Showing 18001 words to 21000 words out of 186776 words

Chapter 7 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6574

laluran ƙafanta,sosai kalan Hijab ɗin da yake dark Brown yai mata kyau,hannunta Qur'ani ne Izu Sittin ta aje sa daga saman kujera ta nufi ɗakin Iya,a bakin gado ta samu Iya tana ƙarisa shiryawa alamun wanka ta fito,ta durƙusa ƙasa tana gaida Iyan,Iya ta amsa da fara'a tana faɗin "Har kin kintsa zaki wuce ɗin TAIMIYYAH,to maza dai ki karya kafin ki tafi,ki kuma shiga ki gaida Baban ku Sani tunda jiya ya shigo kinyi bacci,idan su waɗancen sun shirya sai ku wuce tare ma kawai."


Da "Tuh." Kawai TAIMIYYAH ta amsawa Iya,tana juyowa ta fito zuwa falon ta nufi wajen cin abincin su inda Ladi ta gama shirya komi,Kunun tsamiya ta zuba a Cup ta saka Sugar tana juyawa,kafin ta aje ta buɗe kulan da aka zuba soyayyan Doya me egg ajiki,ta ɗibi guda 4 ta zuba a plate ta fara ci ahankali tana shan kunun,lokacin da ta kammala sai ta goge baki bayan ta ɗan sha ruwa,ta ɗauki Qur'aninta ta fito ta nufi Part ɗin Baba Sani,tana shirin shiga shima Yah Sadeeq da ya taho daga ɓangarensa yana isowa don shiga Sashin nasu,tunda TAIMIYYAH ta jiyo qamshinsa ta waiwayo tana sauke manyan idanunta akansa,ta saki murmushi kaɗan lokacin da ya ƙariso inda take,suna jerawa da juna zuwa cikin gidan,bayan ya amsa gaisuwanta ne ya amshi Qur'anin hannunta ya riƙe mata,a haka suka ƙarisa zuwa cikin falon gidan,su Zuhura da Basmah ne da alamun tashin su kenan,ko wanka basuyi ba TAIMIYYAH ta dube su tana faɗin "Sannun ku dafatan mun tashi lafiya,Basmah baku shirya ba ashe da har ina cewa zamu wuce tare."


TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana ɗauke kai daga dubansu,ganin kallon da Zuhura tai mata wai don ma Yayan su na tsaye a wajen ne,Basmah ta taɓe baki tana faɗin "Ai kinsan mu Malamin mu bai cika zuwa akan time ba zaki iya wucewanki,ma biyo bayanki."


Daga haka suka haɗa baki wajen gaida Yah Sadeeq ɗin,wanda hankalinsa na kan danna waya sai dai yana jin duk abinda suke faɗi,ɗago idanunsa yayi lokacin da yake amsa gaisuwan nasu,ya sauke idanun akan Zuhura yana faɗin "Oya ku tashi kuje ku sanyo Hijab ko bakuyi wanka ba ku tafi haka,tunda ku ƴan banzan yara ne da bakwa son zuwa makaranta,na baku mintuna goma kowacce ta fito cikin shiri shashashai kawai."


Yadda ya ƙare maganan da tsawa yasa su miƙewa,suka wuce fuu zuwa ɗakinsu don cika umurninsa,shi kuma ya maida dubansa kan TAIMIYYAH yana faɗin "Mu je Baby mu gaida Baban kafin su kintsa."


