Showing 66001 words to 69000 words out of 186776 words

Chapter 23 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6630

ka ɗauki rai n....."


Rufe bakinta da Yasmeen tayi ya hanata ƙarisa kalamanta.Yasmeen ta fara magana cikin rawar murya ta ke faɗin "Subhanallah! TAIMIYYAH kar kiyi saɓo please! Mu ma ba jinkiri muka yi ba,za mu tadda su idan lokacin mu yayi,addu'anki kawai su ke buƙata a yanzu ba waɗannan surutan da kuka ba,don Allah kiyi tawakkali tamkar yadda Iyah tayi ita ma."


Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana kasa controling hawayen da ke zubo mata,sai lokacin Anty Laurat da ke share hawayen tausayin TAIMIYYAH,ta iso bakin gadon tana faɗin "Kiyi haƙury TAIMIYYAH ko wani mai rai da kika gani dole zai mutu watan watarana,Allah ya baki haƙury da dangana su kuma Abiee Allah ya haskaka makwancinsu,yasa suna kyakykyawan matsayi." Anty Laurat ta ƙare maganan cikin rawar murya,kafin ta juya ta fice daga ɗakin don zuwa kiran Likita,wanda yace da zaran TAIMIYYAN ta farko a kira shi.


TAIMIYYAH ta kifa kanta a jikin Yasmeen tana kuka me motsa Zuciya.Ji take yi a lokacin ina ma Allah zai ɗauki ranta ita ma tabi su Abie ɗin,wani abu me tsananin nauyi ne ya danne Zuciyanrta,kukan da take yi hawaye na zuba shine kaɗai ke rage mata ɗacin da take ji a maƙoshinta.


Lokacin da Likitan ya shigo ma ƙin tashi tayi daga jikinYasmeen,sai da ƙyar da rarrashi sannan ta tashi zaune,yai abinda zai yi ya fice yana cewa Anty Laurat ta bishi office.


Fitansu ya yi dai-dai da shigowan Yah Sadeeq,tare da Yaseer wani Cousine ɗin su TAIMIYYAN.Dukkaninsu idanunsu ya yi jajir sabida kukan da kowannan su ya sha,don mutuwan su Abiee mutuwa ne da ya girgiza ahalin su baki ɗaya.Babu wanda zaka kalli fuskansa ba ka ga alamun kuka ba,bare Sadeeq ɗin da ke jin Abie a cikin Zuciyansa tamkar shi ne Baba Sani,don Abie yayi masa dukkanin gata a rayuwa.


A hankali ya taka zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kai,ta haɗe kanta da guiwa tana cigaba da rasgar kuka.Qamshin turaren BENTLEY data shaqa yasa ta saurin ɗago kai ta sauke manyan idanunta,da zuwa yanzu suka qanqance sukai jajir sabida kukan data kasa dainawa.


Ya zauna daga bakin gadon idanunsa na kanta,Zuciyansa na wani irin matsanancin suya.Tausayin TAIMIYYAH na zama marainiyan da ba Uwa ba Uba na sake danne Zuciyarsa,ya kai hannu ya riƙo na TAIMIYYAH idanunsa na sake rinewa.Cikin wani irin murya da bai fita sosai ya fara rarrashinta,amma memakon tai shiru kaman yadda yake fata,sai kawai ta faɗa jikinsa da dukkanin sauran kuzarin da ya rage mata,ta saki wani sabon kukan me tsuma Zuciya da raunata Zuciyan duk wani me saurarenta.


