Showing 33001 words to 36000 words out of 186776 words

Chapter 12 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6625

ga Suhailah wanda yake jin idanunta na yawo akansa,yai mata kallo ɗaya yana ɗauke kai ya mayar kan Hajjah yana faɗin "Hajjah ina fata tayi miki bayanin yadda sukai da Dakta? Sakamakon da nake ta guje mata shine ke shirin faruwa,domin a yadda scaning ɗin da akayi ya nuna magungunan da tasha sunyiwa mahaifan illan da zata iya rasa haihuwan ma baki ɗaya,kaman yadda na faɗi tun farko yanzu zan maimaita agaban idanunki Hajjah,bazan iya zama da macen da bazata iya haihuwa ba,don ina buƙatan ganin ƙwaina a duniya idan ko har zamu cigaba da zaman aure da Suhailah tabbas tana da buƙatan abokiyan zama,don a yanzu bamu da tabbacin zata samu haihuwa ko bazata samu ba,zan nema mata Visan zuwa Cairo nan da sati biyu zuwa uku zamu ga wani likitan da aka sanar dani ƙwararre ne,idan har muka je muka dawo aka sake tabbatar da cewa ta samu illa,to daga lokacin ni kuma zan fara neman irin macen da zan iya rayuwa da ita akaro na biyu."


Yadda ya ƙare maganan cikin tabbatar da dukkanin kalamansa babu wasa a ciki,sai Suhailah ta saki kukan da take riƙewa,Hajjah kuma ta tsura masa idanu tana hango tsantsan gaskiyan da ke cikin idanunsa akan dukkanin kalaman da ya furta,kafin tayi magana tana faɗin "To Maleek naji dukkanin kalamanka ka kuma yi tunani me kyau,gara ka ɗauke ta ku je can ɗin kada ma ta fara anfani da magungunan da aka rubuta anan ɗin,ajira har kuje can ɗin aga me bincikensu zai nuna,maganan ƙarin aure bazan iya cewa komi akai ba sai dai ince a yanzu addu'a shi yafi,daga mu har kai mu nemi Allah yai ikonsa ya tabbatar mana da dukkan alkhairy,Suhailah ta riga da tayi kuskure don bazamu kira abinda ta aikata da sunan ƙaddara ba,sai dai mu jingina shi da irin ƙaddaran da mu hausawa muke faɗi na son zuciya,wanda idan muka aikata son ranmu abu mara kyau ya biyu baya sai muyi ta kiranshi da ai ƙaddarace,amma idan muka aikata abinda muke so muka samu kuma biyan buƙata to anan ba Allah ne ya ƙaddara ba,don haka ina addu'a da fatan Allah yasa asamu mafita ya zamo ba kinyiwa kanki illah bane Suhailah."


"Ameen Hajjah." Cewan Maleek yana maida dubansa kan Suhailah,wacce ta kwantar da kanta ajikin Hajjah tana cigaba da kuka,cikin low voice yake faɗin "Tashi mu wuce gida."


Suhailah ta sake lafewa a jikin Hajjah tana faɗin "Please Yah Maleek ka barni anan sai dare sai ka zo mu wuce."


"Idan na fita daga nan bazan sake shigowa ba,sai dai idan kin kai daren Shehu ya maidaki gida,ki kuma tabbatar da ansamar min tuwan Semo da miyan kuɓewa for Dinner,bana son ƴan aiki su sanya hannunsu aciki okey!"


Ya ƙare maganan yana miƙewa tsaye,ya maida idanunsa akan Hajjah yana faɗin "Hajjah zan wuce ina so zan je can Samaru wajen Baba Ali,ya kira yana nema na." Hajjah ta gyaɗa kai da furta "Hakan yayi ka gaida shi idan ka je ɗin,ina ga akwai ƴan Nasihu da zai maka ne da kuma tayaka murnan samun wannan muƙami,tunda kasan jikin girma ƙafafun sun matsa masa baya son yawan fita sai dai a bisa,so nake ma idan ka natsa shima a fitar da shi yaga likita."


"Nima nayi wannan tunanin Hajjah,India zamu fita ni da shi insha Allah bari dai in sake samun nutsuwa in shiga sabon office ɗinnan sai mu ga abinda zai yiwu." Cewan Maleek yana kai hannu ya zaro wayansa daga aljihu da ake kira,Hajjah kuma ta amsa da faɗin "To madallah,Allah ya cigaba da dafa maku yayi albarka."


