Showing 51001 words to 54000 words out of 186776 words

Chapter 18 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6576

Friday ne,tun ƙarfe sha biyu na rana TAIMIYYAH ta dawo daga skull.
Wanka ta sake yi sabida yadda ake zabga zafi.Shiyasa take tunanin,watakila zuwa anjima a samu saukan ruwan sama.Don an kwana biyu ba'ayi ruwa a Zarian ba.


Lokacin data fito daga wankan,sai ta nufi wajen kayanta tana zaro wata riga mara nauyi ta saka.Ba tare data maida lace ɗin da ta saka ta je skull da shi ba ɗazu.
Rigan english gown ne me asalin laushin jiki.Ya zauna ajikinta sosai kaman yadda kalan rigan da ya zo a Coffee Brown ya haska farar fatarta.
Kanta bata ɗaura komi ba sai gashinta da ya ke a tsife baƙi siɗik! Wanda ta kama shi da babban Ribbom.Fuskanta yayi fayau sabida bata shafa komi a kan face ɗinba.


Zama tayi daga bakin Bed ta ɗauki wayanta tana kiran layin Yasmeen.Wacce Iyah ta shaida mata cewa sun fita da Guggo Bilki zuwa Rimi Fam House ɗinsu TAIMIYYAN.


So ta ke yi taiwa Yasmeen ɗin tsiya, don sunyi cewa za su jirata har ta dawo su tafi tare.Amma gashi ta dawo ta tadda sun yi tafiyansu.


Sai dai har wayan ya gama ringing Yasmeen ba ta ɗaga ba.TAIMIYYAH ta saki ƙaramin tsaki lokacin da take aje wayan daga gefe,ta miƙe dafe da ƙafanta ta fara takawa don barin ɗakin.


Kitchen ta nufa don samo abin sha kafin a gama girkin rana.Ladi ta samu tana ta faman haɗa tsakin shinkafa da ta turara shi yai shar!Za ta mayar hawa na biyu bayan ta kammala zuba su Zogale da Rama.


"Babah Ladi sannu da aiki,Yau Dambu ake haɗa mana ne, Allah sa dai za a yi wannan haɗin Sauces ɗin?" Cewan TAIMIYYAH lokacin da take buɗe fridge ta ɗakko goran Hollondia Milk me sanyi.
Babah Ladi ta saki murmushi idanunta akan TAIMIYYAH, da tayi mata kyau cikin rigan da ke jikinta,ta furta "Aiko dai ƴar gida na sai dai idan ke ce za ki zo ki mana haɗin,don kinsan ban iya sosai ba tunda ke ce ke yi dama."


TAIMIYYAH ta saki murmushi lokacin data zauna a saman wani kujeran roba da ke kitchen ɗin.


"To Babah Ladi bari mu gani in cikana ya ɗauki madarannan ko zan iya." TAIMIYYAH tayi maganan tana kai kwalin Hollondian bakinta,ta fara sha a hankali.Sai data sha sosai ta aje tana hamdala,ta dubi Babah Ladi tana faɗin "To Babah Ladi ko zaki taimako da Dankalin.Ina daga zaune in fere shi da pillar."




Babah Ladi ta amsawa TAIMIYYAH da "Tuh!" Tana saurin nufan cikin store ta ɗebo Dankalin Turawa, me ɗan yawa kaɗan cikin kwando,ta haɗo da kayan miya da zata taya TAIMIYYAN gyarawa.


Suna aikin su suna hira sai gashi nan da nan TAIMIYYAH,ta kammala haɗa lafiyayyan sauces ɗin Irish with Liver and Vegetables.Da za a ci Dambun shinkafan da shi,gaba ɗaya Kitchen ɗin ya kaure da qamshin spices da akai anfani dashi.


Babah Ladi ke ta faman jerawa TAIMIYYAH sannu.Lokacin data ke tsane hannunta data wanke da ƙaramin towel,ta amsa sannun cikin smile tana barin Kitchen ta nufi falo.


