Showing 75001 words to 78000 words out of 186776 words

Chapter 26 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6582

je ki soya Awaran mu ci tun kafin Babah Ladi ta gama girki in ji Awaran ya fita kaina."


Daga haka suka fito tare da Yasmeen ɗin zuwa Kitchen,bayan sun ma Babah Ladi da ke ta suyan Waina sannu da aiki ne sai suka fara hidiman gabansu.Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala suyan Awaran wanda suka wadata shi da egg,ya ji haɗin Sauces ɗin Albasa sai qamshi ke tashi duk ya cika kitchen ɗin.


Bayan sun ɗibarwa Babah Ladi ne suka juyo sauran cikin plate su ka nufo falon Iyah,in da suka samu Iyan a zaune tana faman zuba Sugar a cikin bokitin Nonon da za a yi sadaka da shi haɗe da Waina, idan an gama soya Wainar.
Ta ɗago tai wa su TAIMIYYAH kallo ɗaya tana faɗin, "Dama na san wannan qamshin da ke ta zuwar min har nan kune kuke wani abin kwaɗayin.Yanzu Awaran ce ba za a ci ta hakanan ɗinta ba sai an mata wannan haɗin lallai kam!"


TAIMIYYAH ta shagwaɓe face tana duban Iyah take cewa, "Iyah ai yanzu duk haka ake yi,anfi iya ci da yawa idan akai irin wannan haɗin,bari dai a baki naki ki ci ki ji yadda yake."


Iyah tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "ku ci abinku lafiya ni kam bada ni ba."


TAIMIYYAH su kai dariya suna cin abinsu hankali kwance,bayan sun kammala ne Yasmeen ke sanar da Iyah Nass zai zo zuwa anjima.Kuma gobe idan Allah ya kaimu zasu je su duba Mamarsa da aka kwantar a Asibiti, kamar yadda yake ta magiyan su tambayi Iyan izini tun yau.


Iyah ta ɗaga kai ta dubi Yasmeen ɗin da ke mata bayani tana cewa, "To sannu sarkin iya tsari me kaifin baki,ita Zainabun bata da baki ne halan? To duk ba wannan ba ni a gaskiya bana son irin wannan sakarcin,wai saurayi ya fara ɗaukan budurwa yana kaita wajen danginsa tun kafin ai aure ko magana me ƙarfi ya shigo,hakan ba mutuncin ƴa mace bane sam.Amma yanzu tunda ana maganan rashin lafiya ce ta uwa kuma shine ya roƙi ku tambayeni izini,to zan amince amma da zaran kun yi mata sannu ku kamo hanya ku dawo gida.Ban amince daga dubiyan ku bishi ko'ina ba kunji na gaya muku! Don hakan ba mutunci bane sam, ku dinga riƙe martaban ku na ƴaƴa mata,wayewa duk idan bata musulunci bace halaka ce,don haka ku kula kuma shine karo na ƙarshe, dama ke Zainab ina son in gaya miki tunda na ga kun fuskanci juna kina sonsa to zuwa wata satin sai ya zo ya samu Babanki Sani,in yaso sai ya turo magabatansa a zo a yi magana a san da zamansa."


TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana tai ƙasa da kanta,sai yanzu ta ɗago ta dubi Iyan cike da shagwaɓa take cewa, "To Iyah zan sanar masa Insha Allah! Kiyi haƙury nima wallahi bana son zuwa duba wata Mamarsa,shi ne ya matsa da maganan ita kuma Yasmeen ta amsa cewa zata tambayeki,don ni kai tsaye na sanar masa ma ba za ki amince ba."


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana ƙin yarda su sake haɗa ido da Iyah,ganin haka yasa Iyah cewa, "Karki damu tunda uwarsa ce sai ku je ɗin,amma daga haka bazai sake cewa ki bishi ko'ina ba,don ma ga Yasmeen ɗin dai za ta yi muku rakiya da ace ke da shi ne kaɗai bama zan taɓa amincewa ba sam."


Daga haka suka kulle babin wannan maganan,suka ɗakko maganan zaman rabon gadon da za a fara idan an gama tattara abinda Abie ɗin ya bari.Jikin TAIMIYYAH duk sai yayi sanyi hankalinta ya sake tashi,tana jin wani irin kewa me tsanani na danne zuciyarta.