Maleek ya amsa da Ameen yana kai wayansa kunni,ya fara takawa don barin falon,Suhailah tabi bayansa da kallo wani zazzafan son sa na sake keta ilahirin jinin jikinta,ta maida idanunta ta lumshe qamshinsa da ya barwa falon na ratsa kafofin hancinta.


________


"Zuhurah ni kam ina Sister ɗinnan taku me matsalan ƙafa?"


Laurat da take autan Ummman su Zuhurah ta tambaya,idanunta akan Zuhuran da rabin hankalinta ke kan chart ɗin da take yi da sabon saurayinta Ameeru,ta ɗago idanunta ta mayar kan Laurat ɗin tare da taɓe baki tana faɗin "Wai TAIMIYYAH,tana can Sasan Iya mana."


Laurat ta jinjina kai tana faɗin "Allah sarki,wallahi tausayi take bani gashi dai Allah yai mata baiwan halitta amma an rageta ta ɓangaren laluran ƙafa,yanzu bata shigo muku hira kenan,na ga tun jiya dana zo har yau ban ga ta shi go ba." Laurat tayi maganan tana kallon Zuhurah,kafin Zuhurah ta bata amsa Basmah da ke zaune tana sauraransu tayi zaraf tana faɗin "Taɓ! Tun wani zamanin ai Iya ta hanata shigowa,hakama Umma kinsan Umma ta tsaneta muma haushinta muke ji,komi ace ita don anga ta fimu kyau."


Basmah tayi maganan tana wani taɓe baki,hakan yasa Laurat sakin baki tana kallonta,kafin ta furta "Kai! Basmah to miye abin haushi don ta fiku kyau,kuma banda abin Anty Zuwaira miye aibun yarinyar don ta kasance gurguwa har da za'a tsaneta?"


Wannan karon Zuhurah ce ta dubi Antyn nasu Laurat,wacce auta ce a wajen su Umman da ita kaɗai ta rage batai aure ba,ta girmi Zuhurah sosai a ƙallah zatai shekaru ashirin da takwas don dai Allah bai kawo lokacin aure bane ake zaune har yanzu ba'ayi ba,cikin taɓe baki Zuhuran ke faɗin "Hmm! Anty kenan don baki san yadda tsowuwar can ke nuna bambamci tsakanin mu da TAIMIYAH bane,don kawai anga Abie ɗinsu yafi Baban mu kuɗi,sannan ƙarin abin haushi wai da ita Yah Sadeeq yake so har yana iƙirarin ita zai aura,sai da Umma tace zata tsine masa idan bai janye maganam ba shine fa ya haƙura,don Allah kamar Yah Sadeeq me zaici da gurguwa ko min kyanta? Mitsuww...!"


Zuhurah ta ƙare maganan tana jan wani mugun tsaki,ita ko Laurat tai ƙuri da ido tana duban Zuhuran cike da mamakin yadda duk ɗabi'unsu suka canza,domin ta daɗe bata kawowa Anty Zuwairan ziyara ba,ta buɗe baki tana faɗin "Zuhurah ku bi ahankali,wallahi shi Allah ba'a masa haka domin shi yaso maida ta hakan,tunda ke shaida ce tare kuka taso tana tafiyanta qalau dare ɗaya Allah ya aiko da laluran dayai silar komawarta gurguwan,miye laifinta aciki?Kuma miye aibun kasancewanta a hakan da har zakuce ba ku son ta da Sadeeq,ni banga wani aibu ba domin shi soyayyah Allah ke jarabtan bawa dashi kuma babu ruwansa da duba tsarin halitta ko nakasan mutum,amma ina baku shawara ku bi ahankali domin in mutum yasan farkon sa baisan ƙarshe ba,yanzu na gane abinda ya sanya ta daina shigowa,kenan kuna mata gori da cin fuska kenan?"


Yadda Anty Laurat ɗin tai maganan cike da jin zafinsu,yasa daga Basmah har Zuhurah tashi tsam suka bata waje,don sun san ita bata ɗaukan raini yanzu zata ci mutuncinsu,ta girgiza kai kawai tana bin su da kallo har suka shige ɗakinsu,sai itama ta isa Bedroom ɗin Umma wacce tun safe ta fita wai zata ɗakko kayanta da suka iso na sayarwa daga park,sabida ta fara business ɗin sai da kayayyaki irin su atamfofi da kayan yara,ana turo mata daga Lagos shine tunda ta fita har yanzu bata dawo ba,Laurat ɗin ta zari mayafinta ta yafa,tana fitowa daga Sasan nasu Zuhurah kai tsaye ta nufo Sasan Iya,don ita dai tunda daɗewa TAIMIYYAH tana mata kyau tana kuma bata tausayi tunda laluran ƙafanta ya sameta,wayanta riƙe a hannunta take ratso Compound ɗin gidan har ta iso Sasan Iyan.......✍🏻










Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*




_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻


https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb


*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.