Yah Sadeeq bai yi ƙasa a guiwa ba wajen rungumarta da kyau,yana ji tamkar ya tsaga ƙirjinsa ya sanya ta ciki.TAIMIYYAH cikin muryan kukan take faɗin "Yah Deeku su Abie sun tafi sun bar ni ko? Shikenan ni yanzu bani da Uwa bani da Uba,bani da qannin da zan kalla inji daɗi,meyasa mutuwa ba ta ɗauke ni ta bar su Nahar ba.....?" Kuka ne ya ci ƙarfinta har ta kasa cigaba da maganan,Sadeeq da ke shafa bayanta hawaye na sauka daga idanuwansa,kamar yadda kaf su Yasmeen, dake cikin ɗakin su ma kukan su ke taya TAIMIYYAH.
Hatta da Yaseer juya baya yayi yana rufe idanunsa da hanki,yana kukan wannan zazzafan rashi da ya riske su a yau.Yah Sadeeq ya buɗe baki cikin rawar murya ya ke faɗin "Baby kiyi haƙury,su Abie addu'a su ke buƙata daga gareki da mu baki ɗaya,kowa da kike gani zai mutu ya tarar da su,kiyi haƙury kiyi haƙury Zaynab....!!!" Daga haka ya kasa cigaba da faɗin komi,sabida idan ya cigaba da forcing kansa sai ya rarrasheta da baki,to tabbas shi ma kukan zai fashe da shi.Sai ya cigaba da rungumarta a jikinsa yana shafa bayanta,ita kuma TAIMIYYAH ta cigaba da sauke ajiyan Zuciya,ƙirjinta na sake yin nauyi tamkar an danne shi da dutse,


"Ina Iyah Yah Deeku?"


TAIMIYYAH tayi tambayar cikin disasheshshen murya.Yah Sadeeq ya yi ƙasa da kansa wajen kunninta yana faɗin "Iyah tana gida tana fama da masu ta'aziyyah,amma hankalinta na kanki Zaynab,kiyi haƙury Allah ya bamu dangana mu da ke baki ɗaya." Ya ƙare maganan yana son ɗago fuskanta daga jikinsa,amma TAIMIYYAH sai ta sake shigar da kanta ƙirjinsa,tare da sake jefa masa tambayan ina Ummie ta ke ita ma? Yah Deeku ya sake ƙasa murya yana sanar mata da cewa Ummie tana Kaduna anyi admitting ɗinta a wani asibiti,tun bayan da aka sanar da ita mutuwan su Abie ta faɗi bata san inda kanta ya ke ba har kawo yanzu.


TAIMIYYAH na jin hakan sai ta sake fashewa da wani sabon kukan,da ƙyar aka samu tayi shiru kuma har lokacin tana jikin Yah Sadeeq ɗin, wanda yake jin wani irin tausayinta na narkar da zuciyarsa.


Likita ne ya sake shigowa ya gwada BP ɗinta,cikin sa'a jininta kaɗan ne ya hau bai yi hawan da zai zama illa a gareta ba.Yai ma TAIMIYYAH wasu ƴan tambayoyi amma sam bata ba shi amsan ko ɗaya ba,sai ya rubuta magungunan da za a siya wanda zata yi amfani da su,yana sanar da su cewa za su iya tafiya gida,tunda babu wani matsala sai na damuwan da take ciki.Ɗumin jikin ma da Yah Sadeeq yai complain,sai likita yace masa kukan da take yi ne ya kawo ɗumin jikin,da zaran an samu ta ci wani abu ta sha magunguna ɗumin jikin ma zai tafi.


Yah Sadeeq ya amshi takardan Magungunan da aka rubuta,ya fita zuwa Pharmacy ɗin cikin asibitin ya siyo,lokacin da ya fito daga ɗakin sai da Magungunan, ya samu har su Yasmeen sun fito.Anty Laurat ce ke riƙe da hannun TAIMIYYAH har zuwa wajen mota,suka buɗe back seat ta shiga ciki suma suka shiga ita da Yasmeen,Yaseer kuma ya shiga front seat.Yah Sadeeq da xai yi driving ya shiga mazaunin driver,bayan ya miƙawa Yasmeen ledan Magungunan,yana jaddada mata cewa lallai suna isa gida,ta tabbatar TAIMIYYAH ta ci wani abu an bata magungunan.


