Showing 150001 words to 153000 words out of 186776 words

Chapter 51 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6584

gata da kulawa a hannuna, babu me cewa bani na kawo ta duniya ba,gaba ɗaya ta manta da uwarta sai dai idan ta ganta a hoto.Na sanya ta makaranta mafi tsada na boko da islamiya, babu abinda ta nema ta rasa,maraicin uwa ma bata san shi ba don yadda na ke ji da ita ko Hauwa na raye iyakar gatan da za ta bata kenan.
Lokacin da ta girma ta zama budurwa ne na fara lura da zuciyarta ya fara karkata akan Maleek,sabida yadda take gaza nutsuwa idan ya zo gari.Na cigaba da sanya mata ido har na tabbatar da hasashena gaskiya ne, soyayyar ɗan uwanta me zafi ne ya kama zuciyarta,shi kuma wanda ake yi dominsa bai ma san tana yi ba,sabida sam ba yi shiga harkarta sabida ita akwai surutu da rawar kai, shi kuma miskili ne mara son hayaniya,tana shekaran farko a jami'a na tirketa akan ta gayamin gaskiya, idan son Maleek ɗin take yi da gaske kuma za ta iya aurensa,aiko Suhailah babu kunya ta sanar min shi take so,amma sai ta roƙeni akan kada in faɗi masa, sabida tsoransa take ji sosai,don ba ya sakar mata fuska ko kaɗan.
Ni na san yadda nayi da rarrashi da ban baki har na ciyo kan Maleek ya amince zai aure ƴar uwarsa, kuma ƙanwarsa Suhailah,ba don yana jin sonta a zuciyarsa ba ,sai don kawai yayi min biyayya a matsayina na mahaifiyarsa, da ba ya iya saɓa abinda na ke so.
Ba a ja lokaci ba manya suka shigo cikin maganar,mahaifin Suhailah ya fi kowa murna da wannan haɗin,yayin da su ku ma dangin Maleek suka sake ɗaukar zafi damu.Sabida sun so su yi masa tallan yaransu ƴan mata ya aura ,sabida kwaɗayin dukiya sai dai basu ga fuska a wajen Maleek ɗin ba, bare kuma ni da sam na daina shiga sabgar su sai abinda ba a rasa ba.
Haka akai bikin Maleek da Suhailah suka tare a danƙareran gidan da Maleek ɗin ya gina a GRA. Duk wanda ya je ya ga irin daular da ke cikin gidan Suhailah sai yayi mata murna,dangin ubanta su kai ta santin gida da murnan cewa ƴar su ta samu gidan daula,masu hassada kuma su kai tayi mu dai bamu san ma suna yi ba.
Suhailah ta cigaba da karatunta a ɗakin mijinta,amma ma fi zamanta yafi ga gida na,sabida Maleek baya zuwa sai duk bayan sati uku. Ita kuma Suhailah bata son zaman kaɗaici, hakan yasa yana tafiya za ta tattaro ta dawo min gidana,sai da nayi da gaske na samar mata ƴan aiki, da kuma ma'aikatan da Maleek ya zuba maza a gidan,da mai gadi,sannan ne Suhailah ta haƙura ta fara zama ita da ƴan aiki a gidanta. Anyi auren da shekara ɗaya mahaifin Suhailah ya rasu shi ma,ta zama cikakkiyar marainiyar da babu uwa ba uba.
Shekararsu biyar kenan zasu shiga da aure,amma Allah bai bada haihuwa ba,wannan shine taƙaitaccen tarihina dana iyali na Hajiya Fatima."


Hajjah ta kai ƙarshen labarinta tana duban TAIMIYYAH da Iyah da ke saurararta,Iyah ta numfasa ta ce, "Allah sarki,Allah Ubangiji ya yi musu rahama tare da na mu iyayen da ƴan uwa musulmi baki ɗaya."


Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Kafin ta sake amsa gaisuwar da TAIMIYYAH tayi mata, na rashin mijinta da ƴar uwarta,ta dubi TAIMIYYAH cikin ido wacce ta fara gano in da Hajiya Aysha ta dosa,don sunan Maleek da ya shigo cikin labarinta ya bata tabbacin cewa ba kowa bane ya zo wajenta sai ɗan Hajiya Ayshan.