*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.


*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.


A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


--------


Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:


*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*


Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.






#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 18 to19*


_______Da sallama Anty Laurat ta shiga Sasan Iya,wacce suke zaune daga waje saman lallausan Carpet da takan shinfiɗa ta zauna tana bitan karatun Qur'ani duk kusan yamma,daga gefen Iyan Ladi ce zaune itama tana gyaran farce daga gefe guda,Iya da Ladin kusan a tare suka amsa sallaman Laurat ɗin,wacce ta ƙariso ta zube gaban Iya tana kwasan gaisuwa,Iya ta amsa da fara'a tana faɗin "Maraba da Lauratu saukan yaushe,ya mutanan can Yoben ina fata duk iyayen na ku nanan lafiya ko?"


Laurat tayi murmushi tana faɗin "Lafiya Iya duk sunce a gaida ku,wallahi jiya na zo naso shigowa sai dare yayi ga gajiyan zaman mota,shine sai yanzu nace bari in shigo in miƙo gaisuwa,ya TAIMIYYAH hala bata nan ne ?" Laurat ta ƙare maganan da tambayan Iya,Iya ta murmusa tana gyara zaman glass ɗin da take anfani dashi idan zatai karatu sabida ƙara ƙarfin gani,ta amsa da faɗin "Tana nan ta ƙule a ɗaki tana karatu hala ko ana faman danne-dannen waya da bakwa gajiya ku yara." Laurat ta saki murmushi tana faɗin "Allah sarki to bari in shiga daga ciki mu gaisa ankwana biyu ba'a haɗu ba."


"Hakane kam ƴarnan shiga ku gaisa ai kin kyauta da kika taho zumunci."


Cewan Iya tana bin bayan Laurat ɗin da kallo,wacce ta nufi ƙofan shiga falo,Iya na yaba nutsuwan Laurat ɗin da hankalinta,wacce har Iyan ke ji Laurat ɗin tafi kwanta mata arai ma akan Surukan nata Umma,da sallama Laurat ta shigo falon Iya tana sake ɗaga murya da kiran sunan TAIMIYYAH,ita ko TAIMIYYAH na can daga cikin ɗakinta tayi ɗai-ɗai suna kwasan Vid call da qanninta su Nahar,tana ta biye musu suna bata labarin Lagos da irin wajajen da ake kaisu na shaƙatawa duk Weekend,can sama-sama take ji kaman ana kiran sunanta hakan yasa tai sallama da su Nahar tana cewa zata kira su later,ta aje wayan tana miƙewa ta sauko daga Bed ɗin,tana sanye ne da wani gown me kyau na Material da akaima ɗinkin da ya amshi jikinta sosai,ta dafa ƙafanta tana takowa zuwa falo,idanunta ya sauka akan Laurat da ke zaune daga hannun kujera,ai da hanzari TAIMIYYAH ta ƙariso cikin falon,tana faɗin "Laaah! Anty Laurat ce yau a gari,sannu da zuwa saukan yaushe Anty?"


Laurat ta saki murmushi ta kasa ɗauke idanunta daga kan TAIMIYYAH,tana ganin yadda TAIMIYYAN tai wani girma kyawunta ya ninka na da,domin a ƙallah zai kai shekaru uku rabonta da ganinta,har TAIMIYYAH ta ƙariso kusa da ita idanunta na kanta,tana jinjina baiwa da ƙudiran ubangiji wanda ya ƙagi wannan kyakykyawan halitta,hannu ta miƙawa TAIMIYYAN suka cafke Laurat ɗin na faɗin "Wow! TAIMIYYAH haka kika koma wata Big Gal,kinga yadda kika sake zama wata haɗaɗɗiya ta musamman gaskiya ke ɗin matan manyace,Allah kaɗai yasan meyasa ya ɗan tauyeki kaɗan."


TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Anty kenan ina yini kin zo lafiya?"