Lokacin da su TAIMIYYAH suka iso gida.Yasmeen ce ta riƙe hannunta har suka isa Sasan Iya,ita Anty Laurat Sashin su Umma ta nufa,domin dare ya fara yi don tara har ta wuce.


Da sallama suka isa cikin falon Iyah,wanda yake ɗauke da ƴan uwanta na kusa da suka zo.Sai wasu daga cikin ƴan Rimi da za su kwana nan,gaba ɗaya sai idon kowa ya dawo kan TAIMIYYAH da suna sanyo kai falon Iyah,ta ga mutane ta fashe da kuka.


Iyah ta taso da sauri ta iso gaban su TAIMIYYAN tana kama hannunta,suka nufi ɗakinta kai tsaye wani abu me tauri na sake danne zuciyar Iyah.Wacce tunda aka zo da gawan su Abie ɗin,har zuwa sanda akai musu sutura ba a ga ɗigon hawaye a idanunta ba.
Zuciyanta yayi wani irin dakewa sai kukan zuci kawai take iya yi,wanda yafi na fiki ciwo.A yanzu ɗin ma so take yi taji koda kaɗan ne hawaye sun zubo daga idanunta,kaman yadda TAIMIYYAH ke iya kuka da hawaye,ta zaunar da TAIMIYYAH daga bakin gadon ta,tana zama itama kusa da ita sosai hannunta har lokacin riƙe dana TAIMIYYAN.Cikin murya me cike da nuna tausayi da rarrashi take faɗin,


"Zainabu kiyi haƙury,sannan kiyi tawakkali ki ɗauki dangana.Sameer sun riga sun tafi inda ba za su dawo ba,kuka da nuna damuwa bazai sa su dawo garemu ba,addu'a kawai shine abu mafi soyuwa da suke da buƙata daga garemu,musamman ke da kike matsayin ɗiyarsa da ya bari a doran duniya.Don haka kiyi haƙury ki ɗauki dangana duka muma lokaci muke jira Zainab,tabbas mun yi rashin da har abada ba zamu maida tamka ba,yau mun sake zama marayu na sosai da ba Uwa ba Uba,amma hakan ba shi ke nuna cewa rayuwa ba za ta cigaba ba....."
Iyah ta ɗan numfasa tana jin shashsheƙan kukan da TAIMIYYAH keyi,wacce maganganun Iyan ke sake karya zuciyarta,da sake tabbatar mata da cewa da gaske su Abie da su Nahar sun barta bari na har abada.Iyah ta cigaba da cewa "Ina miki Nasiha da ki ɗauki dangana, kada ki saka damuwan da zai janyo miki wata illa da ƙarancin shekarunki,kaman yadda kika rayu babu Uwa sai ni haka yanzu ma zaki cigaba da rayuwa babu Sameer da ƴan uwanki,haka Allah ya tsaro cikin littafin ƙaddararki Zainab,mu bamu isa canza komi ba nima haka nake rayuwa babu Uwa da Uba duk sun rasu,kuma haka rayuwa ta cigaba min cikin godian Ubangiji da kaɗaitarwar sa.Don haka haƙury da tawakkali tare da rungumar ƙaddara shine cikar imanin mumini Zainab,mu yi haƙury ina fata Allah ya bamu ikon juriya da haƙuryn wannan rashi,ya ba Ummien ku dangana da ƙarfin Zuciyan jure wannan rashi." Iyah ta kai ƙarshen maganan,wani irin ƙullutu na sake tokare maƙoshinta.


TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin buɗe baki tana faɗin "Ameen Iyah,Allah ya jiƙan Abiee dasu Raudha har da Mamana,Allah yasa suna aljanna...."