TAIMIYYAH bata ce komi ba ta fara takawa zuwa hanyan da zai sada su da falon Baba Sanin,a tare suka shiga bakinsu ɗauke da sallama,Umma da ke zaune tana facing ƙofar shigowa falon,ta ɗago idanunta ta sauke akan su,xuciyanta na bugawa da wani irin ɓacin rai,amma sai ta danne ta amsa sallaman nasu,TAIMIYYAH ta zube tana gaida Umman,Umma ta jefa mata harara tana amsa gaisuwan a wulaƙance,Sadeeq ma ya gaidata ta amsa tana jifansa da wani kallo da shi kaɗai yasan ma'anansa,Baba Sani ne ya fito daga ɗaki ganin TAIMIYYAH yasa shi sakin murmushi yana faɗin "Zainab idon ki kenan na dawo jiya ke kaɗaice baki min sannu da zuwa ba,lokacin da na shiga wajen Iya kuma kinyi bacci."




Ya ƙare maganan yana zama kusa da Umma,TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Baba kayi haƙury bacci ne ya ɗauke ni da wuri,ina kwana ka dawo lafiya."




"Lafiya lau Zainab,har anyi shirin Haddan ba sannu da ƙoƙari,ina fata su ƴan uwan naki sun shirya sarakan shiririta."




Cewan Baba Sani yana maida dubansa kan Sadeeq da ke gaida sa,TAIMIYYAH ta furta "Yanzu dai zasu shirya Baba."




"Okey! To Allah yayi albarka ya bada ilimi me anfani,zuwa dare zan tara ku akwai maganan da zanyi da ku don haka kar ki yadda ki bacci da wuri kinji Zainab." Baba Sani ya ƙare maganan da raha,hakan yasa TAIMIYYAH sakin murmushinta me faɗi tana bashi tabbacin zata jira,daga haka ta miƙe ta baro falon nasa ta bar Sadeeq ɗin aciki,saman kujera ta ɗosana mazaunanta tana kallon agogo,ganin lokacin na tafiya yasa ta saki ƙaramin tsaki,Yah Sadeeq da ya fito yana miƙa mata Qur'aninta,ganin har time ɗin su Zuhura basu fito ba yasa shi nufan ɗakinsu,ko mintu biyu baiyi da shiga ba sai gasu sun fito kowacce fuska a haɗe suna jefawa TAIMIYYAH mugun kallo,kaman yasan zasu iya mata wani iskancin a hanya,sai yace su jira shi ya ɗakko mukullin mota zai sauke su daga bakin hanya su ƙarisa cikin makarantan,tunda makarantan babu nisa yana da daga farkon shigowa layin su ne,aiko sam basu ji daɗi ba so sukai ya barsu su taka da ƙafafunsu,don su samu daman cin zarafin TAIMIYYAN akan hanya,amma sai Yah Sadeeq ɗin ya toshe wannan kafan,a bakin gate ɗin shiga ma ya sauke su yai tafiyansa,suka shige ciki kowacce ta nufi ajinsu,don TAIMIYYAH ta riga tai musu nisa sosai duka saura Izu huɗu ya rafe su haɗa a yaye su..........✍🏻












#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 9*


Misalin ƙarfe tara da dare Baba Sani ya tara su TAIMIYYAH a babban falonsa,cikin waɗanda ke wajen akwai Umma da Iya,sai Zuhrah da TAIMIYYAH sai Babban Yaya Sadeeq,dukkanin su yaran na zaune daga ƙasan Carfet ɗin ɗakin ,sai Iyayen da ke saman Kujeru.Baba Sani shiya buɗe taron da addu'a kafin ya fara maida dubansa akan Sadeeq wanda yake zaune kusa da shi sosai,ya soma da faɗin "Kai Sadeeq kai ne babba da kai zan fara,da farko sai muce Alhamdulillahi tunda Allah yai maka duk wani buɗi dai-dai gwargwado a rayuwa,tunda ga ka da babban aiki hannu ga kuma gini da saura ƙiris ya rage ka kammala,don haka ina muka kwana akan maganan fito da matar aure?Nayi ta zuba ido inji ka kawo min zancen aure amma shiru,daga baya saina fara tunanin ko ƴar gida za'ai tsakaninka da qanwan naka TAIMIYYAH ganin irin shaƙuwan da ke tsakaninku,amma nan ma banji kace komi ba,har gashi suma sun kammala karatu,me kake shiryawa ne ko ince me kake jira da har yanzu baka shirya aje iyali ba bayan kullum shekaru turawa suke."