Tana isa falon Iyah na fitowa daga ɗakinta riƙe da carbi, da alamu har ta gabatar da sallan Zuhur ita.


"Iyah sannu da fitowa,har kin yi sallah kenan? Nima bari in shiga daga ciki in yo tawa." Cewan TAIMIYYAH tana wuce Iyah ta nufi ɗakinta don gabatar da sallan.
Lokacin data idar tana zaune tana addu'a,Yasmeen ta shigo ɗakin da sallama.Hakan yasa TAIMIYYAH ɗaga idanunta ta sauke akan Yasmeen ɗin,kafin ta danna mata harara ,tana shafa addu'an data yi take faɗin, "Kin kyauta har kun jirani ai." Yasmeen ta saki dariya tana faɗin,


"Sorry Zaynabu,wallahi laifin Mamie ne da tace kawai mu wuce,kin ga can ma na baro ta wai za su wani anguwa da Anty Fati,ni keke napep na hawo ya maido gida"


TAIMIYYAH ta taɓe baki tana faɗin "To ai da kema an je da ke kawai unguwar baki dawo ki dame ni ba." Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "Ai ko yanzu kina iya maidani can,ƴar rainin hankali kawai.Ina sha ba missn ɗina kika fara ba na ga har da min 2 misscall, irin indawo da wuri ɗinnan." Yadda Yasmeen ta ƙare maganan da kashewa TAIMIYYAH idanu,yasa TAIMIYYAN sakin dariya sosai tana faɗin "Wannan Babyn wallahi ƴar duniya ce ke."


Kafin Yasmeen tace komi kiran Nass ya shigo wayan TAIMIYYAH.Wannan kuma shine kira na biyu a yau ɗin da yayi mata, don kafin ta fita skull ma sun yi waya da shi,ta wani narke face da taɓe baki irin zai takura ta ɗinnan.


Ganin kiran zai yanke yasa ta ɗagawa da kai wayan kunni.Tana amsa sallamansa da sweet voice ɗinta, da ke sake narkar da Zuciyar Nass ɗin.




"Baby hope kin dawo lafiya,ina fata dai ranan yau bai taɓa min ke ba?" Cewan Nass ɗin bayan ya amsa gaisuwan da TAIMIYYAH tai masa.TAIMIYYAH ta wani narke murya tana faɗin, "No bai taɓani sosai ba kam,cox around 12 ma na shigo gida." Yadda tai maganan tana wani shagwaɓa yasa Yasmeen da ta zuba mata ido kwashewa da dariya.Murya can ƙasa ƙasa ta furta "Wow! Shegiya luv ta fara aikinta wallahi,duk mutum ya gama cika baki wannan uwar shagwaɓan sace zuciyan duk ta mecece?" Ta ƙare maganan tana sakin dariya cike da tsokana.Ita ko TAIMIYYAH sai faman danno mata harara take,ba daman kulata tunda Nass ɗin yana mata magana.


Sun daɗe sosai da Nass ɗin suna waya.Yana faman zuba mata hira,da gaya mata kalamai na sace zuciya.Daga ƙarshe sukai sallama akan cewa sai ya sake kira zuwa anjima.


TAIMIYYAH bayan ta sauke wayan daga kunni ne,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Wallahi Yasmeen kin shiga uku da sanya ido,in banda gulma ma miye na wani zama ki tasa ni gaba da kallo, har ki ga me nake yi."


Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "An zauna ɗin,nima course nake so inyi, kona samu in iya irin wannan shagwaɓar da zan sake sace zuciyan Aliyu na."
Suka saki dariya a tare lokacin da Yasmeen ta kai ƙashen maganan,kafin su rankaya su fito zuwa falon Iyah don yin Lunch.


Suna cin abincin ne suna hiran su kaɗan kaɗan.Sunyi nisa cikin cin abincin, Zuhurah da Anty Laurat suka shigo ɗauke da abincin Iya.


