Showing 72001 words to 75000 words out of 186776 words

Chapter 25 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6624

da yake tsaye yana ƙoƙarin sanya Links na hannun rigarsa,ta amsa tana sanya masa idanunsu na yawo a jikin juna.Ta cikin dogon mirrow ɗin da ke kafe cikin Bedroom ɗin,ta gama sanya masa Links ɗin tana yin ɗage ta manna masa kyakykyawan sumba a side face ɗinsa,murya ƙasa-ƙasa ta furta, "Luv u My Yah Maleek."


Maleek Ado ya saki ƙayataccen murmushin da ba kasafai ake gani akan fuskarsa ba.Ya ɗan rankwafa dai-dai yadda zai iya manna mata kiss saman goshinta,ya sauke mata kyakykyawan kiss a saman goshi,muryansa very deep yake faɗin "Luv u too sweet wife,and also My lil sis ever."


Suhailah da kalaman da ya kirata dasu su kai mata mugun daɗi.Sai ta lumshe ido ta buɗewa akan face ɗinsa,kafin ta kai bakinta saman lips ɗinsa,tana sake bashi light kiss.A.Maleek ya tallafi fuskarta da hannu ɗaya shi ma yana sake manna mata wani kiss ɗin a forehead ɗinta,kafin su fito suna sarƙe da hannun juna.


Sunusi dake zaune cikin mota yana jiran fitowan ubangidan nasa,yana hango tahowan su yayi saurin buɗe musu back seat.Idanunsa akan A.Maleek lokacin da suka ƙariso bakin motar ya furta, "Ranka-ya-daɗe barka da fitowa,Madam mun tashi lafiya?"


Suhailah ta amsa masa gaisuwan shi kuma A.Maleek hannu kawai ya ɗaga ma Sunusin,yana me gyara zama cikin motar.Sunusi ya rufe motar yana shiga driver seat ya tashi motar,bayan Suhailah ta rufe nata ɓangaren tana me mannuwa da jikin Maleek.Ƙamshin junan su gaba ɗaya ya haɗe da ƙamshin da ke tashi a cikin motar,ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi me sanyaya zuciya.


Ba su wani jima cikin Asibitin ba suka amsa tarin magungunan da aka baiwa Suhailah,wanda za ta yi anfani da su tsayin watanni uku kafin ta dawo Asibitin a sake bincikar lafiyar mahaifarta.Jikin Suhailah a matuƙar sanyaye yake lokacin da Maleek ya aje mata ledan da ke ɗauke da magungunan da za ta yi anfani da su.Ta langaɓar da kanta a jikinsa cikin murya me cike da rauni take faɗin, "Yah Maleek yanzu duk ni zan shanye waɗannan tarin magungunan?"


Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta yana cewa, "Yes! Da waye zai taya ki sha?" Suhailah ta jinjina kai tana cewa "Allah ya bani rabon haihuwa kafin in gama shanye su toh!"


A.Maleek ya amsa da "Ameen wife,Luv u." Suhailah ta ɗaga ido tana kallon cikin idanunsa,kafin ta furta "Luv u too Yah Maleek,don Allah amma kar kayi gaggawan ƙaro aure koda ban haihu nan kusa ba please! Wallahi ina tsananin kishinka Yah Maleek,ina cikin matsananciyar nadaman aikata wautan dana yi a baya."


Yadda ta kai ƙarshen maganan cikin rawar muryan da ke nuna cewa gaf take da sakin kuka,yasa Maleek rungumota zuwa jikinsa sosai,yana shafa tsakiyar bayanta a hankali.


Memakon su koma gida sai suka nufi wani Shopping Mall don Suhailah na son duba wasu abubuwan anfani da zata siya,sabida za su samu kaman 2 weeks a ƙasar kafin su koma gida.Ita da Maleek suka shiga cikin Mall ɗin, sun ɗauki a ƙallah zai kai mintuna talatin,kafin su fito kowannen su hannunsa riƙe da manyan ledoji.Sunusi ne ya nufesu da sauri yana amsan ledojin hannun A.Maleek ɗin,shi kuma Maleek ya amshi na hannun Suhailah aka sanya a boot,kafin Sunusi ya ja motar suka nufi hanyar komawa gida.