Ya ƙare maganan da tsaida idanunsa akan Sadeeq,wanda shi kuma idanunsa na kan TAIMIYYAH wacce ta sake ƙasa da kanta tunda taji Baba Sani ya shigo da sunanta taji ƙirjinta ya shiga bugawa,Sadeeq ya ɗauke kai daga dubanta yana mayarwa kan Mahaifiyansa Umma,wacce tafi kowa tsare sa da ƙananun idanunta,tana kuma fatan kada ya bada ita wajen nunawa ubansa yana son TAIMIYYAN,ganin irin kallon da take masa yasa shi ɗauke idanunsa daga gareta ya mayar kan Baban nasa yana faɗin "Baba har yanzu ana kan neman matar ne,a kwanakin baya na so gabatar maka da wacce nake so,sai dai an samu saɓani tsakanina da ita wanda har na haƙura,yanzu ina kan nema ne da zaran mun dai-daita za'a ji na gabatar da ko wacece."


Yadda ya kai ƙarshen maganan cikin sanyin murya yasa TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa,tana me jin wani irin sanyi ya ratsa zuciyanta,don ba tayi zaton abinda zai faɗiwa Baban kenan ba,Umma wacce tafi kowa jin farin cikin amsan da Sadeeq ɗin ya baiwa Baba Sani itama sai da ta sauke numfashi,Baba Sani ya jinjina kai yana faɗin "To madallah,Allah yayi zaɓi mafi alkhairy ina nan ina sauraran ka,idan kuma ka tsaya ruwan ido ni da kaina zan maka zaɓi."


Baba Sani yai maganan da salon barkwanci wanda ya sanya har Iya murmusawa,kafin ya maida hankalinsa kan su TAIMIYYAH yana komawa Serious sosai,ya sauke ganinsa akan Zuhurah yana farawa da faɗin "To Zuhurah na dawo gare ki,kun kammala karatu kuma akwai manema wanne kika tsayar a cikin tarin maneman da kike tara min a ƙofar gida,kar ki ɗauka don ni ba mazauni bane bani da masu saka min ido akan duk wani motsinku,sanar dani wa kika tsayar kuma ɗan wani gida ne? Aure zan muku tunda ke kin kammala Diploma,ga wannan yajin aikin da ba'asan ranan komawa ba sai a aje batun cigaba da karatu a fuskanci auren don shine cikan mutuncin ku na ɗiya mace,don haka sanar dani waye gwanin?"


Ya kai ƙarshen maganan yana tsare ta da manyan idanunsa,wanda duk kusan gado sukai wajen Iya shiyasa hatta jikoki su TAIMIYYAH suka samu nasu kason na gado manyan idanu farare tas,Zuhurah ta ɗago ta dubi Baban nata cike da kame-kame ta fara faɗin "Umm! Baba ai duk masu zuwan ba da maganan aure suke zuwa ba,har yanzu dai ban ga wanda xuciyata ta aminta dashi ba tukunna dai."


Yadda ta kai ƙarshen maganan ya fusata Baba Sani ya soma faɗa yana faɗin "Maganan banza kenan kice duk samarin da kike tarawa babu wanda zuciyanki ta aminta da shi,to kina sauraransu da sunan shashanci ne kome? To ki sani ni bazaki maida ni mutumin banza ba,lallai ki tsaida mutum ɗaya ki turo min shi yazo ya sameni,idan kuma kinƙi zaki ga matakin da zan ɗauka a gaba."


