Showing 90001 words to 93000 words out of 186776 words

Chapter 31 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6610

ɗin da ya biya kuɗin gidan watanni biyu kafin rasuwan nasa,duk sunzo da komi-da-komi.Ranan da suka dawo TAIMIYYAH kuka ta sanya ma Baba Sani lokacin da ya tara su ita da Iyah da Ummie yana musu bayani,da ƙyar Yah Sadeeq ya rarrasheta tayi shiru.Aamma daren ranan sam idanunta basu rintsa ba sabida matsanancin kewan Abie da ƴan uwanta da ya danne zuciyarta.Sai data tashi tai ta yin nafilfili tana addu'a sannan ta samu nutsuwan zuciya har bacci ya iya ɗaukanta a ƙarshen daren.


Sati ɗaya da rabuwar TAIMIYYAH da Nass wanda har zuwa lokacin bai fasa nacin kiran wayar TAIMIYYAH ba,amma sam bata ɗauka.Ko saƙo ya turo bata iya buɗewa sai dai tayi deleting ɗinsa.
Amma dai number ɗinsa ce ta kasa sharewa daga wayarta,ya kan yi mata magana ta chart ma amma baya samun reply daga gareta.Duk wanda ya ga TAIMIYYAH cikin sati ɗayan zai ga cewa ta ɗan faɗa ta rame kaɗan,sabida yawan tunani da damuwan da ke cinkushe cikin zuciyarta.
Sai dai kullum Iyah da Yasmeen na mata faɗa akan ta cire duk wata damuwa daga zuciyarta ta fuskanci abinda zai zo a goben ta ne.Don wannan ya riga da ya faru hakan yasa TAIMIYYAH ke ƙoƙarin ganin ta danne soyayyar Nass a can ƙasan zuciyarta.Ta kuma manta da shi amma abin yaci tura don ita kanta bata san soyayyarsa tayi mata mugun kamu ba sai a yanzu da take ganin zasu rabu da gaske.
Ranan Thursday za su samu hutun sati ɗaya a skull,hakan yasa TAIMIYYAH yanke shawaran bin Yasmeen Kano.Tunda Yasmeen ɗin Saturday zata wuce gida,sabida bikin cousine sister ɗinsu da za a yi next week.
Koda TAIMIYYAH ta sanar da Iyah cewa tare da ita Yasmeen za ta koma,Iyah bata yi musu ba itama tana so TAIMIYYAN ta jirga daga garin ko zata samu nutsuwan zuciya a wani wajen.Don haka Iyah da kanta ta sanar da Baba Sani cewa TAIMIYYAH za ta bi Yasmeen wajen Guggo Bilki,ta samu koda sati ɗaya kafin ta dawo.
Ya yi fatan Allah tsare hanya don shima kansa ya shaida cewa TAIMIYYAN na cikin damuwa tun bayan rasuwan Abie.Shi kansa ƙarfin zuciyace kawai ke tafe da shi amma mutuwar Yayan nasa na matuƙar illata zuciyarsa.


Ana gobe zasu tafi ne Zuhura ta lallaɓo zuwa Sasan Iyah,don cika ƙudirinsu akan samun lambar wayan Nass ɗin.Don da gaske Basmah ta tubure musu ita fa lallai soyayyar Nass ɗin ya kama zuciyarta.
Don haka ta ƙosa ta ga ta fara aiwatar da plan ɗinsu na son janyo hankalinsa zuwa gareta,kafin Umma tayi tafiya zuwa Yobe inda ta shaidawa Basmah za ta kai sunansa zuwa wajen malaminta.Don a janyo musu hankalin Nass ɗin zuwa ga Basmah kota wani hali......


Cikin tsananin sa'a Zuhurah ta samu nasaran kwashe lambobin Nass daga wayar TAIMIYYAH.
Ta samu wannan nasaran ne ta hanyar ribatan TAIMIYYAH akan cewa tana son ta tura mata hotunan su Nahar a wayarta, kwana biyu tana kewar yaran a xuciyarta.
TAIMIYYAH bata kawo komi a ranta ba ta baiwa Zuhura wayarta da sam bata sanya ta a security code.Shiyasa cikin sauƙi Zuhurah ta samu nasaran kwashe numbar Nass ɗin wanda TAIMIYYAH tayi saving da suna My N, sai Glo line ɗinsa da tai saving da Nass Mine.
Ko da Zuhurah ta kwashe numbar sai ta tura hotunan su Raudhan kamar yadda tace ta miƙawa TAIMIYYAH wayarta ta amsa ta aje ba tare da tunanin komi ba.
Zuhurah kuma sai ta juya wajen Yasmeen da ke faman kammala shirya kayanta cikin akwati tana janta da hira, sai kuma lokacin Zuhurah ke jin cewa tare da TAIMIYYAH,Yasmeen za su wuce zuwa Kanon.