Ganin mood ɗinta ya sauya gaba ɗaya yasa Iyah kawar da maganan,ta hanya sanya TAIMIYYAH ta tashi ta kai Nonon da Iyan ta gama sanyawa Sugar zuwa Kitchen.Daga nan ta duba idan Babah Ladi ta tara Wainar da yawa,sai su fita ita da Yasmeen su haɗo kan almajiran da za a baiwa Sadakan Wainar da Nonon.


Hakan ko akayi su TAIMIYYAH suka fita kiran almajiran da kusan duk Friday sukan taru a ƙofar gidan.Don sun saba amsar sadaka a Sasan Iyan,mussamman idan Waina ko tuwan shinkafa aka yi.
Sai da suka gama raba ma almajiran sadakan tas sannan suka dawo ciki suka nufi ɗakin su don ganin lokacin sallan Zuhur ya yi.


*5:35pm*


Motar Nass ne ta faka a ƙofar gate ɗin shiga gidan su TAIMIYYAH.Ya fito sanye cikin shigan manyan kaya riga da wando na shadda,anyi masa ɗinkin zamani da ya dace da Matashi kamarsa,wanda ya san daraja da ƙiman iya saka kaya.Kalar shaddar Milk ne daya haska shi sosai fuskarsa cike da annuri yake takawa zuwa bakin gate ɗin ya buga.
Tukur Mai-gadi ya buɗe suka gaisa yana faɗin, "Ranka-ya-daɗe barka da isowa."
Nass ya saki murmushi yana faɗin, "Barka dai Malam Tukur ya ƙoƙari."


"Lafiya lau wallahi barka da isowa,bari a sanya maku kujerun zama kafin Gimbiyar ta fito." Cewan Tukur yana nufan inda zai ɗakko fararen kujerun zama ya aje ma Nass ɗin.Nass yabi bayansa da kallo yana me zaro wayansa ya shiga kiran line ɗin TAIMIYYAH.


Basmah wacce ta fito daga Sasan su zata fita can ƙasan layinsu,sai idanunta suka hango mata Nass da ke magana da TAIMIYYAH a waya yana sanar da ita gashinan cikin Compound ya iso.Tayi saurin gyara zaman gyalen jikinta tana wani gyara takun ta cike da yanga,sanye take cikin Riga da Skat da suka fidda suranta.
Idanunta akan Nass yake har ta ƙariso inda yake tsaye tai masa sallama ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana amsa guisuwanta da faɗin, "Basmah ko,ina fata kina lafiya?"


Basmah ta wani kashe murya cike da iyayi take faɗin, "Lafiya lau Bro bari na kira maka Yah TAIMIYYAN kafin na wuce ko." Daga haka ta juya don zuwa Sasan Iyah ta kira masa TAIMIYYAH,ba tare data jira Nass ɗin ya sanar da ita cewa TAIMIYYAN ta san da isowan nasa.


Tana sanya kanta a ƙofar shiga Sasan ita kuma Yasmeen na fitowa,hakan yasa saura kaɗan suyi karo Basmah ta ja baya tana faɗin, "Ayyah! Yah Yasmeen saura kaɗan mu gwabza karo,wai na zo sanar da TAIMIYYAH cewa guy ɗinta ya iso."


Yasmeen tayi wa Basmah wani sakartaccen kallo tana faɗin, "Okey! Ai tuni ta san da isowan nasa Basmah,yanzu ma wajensa na nufa kafin ta fito." Daga haka Yasmeen ta ɗaure fuska tana yin gaba abinta ta bar Basmah da bin bayanta da kallo,tana wani taɓe baki ta juyo itama don tafiya inda za ta.