Zuhurah ta gyaɗa kai tana faɗin "Tuh Baba." Baba Sani ya maida dubansa kan TAIMIYYAH wacce zuwa lokacin ƙirjinta ke wani irin bugu,sam bata son duk wani abu da zai janyo ai mata maganan aure,amma ta gama sarewa yau ɗin ba ta da wani mafita tunda Baba Sanin ƴar titsiye yake jin yi musu,tunaninta ya katsene a lokacin da muryansa ke shiga kunnuwanta yana faɗin "To Zainabu na dawo kanki,waye Surukin nawa?"


TAIMIYYAH ta sake ƙasa da kai sam ta kasa ɗagowa ta kalli kowa,cikin ɗan rawar murya take faɗin "Babu kowa Baba,ni bana kula kowa karatu nake so abar ni in cigaba,munyi magana da Abie zan cike form na wani Computer Training,kafin Asuu su janye Strike ɗin zan samu a ƙalla wata uku ina yi."


Daga haka tai shiru zuciyanta na cigaba da bugawa,tana me addu'an Allah ya ɗaurata akan Baba Sanin,Baba Sani da idon sa ke kan TAIMIYYAH ya gyara zama yana faɗin "Eh! Tuh ba zan ce ba za ki shiga ba tunda kina so kuma abu ne me kyau,sai dai ki sani fito da mijin aure shima abu me muhimmanci,me yasa bazaki baiwa manema daman da zasu zo gareki ba Zainab? Kada kiyi anfani da laluran da ubangiji ya ɗaura miki ki tauye kanki,akwai waɗanda laluransu yafi naki wasu ma sai dai aturasu a keken gurugu,wasu jan gindi suke suna tafiya yayinda wasu a nannaɗe suke sai an musu komi,kin ga ashe ke ɗin naki me sauƙi ne tunda babu abinda ya gagareki yi,don haka kamar yadda na sanar da Zuhurah ta fito da miji,kema lallai ne ki fara sauraran manema duk wanda hankalinki ya tsayu akansa ki turo min shi,kuma yaushe ne za'a fara Computer Training ɗin sai ku shiga tare da ƴar uwanki kuyi tare."


Baba Sani ya kai ƙarshen maganan idanunsa har lokacin na kan TAIMIYYAH,wacce sai a lokacin ta ɗago kanta tana duban sashin da Baba Sanin yake,kafin ta sake ƙasa da kanta tana faɗin "Insha Allah Baba za'ai yadda kace,maganan Training ɗin tuni anfara sai da form ni har na cike online ma yanzu zanyi Registration ne ranan Monday,tunda Abie ya riga ya bani kuɗin komi kafin ya wuce."


"Amma Zainab baki kyauta min ba,don me ni ba za ki dinga sanar dani abinda kike so ba,sai dai kima Sameer magana kina ganin ni idan kin tambayeni ba zan baki bane?"


Baba Sani ya jefawa TAIMIYYAH tambayan,muryansa na nuna ɓacin ransa matuƙa,hakan yasa TAIMIYYAH sake ƙasa da murya cike da ban haƙury take faɗin "Kayi haƙury ba haka bane Baba,kawai mun riga yin maganan dashi ne kafin ka dawo wannan satin nake so in sanar dakai dama,to da ya tambayeni abinda ake buƙata ne na faɗi masa sai kawai ya turo min kuɗin,amma ayi haƙury hakan ba zai sake faruwa ba."


Baba Sani ya gyaɗa kai cike da gamsuwa,da kuma yaba hankali da tarin nutsuwan TAIMIYYAN da sam yaransa basu samu ba,ya furta "Shikenan ya wuce amma karki sake Zainab duk abinda kike buƙata na karatu ne ko buƙatun yau da kullum ni zaki sanarwa ko Yayanku basai kin tambayi Sameer ba kinji ko?"