Cikin murna da farin cikin samun nasara Zuhurah ta koma Sasan su tana baiwa Basmah lambar wayar Nass ɗin.Bayan ta kora mata bayanin yadda aka yi ta kwashe lambar daga wayar TAIMIYYAH.
Basmah ta rumgume Zuhurah tana sakin wani irin ihun murna kafin ta ruga zuwa ɗakin Umma tana sanar da ita an samo lambar........✍🏻




_To fah! Masu karatu ko ya wannan lamari zai kasance? Ga dai TAIMIYYAH sun rabu da Nass ba don zuciyoyinsu sun daina ƙaunar juna ba,ga kuma su Umma na son cikawa Basmah burinta na son ganin ta janyo hankalin Nass ɗin zuwa gareta,ko ya lamarin zai kasance? Mutumiyar fa za ta yi balaguro zuwa Kano,ko ɗan Kano za mu samo ne ? duk amsar na tare da Ɗansabon ku,don haka mu je zuwa yanzu ne labarin zai fara ɗaukan_ 🔥🔥🔥🔥






Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._










#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:09 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_




*40*




TAIMIYYAH ta sake jingina da jikin bangon corridor ɗin,ta yadda zata iya jiyo maganganun da su Guggo Bilkin ke yi da kyau.Kunnuwanta suka cigaba da jiyo maganan da Guggo Bilki keyi inda take cewa Emran ɗin,


"Emrana ka ga ita ɗin ƴar uwarka ce ta jini,duk wacce zaka je ka auro a waje barin ita TAIMIYYAR ce.Kaine nake ganin duk kafi sauran zurfin tunani da hankali,kuma kaine baka fito da matar aure ba ka tsaya shiririta,Anas ya samu mata haka Ahmad shima magana yai nisa,shiyasa nake ganin kaine ya dace ayi wannan haɗin zumuncin da kai,gadai ta nan ka ganta babu abinda ta rasa kuma nakasanta ba abinda zai kawo cikas bane don ka aureta,don babu abinda bata iya yi da kanta,Zaynab tana da tarin nutsuwa da baiwa masu da yawa da zaka ji daɗin kasancewa da ita.Abbanku kansa yayi na'am shi ya bani ƙwarin guiwan in tinkareka da maganan don aji ta bakinka,ko kuwa ka samu wata ne bamu sani ba?"


Emran wanda ke zaune kusa da Mamien tasu,ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta,cikin tsananin mamakin dukkanin kalamanta ya fara cewa, "Yanzu Mamie don kawai ban fito da mata ba daga zuwan Yarinya sai ki fara irin wannan tunanin,arasa wacce za a ce na aura sai gurguwa,musaka Mamie? Gaskiya bazan iya aurenta ba da dai ace ba gurguwa bace yarinyar ta haɗa duk wasu abu da nake so a jikin mace,amma tunda tazo a gurguwa gaskia Mamie bazan iya aurenta ba,haba abokaina ai dariya zasu yi min,ace duk matan garin nan da sauran wurare in rasa wacce zan aura sai gurguw......"


"Ya isa haka Emrana!" Guggo Bilki ta katsesa cikin fishi me tsanani kafin ta cigaba da faɗin, "A gabana Emrana,a gabana zaka riƙa aibanta ƴar uwarka don kawai tana da nakasa? Miye aibun kasancewarta gurguwa kai me lafiyayyun ƙafafu?Ko kana tunanin ka fita gata ne a wajen Allah da ya barka a yadda ka ke, ita ya jarabceta da zama gurguwan? To shikenan tunda abin naka yazo da iskanci da rashin mutunci abar zancen gaba ɗaya,amma kasani nan da watanni uku kacal ka fito da matar aure,sakarai kawai miskilin banza da wofi, da ina maka kallon wanda yasan abinda yake yi ashe kai ɗin baho ne,duk matar da zaka je ka rakito ɗin ba baki zan maka ba Emrana,amma ba za ka taɓa samun me nagarta da kyakykyawan hali irin TAIMIYYAH ba.Amma ka je kai nazari ka kuma sake fuskantar halayyar TAIMIYYAH tunda ga ta nan tana nan tare damu har nan da zuwa sati ɗaya,idan ka ji kana da ra'ayi zan fi kowa farin ciki tashi ka bani waje."


