Showing 39001 words to 42000 words out of 186776 words
Chapter 14 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
roba domin sai da suka samu 50pcs cas,don haka TAIMIYYAH ta zuba cikin wani roba me murfi aka baiwa Ayuba almajirin Iya,ya miƙa gidan Alhaji Bala wani maƙwafcin su Iya,me kirki hakama matarsa Anty Hannah mutumiyan TAIMIYYAN ce sosai,bayan TAIMIYYAH ta ɗibi wanda zai ishe su ita da su Iya,sai tace da Anty Laurat ɗin ta wuce da sauran duka kawai Sasan Baba Sanin,Anty Laurat ɗin tai godia cike da murnan yadda ta samu experience na kwaɓin Doughnut,wanda ita idan tayi tauri yake sabida rashin ƙwarewa,sai gashi yanzu ta gano bakin zaren cikin sauƙi.
Lokacin da ta isa Sasan su Umman ba kunya su Zuhurah suka tare ta,suna amshe roban Doughnut ɗin suka shiga ɗauka suna kaiwa baka,babu kunya babu tsoran Allah kaman ba maƙiyiyansu TAIMIYYAN ce ta sarrafashi ba,ita kanta Umma har cewa tayi Anty Laurat ɗin ta ɗibar mata wani zuwa dare da shi zata sha Tea kafin ta kwanta,tunda ita mayyan shan Tea ce kafin tai bacci,Anty Laurat dai kallon su kawai take tana jinjina rashin kunya irin na wasu mutanen,in banda haka wanda kace kana adawa dashi kana kushe halittansa miye na rawan jikin cin abinda ya fito daga hannun wacce su ke kira da musaka gurguwa? Ta haɗiye takaicin su Zuhuran da ke cinta arai tana musu addu'an Allah ya shiryesu kawai.......✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
*Page 22 to23*
________ Satin TAIMIYYAH biyu kenan da fara zuwa Computer training ɗin.Ta saba sosai,tana kuma sahun farko na ɗaliban da ke matuƙar ƙoƙari,domin duk abinda akayi da ta dawo take zama ta kunna System ɗinta tana gwadawa.
A hankali kuma suka fara sabo da Zee wacce da gaske ita son su ƙullah ƙawance da TAIMIYYAN ta ke yi,don tsakaninta da Allah TAIMIYYAN na matuƙar birge ta.Tun TAIMIYYAH ba ta sake mata har ta fara sabawa da yawan surutun Zee ɗin,don wani lokacin bayan an tashi sukan jima suna hira daga bakin gate ɗin fita wajen kafin ta samu abin hawa kowacce ta kama gabanta.
Sani shi ke kai TAIMIYYAN ita kuma ta maido kanta gida idan an tashi.To yauma kamar kullum bayan sun gama zantawa da Zee Haroun ɗin sai ta tare wa TAIMIYYAH Napep.TAIMIYYAN ta hau sukai sallama suna ɗagawa juna hannu.
Lokacin da TAIMIYYAH suka iso layinsu sam bata kula da motar da ke biye da Napep ɗin data hawo ba.Bayan ta sauka tana ba me Napep ɗin kuɗinsa ne kaman ance ta ɗaga idanunta zuwa farkon shigowa layin,sai ta hangi wata farar mota na yin reverse tana komawa da baya.Bata kawo komi cikin ranta ba ta amshi canjinta da me adaidaitan ke miƙo mata,tayi shigewanta gida. Sallah kawai tayi ta fito cin abinci,tana jin ɗakin tsit don Iyah bata nan ta fita can ƙasan layin nasu anyi wani rasuwa.Taje gaisuwa Ladi ce kawai a Sasan,kuma tana ɗakinta da ke daga waje.Don haka TAIMIYYAH na gama cin abincin ta shige ɗaki don kwanciya,ta riga tayi sabo da yin baccin rana duk idan ta dawo.
Bata wani jima da kwanciyan ba bacci yai gaba da ita,don haka ta tashi ne ta ga har huɗu na yamma ta gota.Tayi saurin faɗawa toilet ta ɗauro alwala,ta fito ta gabatar da sallah.Ko data idar wayanta kawai ta ɗauka ta fito falo,Iyah ta samu da itama fitowanta falon kenan daga ɗaki bayan tayi sallah.TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana faɗin "Iyah ashe har kin dawo, ina ta faman bacci sannu da dawowa."
