Showing 36001 words to 39000 words out of 186776 words
Chapter 13 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
farko da ya kai bakinsa ya tauna ya haɗiye,ya aje spoon ɗin manyan idanunsa ya sauke akan Suhailah,yana faɗin "Ɗauke min wannan abincin daga gabana please!"
Yadda yai maganan muryansa na bayyana ɓacin ransa a fili,yasa Suhailah dubansa a razane,ya cigaba da furta "Mena faɗi Suhailah tun a gidan Hajjah game da yin wannan abincin? Amma sabida ban isa ba sai da kika baiwa bayinki suka yi sabida ki nuna min iyakata ko?"
Yayi maganan a mugun fusace yana miƙewa ya nufi ɗakinsa,ya bar Suhailah da baki sake gaba ɗaya ta rasama abin cewa,bata san meyasa yake iya bambamce girkin da tayi dana masu aiki ba,duk da cewa Ameena da take gani ƙwararriyace ita ta saka tayi masa,amma gashi sai da ya gane ɗin,ta lumshe idanunta tana jin babu daɗi,dama ya lafiyan giwa ita me laifi ce gashi ta sake ɗaura wani laifin,jikinta a sanyaye ta miƙe ta nufi ɗakinsa,sai dai tana shirin shiga shi kuma ya fito,hannunsa riƙe da mukullin mota ya sauya kaya zuwa wasu Riga da Wando na Gucci,saura kaɗan su gwabza karo Suhailah tayi saurin ja baya tana duban fuskansa da babu annuri take faɗin "Don Allah kayi haƙury Sweet wallahi kaina ne ya dinga ciwo dana dawo,shiyasa na kasa yi da kaina gudun karka dawo kuma ka tadda ba'a yi ba yasa nace Ameena tayi,don Al......"
"Alright! yayi kyau."
A.Maleek ɗin da ya katseta ya furta,yana raɓata zai wucewansa tayi saurin shan gabansa tare da riƙo rigansa,wani mugun kallo yai mata yana zare hannunta daga jikinsa,ya wuce da sauri zuwa Stairs da bibbiyu ya dinga haɗa steps ɗin benan har ya sauka ƙasa,da kansa yake driving ya bar gidan megadi na ɗaga masa hannu da fatan dawowa lafiya,Apple white ya nufa yayi Ordern wani irin Tea nasu me daɗi haɗi da Snacks,bai tsaya ci anan ba akai masa take away ya fito zuwa mota,ya sake isa wani wajen sai da ƙoda ya siya sannan ya wuto gida lokacin da agogo ke buga sha ɗaya har da mintuna biyu,nan falon ƙasa ya zauna yaci komi iya yadda xai iya ci,yana cikin ƙarisa shanye tea ɗinsa Suhailah ta sakko,tana sanye cikin kayan bacci Riga da wando da suka fidda suranta,gaba ɗaya qamshinta ya cika wajen lokacin da ta iso,amma kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai ita kuma ta zauna idanunta na kansa bayan ta gama kallon yadda ya barbaje packs ɗin da aka zuba masa komi ciki,cikin wani irin salo na bada haƙury ta buɗe baki zatai magana,yayi saurin ɗaga mata hannu,yana tashi tsam ya bar mata falon gaba ɗaya ya haura zuwa sama,murzawa ɗakinsa key yayi don bayama buƙatan damu bare ya saurari ban haƙurinta,sabida tana sake fusata zuciyansa ne sosai,ya daɗe yana gayawa kansa abubuwa da yawa da yake shayewa daga gareta tana cin albarkacin Hajjah ne,da kuma ƙarfin zumuncin da ke tsakaninsa da ita,uwa uba Soyayyan da Inna Kareeman ta gwada masa,wato mahaifiyan Suhailan yana sake taka rawa wajen danne zafin zuciyansa akan Suhailah,amma baya ji idan aka cigaba da tafiya a yadda Suhailah take masa yanzu baza'a samu matsalaba,don sosai take son ƙure duk wani haƙurinsa da kauda kan da yake yi a wasu lamuran,yana ji tana faman nocking yai biris da ita,sai ma wayoyinsa da ya janyo ya kashe su baki ɗaya,dama baya kwana da waya a kunne sam,har bacci ya ɗauke sa bayan ya kwanta baisan yadda ta ƙare tsaye abakin ƙofar ɗakin nasa ba.........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 20 to21*