Guggo Bilki ta kai ƙarshen maganan tana saita masa hanyar fita daga ɗakin.Fuskarta har lokacin a ɗaure yake don maganganun da Emran ɗin yayi ya ɓata ranta.
Emran ya zube daga gabanta yana cewa, "Mamie kiyi haƙury na ga ranki ya ɓaci,ina gaya miki gaskiyan abinda ke zuciyata ne amma zan duba inyi tunani kiyi haƙury please...!!"


Iyah abinda TAIMIYYAH ta ji kenan tayi gaggawar juyawa tabar wajen,wani irin yanayi na ɓacin rai da takaici na lulluɓe zuciyarta.
Itace yau ake wa wani talla yana gudunta don tana matsayin gurguwa? Wasu hawaye masu tsananin zafi suka cika idanunta,haushi da tsanan Yah Emran ya dira a zuciyarta farat ɗaya.Har ta isa wajen dining ɗin gidan zuciyarta suya yake yi matuƙa,hatta da Guggo Bilki haushinta take ji sosai a ranta,tana ayyana me zaisa tai mata haka?Meyasa zata tallata ma Emran ita har ya samu chance na aibanta nakasanta? Ta kai hannu tana share hawaye masu zafi da suka kwaranyo daga idanunta,bata so sam ta nuna wani alama na cewa taji zancen nasu shiyasa tayi matuƙar ƙoƙari wajen danne zuciyarta.Cike da ƙarfin hali ta zuba abinci kaɗan ta fara ci,sabida yadda yinwa ya dameta kuma bata so ulcer ɗinta ya motsa.
Akan idanunta Yah Emran ya fito daga ɗakin Guggo Bilkin, sai dai shi sam bai kula da ita ba,sabida bai kallo sashin dining ba har ya fice daga falon.Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Guggo Bilki itama ta fito,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta aje spoon ɗin hannunta,tana ɗaukan cup ta zuba ruwan juice kaɗan ta shanye.


Guggo Bilki ta ƙariso wajen dining ɗin tana cewa,"TAIMIYYAH dama har kun dawo ne shine ban ji motsin ku ba,ina Yasmeen ɗin take ita?"


TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Guggo Bilki,tana ƙirƙiran murmushi a saman face ɗinta, lokacin da take baiwa Guggo Bilki amsa da cewa, "Aiko na dawo bada jimawa ba Guggo Bilki,yinwa ce ta haukatani na yo nan banje na sanar miki mun dawo ba,Yasmeen tana can gidan zuwa anjima zata dawo tace."


Idanun Guggo Bilki akan Lallin da suka zanu a kyawawan yatsun TAIMIYYAH,lokacin da take faɗin,
"Shiyasa kice ban ji shigowan naku ba muna ɗaki da Yayanku,aiko Lallin yayi kyau TAIMIYYAH ina fata har a ƙafa akai miki ko?"


TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Aiko su Yasmeen sun matsamin da mita Guggo Bilki hakanan na bada har ƙafafun akayi kin gani ma."


Ta ƙare maganan tana ɗago ƙafanta me lafiyan ta nunawa Guggo Bilki Lallin.Guggo Bilki tabi zanen da yai raɗau a farar ƙafar TAIMIYYAN tana cewa, "Kai Masha Allah,Lalli yayi kyau kam ai sun ƙware sosai indai a iya lalli ne."


TAIMIYYAH ta saki murshi yaƙe kaɗan tana cewa, "Ai nan Kano ƙarshe ne wajen iya Lalli Guggo Bilki,mu Zaria babu ƙwararru sosai gaskiya kaman nan,duk da cewa ba laifi yanzu ana ta samun wanda suka iya amma basu kai nan ɗin ba gaskiya."


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana miƙewa tsaye,don so take kawai ta jita a ɗaki daurewa kawai take yi wajen kula Guggo Bilkin,amma maganganun Yah Emran ne kawai ke kai kawo cikin zuciyarta.
Guggo Bilki ta bi TAIMIYYAH da kallo lokacin da take ƙoƙarin wuce ta xuwa ɗaki TAIMIYYAN na cewa, "Guggo Bilki zan je na huta kaɗan kafin yamma ta ƙarisa yi,wallahi na gaji ne sosai zaman gidan Lallinnan."