"Yauwa sannu Zainabu,aina leƙa ki na ga kina bacci,ya karatun Allah yayi albarka." Cewan Iyah TAIMIYYAH na amsawa da "Da Ameen." Kafin ta aje wayanta saman kujera tana faɗin "Iyah bari in zubo furannan na jiya da ban samu sha ba ai nasan bai komai ba tunda yana cikin Fridge.Wani yinwa nake ji amma na kwaɗayi bana abinci ba." Tayi maganan tana ɗan dariya Iyah ta aika mata harara tana faɗin "Aifa nan kika fi auki,a wajen kwaɗayi saura ki kwashe min madara duk ki lafta a cikin furan.Duk da dai ubanki da Sani ke sayan madaran."
TAIMIYYAH dai dariya kawai ta ke yi har ta shige Kitchen ɗin tana ma Ladi sannu da aiki.Ladi wacce take aikin wanke kuɓewan da xata yanka, ta amsa TAIMIYYAH da fara'a kafin TAIMIYYAN ta ɗaura da faɗin "Babah Ladi yau kice miyan kuɓewa za mu sha,da tuwan Semo ne ko tuwan shinkafa?" TAIMIYYAH tayi maganan lokacin da take ciro Jug ɗin data aje furan a ciki.Ta tsiyayi iya wanda zai mata tana maida sauran cikin Fridge ɗin,Ladi ta saki murmushi tana faɗin "Ai mutumiyata da tuwan Semo ɗin ne, don itama Iyah ta san kinfi son shi ai."
"Wow! Aiko bari ki gani in gama shan furan nan inzo in amshi yin miyan,ke sai kiji da yin tuwon Babah Ladi." Cewan TAIMIYYAH tana dafe da ƙafanta me laluran tana tafiya don fita daga Kitchen ɗin.
Ladi na faɗin "Yauwa ƴar gida na jeki ki dawo ɗin indai miya ne sai ki zo ki mana irin naki me daɗinnan." Ta ƙare maganan cike da raha ƙaunar TAIMIYYAN na sake kama zuciyanta.Don baƙaramin birgeta yarinyan ke yiba,gefe guda tana tausayinta har cikin ranta tare da yi mata addu'an samun mijin da zai ƙaunace ta tsakaninsa da Allah.
Kaman yadda TAIMIYYAH tace tana gama shan furan da ta narkawa uban madara,ta nufo kitchen ɗin.Ta isa wajen Sink tana wanke cup ɗin da ta ɓata ta kife,direct wajen da Ladi ta aje kayayyakin yin miyan ta nufa.Tana duba duk abubuwan da Ladin ta aje, tashin farko sai data ƙaro yawan naman da za'a zuba a cikin miyan.Cikin ƙwarewa ta tada haɗin miyan ɗanyar kuɓewan,wanda ke ta faman zuba qamshi yaji naman shanu haɗi da ƙashin naman rago.Sosai miyan yai yauƙi yai kyau a ido sosai.
Bayan ta kammala barin kitchen ɗin tayi Ladi na faman jera mata sannu.basu jima da Iyah ba suna kallo aka fara kiran Magrib, hakan yasa duk suka nufi ɗaki don yin sallah.Ko da TAIMIYYAH ta idar karatun Qur'ani ta cigaba da rerowa cikin ƙira'anta me taushi da daɗin amo.Sai da akai kiran Isha'i tana zaune tana rero karatun ta,kafin ta tashi ta gabatar da sallan ishan.Sannan ta fito falo,zuwa lokacin itama Iyah ta fito sai suka nufi wajen zaman cin abincinsu.TAIMIYYAH na zama ta fara buɗe kulolin da aka kawo abincin dare daga Sanan Baba Sani.Ganin Cous Cous da miya suka yi yasa ta rufe kulolin tana taɓe baki,don ita sam bata fiya son Cous Cous ba.Garama idan jallop ɗinsa akayi yaji liver da kayan lambu a wadatashi da Irish kuma,to zata ci sosai amma indai da miya ne bata so.
Ƙullin tuwo ɗaya ta juye a plate ta zuba miya,tana janyo roban yajinta daga saman wani ɗan cabinet da akai a wajen suna ɗaura tarkacen su cups da su plates.Sunyi nisa a cin abincin su babu me magana,Tukur mai-gadi yayi sallama daga bakin ƙofan shigowa falon Iyah.Iyah ta tsame hannunta daga plate ɗin tuwan ta tana amsa sallaman Tukur,tare da faɗin "Malam Tukur lafiya dai ko?"