Laurat ta amsa da "Lafiya lau Zaynab ya bayan rabuwa."


"Alhamdulillah! Anty sannu da zuwa,bari a kawo miki ruwa ko."


Cewan TAIMIYYAH tana yinƙurin miƙewa tsaye,Laurat tayi saurin dakatar da ita da faɗin "Wallahi zauna abinki bana jin ƙishi,tun jiya fa na shigo garin nanne bansamu shigowa ba sai yanzu,ya karatu ana ta strike kuma Allah dai ya kawo ƙarshensa,ko da yike Zuhurah tace duk kun gama sai jiran a koma ku ɗaura daga inda kuka tsaya,tuh Allah ya taimaka in kuma Allah ya kawo miji sai mu sha biki kawai ba."


Yadda Laurat ɗin ta kai ƙarshen maganan yasa TAIMIYYAH sakin dariya kawai,ba tare da tace komi ba Laurat ɗin da yake gwanar iya hirace,ita ke ta janyo zance har TAIMIYYAH ta sake suna ta hira,sai kusan biyar ta bar Sasan Iyan tana cewa TAIMIYYAH zuwa anjima don Allah ta shiga can Sasan ayi hira,domin ita har ga Allah ƙaunar TAIMIYYAN take ji da zuciya ɗaya,dariya kawai TAIMIYYAH tayi don tasan Iya ma bazata bari ba,uwa uba ita kanta ma bazata shigan ba,don tasan ƙarshenta da ɓacin rai zata fito Sasan,ita ko a yanzu babu abinda take tattali irin farin cikinta,shiyasa gaba ɗaya ta ɗauki duk wata soyayya da takewa su Zuhuran da qawazucin su ta adana shi can ƙasan zuciyanta,babu abinda take so da ƙauna da bashi muhimmanci a yanzu irin karatu,ga kuma wayanta da ke ɗebe mata kewa tana karance-karancenta masu muhimmanci da take ƙaruwa dasu,ga groups na karatuttukan manyan malamai da ake turowa suna sake wayar da kanta da samun tarin ilimi,shiyasa ko kaɗan yanzu zaman kaɗaici baya damunta,ko da Anty Laurat ɗin ta tafi ma ɗaki ta koma ta kunna karatun Qur'ani cikin suran da zata kai hadda sati me zuwa,tana saurara har akai kiran sallan magriba,sannan ta kashe karatun da yike tana period ba sallan zatai ba kawai sai ta fito zuwa Kitchen,tana jin sha'awan cin wainan fulawa ko Pancakes,don ita idan tana al'adah komawa take kaman wata me yaron ciki,bata iya cin abinci sosai sai kwaɗayi kala-kala, buɗe can rufe can tana tunanin me xata ƙaƙala tayi,har dai zuciyanta ya tsayu akan yin wainan fulawan,hakan yasa ta ɗebo fulawan ta tankaɗe ta jajjaga tarugu da albasa kaɗan,haɗi da yanka albasa me dama ta zuba a kwaɓin,ta fasa egg guda biyu ta zuba spices da maggi ta motsa sosai,sannan ta ɗaura nonstick pan ɗinta a wuta,manja ta zuba me bala'in kyau irin wanda ake kawowa Iya daga Lagos,nan da nan qamshi ya fara tashi na suyan wainan fulawan,already tana da dakakken yajin da take dakawa da kanta tana ajewa,don ita Iya bata cin yaji sam TAIMIYYAN ma da take so kullum cikin yi mata faɗa Iya take,qamshi ne ya ishi Iya da ke zaune a falo ta ɗaga murya tana faɗin "Wai ni kam me kike soyawa ne haka TAIMIYYAH?"


TAIMIYYAH da ta gama arranging wainan fulawan cikin plate ta wani zubo yaji daga gefe,sai qamshi ke tashi ta fito hannunta riƙe da plate ɗin,ɗaya hannun na dafe da ƙafatan tana takowa har zuwa cikin falon,sai lokacin ta saki murmushi tana duban Iya take faɗin "Iya wainar fulawa ce fa kawai na ɗan soya,in matso mu ci ne tare na ga cewa kike ke bata dame ki."