Lokacin da Basmah ta fita wajen gate ɗin gidan nasu idanunta akan haɗaɗɗiyar motar Nass suka fara sauka.Tayi tsaye cak! Tana bin motar da kallo zuciyarta na wani irin kaɗawa,ta cigaba da tafiya tana ƙarewa motar kallo cikin Zuciyarta take cewa, 'Taɓɗi! Yanzu wannan motar tasa ce,shine duk haɗuwarsa da ajinsa ya rasa wacce zai so sai Yah TAIMIYYAH,wacce take gurguwa musaka shi ko me zaici da ita? Alhali ga ƴan mata kamarta lafiyayyu da basu da nasakan komi a tattare da su."
Ta cigaba da tafiya zuciyar na raya mata wasu tarin lamura, da take ji dole ma tayi anfani da basirarta wajen karkato da hankalin wannan Zuƙeƙen saurayin zuwa gareta.
Har ta kai gidan su Zeenah wata qawarta anan ƙasan layin, zuciyarta bata bar ta sukuni ba.Don gaba ɗaya Nass ya tafi da dukkanin nutsuwarta,sai yau ne ma ta sake ƙare masa kallo ta ga haɗuwarsa sosai.


Allah Sarki ita ko TAIMIYYAH suna can suna shan luv ɗinsu da Nass ɗin,bayan ta fito ta same shi zaune shi da Yasmeen.
Isowan TAIMIYYAH wajen yasa ta basu waje ta je kawo ma Nass ɗin lafiyayyen samosa da meat pie ɗin da sukai masa haɗe da lemun Abarba da yaji Kwakwa da Madara.
Koda ta kawo bata sake zama ba ta koma cikin gida ta basu waje don TAIMIYYAH ta sake da Nass ɗin sosai,wanda gaba ɗaya tun isowan TAIMIYYAH wajen ya wani rikice sai faman bin ta da azababban kallo yake.
Gyale ta yafa yau ba Hijab ba hakan yasa tai masa kyau sosai fiye da kullum.Shiyasa ya kasa ɗauke idanunsa akanta har abin ya dinga bama TAIMIYYAH haushi, ta ji dama bata biyewa Yasmeen ta fito sanye da gyale ba.


Sun ɗauki a ƙallah awa ɗaya da rabi kafin yai mata sallama yana aje mata sabbin kuɗi wai ta sayi credit.Babu yadda TAIMIYYAH bata yi akan ya ɗauki kuɗinsa ba amma fir! yaƙi,sai ma rigiman da ya kafa mata akan cewa sai tayi masa rakiya bakin gate.
Hakanan ba don ta so ba ta raka shi sukai sallama da juna,ta juyo don komawa cikin gidan bayan ta tsaya ta ɗauki kuɗi da tray ɗin abinda Yasmeen ta kawo,wanda kaɗan ya ci ya bar sauran.


Lokacin data isa ciki a falo ta aje tray ɗin hannunta tana nufan ɗakin Iyah don bata kuɗin hannunta ta aje.Faɗa sosai Iyah ta yi ma TAIMIYYAH akan amso kuɗin da tayi har sai da TAIMIYYAH ta fara mata alamun za ta yi kuka sannan Iyah ta amsa kuɗin ta adana.


"Yah Zuhurah kin ko ga motar da Guy ɗinnan me son Yah TAIMIYYAH yake hawa? Gaskiya wallahi guy ɗinnan ya haɗu ƙarshe....Sam bai ma dace da Gurguwa kamar Yah TAIMIYYAH ba.Gaba ɗaya ya gama tafiya da zuciyata Allah ya sani na kamu da son sa farat ɗaya kuma sai na san yadda nayi ya zama mallaki na.Don baxan bari ina ji ina gani ya auri wata gurguwa can musaka,alhali na gani na ƙyasa sam hakan bazai taɓa yiwuwa ba."


Zuhurah da tun fara maganan Basmah ta zuba mata ido,sai yanzu da Basman ta kai aya sannan ta dube ta cikin ido tana faɗin, "Basmah kinsan me kike faɗi kuwa? Snatching ɗinsa za ki yi ko me kike nufi da waɗannan kalaman?"


Basmah ta wani watsa hannuwa baya tana faɗin, "Yadda kika faɗin shi za a yi snatching idan nayi aiba kaina farau ba,wallahi Numbern sa zan sata in gwada sa'ata,idan an dace shikenan sai labari ya canza,shi ma banda abinsa me zai ci da gurguwa? Duk abinda yake nema a jikinta nima ina da shi kyau da farar fata kawai zata nuna min."


