki ta duba Iyah tana cewa, "To Iyah bari in je in kira su,na ga alama wannan Hajiya ta shiga ranki kamar yadda itama na ga alamun tana ji da ku daga ke har TAIMIYYAH, gaskiya na jima ban ga mace me mutunci irin ta ba, shiyasa ake cewa bawa ya dinga addu'a akan Allah ya haɗasa da masoyansa,sai ki ga sanadi kaɗan ya haɗaka da mutanen arziƙi masu son ka da zuciya ɗaya."


Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Bari kawai Bilki wallahi matar ta san darajar mutane akwai mutunci matuƙa."


Guggo Bilki ta je ta isar da saƙon Iyah wajen su Ummie da Umma.Ummie dama ta gama shiryawa cikin baƙar Abaya da ya amshi jikinta yayi mata kyau matuƙa,tana shirin fita zuwa sasan Iyah ne Guggo Bilkin ta shigo,sai kawai suka rankaya tare suka fito zuwa sasan Iyan bayan Ummie ta yafa mayafi a jikinta.


Gaggaisawa da mutanen dake zaune cikin falon Ummie tayi, waɗanda rabi duk ƴan Rimi ne can FAM house ɗin su Abie,sai ta wuce zuwa ɗakin Iyah don ta miƙa gaisuwa wajen baƙuwar Iyah, kamar yadda Guggo Bilki ta sanar mata.


Iyah na zaune daga bakin gado sai hira Hajiya Aysha ke mata, tana bata labarin mijinta da aka kashe a garin Lagos,shekaru goma sha shida baya.Ummie tayi sallama ta shigo,hakan ya katse hiran na su Iyah ta amsa sallamar Ummie ɗin tare da bata izinin shigowa,ta samu waje daga ƙasan carfet ta zauna tana gaida Iyah,kafin ta juya tana gaida Hajiya Aysha wacce idanunta ke kan Ummien.


Iyah ta dubi Hajiyar tana nuna Ummie da hannu take faɗin, "Wannan itace matar ɗan nawa daya rasu mahaifin TAIMIYYAH,yaransu biyu mata a tsakani,kuma duk ajalin ya sauka musu rana ɗaya watanni biyu kenan."


Hajiya Aysha ta jinjina kai cike da nuna jimami take cewa, "Allah sarki,Allah ya gafarta musu yasa suna kyakykyawar matsayi, tabbas an muku rashi me ciwo sannu kinji,Allah ya ƙara miki dangana."


Ummie da kanta ke ƙasa ta amsa da cewa, "Ameen." Tana miƙewa tace wa Iyah bari ta duba su TAIMIYYAH a ɗakinsu.
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "To badamuwa."


Ummie ta tashi zata fita daga ɗakin sai Hajiya Aysha tayi saurin cewa, "Don Allah ki ce da Zainab ɗin idan sun gama shirin ta zo ina son ganinta."


Ummie ta amsa tana ficewa daga ɗakin Iyah,ta bar Iyah suna cigaba da magana da Hajiyan, Iyah na sake bata labarin rasuwan ɗan nata Sameer.


Lokacin da Ummie ta shiga cikin ɗakin su TAIMIYYAH ta samu Yasmeen da TAIMIYYAH na shiryawa.Duk suka gaida Ummie ɗin TAIMIYYAH na cewa, "Ummie yanzu nake cewa Yasmeen zan je in miki godia,mun ga abin arziƙi na gode Allah saka da alkhairy."


Ummie ta zubawa TAIMIYYAH idanu tana kallon tsantsar kyawun da tayi cikin rantsatstsiyar Abayar data sanya kalar Dark Coffee,wanda akaiwa ado a wuya da hannu zuwa ƙasar rigar da kalar zare golden.
Tayi matuƙar yin kyau cikin Abayar yadda baki bazai misalta ba.Yasmeen ce ta siya musu iri ɗaya sak don su yi anko da TAIMIYYAR,bambamcin kala ne kawai ya raba, amma komi iri ɗaya ne shiyasa TAIMIYYAH ta aje wanda ta siya ta saka wannan ɗin, don yama fi wanda ta siya tsada tunda Abban Yasmeen ɗin ne ya bata kuɗi masu nauyi ta siya musu a Algazaru.


Ummie ta dafa kafaɗun TAIMIYYAH tana cewa, "Daughter ki daina min godia ina jin wani iri a raina,sai in dinga ji tamkar baki ɗauke ni matsayin uwa ba,bayan yanzu duk duniya ke kaɗai nake ma kallon ƴa ina jin sanyi cikin zuciyata,kinyi kyau matuƙa Zainab Allah ya kawo mijin aure na gari.Baƙuwar Iyah tace a sanar miki idan kin gama kintsawa ki sameta a ɗakin baccin Iyah,ni zan koma sai anfara walimar zan sake fitowa,Allah yayi miki albarka ya jiƙan su Abie."