Direct wajen cin abincin suka nufo suna aje kulolin abincin daga gaba kaɗan.TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta tana dubansu kafin ta furta, "Sannunku Anty Laurat."


Laurat ta saki murmushi tana faɗin "Yauwa sannu Besty,ashe kin dawo skull ɗin koda yake yau Friday, na manta da wuri ku ke tashi." Ta ƙare maganan tana zama kusa da TAIMIYYAN.Ita ko Zuhurah sai ta samu kusa da Yasmeen ta zauna suna magana, ba tare da tabi ta kan sannnun da TAIMIYYAH tai musu ba.Yasmeen suka gaisa da Laurat,tana musu tayin cin Dambun da a kallo ɗaya Laurat ta ji ya shiga ranta.Hakan yasa ba ta wani ɓata lokaci ba wajen ɗaukan spoon ta fara ci,daɗin Dambun dana sauces ɗin da akai masa na ratsata.
Ita ko Zuhurah cewa tayi bata ci ,sabida ita ƴar gaye ce ba ta cin Dambu.Shiyasa ma ta baro wajen cin abincin ta nufi cikin falo don gaida Iyah,wacce ke zaune ta kunna TV tana kallon tashar Saudi Sunnah.
Da sakin fuska ta amsa gaisuwar jikanyan nata tana faɗin "Yau an ga daman shigowa gaida ni kenan,ya uwar ta ku?"


"Lafiya lau Iyah,ai dama ke ɗin ce baki son muna shigowa.Sai kice wai muna hantaran TAIMIYYAH,kaman wasu yara ai yanzu an girma Iyah."
Cewan Zuhurah tana hararan Iyah ƙasa ƙasa.Iyah dake kallonta kar! Ta aika mata daƙuwa tana faɗin "Ungu nan mutumiyar banza,kin harari Zuwairah ne ba Iyah ba.Kuma da kike faɗin kun girma ina girman yake tunda baku fasa ci mata fuska da kiranta da gurguwaba,daɗin abin dai kuma mata ne.Ina jiye muku randa Ubangiji zai nuna muku isar sa da ikonsa,shashashai kawai marasa tunani.Inma banda sakarci ku taso tare gunin sha'awa, lokaci ɗaya don uwar ku na muku huɗuban tsiya,sai ku biye tata ku watsar da haɗin kan da kuka ta so da shi.A ce Sadeeq ne kawai me hankali a cikinku da bai biye ta uwar na ku, tunda shi yasan abinda ya ke yi.To ku dai bi a hankali ni gaskiya na ke faɗa muku,ku da kuke ganin ba'a jarabce ku da nakasanba ba wai kun fita bane.Haka Allah yaga dama ya bar ku, itama kuma bawai baya son ta bane da ya mayar da ita hakan.Ni dai ina muku nasiha da ku haɗa kai ku so juna kuyi zumunci a tsakanin ku,idan kuma baku ji ba akwai ranan da za ku yi nadama yana zuwa."
Daga haka Iyah ta maida hankalinta kan TV. Bata sake bi takan Zuhurah da ke wani kumbure kumburen fuska ba,daga ƙarshe ma ta koma can ƙarshen kujeran falon ta zauna tana danna waya.
Dawowan su TAIMIYYAH cikin falon yasa Zuhurah maida hankalinta wajen Yasmeen suna hira.Ita kuma TAIMIYYAH suna hiran su da Anty Laurat, akan wani online class da zasu shiga, na koyan yadda ake haɗa Graphics.


Su Zuhuran sun daɗe sosai a Sasan Iyah, don har Guggo Bilki ta dawo suna nan,sai da aka kira la'asar sannan suka bar Sasan Iyah.




*Around,8:45Pm.*


Su TAIMIYYAH ne zaune gaba ɗayansu suna yin Dinner.Bayan ita da Yasmeen sun dawo daga gaida Baba Sani,da ya dawo ɗazu da Magriba.