Daga waje Tukur ya amsawa Iyah da faɗin "Lafiya lau Hajiya,wani ne dama yazo a wata farar mota yace inyi masa sallama da TAIMIYYAH.To yadda ya kwatanta min tafiyanta da siffanta ne na gane TAIMIYYAN yake nufi,shine nazo isar da saƙo."
"To madallah je kace masa tana zuwa.Amma ka shaida masa ya ɗan shigo daga cikin gidan sai ka sanya fararen kujerun nan daga wajen shigowa nan ya zauna ya jirayi fitowanta.Don tsayuwannan daga waje akan layi mutane na gilmayya ba mutunci bane,gara ya shigo nan ɗin kana aikinka idanunka na kansu hakan zaifi."
Cewan Iyah tana kallon yadda TAIMIYYAH ta dakata daga cin abincinta.Fuskannan ta cuskune shi kaman zata fashe da ihu,shi ko daga waje Tukur ke faɗin "An gama Ranki ya daɗe sai ta fito ɗin,bari inje inyi yadda kika ce." Daga haka yabar wajen ya fice daga Sasan baki ɗaya don zuwa isar da saƙon Iyah wajen Matashin saurayin.
"Yanzu Iyah daga cewa ana sallama sai ki wani ce a shigo da mutum ciki,baki san ko waye ba haka akeyi? Ni gaskiya da kin rabu da shi an sallamesa ni bansan waye ba kawai sai inkama fita wajen......"
"Dallah! Rufe min baki,ki kuma tashi kije ki samu koma waye ɗin.Ina sha idan kin fitan idanunki zasu gane miki? Da kike cewa waye waye ba sai an ba mutum dama ake sanin ko shi waye ɗin ba.Bana son sakarci maza kije ki sanyo Hijab ki fita,kin dinga zama kenan ana zuba miki ido ba za ki fitar da miji kiyi aure ba,sabida kawai kina da lalura to tun ba'a ji kanmu ba ki tashi ki fita."
Iya tayi maganan cike da faɗa sosai.Idanunta akan TAIMIYYAH da har idanunta sun fara tara ƙwallah,amma musu da Iyah ta san ba abune da zai yiwu mata ba.Musamman yadda ta ɗauki zafin nan,sai kawai ta miƙe tana barin plate ɗin tuwan da take ci ba don ta ƙoshi ba.ko da ta shiga ɗakinta sai data ɗaurayo bakinta da Mouth Wash a toilet,sannan tazo ta zura Hijab ɗin sallan ta.Ta fito ta wuce Iyah fuskanta ko kaɗan babu annuri,ga ƙirjinta da ke faman dakan lugude har ta fito daga Sasan Iyah.
Daga gaba kaɗan ta hango inda Tukur ya jera musu fararan Kujeru biyu.Mutumin da sam bata hango fuskansa ba yana kame saman kujeran.Ta ɗauke kai tana takawa zuwa wajensa bisa tsarin halittan da Allah ya nufeta da takawa ahakan.
Tun da TAIMIYYAH ta doso shi idanunsa ke kafe akanta ƙur...! Har ta ƙariso ta ja kujeran ta zauna,kanta a ƙasa take faɗin "Assalamu alaikum." Ya amsa da "Wa'alaikissam warahmatullah wabarakatuh! Ranki ya daɗe barka da fitowa."
TAIMIYYAH ko kaɗan bata yi gigin ɗago fuskanta daga sunkuyar dashi da ta yi ƙasa ba.Ta amsa masa da "Barka dai ina yini ina gajiya."
Matashin da idanunsa ke kanta, ya saki murmushi har haƙoransa na bayyana.Kafin ya furta "Lafiya lau Sarauniyata! Nasan za kiyi mamakin yadda na samu address ɗin gidan ku,har na kawo kaina zuwa gareki.To hakan ba wani abun mamaki bane,idan akai la'akari da yadda shi masoyi a kullum burinsa shine dama ya iso wajen abin son sa.Zan kai kaman sati guda ina bibiyan duk wani motsinki,a wajen da kike zuwa yin Computer training.To a jiyane na samu nasaran biyo bayanki a motata,ke kuma kina cikin a daidaita. Malama TAIMIYYAH kaman yadda naji Baba Mai-gadi yace,ga Naseer zaune a gabanki ya kuma zo da ƙoƙon baransa ne,akan ki daure ki bashi dama ya shiga cikin sahun manema.Banzo da wasa ba ni da gaske nake aure nake son yi nan ba da jimawa ba.Idan har nayi nasaran samun zuciyanki,sabida shekaru kullum ƙara turawa suke TAIMIYTAHH." Yadda yaja sunanta cikin wani irin salo ya tilasta mata ɗago manyan idanunta ta dubesa.Haske ne ƙau ƙaman rana domin wajen akwai wadatan manyan fitillu masu haske,wanda Abie ne duk ya saka aka sanyasu,har da manyan fitillun sola da ke aiki ko da babu wuta wajen baya rabo da haske.Hakan yasa TAIMIYYAH samun daman kallonsa.