Kukan da ya sake ƙwace mata ne ya hanata cigaba da maganan.Ta kwantar da kanta a jikin Iyah tana yin kukan sosai,a haka Yasmeen ta shigo ta samesu hannunta riƙe da Cup ɗin data haɗowa TAIMIYYAH Tea yana turiri.Ta aje Cup ɗin daga bakin side drawer tana faɗin "Iyah har yanzu dai kukan take yi? TAIMIYYAH don Allah kiyi haƙury kiyi shiru kukan yayi yawa.Addu'a ya kamata ace kina musu ba wannan kukan ba,muma kina sake tayar mana da hankaline da wannan kukan da yaƙi ƙarewa,don Allah kiyi haƙury yanzu ki tashi ki sha wannan tea ɗin,sai a baki magani daga nan sai ki samu ƙarfin da zaki rama sallan Magriba da Isha'i da suka wuce ki."


Yasmeen ta ƙare maganan tana tayar da TAIMIYYAH daga jikin Iyah.Ganin hakan yasa Iyah zamewa ta bar musu ɗakin,tausayin TAIMIYYAH na sake kama Zuciyarta.


*30minutes Later.*


TAIMIYYAH ce zaune daga ƙasan carfet ɗin ɗakin Iyah.Yasmeen na zaune itama kusa da ita,sun tasa plate ɗin tuwan Semo da miyan Kukah a gaba,wanda Yasmeen ɗin ta zubo musu,wai ko zasu iya ci amma daga TAIMIYYAN har ita da ƙyar suka iya yin loma uku uku.Wayan TAIMIYYAN ne da ke kusa da ita ya fara ringing,wanda Yasmeen ce ta ɗakko mata wayan daga ɗakinsu ta kawo mata nan,ganin Nass ne me kiran yasa TAIMIYYAH turawa Yasmeen wayan tana mata alamu da hannu akan ta ɗauka.Don sam TAIMIYYAH ji tayi bata son yin magana da kowa ma,duk wanda suka shigo yi mata gaisuwa da kai kawai take iya amsa musu.


Yasmeen tayi receiving call ɗin tana kai wayan kunni,ta fara da amsa sallaman Nass ɗin.Kafin ta ɗaura da sanar da shi mummunan rashin da TAIMIYYAH tayi a yammacin yau ɗin,daga haka ta miƙawa TAIMIYYAH wayan bayan Nass ɗin ya gama yi ma su Abie ɗin addu'an samun Rahama a wajen Allah.


TAIMIYYAH ko data amsa wayar kara shi kawai tayi a kunni,ba tare da tace uffan ba sai ma wasu hawaye dake taruwa a idanunta.Har Nass ya gama yi mata ta'aziyyah taƙi buɗe baki tayi masa magana,daya matsa mata ma sai ta sanya masa kuka kawai,abinda ya ɗaga hankalinsa sosai yana ji kaman yai tsuntsu ya ganshi a Zaria,domin yana buƙatan ganin halin da take ciki.Sai dai duk iya yadda zai kai ga son ganinta dole ya jira sai zuwa Thursday,sannan ya samu ya yi squeezing shigowa Zarian,tunda bai jima da komawa bakin aiki daga hutun da ya ɗauka ba.


Da ƙyar TAIMIYYAH ta yadda ya maida kiran ta vid call,ta yadda zai fi samun nutsuwan rarrashinta idan yana kallon face ɗinta.Ya jima sosai yana kwantar mata da hankali da kawo mata misalai na waɗanda su ka rasa iyayensu,ciki har da shi da shima Mahaifinsa ya rasu tun yana Secondary Skull,sai Mamansa kawai da Yayyinsa mata da ke gidajen aurensu suka rage masa,sai Qanin Babansa daya maye masa gurbin Uba a yanzu.TAIMIYYAH dai ba umm! ba umm-umm! Tana dai sauraran Nass ne kawai amma bata ji cewa Zuciyarta zata daina ciwo akan wannan rashi da tayi har sai ranan da nata mutuwan ya zo.