Yadda Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani jujjuya jiki yasa Zuhurah kwashewa da dariya dai-dai kuma lokacin da Umma ta fito,tana duban Zuhurah take faɗin, "Dariyan me kuke yi haka kaman wasu taɓaɓɓu?"


Zuhurah sai ta sake kwashewa da dariya,cikin dariyan take sanar da Umma komi,sai Umman ta xauna tana faɗin, "Ke Basmah da gaske kike yi motar da yake hawa har ta fi ta Sadeeq kyau? To ɗan gidan uban waye ta rakito tana gurguwa musaka da ita,anya ko ba Iyah ke shige da ficen da take nemowa Yarinyar can maganin farin jini ba? Ana kulle idanun Samari su daina ganin nakasan Yarinyar in banda haka ina hakan zai yiwu kana lafiyayye ka auri me nakasa."


Umma tayi maganan tana jin wani abu na tokareta a ƙirji.Basmah tayi saurin faɗin, "Sai ma kin ga haɗuwan guy ɗin Umma,wallahi bazai yiwu ace kamansa ya kawo kansa wajen musaka gurguwa wacce sai da taimakon dafa guiwa take iya tafiya a duƙe,ni dai yanzu da gaske na ke sonsa ya kama Zuciyata Umma,kuma idan ma muka zuba ido ta aure shi ai mune da kunya tunda kin hana ya Sadeeq ya aure ta, to kuma kawai sai a ga ta samo wanda ya fi Yah Sadeeq ɗin komi ai mun ji kunya kenan Umma."


"Ƙwarai maganarki a kan hanya ta ke Basmah,idan har na zuba ido ta auro wanda yafi Sadeeq na ji kunya,sai Iyah ta zuba ruwa a ƙasa ta sha,don haka idan har da gaske kina son sa kiyi ƙoƙarin sato numbarsa a wayanta,sauran bayanin duk zan kitsa miki shi,ke inma bazai so ki ba to sai dai kuyi biyu ba bu,amma In Sha Allah ba za ta auri wani mutum me daraja ba sai musaki ɗan uwanta,shegiyan yarinya me kama da Aljanu."


Zuhurah data saki baki tana duban Umma sai cewa tayi, "Umma yanzu sai ki goyawa Basmah baya tayi ƙwacen saurayi,ni aganina hakan duk bai taso ba,ku ma tsaya ku ga yadda tarayyan nasu da shi zai kaya mana,ku ka sani ma ko jikinta take bashi yana anfana da shi tunda har ta iya sakewa ya Deeku ya kwashi rabonsa waye za ta ki baiwa kanta,tunda ta san da wuya ta auru ku kuna ganin kyawun da take ƙarawa na banza ne? Ni hatta cikar ƙirjinnan ban yadda ba hannun maza yaji ba yake ƙara bunƙasa."
( _Allah ka raba mu da sharrin maƙiyi,readers wannan irin sharri da Zuhurah kewa TAIMIYYAH na lafiya ne kuwa? Dole ka nemi tsari daga sharrin maƙiya,duk wanda baya son ka babu abinda ba zai iya yi ma na ɓatanci ba arayuwa,sai dai mu ce Allah ya sakawa Baiwar Allah TAIMIYYAH_ 😰).


Umma ta dubi Zuhurah tana cewa, "Oho! Koma dai mene ne tunda ƴar uwanki ta kamu da sonsa ai sai ki mara mata baya tai iya yinta wajen janyo hankalinsa.To wai ma yaushe kika fara sonta da har za ki ji tausayinta? Ke abin sonki ne ta auri wanda yafi Yayanki komi,waya sani ma yafi har Ameerun da kike taƙama da shi tunda ba a ma san ɗan gidan uban waye ba,yanzu haka irin ƴaƴan attajiran garin nan ne ma waya sani?"


Zuhurah sai taji maganan Umma ya soki Zuciyarta,wani kishi da tsanan TAIMIYYAH na taso mata,tare da wani tsoro me tsanani tana ji kada fa maganan Umma ya tabbata Nass ɗin yafi Ameerun ta,aiko da ita da kanta zata iya ƙullawa TAIMIYYAN makircin da ba za ta auri Nass ɗin ba,tayi saurin haɗe face tana faɗin, "Don Allah Umma ki daina wannan fatan,hakan ma ba zai taɓa kasancewa ba,Ameeru fa Babansa har Muƙamin ɗan Majalisan Jiha ya yi a baya,kin san ko sun tara arziƙi ba kaɗan ba."