*END OF THE FREE PAGES*
*To masu karatu a wannan page ɗin Free pages ya zo ƙarshe.Don haka sai ku hanzarta biyan 500 ɗinku don jin cigaban labarin,domin duk yadda zan gutsira muku ya labarin TAIMIYYAH yake ba za ku gane inda aka dosa ba har sai kun shiga cikin labarin tsindim sannan za ku gane inda tafiyan ya dosa.Don haka kar ku bari a barku a baya ku bi sahun masu rubdugun shiga Payment Group don jin ya labarin TAIMIYYAH zai kasance? Yah Maleek da Suhailah za su kwashe a gaba,shin da gaske zai iya sake auren wata mace don samun haihuwa,ko bazarana ce kawai yake? Duk za a warware muku zaren labarin a gaba.Ku dai kawai ku biya ku shige cikin group don kwasan karatu.Saina ga ruwan ƙauna daga Fans ɗina* 😍
_______Washegary Suhailah da kanta ta tashi ta shiryawa A.Maleek Breakfast,sai dai cikin rashin sa'a A.Maleek ɗin tun ƙarfe takwas ya bar gidan ba tare da sanin Suhailan ba,sai da ta gama tsara kwalliya ta nufi ɗakinsa ta tadda babu kowa ciki,sai ɗakin da ya bari a hargitse duk kayan da yai anfani da su gasu nan zube bisa Bed ɗin,waya ta ɗauka ta kira shi zuciyanta na bugawa da ƙarin takaicin kanta da kanta,yana ɗaga wayan sai ta nemi sanya masa kuka yayi saurin dakatar da ita,yana sanar da ita ya wuce Kaduna daga can kuma zai bi jirgi ya wuce Lagos,sai next week zai dawo bayan an rantsar da shi akan sabon muƙamin da aka bashi,wanda za'a rantsar dasu a Abuja sati me zuwa, don haka ya bar mata garin tayi yadda take so,ai Suhailah bata san lokacin da ta rushe da kuka ba shi kuma yai cuting call ɗin yana jan ƙaramin tsaki,zama tayi a ɗakin taci kukanta ta more kafin ta fice ta koma zuwa nata ɗakin,ta cigaba da neman layin Zuby cikin sa'a bugu biyu Zubaidan ta ɗauka,sai Suhailah ta sanya mata kuka,cikin nuna kiɗemewa Zubyn ke tambayan Suhailah abinda ke faruwa amma sai Suhailah ta shaida mata cewa zancen bana waya bane,don haka idan ta samu lokaci kawai ta zo gidan nata akwai maganganu,daga haka sukai sallama Suhailah ta aje wayan,zuciyanta sam babu daɗi tana tsoran ace Maleek ya juya mata baya a dai-dai wannan lokacin,takaicin kanta na yadda take kasa binsa a yadda yake so na sake lulluɓe zuciyanta.
________
*Monday,10:10am.*
TAIMIYYAH ce tsaye daga bakin titin kwaltan shiga layinsu,sanye take da dogon Hijab kalan sararin samaniya,kaman yadda kalan Material ɗin jikinta yake,Napep take jira don zuwa wajen Computer Training ɗin da zasu fara a yau ɗin,sai dai da alama yau ɗin za'ai wahalan abin hawa,ta sake kallan agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta,ta ga lokaci na sake tafiya sai takaicin rashin barin Sani Drivern Iya ya kaita ya kamata,don ba yadda Iya ba tayi akan ta kira Sanin ba amma ta nuna tafi so ta dinga zuwa da kanta,tsayuwan mintuna kusan goma ta ƙara bata samu abin hawanba gashi ita ba gwanar jurewa tsayuwa bace sabida laluran ƙafanta,wayanta take shirin cirowa a jaka ta kira Sanin ta ji idan yana kusa kawai yazo su wuce,sai dai tsayuwan wani me Napep a gabanta yana faɗin "Hajiya tafiya ne?" Shi ya katsewa TAIMIYYAH hanzari ta ciro hannunta daga cikin jakan tana gyaɗa masa kanta,kafin ta furta "Eh tafiya ce,can gaban Congo kaɗan zaka kaini."