TAIMIYYAH ita ce tai sarving Iya da Guggo Bilki tuwan shinkafa miyan taushe.Wanda aka wadata miyan da naman kan sa,da zallan tsokar kaza sai qamshi yake.


Bayan ta gama zuba ma su Iyah, ita sai ta zuba Rice and Stew da aka kawo daga Sasan Baba Sani.Ta zabga uban haɗin Salad da ya rinjayi rabin shinkafar da ta zuba ɗin.


Yasmeen kuwa ita tuwan ta zuba tana ci,kaman su Iyah. TAIMIYYYAH kaɗai ce dama bata faye son tuwan Rice ba sam!


Sunyi nisa cikin cin abincin,sallaman Yah Sadeeq daga can ƙofan shigowa falo ya katse musu ɗan hiran da suke yi.Iyah ce ta ɗaga murya tana amsa masa sallaman, da bashi izinin shigowa.


Lokacin da ya iso cikin falon tuni qamshinsa na turaren BENTLEY ya gama isowa hancin TAIMIYYAH.Ta ɗaga manyan idanunta tana kallonsa a lokacin da yake ƙarisowa har wajen da suke cin abincin,ya samu wajen zama kusa da Guggo Bilki yana gaisheta.Ta amsa cike da kulawa tana faɗin "Su Sadeeku an zama magidanci auren kawai ya rage,gaskiya ayi a fito min da suruka haka nan." Ta ƙare maganan cike tsokana,shi ko Yah Sadeeq ɗin sai ya maida dubansa wajen da su TAIMIYYAH ze zaune yana amsa gaisuwan Yasmeen,kafin ya baiwa ya mai da wa Guggo Bilki martani da faɗin "Soon zan fito da ita Guggo Bilki ku dai kawai ku taya ni addu'a." Ya ƙare maganan yana maida hankalinsa wajen Iya ya gaida ta,ta amsa da kulawa kafin muryan TAIMIYYAH ya ratsa kunnuwansa tana faɗin "Yah Deeku sannu da zuwa ina yini." Sadeeq ya ɗaura manyan idanunsa akanta yana faɗin "Lafiya lau Baby ya skull?" TAIMIYYAH ta dubesa tana bashi amsa da "Lafiya lau Yah Deeku." Sai dai kafin Yah Deekun yace komi wayan TAIMIYYAH ya fara haske alamun shigowan kira,sai tayi saurin duban screen ɗin wayan don ganin waye me kiran? Idanunta suka sauka akan sunan da tai saving da NASS,sai kawai ta ɗauke kai ta basar da kiran har ya yanke ba ta ɗaga ba.Lokacin da wani kiran ya shigo dai-dai da sallaman Megadi ne daga bakin ƙofa,Yasmeen ta amsa sallaman Baba Megadin tana tambayansa ko lafiya? Kansa tsaye ya furta "Ranki ya daɗe baƙon TAIMIYYAH ne ya iso yana waje,shine yace don Allah na isar da saƙo ya kira bata ɗaga ba,a shigo da shi kaman wancan lokacin?" Iya tayi karaf ta amsa da faɗin "Eh! Kace ya shigo sai ka aje musu kujeru kaman yadda ka yi wancan karon." Tukur Megadi ya amsa da "Angama Hajiya." Daga haka ya bar wajen don zuwa ya aiwatar da umurnin Iya,daga cikin falon Iyan kuwa Yah Sadeeq ne ya zubawa TAIMIYYAH idanu babu ko ƙiftwa,zuciyansa na wani irin gudu da baisan dalili ba.Ita ko TAIMIYYAH tai ƙasa da kai takaicin duniya na rufeta na yadda Nass zai zo bai sanar mata ba,bayan sunyi waya har sau uku a yau ɗin,ta kasa kallon kowa sabida kunyan da ya mamayeta.Muryan Iya ne ya shiga kunnuwanta inda take faɗin "Maza tashi ki je kinyi wani zaune kaman mara gaskiya,Yasmeen rakata ku je in kun gaisa sai ki dawo ki ɗaukar masa ruwa da lemu." Iya tayi maganan cike da bada umurni,hakan yasa daga Yasmeen har TAIMIYYAN suka miƙe simi simi Suka nufi hanyan ɗakin TAIMIYYAN,Sadeeq ya bi bayan TAIMIYYAN da kallo tamkar idanunsa za su faɗo ƙasa,tuni yaji wani irin duhu na mamaye zuciyansa,bai kuma cewa komi ba ya miƙewa ya bar falon.Daga Iya har Guggo Bilki da tausayin Sadeeq ɗin ya kama su ka bi shi da ido,Iya na faman taɓe baki.Guggo Bilki ta furta "Allah sarki! Da gaske Sadeeq soyayyar TAIMIYYAH ya yi masa kamu me kyau,da alamu dannewa kawai yake don yasan hakan shine mafita tunda uwarsa ba ta so,wallahi tausayi yake bani sosai Iya." Iya ta sake taɓe baki tana faɗin "Sai haƙury Bilkisu don ni tausayinsa ba zai rufe min ido ayi abinda zai zo ya cuci baiwar Allah ina ji ina gani ba,don yadda Zuwairah ke nunawa yarinyar ƙiyayyah tun tana ƙarama abin bana lafiya ba ne.To kin ga ina zan yadda in ɗaure gindi ayi haɗin zumunci su haɗu da uwarsa da qannensa suna cusguna mata,o'o'oh! Gara kowa Allah ya haɗa shi da dai-dai shi." Iya ta ƙare maganan tana tashi ma ta barwa Guggo Bilki wajen,don ita sam bata ma son ana ɗakko maganan wai Sadeeq na son TAIMIYYAH.