Hajjah ta cigaba da duban TAIMIYYAH tana zayyane musu, yadda suka yi da Maleek akanta,tun daga maganar da tayi masa akan cewa ya zo ya ga TAIMIYYAR,har kawo yadda suka yi da shi a jiya kafin ya bar gari,ta ƙare maganar da cewa, "Zainab Maleek ɗa na ne, wanda shi kaɗai na mallaka a duniya, na so ace ina da wani ɗan wanda bai taɓa aure ba, sabida in saka shi ya zo ya nemi aurenki,amma ba ni da kowa sai Maleek. Shiyasa shi ɗin dai na ke da burin ya sake samun nagartacciyar mace me tarbiya a karo na biyu,ina fata za ki amshe sa a matsayin miji,ba tare da kin yi la'akari da aurensa ko dangantakar da ke tsakaninsa da matarsa ba,Maleek ya kamu da ƙaunarki ne tun lokacin da yake mafarki da me irin siffar idanunki,bai gane hakan bane sai a shekaranjiya da ku kai ido huɗu da shi,daga yana yin da ya dawo min a gigice, da irin kamalaman da yake yi akanki,na gano tarin ƙaunarki da ya taso daga can ƙasar zuciyarsa ya bayyana kansa. Zaynab ina fata za ki amince mu haɗa jini da ke,domin ɗorewar zumunci da samun iri me kyau daga gare ki.Ina miki albishir da cewa Maleek zai riƙe ki da amana,zai kuma zame miki mijin marainiya kamar yadda ya ke shi ma maraya.Sai dai banzo nan don na tirsasa zuciyarki ta amince da abinda baki da ra'ayi akai ba,idan har kin ji baki son Maleek, ba za a yi miki dole ba,Hajiya ina fata ke ma za ki amince ɗan ki ya zama surukinki idan Allah ya yi nufin kasancewar hakan?"


Hajjah ta ƙare maganar tana duban Iyah,wacce tayi sakato tana duban Hajjahn,ta rasa ma me zata ce sai da ƙyar tayi ƙarfin halin faɗin, "Hajiya na rasa da wani baki zan bayyana irin ƙauna da alkhairin da kike nufin wannan yarinya da shi,tabbas idan har Zainab ta amince da ɗan mu zan yi farin ciki mara misaltuwa,babu abinda zan ce dangane da wannan lamari, duba da irin mafarkin da yaron ya fara yi tun farko,don Allah kaɗai ya san me ya ke nufi da hakan,sannan haɗuwar mu da ke da bayyanar TAIMIYYAH, a matsayin wacce yaron ki ke mafarki da wani ɓangare na siffarta, shima babban lamari ne da sai dai mu bi da addu'a,kar ki damu Hajiya idan har yaran suka fahimci juna, ina baki tabbacin zan shige gaba wajen ganin an ƙulla alkhairy ,in dai har zai riƙe min jika da amana ya kare mata martabarta,su kuma zauna lafiya da matarsa,to ni bani da haufi domin me sonka da gaskiya ne zai so ɗansa ya haɗa zuriya da naka,babu abinda zance miki sai godia akan ƙauna da tausayin da kike nunawa Zaynab."


Iyah tayi maganar har muryarta na ɗan rawa,TAIMIYYAH kuwa ƙasa ta yi da kanta, ƙirjinta na wani dokawa da yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.Hajjah ta dubi TAIMIYYAH cike da ƙauna ta ke cewa, "Ƴa ta tashi ki je daga ciki na ga alamun kin shiga ruɗani,za mu gama magana da Iyah amma ina roƙarwa Maleek alfarma, a riƙa ɗaga wayarsa idan ya kira,sabida shi mutum ne da bai iya saka abu ransa da sauƙi ba,ina fata tsoro ya kau tunda kinji waye shi, daga ina kuma ya ke,so please ki ɗauki wayarsa ki sauraresa, ta hakane za ki gane idan za ki iya amincewa da shi,Allah ya yi miki albarka ya kuma haɗa zuciyoyinku ke da shi Zainab."