Ta ƙare maganan tana shiga cikin Napep ɗin ta zauna,shi kuma ya ja sukai gaba ko da suka isa sauka tayi ta nufi cikin wajen bayan ta biya shi kuɗinsa,shi kuma yaja mashin ɗinsa yai gaba,Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi kaman yadda aka sanar dasu tsarin karatun,su shiga ten afito one ga mamakin TAIMIYYAH kuma suna da yawa sosai wanda suke karatun tare maza da mata,cikin wanda suka fito kusan a tare wata budurwace me yawan fara'a,baƙace sosai sai dai tana da kyau dai-dai misali,ta dubi TAIMIYYAH lokacin da suka gama fitowa daga cikin ajin ɗaukan karatun,ta miƙa mata hannu tana faɗin "Salamu alaikum,sunana Zaynab Haroun." TAIMIYYAH itama sai ta miƙa mata nata hannun sukai musabaha,da murmushi a saman fuskarta take faɗin "Sunana Zaynab Sameer."
"Wow! nice name Namcy,ina farin cikin haɗuwa da takwarata." Cewan budurwan itama murmushi kwance saman fuskanta,suka jero a tare da TAIMIYYAH har zuwa bakin titi,budurwan na ta ɗan jan TAIMIYYAH da magana akan Programme ɗin da zasuyi na Computer Training ɗin,zuciyanta cike da tausayin yadda TAIMIYYAN ke tafiya,a zuciyanta take ayyana mace har mace kyakykyawa da ita ga dirin jiki amma Allah ya jarbceta da nakasan ƙafa ɗaya,ita dai TAIMIYYAH tana amsa mata jefi-jefi,suna tsaye tare har suka samu abin hawa,TAIMIYYAH ta shaida masa gyallesu zata nufa,yayin da itama Zaynab tace Gaskia ita ta nufa,hakan yasa sukai sallama da juna TAIMIYYAH ta shiga ya wuce da ita.
Ta iso gida a gajiye sosai burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iya ba,tayi wanka ta sawa cikin ta abinci don yinwu take ji sosai,a hankali take shigowa cikin Compound ɗin gidan,bayan ta tsaya sun gaisa da sabon megadin da Baba Sani ya kawo a shekaran jiya me suna Tukur,matashi ne kuma bamai nisan shekaru sosai ba don bazai wuce shekaru arba'in ba,tana cikin tafiya sai ji tayi ana kiran sunanta,sai ta dakata da tafiyan hannunta dai dafe da ƙafanta me laluran,ta waiwaya baya idanunta na sauka akan Anty Laurat da ke tahowa daga Sasan su Zuhurah,sai TAIMIYYAH ta saki murmushi tana cigaba da tsayuwa har Anty Laurat ɗin ta ƙariso wajen,tana furta "Daga ina ƴan mata da uwar ranannan?"
TAIMIYYAH ta sake faɗaɗa murmushinta tana sanar da Laurat ɗin daga inda take,Laurat ta furta "Ayyah! Sannu da dowawa tuh,ya karatun hope ya fara daɗi?" Yadda tai maganan da zolaya yasa TAIMIYYAH sakin murmushi tana faɗin "Anty Laurat kenan sai mu ce Alhamdulillah!"
Laurat itama ta saki dariya kaɗan tana faɗin "Bari na barki ki ƙarisa daga ciki,nima wai na fito zan ɗan je kasuwa ne akwai abinda zan nemo,zuwa anjima zan shigo ai yau ina so ki ɗan gwada yin Doughnut irin wanda ki kai shekaranjiya ɗinnan,yayi daɗi ina so na ga yadda kikai kwaɓin."
"Ok ba matsala Anty Laurat,sai kin shigo ɗin bari in ƙarisa na gaji sosai." Cewan TAIMIYYAH daga haka kuma ta cigaba da takawa zuwa Sasan su inda tafi wayo,a falo ta tadda Iya tayi baƙuwa qawanta Hajiya Sahura ne ta zo,da alama tazo garin kenan sabida ta bar Zaria da daɗewa,ta koma can Bauchi wajen Yayanta namiji da ya ɗauke ta tun bayan rasuwan mijinta,TAIMIYYAH ta durƙusa har ƙasa ta gaida Hajiya Sahuran da ke mata sannu da zuwa,ta amsa da fara'a tana faɗin "Sannu TAIMIYYAU ai ina zuwa na tambayeki Iya tace kina wani makaranta na koyan na'urannan me ƙwalƙwala,to Allah ya bada sa'a." TAIMIYYAH ta amsa da "Ameen,amma Hajjaju ki dinga faɗin sunan dai-dai TAIMIYYAH ne fa ba TAIMIYYAU ba."