"To shikenan TAIMIYYAH a huta lafiya,ai zaman kunshi akwai gajiyarwa shiyasa nima ban damu da yi ba sam." Daga haka TAIMIYYAH tayi wucewarta zuwa ɗaki.Guggo Bilki na bin bayanta da kallo da yanayin tafiyarta,wanda sam ita bata hango aibu a cikinsa da har Emran zai ce wai idan ya auri TAIMIYYAH za ai masa dariya ba,ta jinjina kai kawai kalamansa na sake ɓata zuciyarta.


TAIMIYYAH ko tana shiga ɗakin Yasmeen kwanciya tayi akan gado,ta me lumshe idanunta kalaman Yah Emran na dawo mata inda yake cewa, " _Da dai ace ba gurguwa bace Mamie ta haɗa duk wasu abu da nake so a jikin mace."_


'Kenan shiyasa take yawan kama shi yana satar kallonta?" TAIMIYYAH tayi tunanin hakan cikin xuciyarta,tana sake jin zafin dukkanin kalamansa.Ta lumshe idanunta tana me jin kaman tai tsuntsu ta ganta a gaban Iyah,gaba ɗaya sai taji zaman Kanon ma ya gundureta.
Amma sai dai bata son ko Yasmeen taji maganan bare har Guggo Bilki ta gane tai musu laɓe, har ta ji zancen su da Emran ɗin,don haka dole ta daure ta kai iya kwanakin data ambata zata yin.
Tana me shan alwashin ko gaisuwa ba zai sake haɗa ta da Emran ɗin ba.Dama haka kawai ita jininta bai haɗu dashi ba, girmansa kansa da miskilancinsa sam bai mata ba.


Ta cigaba da kwanciya tunanika kala-kala na kutsowa cikin kwanyarta.So take yi ta gano ko ita ɗin tana da wani laifine wajen zamantowarta gurguwa? Amma har ta gama tunaninta bata gano hakan ba. Abu ɗaya kawai ta sani shine Allah haka yaso ganinta,kuma babu wanda zai fi ta son ta kasance cikin lafiyayyu marasa nakasa,amma bata da yadda zata yi tunda haka Ubangiji ya jarabceta ya so ta da kasancewa.Kuma tana masa godia tunda ya bata tarin baiwa da ni'imomi, wanda zata iya alfahari da kanta a hakan.
Ta kai hannu ta share hawayen dake saukowa daga idanunta, zuciyarta na sake shiga ƙunci a duk sanda ta tuno cewa masu ƙinta duk sabida kasancewarta gurguwace suke gudunta.Ta tuno da irin cin fuskar da Mummyn Nass tai musu a asibiti, wani irin ƙunci ya cigaba da danne zuciyarta har bata san sanda ta sanya kuka ba.
Ta cusa kanta a cikin pillow tana kuka sosai har sai da ta gaji don kanta,sannan ta ɗago kai tana share hawayenta.


A kuma dai-dai lokacin Yasmeen ta shigo ɗakin,kallo ɗaya tai wa TAIMIYYAH tayi saurin ƙarisowa cikin ɗakin tana faɗin, "Lafiya TAIMIYYAH kika kunshe ke kaɗai a ɗaki kina kuka,meke faruwa ne?"


TAIMIYYAH tai ƙasa da kanta tana yamutse fuska take faɗin, "Yasmeen kaina ne da cikina ke ciwo,ina ga sabida yadda na wahala a gidan kunshinnan ne banci abinci ba,ni kinsan ciwan kai na ɗaga min hankali dana nemi magani ban gani anan ɗaki shine nayi ta kuka abina."


Baki sake Yasmeen take duban TAIMIYYAH tana jinjina shagwaɓarta.Don ita har ga Allah ta kama da gaske hakan ne,tunda dai tasan babu kowa da zai ɓata ran TAIMIYYAN a gidan, bare ta kawo cewa ko wani abin akai mata.Ta buɗe baki tana faɗin, "Eh! Lallai ke wannan matar shagwaɓarki har ta yi yawa,kawai ki fita kiwa Mamie magana abaki magani shine sai ki wani zo ki kunshe a ɗaki kina kuka,bari inje in samo miki maganin a ɗakin Abbah ki sha." Daga haka Yasmeen ta juya don zuwa ɗakkowa TAIMIYYAH maganin,ita kuma TAIMIYYAH sai ta miƙe dafe da guiwar ƙafarta ta fara takawa ta nufi toilet don wanke face ɗinta,idanunta har yaji-yaji suke sabida kukan data sha.