Hajjah ta ƙare maganar tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,wacce ta ke takawa a hankali tamkar wacce ƙwai ya fashemawa a ciki,sabida yadda zuciyarta ke cikin wani irin ruɗani da kullewar kai..........✍🏻














#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*61*


Kwanakin Hajjah biyar da xuwa gidansu TAIMIYYAH,ya kama ranar Friday. Misalin ƙarfe takwas na dare, Baba Sani ya shigo sasan Iyah don gaisheta, kamar yadda ya saba duk sanda ya dawo weekend.


Bayan sun gama gaisawa da Iyah,ita ma TAIMIYYAH ta fito suka gaisa sai ta koma ɗakinta,kamar yadda ta saba don basu waje shi da Iyah su zanta,Iyah ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Baba Sani, kafin ta fara da cewa, "Sani za ka iya tuna labarin Hajiyar nan me kirki dana baka,wacce suka kaɗe Zainab wata ɗaya da ya wuce?"


Baba Sani ya gyaɗa kai yana cewa Iyah, "Eh Iyah na gane ta, wacce ki ka ce har ta zo nan gidan ranar walima,har ta baiwa TAIMIYYAH ɗankunnin gwal ko?"


Iyah ta yi saurin faɗin, "Eh tabbas kuwa ita nake nufi Sani,to ita ce ta sake dawowa yau kwanaki biyar kenan,sai dai wannan karon ta zo da wani lamari me girma ne......"


A hankali Iyah ta zayyanewa Baba Sani yadda suka yi da Hajjah,da kuma wayar da Maleek ɗin suke yi da TAIMIYYAH,don tun daga ran da Hajjah ta zo ta tafi ,ya maida kiran TAIMIYYAH a waya tamkar ibada,tun tana wa Iyah ƙorafin ya faye naci da miskilanci,har Iyah ta gaji da jin ƙorafin ma ita,Iyah ta kai ƙarshe tana cewa maganar da cewa, "To ka ji yadda muka rabu da ita, don haka ina so daga yau zuwa jibi ka bincika can Family House ɗin nasu, don a ji ya ya mu'amalarsa da danginsa ya ke? Sannan kuma ka binciki abokanan Sameer na kusa,waɗanda da ke can Lagos don a binciki halayyar Maleek ɗin da abokanan aikinsa,tunda shi ma duk wajen da marigayi yayi aiki yake,sai dai shi Hajiya tace a ɓangaren shiffin board yake,wanda a yanzu haka ma shi ke riƙe da kujeran chairman na shiffing board gaba ɗaya."


Baba Sani ya jinjina kai cike da mamakin wannan lamari ya dubi Iyah ya ce, "Ai Iyah wannan abu ya kwana gidan sauƙi ,in dai ɗan magariya former Assitant Controler ne da na sani, Yaron Alhaji Ado Ibrahim da family House ɗinsu ke lowcost, ai maƙotan abokina Alhaji Buhary ne,zai san komi akan duk wani labari da ya shafesu,zan kira shi mu yi magana anjima nan,sannan kina nufin shi Chairman ɗin da kansa ma ya tako har nan ya ga Zainab,lallai wannan lamari me girma ne da Allah kaɗai yasan abinda ya shirya.Sai mu cigaba da addu'a Allah tabbatar mana alkhairy,amma fa ba ƙananun mutane bane waɗannan."


Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane Sani addu'ar mu ke kan yi, sai ka taya mu kaima,amma ina so wannan maganar ya zama tsakanina da kai ne, ban amince Zuwairah ta ji komi ba har sai lamarin ya tabbata, sabida bana son surutu da sanya ido."


Baba Sani da tun fil-azal ya san Iyah bata son Umma sabida halayyarta,sai ya jinjina kai yana cewa, "In sha Allah Iyah babu wanda zai ji daga gareni,Allah ya shige mana gaba ya tabbatar mana da alkhairy,amma ita Zainab ta amince za ta iya aurensa?"


Iyah ta murmusa ta bai wa Baba Sani amsa da cewa, "To tunda take sauraransa a waya,su shafe mintuna masu yawa ka ga kenan akwai alamun zai samu kanta,tana dai yawan complain cewa ya cika miskilanci, ga shi yana da mata ita tana jin tsoro kaza da kaza,amma tunda a hakan dai basu fasa waya ba, kuma bana ganinta cikin wani damuwa, ka ga akwai alamun ta fara ba shi zuciyarta kenan."


Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "Hakane, to Allah yayi mana jagora ya tabbatar da alkhairy."


Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Daga haka Baba Sanin ya yi mata sallama,ya baro sasan zuciyarsa na cigaba da al'ajabin wannan labari,sosai ya dinga addu'ar Allah ya ƙulla alkhairy,don zai fi kowa murna ace Zainab ɗin ta samu gidan hutu da za a kula da ita."


TAIMIYYAH da ke cikin ɗakinta tana operating system ɗinta,ta jiyo muryar Iyah na ƙwallo mata kira,ta amsa tana tsaida aikin da take yi, ta miƙe ta fice daga ɗakin zuwa falon Iyah.


Iyah da idanunta ke kan TAIMIYYAH har ta ƙariso wajen da ta ke zaune ta furta, "Zainabu zauna mu yi magana."


TAIMIYYAH ta zauna tana maida dubanta kan Iyah,Iyah ta cigaba da cewa, "TAIMIYYAH so na ke ki sanar dani za ki iya auren wannan mutum, Abdulmaleek ko kina amsa wayarsa ne don gudun kar ran Hajiyarsa ya ɓaci? Na san kin yi istikhara kina kuma addu'a kullum, kamar yadda nima na ke tsaye akan yin addu'ar neman zaɓin Allah,shin kina jin ya kwanta miki a zuciyarki, ko kuwa dai biye masa kawai kike yi sabida uwarsa ta roƙi alfarman ki riƙa ɗaga kiransa? maza ki sanar dani gaskiyar abinda ke cikin zuciyarki,don bana so a shiga hakkinki,matuƙar kin ji bakya ra'ayinsa duk son da Hajiya ke miki da son mu haɗa jini dole za a haƙura,don bazan tilasta ki auren wanda baki so ba."


TAIMIYYAH sai tayi ƙasa da kanta ta fara faɗin, "Iyah tabbas nayi Istikhara na nemi zaɓin Allah,sai dai bazan iya cewa kai tsaye ina jin son sa a zuciyata ba,amma dai duk wani tsoro da fargaba da nake ji ada bana ji yanzu,ina jin nutsuwar zuciyar da ta ruhi a duk lokacin da mu ke waya da shi,kuma ga dukkan alamu mutum ne daya san abinda ya ke yi,don sam bai taɓa min zancen banza ba,bani da zaɓi sai na ki Iyah.In dai har ya kwanta miki an kuma yi bincike a kansa, an samu kyakykyawar shaida akansa shikenan,ba ni da sauran buri akan soyayyah tunda na rasa Nass."


TAIMIYYAH ta yi maganar kanta a ƙasa don ta kasa duban Iyah,wacce ke faman zabga mata harara jin sunan Nass da TAIMIYYAN ta furta,kafin ta buɗe baki ta ce, "Au! Zainab har yanzu kina nan kina ƙawazucin wannan yaron a ranki?Ni na ɗauka tuni kin daɗe da kulle babinsa,to madallah kada Allah ya sa ki yi lokacin soyayyar wanin, tunda Naseeru shine autan masu iya soyayyah a duniya ko?"


Iyah ta rufe ido ta cigaba da zazzagawa TAIMIYYAH faɗa,har sai da TAIMIYYAH tayi danasanin yadda aka yi sunan Nass ya shiga cikin kalamanta.Ta dubi Iyah da fuskar tausayi, hankalinta a tashe da fassarar da Iyah tai wa kalamanta ta ce, "Iyah don girman Allah ki yi haƙury,ni ba haka na ke nufi ba baki fahimce ni bane,wallahi na daɗe da cire Nass daga zuciyata,kawai sunansa ne ya suɓuce akan harshena,ki yi haƙury ki daina wannan faɗan, ni babu Nass a cikin zuciyata a yanzu,na cire shi har abada daga cikin zuciyata,ina kuma addu'a Allah ya maye min gurbinsa da mafi alkhairy."


TAIMIYYAH ta yi maganar muryarta na rawa, alamun gaf ta ke da ta sakarwa Iyah kuka,ganin hakan yasa Iyah sassauta fushinta ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "To shikenan na ji tashi ki je,duk yadda muka yi akan Maleek ɗin za ki ji,don ana bincike akansa zan sanar da Hajiyarsa,sabida a turo magabatansa su nema masa izinin fara xuwa zance."