A ƙallah sun ɗauki tsayin 30minutes kafin Nass yai hanging up! TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni,tana me lumshe idanunta sabbin hawayen da suka taru suka samu daman zubowa.A lokacin ne kuma sallaman su Zuhurah ya doki kunnuwan su,suka ƙariso cikin ɗakin Iyan suna zubewa a gaban TAIMIYYAH,su kai mata gaisuwa kowacce a cikin su idanunta yayi jawur,da alamu su ma sun sha kuka ba kaɗan ba.TAIMIYYAH kai kawai ta iya jinjina musu,daga haka su ka tashi su kai wa Yasmeen sai da safe suna barin ɗakin.


Umma ce itama ta shigo bayan fitan su Zuhuran,ta zauna a kusa da TAIMIYYAN tana mata ta'aziyyah.Karon farko data ji tausayin TAIMIYYAN ya ɗan taɓa zuciyarta kaɗan,ita ma ɗin dai TAIMIYYAH kanta kawai ta iya gyaɗa mata ba tare da tayi magana ba,hakan yasa Umma tashi ta baro ɗakin,Yasmeen na mata sai da safe.


Kiran Anty Mardiyyah ne qanwar Maman TAIMIYYAH ya shigo wayan TAIMIYYAN,hakan yasa Yasmeen amsa call ɗin suka gaisa.Yasmeen na bata tabbacin mummunan rashin da suka yi a yau ɗin,da yake Anty Mardiyyan sun jima da tashi daga nan Gyallesu kusa da su Iyah,sun koma Jigawa anma Mijinta transfer.Yanzu ma wani maƙwafcinsu ne sukai waya da Mijin nata shine yake sanar da shi rasuwan su Abie ɗin,shiyasa tayi saurin kiran wayan TAIMIYYAN don tabbatarwa.


Salati sosai ta saki a lokacin da Yasmeen ta bata tabbacin rasuwan.Sai Yasmeen ta miƙawa TAIMIYYAH wayan,ta amsa murya a shaƙe taiwa Antyn nata sallama,Anty Mardiyyah ta amsa daga ɓangarenta,tana wa TAIMIYYAH ta'aziyyah cike da alhini.TAIMIYYAH ta sakin mata kuka me taɓa Zuciya,nan ta dinga aikin lallashi tare da tabbatar wa TAIMIYYAN cewa zuwa jibi zata iso Insha Allah.Daga haka sukai sallama da juna TAIMIYYAH na jifa da wayan bisa kan Bed,basu bar ɗakin Iyah ba sai wajen 11:30pm,sannan suka koma ɗakinsu zuwa lokacin babu motsin kowa, duk mutanen da za su kwana sun yi bacci.


A kan idanun Iyah su TAIMIYYAH suka fito zuwa ɗakin nasu.Iyah na zaune daga can ƙarshen kujeran falon, tana faman jan Carbi gaba ɗaya idanunta a ƙyaƙashe suke,babu alamun bacci zai samu mata a daren yau ɗin,ganin su TAIMIYYAN sun baro mata ɗakin ne yasa ta miƙewa ta isa ɗakin nata.


Kusan zan iya cewa tsakanin Iyah da TAIMIYYAH,har zuwa kan Baba Sani da Sadeeq babu wanda ya iya rintsawa a daren,sai dai bacci da ake cewa ɓarawo.Wanda duk iya satansa ya kasa sace idanun Iyah da TAIMIYYAH,yadda suka ga rana haka suka ga dare,domin da zaran sun kulle ido fuskan Abie ɗin suke gani da su Nahar.Daga ƙarshe ma kaman haɗin baki sai suka yankewa kansu shawaran ɗaura alwala,sukai ta sallah suna roƙon Allah ya basu juriya da dangana,tare da roƙa ma Mamatan gafara.


Washegary kan ace kwabo gida ya cika damƙan da jama'a,ƴan zaman makoki duka ƴan uwa na kusa dana nesa sun bayyana.Ciki har da Guggo Bilki da Bakwai na safe ma a Zaria yai mata ita da Abban su Yasmeen ɗin,tare da yayyin Yasmeen ɗin Maza Samari su huɗu,don duk yaranta Maza ne Yasmeen ita kaɗai ce mace,kaman yadda Guggo Bilkin ita kaɗaice mace a gun Iyah.