TAIMIYYAH da Yasmeen har ma dasu Maryama dake zaune cikin ɗakin suka amsa da cewa, "Ameen." TAIMIYYAH na jin wani irin kewan Abie ɗin na danne zuciyarta,Ummie ma cikin sauri ta bar ɗakin zuciyarta na motsawa da tarin kewa me tsanani na Sameer ɗin da yaranta su Raudha.


TAIMIYYAH ta ƙarisa shiryawa duk jikinta a sanyaye,su Maryama sai bin ta da kallo suke yi suna yaba kyawun da TAIMIYYAH tayi.Zee ta kasa daurewa sai da ta tanka tana cewa, "Kai Namcy wannan irin kyau haka,gaskiya ban taɓa ganin shigar da ke ɗaukar jikinki irin shigar Abaya ba,tana yi miki kyau matuƙa da gaske,duk wanda zai aureki zan bashi shawara ya zubo mana su da yawa cikin lefe."


TAIMIYYAH ta saki murmushi me faɗi tana faɗin, "Zee baki da dama wallahi."


Daga haka ta gama sanya ɗankunni tana fesa turarenta na GIORGIO PINK bayan body mist ɗin data sanya daga ciki.Ɗakin ya buɗe da daddaɗan ƙamshi me kwantar da zuciya.


Lokacin da ta isa zuwa ɗakin Iyah, Hajiya Aysha ta samu zaune ita kaɗai,don Iyah na can na fama da mutanen da suka fara taruwa.


TAIMIYYAH ta shiga cikin ɗakin tana tana takawa dafe da guiwar ƙafarta cikin nutsuwa.Idanun Hajiya Aysha fes akanta tunda ta shigo har ta ƙariso bakin gadon Iyah ta zube daga ƙasa tana cewa, "Sannu Hajiya,Ummie tace kina nema na."


Hajiya Aysha ta miƙa mata hannunta tana cewa, "Taho ki zauna nan kusa dani ƴata,tubarkallah Masha Allah! Kin yi kyau sosai kamar na saceki na gudu da ke zuwa gidana Zainab."


Yadda Hajiya Aysha tayi maganar cike da nuna kulawa yasa TAIMIYYAH sakin murmushi,tana tashi ta zauna daga bakin gadon,hannunta cikin na Hajiya Aysha da ta riƙe.


Hajiya Aysha ta saki hannun TAIMIYYAH tana janyo jakarta ta buɗe,ta ciro kuɗi rafar ƴan ɗari biyu sabbi kar ta aje ajikin TAIMIYYAH,tare da ɗaurawa da wani ƙaramin box a saman kuɗin tana cewa, " Ƴata gashinan babu yawa,wannan box ɗin ɗankunni ne a ciki ki cire wannan ki sanya in gani, kuɗin kuma ki sayi wani abu tunda kinƙi sanar dani abinda kike so"


TAIMIYYAH baki buɗe take kallon kuɗin tama kasa magana,don bata san me xata cewa wannan mata da tun haɗuwansu take ta nuna mata ƙauna ta zihiri ba.Ta dubi Hajiyan karon farko cikin ido kafin ta ɗauke ganinta ta mayar kan box ɗin tana cewa, "Mama na gode Allah ƙara girma da arziƙi,nama rasa wani irin godia zan yi Allah ya saka da alkhairy." Ta buɗe box ɗin tana ciro madaidaicin ɗankunnin gwal dake faman sheƙi,ta ciro na kunninta ta sanya na gwal ɗin kamar yadda Hajiyar ta buƙata.


Take fuskarta ya sake haskawa da wani irin kyawu mara misaltuwa,Hajiya Aysha ta murmusa tana sake jin ƙaunar TAIMIYYAH na ratsa jinin jikinta.Ta buɗe baki tace, "Masha Allah Zainab Kin yi kyau tubarkallah! Allah ya kawo miki nagartaccen miji me tsoran Allah."


TAIMIYYAH tayi ƙasa da kanta tana amsawa da "Ameen." cikin zuciyarta dai-dai lokacin kuma Iyah ta shigo cikin ɗakin,ta tadda wannan abin arziƙi da Hajiya Aysha ta baiwa TAIMIYYAH,tayi godia me tarin yawa tare da addu'an fatar alkhairy wa Hajiya Ayshan.


TAIMIYYAH sai ta baiwa Iyah kuɗin ta ajiye,ita kuma fito don koma zuwa ɗakinta,ta nunawa su Yasmeen abin arziƙin da Hajiyan ta kawo mata........✍🏻














#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login