TAIMIYYAH tayi maganan tana sakin dariya,ganin irin hararan da Iya ke aiko mata,kafin Iyan ta furta "To sai dai naci wannan irin qamshi haka,wallahi raina ya biya maza matso da shi ince ko ɗaya ne,ai da ne dai nake cewa bata dameni ba,amma banda yanzu da kika ɗanɗana min irin wannan haɗin daɗin da kike masa." TAIMIYYAH tana dariya ta ƙarisa gaban Iya suka fara ci tare,Iya me cewa zata ci ɗaya sai ga shi ta tada guda uku tana faman santi,me TAIMIYYAH xatayi inba dariya ba,Ladi aka rage ma guda biyu TAIMIYYAN ta fita kai mata ɗakin ta,ita kuma Iya ta shige ɗaki don gabatar da Sallan isha'i,TAIMIYYAH ɗaki itama ta shige bayan ta dawo kaima Ladi wainan fulawan,ta ɗauki wayanta tana turawa Abie saƙon Text Message akan tana son ya siya mata sabuwan Laptop,amma samfurin Apple take so,can zuwa anjima kaɗan kawai taji alert ya shigo wayanta na kuɗi masu kauri,sai kawai ta shiga kiran line ɗinsa,buga biyu ya ɗaga da yake vedio call ta kira,yana ɗagawa idanunsa suka sauka akan ƴar nasa da yake matuƙar jinta cikin zuciyansa,domin duk idan ya ɗaura idanunsa akanta Zaynab ɗinsa yake gani,wata ƙwayan mace guda ɗaya da bazai taɓa iya haɗa soyayyanta dana kowace ɗiya mace ba "I miss u Abie ka rabu da shigowa Zaria." Muryan TAIMIYYAH ya shiga kunnuwansa,ya sauke numfashi me sanyi yana duban ɗan ƙaramin bakinta da ya iya shagwaɓa,ya saki murmushi sosai yana faɗin "Miss u too Zayab,na ga saƙon ki ina fata kinji alert?"


Yayi maganan idanunsa akanta,ta sake narke masa da shagwaɓa tana faɗin "Eh Abie naji nagode,Allah ƙara buɗi yasa kafi haka, idan Yah Sadeeq ya dawo shi kawai zan baiwa kuɗin ya siyo min."


"Hakan yayi Daughter ina Iyan taki take,hope duk kuna lafiya zan shigo garin zuwa next week insha Allah,har kin fara zuwa Cimputer skull ɗin kenan?"


TAIMIYYAH da ke sauraran Abie ɗin amma bata kalli face ɗinsa ba ta furta "Lafiya lau Abie Iya tana sallah ne,skull kuma sai monday xa'a fara ina so ne kafin afara na mallaki Computern yadda duk abinda aka koya mana zan zo in sake gwadawa a nawa."


"Gud gal! to Allah ya taimaka ki gaida Iya ai munyi waya ɗazu bye zan amsa wani call."


Daga haka yai cuting call ɗin,TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya tana jin ƙaunar Abie ɗin me girma a cikin xuciyanta,duk da basu da shaƙuwa me zurfi tsakaninta da shi,amma ita da kanta ta san yana son ta sosai domin idanunsa basa iya ɓoye hakan,wanda Iya tasha gaya mata cewa Soyayyar da yakewa Mamanta dole ya shafeta don yayi mata wani irin so me wuyan misaltawa,ashe rayuwansu bazai yi tsayi tare da juna ba,ta lumshe idanunta tana jin inama ta taso tare da wannan uwa nata,sai dai ko kaɗan bata maraici don bata ma san daɗinta ba tunda bata rayu da ita ba,Iya itace ta taso ta gani a matsayin uwarta,sai dai har kullum Iya ta kwaso pic ɗin Maman nata tana jimawa riƙe da shi,tana kallon tsantsan kaman da suke da juna,hatta a wayanta tayi snaping copys ɗin hotunan marigayiyan da yawa,ta adana lokaci zuwa lokaci takan shiga folder ɗin tai ta kallon kyakykyawan fuskan mahaifiyan nata,to a yanzu ma da son ganin pic ɗin ya motsa take ta shiga ta danno pics ɗin tana gani ɗaya bayan ɗaya.
_________


*9:40pm*


A.Maleek Ado ne zaune daga cikin falon da ke upstairs,yayi zaman dirshan don cin tuwan Semo da ya sanar da Suhailah yana so,daga gefensa Suhailan ce zaune sanye da wani pencil skat da Riga me siririn hannu,sosai kayan sukai mata kyau ƙirjinta ya fito sosai ta saman rigan,idanunta har lokacin basu gama wartsakewa daga uban kukan da ta sha a yau ɗin ba,loman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login