"Naji Baba kayi haƙuri hakan bazai sake faruwa ba." Cewan TAIMIYYAH muryanta can ƙasa,ta ɗago ido don duba ko Iya na cikin falon kuwa,don bata ji ko tarin ta ba tunda aka fara maganan,sai kawai idanunta suka sauka akan Yah Deekun da yake ta kallonta,yana ji a ransa inama Umma zata janye tsanan da takewa TAIMIYYAN da ayau zai miƙa ƙoƙon baransa wajen Iya da Baba Sani akan su bashi aurenta,sai dai ko kaɗan baya hango alamun risina a idanun Umman,TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke idanunta akansa ta mayar kan Iya wacce ke hakince tana kallo da sauraren komi,Baba Sani ya kalli Iya yana faɗin "Iya ko kina da abin cewa?" Iya ta gyara zama tana faɗin "O'o'o'oh bani da abin cewa sai dai kawai fatan Allah ya fito musu da abokan rayuwa nagari yai musu albarka,ya tsare mana su da mutuncin su tare da ɗaukacin ƴaƴan musulmi baki ɗaya."


"Ameen ya hayyu ya qayyum,Iya mun gode sosai da addu'a." Cewan Baba Sani kafin ya maida dubansa ga gimbiyar tasa yana tambayanta ko itama tana da abin faɗi,amma sai ta taɓe masa baki tare da girgiza kai alamun bata da abin cewa,hakan yasa Baba Sanin ya rufe taron da addu'a ya sallami kowa yace su je su kwanta,gobe kuma Zuhura ta tuna masa ya bata kuɗin Form taje ta siyo ta cike,ta amsa masa da "Tuh." Lokacin da suke tashi don barin falon nasa,Sadeeq bai tashi ba don Baban ya tsaida shi,kusan a jere TAIMIYYAH da Zuhurah suka fito daga falon Baban,Zuhura ta jefawa TAIMIYYAH wani kallo tana magana ƙasa-ƙasa yadda TAIMIYYAN kawai zata jiyo ta,ta soma faɗin "Wallahi ke baki isa ki jajibo wani shegen karatu kisa asakani yi dole ba,ni babu wani Computer Training ɗin da zan yi,ke karatu ya gani don kin rasa madafa inba karatun ba,tunda babu me zuwa ya taya ki ahaka kina gurguwa,ba dole ki ta jajiban karatu daga wannan ki faɗa wancan ba,sai kiyi tayi kila a yawon gantalin karatun kya samu ki haɗu da gurgun irin ki da zai kwashe ki,ko kuma ki samu wani ɗan wahalan da zaice zaiyi maneji dake mitsuww!" Ta ƙare maganan tana jan dogon tsaki ta wuce TAIMIYYAN fuu! Hakan yasa TAIMIYYAH bin bayan Zuhuran da kallo,ta saki wani murmushi me ɗaci akaron farko da Zuhuran taci fuskanta hawaye bai nemi zubo mata ba,ta riga ta ɗaukarwa kanta da Iya alqawarin ba za su sake ganin hawayenta don sun goranta mata ko sun kirata da kalmar gurguwa ba,ta cigaba da takawa tana baro Sashin na su,can ta hango Iya wacce ita ta ƙofan Falon Baba Sani ta fice bata biyo ta cikin gidan ba,hakan yasa kusan a tare suka isa Sasan Iyan da TAIMIYYAH.


"Zainab kin dai ji me Baban ku yace ko? To kaman yadda na sha faɗi miki ne,ki shiga hankalinki ki baiwa duk wasu masu son ki dama,ta hakane zaki fuskanci me ƙaunarki tsakani da Allah har ku fahimce juna."