Umma ta danna ma Zuhuran harara tana cewa, "To shi ma sai ki bari mu san ko shi waye ɗin,kuma ta ina zamu sani ba tare da Basman ta saci number ɗinsa mun fara bibiyansa ta waya ba."


Dukansu su kai na'am da maganan Umma,sun daɗe suna tattauna yadda za a yi Basmah ta sato Number ɗin Nass a wayar TAIMIYYAN,daga ƙarshe Zuhurah ce ta basu tabbacin su bar komi a hannunta zata samo numbern cikin ruwan sanyi.Daga haka suka rufe maganan zuciyoyinsu cike fal da ƙyashi da hassadar yadda TAIMIYYAH ta fi su tarin abubuwa masu yawa alhali tana matsayin gurguwa musaka da suke ganin ita ɗin bakomi bace.


_To masu karatu ya ku ke ganin wannan Cakwakiyan za ta kaya? Su Umma za su yi nasaran raba soyayyan data riga ta ƙullu tsakanin Nass da TAIMIYYAH ko kuwa wata ƙaddarance za ta raba? Sai ku cigaba da bibiyan yadda rayuwar TAIMIIYAN zata kasance.......✍🏻_








Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._




#Ɗansabo ce #
[12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_




*38*


__________Suhailah ce zaune tana kallo a cikin makeken falon nata da ke down-stair.
Daga gefenta ƙaramin Bowl ne da aka ciko shi da milky cin-nin wanda tayi ordering daga wajen BAMS,wata shahararriyar me yin Snacks a nan gaban layinsu kaɗan.Gefe guda kuma kwalin Hollandia Milk ne da cup wanda ta cika da milk ɗin tana korawa da cin-cin ɗin kaɗan-kaɗan.


Wayarta da ake kira yasa ta ɗauke ido daga kan makeken smart TV ɗin ta mayar kan wayar, tana duba sunan me kiran ganin sunan Bala Mai gadi ne, yasa ta ɗaga wayar ta kai kunni.


Amsa gaisuwarsa tayi kafin tayi shiru ya biyo baya tsayin seconds sannan ta furta, "Okey Bala na santa ba matsala ta shigo kawai."
Daga haka ta sauke wayan daga kunni murmushi na blushing saman face ɗinta tunawa da tayi da gargaɗin A.Maleek, da kashedin da yace yaiwa Bala akan duk wacce zata zo wajen Suhailah sai ta faɗi sunanta.Shi kuma Bala sai ya kira Suhailan ya sanar mata, idan ta bada izinin shiga sannan ya bar kowacece ta shiga.
Amma idan har ya ji cewa sunanta Zubaida to bai yarda ta shigar masa gida ba,kada ma ya kira Suhailah ya sanar mata kai tsaye ya hana ta shiga masa cikin gida.Suhailah gani take kaman wasa yake yi a lokacin da ya sanar mata umurnin da ya ba Bala kenan,sai yanzu da Balan ya kira yana sanar mata da zuwan wata Friend ɗinta Ameena Waziri,sannan tw gane da gaske Maleek ɗin yake yi bada wasa ya faɗi maganar ba.


Sallaman Meenah Wazir daga bakin ƙofar shigowa falon yasa Suhailah tashi ta nufi bakin ƙofar falon tayi welcoming Ameenan,sukai Hugging juna kowanne da murmushi saman fuskarta.
Suhailah ta furta, "Welcome dear yaushe kika shigo gari ba labari sai zuwan bazata haka?"


Ameen ta saki murmushi suna sakin juna take cewa,"Mrs.Maleek Ado kenan walllahi shekaranjiya muka shigo gari da ogan,shine na ce yau dai lallai sai na zo wajenki kafin mu wuce jibi."


"Gaskiya kin kyauta sosai dear cox i miss u so much,ke sam ko a online ba a ganinki sai in mutum ya ɗaga waya ya kira ki,har yanzu dai harkan social media ɗinnan bata dame ki ba Meenah tun muna skull ai ta miki ciwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login