Yadda TAIMIYYAH tai maganan a shagwaɓe yasa Iya da Hajiya Sahuran yin dariya,Iya na faɗin "Ja'irah to ya karatun na ga kin jima nema baki dawo ba."
"Lafiya lau Iya,rashin abin hawa ne wallahi ya tsaidani,don da zani ma da ƙyar na samu,ina ga dai naki zanbi Sanin kawai ya dinga zuwa ya kaini idan zan dawo na dinga dawowa ni kaɗai ɗin."
Cewan TAIMIYYAH tana tashi don shigewa ɗaki,Iya tabi bayanta da kallo tana faɗin "A tuh! Da dai yafi miki kam."
Bayan shigan TAIMIYYAH ɗaki ne Hajiya Sahurah ta dubi Iya tana faɗin"Kinga yarinya yadda ta zama ƙatuwar budurwa kyau kaman ita tai kanta,lallai na jima rabo na da Zaria Iya wallahi kamanninta da marigayiya uwarta har ya ɓaci,inama ina da ɗa namiji da anyi haɗin zumunci don ni dai ina ƙaunar wannan ɗiya ina kuma tausayinta matuƙa,Allah yai mata zaɓi ya kareta daga sharrin samarin zamanin nan." Iya tayi caraf tana amsawa da "Ameen,ke dai bari kawai Hajjaju kullum addu'an da nake kenan Allah fito mata da nagari,ya kaita inda bazata cutu ba ko dan laluran ƙafannan nata,kinsan halin mutanan mu koya suka ga mutum da nakasa sai ya zama abin rainawa,bayan basu san irin baiwan da ubangiji ya aje a garesa ba,Allah dai ya shige mana gaba yai mata kyakykyawan zaɓi Ameen." Daga haka suka cigaba da hiransu Iya na ba qawan nata labarin yadda Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa TAIMIYYAN,Hajiya Sahuwa abinka da mace me saurin ɗaukan zafi,nan take ta dinga la'antan baƙin halin Umma,har tana mata fatan Allah ya gwada mata samun nakasasshen cikin jikokinta in tana ganin ta gama haihuwa ne a yanzu da har take nunawa TAIMIYYAH baƙin tsana irin haka,ita dai TAIMIYYAH da ta fito daga wanka tana jiyo tashin zancen su Iyan sama-sama daga ɗakinta,har ta gama shiri ta fito kai tsaye ta nufi wajen cin abinci,ta zuba wanda zataci ta fara ci bayan ta kammala ɗaki ta shiga,tana ɗakko sabuwar Laptop ɗinta da Yah Sadeeq ya taho mata dashi daga Kd,randa yazo Weekend domin tunda Abie ya turo mata kuɗin sayan sai taiwa Yah Deekun magana ta waya akan tana so ya siyo mata yazo mata dashi,tayi-tayi ya turo mata details ɗinsa ta saka masa kuɗin,amma sai yai mata wayau yace ta bari idan ya shigo Weekend zasuyi magana,sai kawai ganinsa dashi tayi randa ya diro garin ya kawo mata Sasan Iya,yana mata dariya wai Suprising ɗinta yayi,aiko murna a gun TAIMIYYAH kaman ta rungumeshi haka taji,musamman da ta duba taga Exactly irin wanda ta tura masa hotonsa ta chart ne tace irin shi take so,hatta Iya tayi murna da wannan kyauta da yaiwa TAIMIYYAN,tai ta masa godia yana hararanta a lokacin yana faɗin shi baiga abin godia ba don ya saiwa TAIMIYYAN Laptop kawai.ta saki murmushi lokacin da take buɗe Laptop ɗin ta kunna,cikin sauƙi ta fara operating ɗin abinta cike da farin ciki,tayi abu me yawa a ciki duk cikin karatun su na yau ɗin,kafin ta rufe ta mayar ta aje tana komawa gado don ta samu ta ɗanyi bacci kafin akira sallan La'asar.