Suhailah kaɗai aka sauke lokacin da suka iso gidan,shi Maleek Sunusi zai fita da shi wani wajen.don akwai abubuwan da yake son dubawa na harkokin Business,wanda yake son fara aiwatar a ƙasar.Don haka ita kaɗai ta buɗe gidan ta shige Sunusi na biye da ita da tarin ledojin siyayyar da suka yo a mall ɗin.
Sai daya kai mata kayan har cikin falo sannan ya juyo zuwa mota,sukai gaba shi da Uban-gidan nasa.


Suhailah Abayar jikinta ta cire bayan ta isa ɗaki,yai saura daga ita sai ƙaramar rigan dake jikinta mara hannu.Wanda tsayin rigan iya cinyanta ya tsaya gaba ɗaya rabin ƙirjinta a bayyane yake,sabida wuyan rigan me yankan V-shape ne.


Siyayyan da suka yo ta juye saman gado,tana arranging ɗinsu inda ya dace.Lokacin data kammala Kitchen ta nufa don ɗaura musu Lunch sabida babu abinda Maleek bai sa Sunusi ya siyo ba na kayan abinci.Har zuwa kan duk wani abun buƙata kama daga kayan miya har zuwa Kaji da Kifi duk an damfare su cikin Freezer.Shiyasa basa siyan abinci ita ke musu girki kuma hakan Maleek ke so shiyasa yaƙi kama Hotel sai gida.


Cikin awa ɗaya ta kammala dafa Jallop ɗin Macaroni da yaji Mince Meat da Potatos with Vegies a ciki.Sai tayi Pepesoup na Kaza wanda yaji spice sosai da Garlic a ciki,sabida haka Maleek ke son a cika Garlic a cikin Soup ɗin Kaza idan zai ci.


Ta kammala komi bisa dining area da ke cikin falo,sannan ta koma ta gyara inda ya ɓaci a Kitchen ɗin kafin ta fito ta nufi Bathroom don yin wanka.


Cikin wasu English Wears riga da pencil skat ta shirya kanta,kayan sunyi mata kyau matuƙa tare da fidda shape ɗinta.Daddaɗan ƙamshi ke tashi a jikinta duk yadda ta motsa,tana tsaka da da ɗaure gashinta data warware Maleek ya shigo cikin ɗakin.Suka haɗa ido ta jikin madubin ɗakin Suhailah na sakin masa murmushi,ya tako a hankali zuwa gare ta yana tsayawa a bayanta ya kai hannu ya rungumota ta baya, tare da ɗaura kansa bisa kafaɗunta hancinsa na cika da sassayar ƙamshita.Suhailah data lumshe ido jin ɗumin numfashinsa a wuyanta,sai ta buɗe idon tana faɗin, "Sannu da zuwa My Maleek."


Bai yi magana ba sai juyo da ita da yayi suna facing juna,ya kai bakinsa a hankali ya sumbaci ƙirjinta idanunsa a lumshe.Kafin ya buɗe ido yana ɗauke kansa daga ƙirjinta ya mayar saman fuskarta yana haɗe bakinsu waje guda,cikin wani irin salo ya zura harshensa cikin bakinta yana laluban harshenta ya fara tsotsa....
Tuni Suhailah ta sarƙe hannuwanta a bayansa tana sake manne ƙirjinta a jikinsa,suka shiga bai wa juna zazzafan deep kisses.
Da ƙyar ta iya janye jikinta daga garesa jin Maleek ɗin na ƙoƙarin rabata rigan jikinta.Ya ɗago idanunsa masu cike da zallan rikici ya sauke a kanta yana mata alama da hannu akan ya zata hana shi abinda yake so? Suhailah ta narke masa tana sanar da shi yinwa take ji ya bari su yi Lunch sai ta ba shi dukkanin abinda ya ke nema daga gareta. Da haka ta lallaɓashi suka nufi dining don cin abinci,bayan sun kammala kuwa shi ya ɗauke ta gaba ɗayanta zuwa Bedroom ɗin,bai direta a ko'ina ba sai saman Bed,yana hanata duk wani motsi har sai da ya tabbatar ya cire rigan jikinta yai wurgi dashi......


Lamuran da suka biyo baya masu tarin girma ne da alqalamina bazai iya rubutowa ba,ban kuma sake jin ɗuriyan su ba sai gaf da La'asar.