Hatta da qawayen TAIMIYYAH su Maryam Sunusi,da su Zee duka babu wacce bata zo mata gaisuwa a yau ɗin ba.Kuma dukansu sun tausayawa TAIMIYYAH wannan Babban rashi da tayi, na rasa Uba da Qanni duk a lokaci guda.


Nass ma duk bayan awa ɗaya sai ya kira yayi magana da TAIMIYYAH na sake kwantar mata da hankali.Hakan kuma ba ƙaramin tasiri yayi wajen sanyawa TAIMIYYAN nutsuwan Zuciya da dangana ba,duk da cewa idanunta basu fasa zuban hawaye ba,sai dai ba a zo gabanta da sunan yi mata ta'aziyyah ba.


A ɓangaren Ummie da ke can Kaduna a Asibitin GARKUWA Kaduna,har lokacin bata farfaɗo ba daga dogon suman da tayi.Shiyasa a yau ɗin su Baba Sani da wasu cikin mata ƴan Family ɗin Abie ɗin suka nufi Kadunan dubo ta,basu dawo ba sai wajen Zuhur Prayer,suka cigaba da zaman amsan makoki har zuwa yamma inda kowa ke kama gabansa daga an kira Sallar Magriba.Sai ƴan uwa na nesa da za su yi ta kwana har sai anyi Uku sannan za a watse zaman makokin,sai dai na jikin Mamatan kawai da za su yi a ƙallah kwanaki bakwai kafin a watse........✍🏻






Allah sarki TAIMIYYAH kinyi babban rashi....😰






Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




#Ɗansabo ce#[12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *33*


Ranan da su Abiee ke da kwana uku da rasuwa,ranan aka iso da Ummie zuwa Zaria,wacce sai a ranan da Abie suke da kwana biyu aka sallameta daga asibiti.
Faɗin irin mummunan yanayin da take ciki ma bazai faɗu ba,don haka sai mutuwan ya dawo sabo a lokacin da ƴan uwanta suka iso da ita cikin gidan.
Sasan Iyah su ka fara sauka kafin daga nan a wuce da Ummie Sasan su dasu ke sauka duk idan sun zo garin,wanda a yau da safe aka sanya Babah Ladi ta gyare shi tsaf.


Kwanaki biyar da rasuwan ya kama Thursday ranan ne kuma Nass ya baro Abuja zuwa Zaria.Ƙarfe huɗu da wasu ƴan mituna motarsa ta tsaya a ƙofar gate ɗin gidan,yayi mamaki da babu kowa sai tsirarun mutane masu shiga su fita.Don tun randa akai addu'an uku aka dakatar da zaman makokin,sabida bai da wani anfani in banda zaman gulma da yi da mutane ba abinda ake yi.
Hakan yasa Iyah ta sanar da Baba Sani adakatar da mutane kawai,sai dai a shigo a fita idan anyi gaisuwa ya wadatar.


Nass ya ɗaga wayansa yana dialling number ɗin TAIMIYYAH,bugu biyu ta ɗaga wayan cikin muryanta da a ƴan kwanakin ya sake komawa very low.Bayan ya amsa gaisuwanta ne yake sanar ita cewa gashi daga bakin gate ko zata fito? TAIMIYYAH ta sauke numfashi tana faɗin,


"Alright gani nan zuwa Insha Allah!"


Daga haka ta sauke wayan daga kunni,tana duban Yasmeen dake kan gado tana faman danna waya ta furta, "Yasmeen ga Nass nan fa a waje ya iso."
Yasmeen ta aje wayan hannunta tana faɗin "Okey tuh sai ki saka Hijab ki fita,in yaso sai ki shigo da shi har Iyah yaiwa ta'aziyyah ko?"


Yasmeen tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta nufi wajen kayanta tana ciro gogaggen Hijab ɗin da zata saka.Sanye take dama da doguwar riga mara nauyi,fuskanta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login