Sanye da dogon Hijab TAIMIYYAH ta fito kalan Coffee da ya haske fuskarta.Ita kuma Yasmeen ta yane kanta da babban Veil hannunta riƙe da wayanta,suka wuce Guggo Bilki suka nufi can wajen Nass,wanda tuni ya jima da shigowa cikin Compound,yana zaune bisa ɗaya daga cikin fararen roba guda biyu da Tukur ya aje,bayan ya sanya farin tebur daga tsakiya idan za'a iya aje abin motsa baki akai.




Tunda su TAIMIYYAH suka fito daga Sasan Iya,idanun Nass ke kan TAIMIYYAN yana kallon yadda suke jerowa da juna cikin nutsuwa,salon tafiyan TAIMIYYAN na motsa zuciyansa matuƙa.Tare da jin ƙarin ƙaunar ta da tsa-tsan tausayinta na sake ratsa jinin jikinsa.........✍🏻






Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*










#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 28*


__________Lokacin da su TAIMIYYAH suka ƙariso wajen.Nass ne yayi saurin tashi yana janye ɗaya kujeran baya TAIMIYYAH ta zauna,yana faɗin,


"Ran Babyna ya daɗe, barkan ku da fitowa.


Yasmeen ta saki murmushi tana gaida Nass,ya amsa da sakin fuska sosai,sai lokacin TAIMIYAH ta saci kallonsa.Yana sanye cikin wata Light Brown Wagan-bari,da ya yi masa matuƙar kyau.Kansa sanye da hulan ƙube daya zauna akan sosai,sai qamshin AZZORO WANTED,ke tashi a wajen.


Yasmeen komawa tayi cikin gida bayan sun gama da Nass ɗin,don kawo masa lemu da ruwa,kaman yadda Iyah tace.


Har Yasmeen ta kusa isa bakin ƙofan shiga Sasan Iyah.ta jiyo muryan Yah Sadeeq na kiran sunanta.
Hakan yasa ta waiwaya tana hangosa daga can wajen parking space na gidan.Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa,sai ta juya tana takawa zuwa wajen nasa.
Ta tsaya daga gefen damansa tana faɗin ,"Yah Sadeeq kaine anan,gani tuh."