Kwanakin da suka biyo baya a ƙasar ta Cairo gaba ɗaya shafin soyayya Maleek da Suhailah suka buɗe,tamkar zasu cinye juna da zallan luv me tsayawa a rai.Gefe guda Suhailah ta fara nisa a shan magungunan ta,tana kuma addu'an akan cewa Allah yasa ta samu rabo cikin sauri.....
Satinsu biyu cir! Suka biyo Flight don dawowa ƙasar su ta gado wato Nigeria,inda suka sauka a garin Abuja don nunawa Suhailan sabon gidan da ya saya a Asokoro.wanda tuni aka kammala zuba komi a ciki na kayan alatun more rayuwar duniya,sabida nan yake so su dawo da zama baki ɗaya su baro Zaria,sabida wannan sabon muƙamin da aka bashi,zaman shi a yanzu zai fi ƙarfi ne tsakanin Lagos da Abujan.Shiyasa ya yankewa kansa zaman Abuja don yasan Hajjah ba za ta so shi da zaman Kudu din-din-din ba.


Suhailah ba ƙaramin ruɗewa da tsaruwan gidan tayi ba,don gini ne da aka tsara shi tamkar ba za a bar duniya ba.Manya-manyan faluka ne guda biyu daga ƙasa,sai ɗakunan bacci guda biyu,sannan ƙaton kitchen wanda yake manne da babban Store daga gefen hagu idan ka shige corridor.A kwai kuma ƙofan da zai kaika Backyard daga cikin Kitchen ɗin,idan ka haura sama kuwa a kwai Ƙaton falo sai ɗakunan bacci guda uku masu ɗauke da toilet a jikin kowanne Bedroom.Ɗakin da yake daga can ƙarshe shine na Maleek ɗin,wanda duk yafi sauran Bedrooms ɗin girma da tsaruwa.


Yadda aka qawata gidan da kayan alatu masu asalin kyau da tsada,zai baiwa me kallo tabbacin cewa,wanda ya mallaki gidan ba ƙaramin arziƙi ya tara ba.


Daga can wajen Compound ƙaton parking space ne,da aka adana manyan motoci sabbi dal guda huɗu.Hatta sabbin Drivers da aka bashi daga Office sunanan ready suna jirane kawai su tare a gidan, su fara aikinsu don muƙamin da aka bashi ba ƙarami bane.A kwai BQ me ɗauke da 2 Bedroom da single falo,sai ƙaramin Kitchen daga cikin corridor,sai toilet da ke manne jikim kowani Bedroom.


Kwanansu biyu a garin Abujan suka biyo jirgi zuwa Kano,daga Kano Yusuf driver ɗin Maleek ya ɗakko su zuwa Zaria.


____________


*Zaria.*


Yau kwanakin su Abie goma sha biyar kenan da barin gidan duniya.Su TAIMIYYAH sun ɗauki dangana tare da komawa harkokinsu na yau da kullum,don har TAIMIYYAH ta cigaba da zuwa Computer Training ɗinta.Sai dai har lokacin ba za a ce alhinin mutuwan ya sake su baki ɗaya ba, sabida gaba ɗaya TAIMIYYAH ta koma wata irin shiru-shiru mara son yawan magana sosai ba kaman daba.
Duk yadda Iyah da Yasmeen ke ƙoƙarin ganin ta koma kaman da abin yaci tura.Sai Iyah ta maida kai wajen yi mata addu'an samun ƙarin dangana,daga ɓangaren Ummie kuma takaba ya fara nisa,itama kuma ba laifi ta dangana.Sai dai ita ma ta sake zama mara son magana kullum cikin tunani da mafarkin mijinta da ƴaƴanta ta ke.Iyah har lokacin ba ta fasa sa ana mata rubutu tana sha ba,tana kuma ƙoƙari matuƙa wajen ganin Ummien ta samu nutsuwan zuciya.


Daga ɓangaren Soyayyar Nass da TAIMIYYAH kuwa kullum daɗa samun cigaba ake yi.Don wani irin zazzafan soyayyar Nass ɗin ne yai mata mugun kamu,wanda har abin ke bata tsananin mamaki ta yadda bata iya cikakken awa biyu bata ji muryarsa ba,sabida yadda ya saba mata da yawan kira.
Bai cika zuwa Weekend ba sai duk bayan Sati biyu,shiyasa rabon su da ganin juna a zahiri tun ranan da yazo yai mata sallama zai wuce Abuja kwanaki goma sha uku kenan baya.Tun daga lokacin bai sake shigowa garin ba sai gobe Friday ne yake saka ran shigowa,don an kwantar da Mamarsa ma a asibiti ciwan Sugar ɗinta ya tashi yau kwana biyu kenan.
Shi yake gayawa TAIMIYYAH hakan a jiya da suke waya da daddare,har yana sanar da ita idan ya shigo dole zai ɗauke su ita da Yasmeen su je duba Mamar tasa.


Ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai tayi a lokacin,amma sam ba ta tunanin za ta iya binsa su je gaida wata Mamarsa.


"TAIMIYYAH ki zo in ji Iyah."


Cewan Yasmeen data shigo cikin ɗakin dawowanta daga kasuwa kenan,don ita TAIMIYYAH ta shiga Skull a yau ɗin shiyasa basu tafi tare ba.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Yasmeen ɗin tana cewa, "Yaameen har kin dawo,Allah dai yasa kin samu siyo wiffing cream ɗinnan da cocoa powder."


Yasmeen data aje jakan hannunta ta dubi TAIMIYYAN tana faɗin, "Hmm! Na siyo amma da ƙyar wallahi don komai yayi tsada sosai , duk abinda ka taɓa sai ka ji ya ƙara kuɗi wannan tsadan rayuwa dai kullum gaba ya ke yi TAIMIYYAH,ni wallahi abin har tsoro yake bani fa."


Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana sake jinjina irin yadda kullum ka je kasuwa,sai ka tadda ƙarin hauhawan farashin kayayyaki.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tare da dafe ƙafanta me laluran tana cewa, "Hmm! Ke dai Allah yasa mu dace kawai,amma abin sai Addu'a Allah dai ya kawo mana ɗauki,bari in je wajen Iyan."
Daga haka ta fara takawa don barin ɗakin lokacin da Yasmeen ke amsa Addu'ar da tayi da,


"Ameen."


"Iyah gani Yasmeen tace kina kirana."


TAIMIYYAH tayi maganan lokacin da ta iso wajen Iyah da ke zaune a falo tana irga wasu kuɗi.Iyah ta sauke manyan idanunta akan TAIMIYYAH tana faɗin, "Eh dama waɗannan kuɗin zaki tayani irgawa,don ni ina yi ina daburcewa na rasa gane ko nawa ne duka kuɗin."


TAIMIYYAH ta zauna kusa da Iyah tana kwashe kuɗin daga gabanta ta fara irgawa tana cewa,"Ke dai Iyah irgan kuɗi wahala suke baki waye ya kawo miki kuɗi haka masu yawa?"


Iyah ta ɗan taɓe baki tana faɗin, "Kuɗin hayan gidana ne na Samaru ɗazu Kallamu ya kawo kinsan ai lokacin amsan kuɗin yayi."


"Oh..! Hakane fa na manta wallahi,kice mun yi kuɗi yau zaki siyan mana rousted fish mu ɗanci ko?"


Cewan TAIMIYYAH cike da tsokana,Iyah ta harareta tana faɗin, "Ai bakinki ne fish ɗin,ki gama irga kuɗin dai sai ayi magana koma me za'a siya,Allah ya ji ƙan wanda ya siya min gidan yasa suna kyakykyawan matsayi,su da iyayenmu baki ɗaya da suka rigamu gidan gaskiya."


Iyah ta kai ƙarshen Addu'ar wani abu na motsawa a zuciyarta,tunawa da tayi da Abie don shine ya siya mata gidan yace a zuba ƴan haya,ta dinga samun kuɗin shiga duk ƙarshen shekara.Banda jarin kuɗin da ya bata a hannu tana ɗan siyan irin su Barkono da waken Suya idan farashinsu ya hau an samu riba sai a siyar a sai wani.


TAIMIYYAH ta amsa da "Ameen." Itama zuciyarta na motsawa da wani irin kewa me tarin yawa na Abiee ɗin,har ta kammala irga kuɗin babu wanda ya sake magana a cikin su.Ta baiwa Iyah kuɗin tana sanar da ita adadin yawan su,kafin ta tashi ta koma ɗaki tana kwanciya tayi lamo a kan gado,haka kawai ta ji tana son jin muryan Abie ɗin nata.Hawaye suka fara zarya a fuskarta suna sauka bisa pillow,amma bata damu data share su ba.
Yasmeen ce ta ƙariso bakin gadon ta zauna tana faɗin, "Haba TAIMIYYAH wai don girman Allah sai yaushe ne idan kin tuno su Abiee zaki daina kuka sai dai kiyi musu Addu'a? Don Allah ki sanyawa Zuciyarki cikakkiyar dangana,idan kin tuno su kiyi musu kyakykyawar Addu'a ne ita suka fi buƙata ba yawan kuka da sanya damuwa a rai ba.Gashi nan shiyasa har yau baki maida jikinki ba duk kin bi kin rame ba kamar da ba,ina sha kinma Yah Sadeeq alqawarin daina kuka duk idan kin tuno su yace kiyi musu addu'a ne don haka yanzu zan kira shi in ce gaki nan kina ta faman kuka."