Lokacin data fito daga toilet ɗin har Yasmeen ta kawo mata magani haɗe da table water ta aje akan bedside.
Hakan yasa TAIMIYYAH zama daga bakin gadon, tana ɗaukan paracetamol ɗin ta ɓalli guda biyu ta kai baki tana korawa da ruwan ta shaye.Ta aje goran ruwan tana cewa, "Yasmeen gobe kuma me zaku yi,hala dai Angon ustaz ne shiyasa ban ji kince za a yi wani bidi'a a bikin ba?"
Yasmeen ta murmusa lokacin da take aje wayarta akan madubi.Ta juyo tana fuskantar TAIMIYYAH sosai kafin ta fara faɗin, "Aiko dai babu abinda za su yi daya wuce walima gobe da ƙarfe huɗu za a tafi MIEMAH a can za a yi walimar.Ina fata dai zaki mana tunda walimace dai a ci a tashi ba wani abu za a yi ba."


TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "See ur mouth like kece walimar,to bari mu gani kila in je kila kuma ba za ni ba,nifa ban son shiga mutanene kema kin sani."


"Sai aljanu kike son shiga ko?" Cewan Yasmeen tana ballawa TAIMIYYAH harara.
TAIMIYYAH bata san lokacin data kwashe da dariya tana cewa, "Ki rifa min asiri da jinnu,Allah yai mana tsari dasu abar zancen zani Insha Allah shikenan ko?"


Wani hararan Yasmeen ta sake aika mata tana faɗin, "Eh shikenan kin tsira tunda kin miƙa wuya za ki ɗin." Daga haka suka dasa hiran bikin har aka kira sallah kowacce ta ɗauro alwala don bada faralinta.


Da daddare ƙememe TAIMIYYAH taƙi fita falo zaman hira yadda suka saba zama dasu Yah Anas.Abincin ma nan ɗaki tasa Yasmeen ta kawo musu suka ci tare.
Guggo Bilki data shigo tana tambayan dalilin da zasu ƙi fitowa falo,sai Yasmeen ta bata amsa da cewa TAIMIYYAH ce bata jin daɗi,amma ta sha magani,sai Guggo Bilkin tai mata sannu tana juyawa ta bar ɗakin.


Washegari ƙarfe huɗu da rabi su TAIMIYYAH suka isa wajen walimar.
TAIMIYYAH ta gama haɗuwa cikin wani ubansun Abaya kalar Dark Gray da yaji adon zane da cream colour.
Duk inda ta wulga ƙyalli take yi cikin kayan,fuskarta babu kwalliya komi amma tayi mugun kyau.
Tana ji mutane da yawa na gulmar kyawunta a wajen,suna kuma tsegumi akan kasancewarta gurguwa.Shiyasa tunda ta samu waje ta zauna bata kuma motsawa ba har aka tashi daga walimar.


Lokacin da suka iso gida ana ta kiran sallar magriba.Suna sanyo kansu cikin gidan kenan sukai arba dasu Yah Anas zasu fita zuwa masallaci.
TAIMIYYAH ta ja baya don basu hanya lokacin da Yah Anas ke faɗin, "Wow! Kin ga yadda kika zama wata balarabiya kuwa Sis,gaskiya shigar Abaya tana miki kyau Sister."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin, "Kai Yah Anas banda ziga fa."


Anas ya saki dariya yana cewa, "Ba wani ziga fa,da gaske shigar yai miki kyau TAIMIYYAH."


TAIMIYYAH ta ɗago face don yiwa Anas magana, sai idanunta suka shige cikin na Yah Emran da yai tsaye yana faman ƙare mata kallo.
Tayi saurin fara takawa don barin wajen tana cewa Anas , "Thank u Yah Anas sai kun dawo."


Tuni Anas yayi gaba abinsa ba tare da TAIMIYYAN ta sani ba. Emran daya tsaya kaman wanda aka dasa.Yabi bayanta da wani irin kallon ƙurilla

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login