Ya ɗaga manyan idanunsa da suka sauya launi.Yana kallon Yasmeen ɗin cikin ido yake faɗin,


"Waye wancan Guy ɗin Yasmeen,tell me yaushe ta fata sauraransa?"


Ya yi maganan cikin very low voice,daya sanya Yasmeen saurin dubansa.Ya aika mata harara yana faɗin "Amsa zaki bani ko kallona zaki tsaya yi?"


"Kayi haƙury Yah Sadeeq,ni ma bansan yaushe ya fara zuwa ba,amma dai bana jin sun kai 2 weeks da haɗuwa."
Yasmeen tayi maganan tana gujewa sake duban fuskarsa.Shi kuma ya wani sauke numfashi a hankali yana faɗin "Aright! go."


Daga haka bai sake cewa komi ba.Ya buɗe front seat na motansa ya zauna,yana me jingina jikinsa da jikin seat ɗin sosai,tare da maida idanunsa ya lumshe.Zuciyansa na sake ɗaukan wani irin zafi da suya,gaba ɗaya soyayyan TAIMIYYAH da yake ƙoƙarin adanawa ya binnesa can ƙasan zuciyansa ne ya taso baki ɗaya.


Don a yanzu gaba ɗaya wani irin zazzafar soyayyarta haɗi da kishinta me tsananin zafi yake ji.Irin wanda bai taɓa tunanin zai ji ba.


'Yaushe TAIMIYYAH ta fara soyayyah ba tare da ya sani ba.A ina ta haɗu da gayen kuma shin tana son shi kenan,da har ta bashi daman zuwa wajenta taɗi?"


Waɗannan tarin tambayoyin ne suka haɗu suna amsa kuwwa! A tsakar kansa.Ba ya ji kuma zai iya rintsarawa a daren yau ba tare da yaji amsa daga bakin TAIMIYYAH ba.


Yasmeen kuwa bayan ta baro wajen Yah Sadeeq ɗin.Tana tafe ne tana mamakin yadda duk ya wani birkice daga ganin TAIMIYYAH da wani.Don ita ta ɗauka cewa tunda ya haƙura da TAIMIYYAN idan ya ganta da wani bazai ji komi ba,har ta kai Sasan Iyah mamaki bai bar zuciyanta sukuni ba.


Direct kitchen ta nufa ta ɗauki madaidaicin Tray.Ta ɗaura ruwa biyu da Juice ɗin 5alive Babba guda ɗaya,sai ta ɗauki Glass cup guda ɗaya ta ɗaura akai,sannan ta fito don zuwa ta kaima su TAIMIYYAH.


Ko da ta kai ta aje TAIMIYYAH taso Yasmeen ɗin ta tsaya a wajen,amma fir Yasmeen taƙi tayi komawanta Sasan Iyah.
Nass ya cigaba da zubawa TAIMIYYAH kalaman Luv masu ratsa zuciya.A lokacin ne kuma yake sanar mata cewa gobe zai wuce Kd ne,daga can kuma ran Sunday ya wuce Abuja.
Dama hutu ya ɗauka na 2 weeks gashi kuma hutun ya ƙare.Dole Monday zai shiga office, ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai take tana amsa shi da eh! ko umm!


Ya ɗauki a ƙallah awa ɗaya da wasu mintuna kafin yai mata sallama don wucewa gida.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tana ɗan dafa kujeran da ta tashi,idanunta a ƙasa take faɗin "To Allah ya kiyaye ya tsare hanya agaida su Mama."


Yadda take magana cikin sanyi da wani irin narke murya,ba ƙaramin motsa zuciyan Nass yake ba.Ya tsura mata ido yana sake ganin yadda kalan Hijab ɗin da ta sanya yai mata kyau matuƙa,ya zura hannu cikin aljihu yana faɗin,


"Thank u Luv,za su ji insha Allah,sai dai please ki bar wayanki a kunne, ina isa gida zan kira muyi gud night call, kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login