Jin abinda Yasmeen ɗin tace yasa TAIMIYYAH saurin kai hannu tana share hawayen ta dubi Yasmeen da face ɗin tausayi kafin ta fara faɗin, "please! Yasmeen kar ki kira shi na bari wallahi,yanzu ma na kasa controlling tears ɗin ne shiyasa."


Yasmeen da tausayin TAIMIYYAH ya cika Zuciyarta sai ta gyaɗa kai tana faɗin, "Naji ba zan kira shi ba amma don Allah ki daure ki daina irin haka Baby Sis ɗina kinji ko?"


TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana ɗan sakin ƙaramin murmushin yaƙe jin sunan da Yasmeen ɗin ta kira ta da shi tamkar wata ƙaramar Baby.......✍🏻














Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._






#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *35*


Yau ya kama Friday tun misalin sha biyu da rabi TAIMIYYAH ta dawo daga Computer Skull.Lokacin data shigo gidan ta samu Yasmeen na Sasan Baba Sani don haka kai tsaye kayan jikinta ta cire ta nufi toilet don watsa ruwa.Duk da anyi ruwa da safe bai hana rana ƙwallarewa ba,shiyasa ɗan tafiyan da sukan yo daga cikin Class zuwa bakin gate ya gajiyar da ita,shiyasa da ta dawo tafi gane ta ɗan watsa ruwa sannan take jin daɗi.


Ta fito wankan kenan Yasmeen ta shigo ɗakin hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano.TAIMIYYAH ta dube ta tana faɗin, "Yasmeen me kuma kika samo a Sasan Baba Sani?"
Yasmeen ta aje kwanon a saman drawer tana faɗin,
" Awara ce Mero me aiki tayi ya bani sha'awa shine na amso a ɗanyenta,zan soya da kaina da Egg in masa sauce.


TAIMIYYAH ta furta, "Wow! Aiko ni ma zan ci wallahi,na rabu da cin Awara ma ni kam."


Kafin kowa ya sake cewa komi wayan TAIMIYYAH ya fara kiɗa,tuni ta gane Nass ne sabida a yanzu ringing ɗin data sanya masa na daban ne.Don haka ta ɗauki wayan tana faman narke murya basu wani jima suna magana ba ta aje wayan tana duban Yasmeen take faɗin, "Yasmeen Nass fa ya dage sai ya zo ni kuma ina tsoran wannan karon suyi arba da Baba Sani,ga Yah Deeku ma duk yau ɗin za su shigo weekend."


Yasmeen ta saki murmushi tana duban TAIMIYYAH take faɗin, "Waya ce miki zasu dawo yau? Lagos fa za su wuce don haɗo abubuwan Abiee da suke can,sabida za a fara zaman rabon gado don sauke masa nauyi,ina ga bama a gobe zasu dawo ba sai zuwa jibi,haka na ji Iyah suna waya da Baba Sanin bayan kin fita Skull ɗazu da Safe."


TAIMIYYAH sai ta tsaya tai shiru tare da faɗawa duniyan tunani, 'Yanzu har za a fara maganan raba gado?" Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani abu na son tokare mata maƙoshi, jikinta a sanyaye ta nufi wajen kayanta tana ciro rigar da zata saka.


Doguwar riga ce ta ciro na wata Atamfar Java Holland me kyau.Kalan red and black da akai wa ƙananun zane da kalan golden and green colour,ɗinkin free gown ne da ya yi mata mugun kyau,kaman yadda kalan ya haska farar fatarta.


Ta ɗaura ɗankwalin kayan tana ɗaukan Turarenta ta fesa kaɗan ta aje kwalban tana maida dubanta akan Yasmeen da ke ta faman bin ta da kallo,ta aika mata harara tana faɗin, "Wannan kallon fa Yasmeen sai kace baki taɓa gani na ba."


Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin, "Ke baki ga yadda ki kai kyau bane shiyasa,daga nan har zuwa lokacin da Nass zai zo karki sauya wannan shigan please,wallahi kayan sun amshi jikinki sosai Masha Allah!"


TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "Ke dai Yasmeen ba dama ne wajen iya ziga mutum,ni tashi mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login