Iya tayi maganan lokacin da TAIMIYYAH ke takawa don shigewa ɗaki ta kwanta,TAIMIYYAH ta waiwayo tana sauke idanunta akan Iya tare da gyaɗa kai,daga haka ta wuce ɗakinta don sosai take jin bacci,Iya tabi bayanta da kallo tana tuno wasu shekaru da suka shuɗe abaya....
Bari mu ji miye asalin waɗannan bayin Allan.
_______
Alhaji Amadu haifaffen garin Zaria ne,a wata anguwa da ake kira da Rimin tsiwa,tun asali ya taso da son karatun zamani dana addini,hakan yasa ya kasance me tsananin ƙwazo da maida hankali,har yakai matakin shiga jami'a inda ya karanci MASS COMMUNICATION,lokacin da ya kammala karatun bai wani jima ba ya fara aiki da gidan Radion tarayya da ke Kaduna,a lokacin ne kuma Allah ya haɗa shi da Fatima wato Iya kenan,ba'a ɗauki lokaci ba suka fahimci juna Iyaye suka shiga cikin maganan akai aure,Iya itama Iyayenta duk haifaffun Zarian ne suna zaune a anguwan Juma,lokacin da biki yazo sai ya kama mata haya a wani anguwa da ake jira Tudun Jukun a cikin birnin Zazzau ɗin,yana tafiya aiki Kaduna ya dawo duk ƙarshen mako ko kwanaki uku,Fatima wayayyace itama ƴar boko wacce ta kai matakin kammala Sakandiri Skull,sai dai daga matakin Sakandiri sam bata cigaba da karatun boko ba,sai ta dagewa zuwa islamiya na matam aure tana kwasan tarin ilimin addini,cikin shekaru biyar da auren su Allah ya azurta su da samun ƴaƴa uku,na farko me suna Sameer sai Sani sai mace me suna Bilkeesu,daga nan Iya bata sake samun haihuwa ba,shi kuma Alhaji Ahmad bai kuma wani auren ba,duk da a lokacin ƴan uwa sun sha zuga shi akan hakan,musamman lokacin da aka ga buɗi ya same shi yayi kuɗi har ga gina ƙaton gidansa a Gyallesu sun tare,amma yai biris ya maida hankalinsa akan gina rayuwan ƴaƴansa,da basu nagartaccen ilimin zamani dana addini,hakan yasa yaran suka taso da wani irin nagarta da tarbiyya me kyau,don Iya ta kasance jajirtacciyar uwa,mara wasa da ɗaukan wargi, ta tsayu matuƙa akansu har suka kawo lokacin girma,manyan mazan suka shiga jami'a ita kuma Bilkisu na matakin gama Sakandiri a lokacin,da yake ta taso da jikin girma da kyawun halitta wanda ta gado a wajen Iya ,sai manema suka fara mata sallama,ganin hakan yasa Alhaji Amadu cewa da zaran ta kammala Jarabawan kammala Sakandiri aure zai mata,ta cigaba da karatun a ɗakin mijinta,hakan ko ya kasance bata ɗauki dogon lokaci ba wani ya fito da aka aminta da shi me suna Ameenu,ɗan Zaria ne amma yana aiki a Kano,aka sanya lokaci kaɗan akai bikinsu tare da kai Amarya Kano,su kuma su Baba Sani aka cigaba da karatu,lokacin da suka kammala karatu kowa ya fara kawo ƙarfi don suna sana'a bawai bokon suka tasa agaba ba,musamman Sameer yafi ɗan uwansa son nema da dogaro da kai,kuma cikin sa'a duk abinda yasa agaba sai ya samu buɗi,bayan sun kammala bautan ƙasa ne Allah ya haɗa shi da Zainab,wata irin kyakykyawan budurwa me tarin hankali da nutsuwa,anan ƙasan layinsu take gidan da ake riƙonta,don asalinsu ƴan Daura ne katsinawa,aure ya kawo Yayarta Zaria da take kira da Anty Mardiyyah shine take riƙonta,tunda Sameer ya ƙyalla ido akanta su Iya basu sake ganin nutsuwansa ba,har sai da Allah ya nufi aurensu da ita,wani irin soyayya suke gwadawa juna na ban mamaki,lokacin da akai musu aure Zainab da ake kiranta da TAIMIYYAH a gidansu tana matakin Degree

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login