Kamar yadda suka rabu da Anty Laurat zata shigo koyan Doughnut,aiko ana idar da sallan la'asar ta shigo Sasan Iya,bayan sun gaisa da Iya a falo ne ta wuto ɗakin TAIMIYYAH,wacce ke amsa call ɗin Maryam Salis da ke sanar da ita rashin lafiyan mamansu da aka kwantar a asibiti,TAIMIYYAH ta bata tabbacin zata sanar da Iya su je su dubo Mum ɗin a asibitin kafin a sallamesu,ta sauke wayan daga kunni bayan sunyi sallama da Maryam ɗin,manyan idanunta ta ɗaura akan Anty Laurat da ke bin TAIMIYYAN da kallo,ganin yadda Rigan jikinta yai mata kyau,tare da fito da kyawun halittan TAIMIYYAN a sarari "Anty Laurat har kin shigo?" Cewan TAIMIYYAH da murmushi saman face ɗinta,Laurat ɗin itama murmushi tayi tana faɗin "Eh! Wallahi TAIMIYYAH gani na shigo,gara afara yanzu kada muyi dare ko?"
Daga haka suka fito zuwa kitchen ɗin Iya,da yake babba ne sosai sam babu wani takura,Ladi na ta hidiman ɗaura abincin dare su kuma suna aikin kwaɓa Doughnut ɗin,wanda TAIMIYYAH tace a kwaɓa na mudu ɗaya kawai,aci har ayi sadaka da sauran wa maƙwafta,hakan ko akayi ta fiffito da kayayyakin yin,fulawa mudu ɗaya (8 cups) ta baiwa Anty Laurat ɗin tace ta tankaɗe cikin wani bowl,ita kuma ta fito da 2 eggs, sai Sugar 1 and half cup, sai 2tbsp na Yeast ,sai 1tsp Salt,sai Half Simas,sai 2 cups liquid milk(warm),sai 1tsp Vanillah powder.
Bayan duk ta gama arranging Ingredients da take buƙata sai ta ɗakko Mixer ɗinta ta jona jikin sucket,ta fara da zuba fulawan da aka tankaɗe cikin Mixing bowl ɗinta,sai ta zuba Vanillah powder ɗinta da Salt and Sugar ɗin,ta juya suka haɗe jikinsu,sannan ta fasa egg ɗin a wani bowl ta zuba Yeast and Warm milk ɗinta,ta kaɗa sosai ta juye akan fulawa ɗin,sai ta zuba butter ɗin akai ta fara mixing with high speed,sai da ta tabbar yayi mixing sosai zaku ga tun anan ya fara kunbura yayi wani irin laushi,tana yi tana zuba butter ɗin har buttern ya ƙare,sai ta kwashe shi cikin wani Bowl wanda ta shafeshi da Butter,sai ta rufe da clin film ta ajesa yayi some minutes,za ku ga ya kunburo sosai sannan sai suka fara murzawa a abin murji suna cire shape ɗin Ring Doughnut,wani kuma sai TAIMIYYAH ta naɗe shi as twisted Doughnut,ita dai Ladi da Laurat bin TAIMIYYAH suke da kallo tana sake birgesu matuƙa,yadda take kominta a nutse cike kuma da ƙwarewa,lokacin da suka kammala sai suka bashi some another minutes,za ku ga duk shapes ɗin sunyi doubling sun kumbura sosai,sannan suka ɗaura mai Anty Laurat ita ta amshi suyan tana faman jerawa TAIMIYYAH sannu,wanda hakan ya baiwa TAIMIYYAH dariya ma,don ita ta riga da ta saba yin waɗannan ayyukan don haka ta taso ita me son girke-girke da harkan su snacks ne,shiyasa take shiga online classes kala kala,kuma duk anan ta sake samun ƙwarewa,abinda bata gane ba sai ta tafi youtube ta dubo a haka har ta zama ƙwararriya sosai a fannin girkin zamani da haɗa su Snacks kala kala,wani irin result me kyau Doughnut ɗin ya bada,yayi wani irin laushi da kyau sosai,kallo ɗaya zakai masa kasan daɗin da zaiyi tun kafin akai baki,yanzu ne kuma Anty Laurat ɗin ta gane bambamcin da TAIMIYYAH ke faɗi na kwaɓin Mixer yafi na hannu kyau da laushi,domin duk yadda zakai kneading ɗinsa da hannu ba kaman yadda mixer zaiyi ba don texture ɗin bazai taɓa zuwa ɗaya ba.
Iya dai da ke can Falo tuni qamshi ya gama cika sasanta,tana alfahari da ƙwarewan TAIMIYYAH da baiwan da Allah yai mata kashi kashi,tasan ko da wannan baiwan na iya sarrafa girke-girke aka barta zata mallaki zuciyan miji.Lokacin da suka kammala suyan ya cika wani babban