TAIMIYYAH ita dai tashi ta yi ta nufi hanyar ɗakinta, ba tare da ta sake cewa Iyah komi ba,tana shiga ɗakin kashe system ɗinta ta yi ,sabida bata ji za ta iya cigaba da aikin tunda Iyah ta riga ta ɓata mood ɗinta a yanzu.Tana cikin saka kayan bacci kiran Maleek ya shigo,sai ta saki ƙaramin tsaki tana cigaba da sanya kayanta,don ringing ɗin da ta sanya masa daban ne,shiyasa ta gane shi ne ya kira ɗin.


Tana kammala saka kayan kenan wani kiran ya sake shigowa,sai ta sanya hula akanta tana ɗaukan ƙaramin hijab ta saka don ta san vid call ne,ilai kuwa tana ɗaukar wayar ta ga vid call ɗin ne, sai ta zumɓure baki tana receiving call. Kyakyawar fuskar Maleek Ado ya bayyana a allon screen ɗin wayarta,kamar yadda tata fuskar ya bayyanawa Maleek Ado,wanda ke kishingiɗe daga cikin Sofa da ke cikin bedroom ɗinsa na gidansa da ke lagos.


TAIMIYYAH ta fara gaida shi cike da zallar shagwaɓa, wanda hakan ke ruruta wutar ƙaunarta a zuciyar Maleek,har ya ke jin tamkar shekaru biyar suka yi da sanin juna, ba kwanaki biyar zuwa shida ba.Idanunsa akan kyakykyawar fuskarta yake, lokacin da ya amsa gaisuwar a taƙaice,kafin ya ɗaura da faɗin, "Zaynabb me ya ɓata mood ɗinki,na ga kamar kina fishi?"


TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa cike da mamakin yadda yake saurin karantar yanayinta,ta sake shagwaɓe murya tana cewa, "Babu komi fa, kawai ni ma haka na ji mood ɗina ya sauya yanzu."


A.Maleek da ya zurawa ƙaramin bakinta,da ke furta kalaman ido,ya wani taɓe baki yana faɗin, "Tunda ba za ki sanar da ni ba shikenan,yanzu ni yaushe za a bani daman fara zuwa na ganki ne,cox ina buƙatar hakan da gaggawa ,wannan wayar da mu ke duk bawani gamsar da ni yake ba Zaynabb,sabida ba ki sakin kiji ki barni na kalli idanunki ,da fuskarki yadda na ke so,amma zan yi magana da Hajjah in ji halin da ake ciki,sabida na matsu na mallake ki Zaynab don bani da isasshen lokacin ɓatawa, mu na soyayyar yara gwara a ɗaura ayi me dalili da hujjah ko?"


Ya ƙare maganar cike da son TAIMIYYAH ta ɗago ta kallesa,amma sai ta ƙi yin hakan don kunyarsa ne ya sake lulluɓeta,tana kuma mamakin yadda ya iya zaro kalamai a miskile, tamkar ba daga bakinsa kalaman ke fitowa ba. Shi ko Maleek ko a jikinsa ya cigaba da zaro mata manyan kalamai, TAIMIYYAH na jin kamar ta kashe wayar amma babu halin hakan,don ta fi kowa sanin ya tsani hakan kuma tun daga randa ta kashe masa waya a karo na biyu, ya nuna ɓacin ransa sosai,shikenan ta ke kiyaye hakan don a yanzu ji ta ke yi bata ƙaunar ransa ya ɓaci, bata san dalilin hakan ba kuma don ba za ta ce tana jin soyayyarsa a zuciyarta ba,kuma ba za ta iya cewa tana ƙinsa ba ,sai dai ma wasu irin feelings da take ji akansa wanda za ta iya cewa ba ta taɓa jin hakan akan Nass ba.


Sun ɗauki fiye da rabin awa yana mata hira,har sai da kiran Suhailah ya shigo ɗaya wayarsa,sannan ya ɗauki excuse ya kashe wayar don amsa kiran Suhailah.


TAIMIYYAH sai ta aje wayarta tana jin wani abu me kama da ɓacin rai na danne zuciyarta,wannan shine karo na biyu da suna cikin waya kiran matarsa ya shigo masa, Maleek na yanke wayar da ya ke yi da ita don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login