Baƙi ne amma yana da kyau dai-dai misali,musamman manyan idanunsa da giransa masu kauri,sai ƙaramin bakinsa masu ɗauke da cute lips masu kauri.Sune abinda suka sake qawata kyawun fuskarsa.
A kallo ɗaya za ka san dogo ne ko bai miƙe ba.Yana sanye da fararan kaya tas da sukai masa kyau,daga yanayin shigan nasa zaka iya fahimtan ɗan gaye ne sosai,ma'abocin sanin kan iya sanya kaya.Daddaɗan qamshin turaren AZZARO WANTED ya gama mamaye wajen,duk TAIMIYYAH ta ƙare masa kallo ne cikin daƙiƙa kaɗan.Ba kuma kai tsaye tayi hakan ba,don sam bata ji ma zai gane tayi masa kallon da tai masan.
Ta sake yin ƙasa kanta sosai kafin ta fara magana cikin sanyin muryarta tana faɗin "Bawan Allah naji duk kalamanka,amma sai dai kayi haƙury ni babu maganan yin soyayya da kowa ma a lissafina.Karatu nake so,shine kuma kaɗai a cikin lissafina.Kuma in banda abinka taya soyayyah zai ƙullu tsakanin gurguwa da me ƙafafunsa biyu lafiya?Kaga kaman bazai yiwu ba,don haka kayi haƙury tunda aure kake so zan tayaka da addu'an Allah ya zaɓa maka ta gari lafiyayya wacce ba gurguwa ba."
Tunda TAIMIYYAH ta fara magana Naseer ya tsura mata ido,wani abu na sake yawo a ilahirin jinin jikinsa.A yanzu kawai da take gabansa sai ya ga kaman an sake ninka kyawunta ne,gaba ɗaya sai yaji duk yadda yake hasaso jin muryarta,sai yaji zaƙi da taushin muryan har ya zarce tunaninsa.
Ya saki wani ƙayataccen murmushin da suka bayyana jerarrun haƙoransa,yana faɗin "Malama TAIMIYYAH kenan,kece kike ganin hakan,amma ni ke na hango a hakan kika kuma tafi da dukkanin zuciyata da nutsuwata.Idanuna sun fi naki yawatawa akan tarin ƴan mata kala kala,amma ni gurguwan dai itace zaɓi na.Idan har zaki amince ki bani dama zan tabbatar miki da gaske ƙaunarki nake da dukkanin zuciyata.Don haka ki aje wannan maganan a gefe,yanzu dai ki sanar dani wani abu akanki ko da kaɗan ne please TAIMIYYAHH."
Ya kai ƙarshen maganan a wannan ƙaron ma cikin jan ƙarshen harafin sunanta,da wani irin salo da ya sake fisgan hankalin TAIMIYYAH.Har ta sake ɗago idanunta akaro na biyu ta aza akansa,amma ganin yadda ya tsura mata nasa idanun ya sata saurin sake yin ƙasa da kanta.Wani matsanancin kunya na lulluɓeta,ta wani tunzuro baki gaba alamun kallon na bata haushi.Sai dai duk abinda take yi yana gani kuma tana sake motsa zuciyansa ne ba tare da tasani ba.
Ganin bata da alamun sake tanka masa yasa shi buɗe baki don yin magana,amma sai isowan Anty Laurat da sallamanta ya katse hanzarinsa.Kusan a tare suka waiwayo suna duban Anty Laurat data ƙariso wajen sosai,fitowa tayi za ta maida roban da ta tafi da Doughnut aciki.Shine tana dosowa don shi ga Sasan Iyah ta hango TAIMIYYAN da baƙo shine ta zarto don tayi tsokana.Sallamanta Naseer ya amsa har da zamowa kaɗan daga kujera yana gaida Anty Laurat ɗin.Ta ko amsa da fara'a tana faɗin "Sannunka da zuwa sirikina,ina fata dai kaine za ka ci nasaran sace min zuciyan wannan Daughter ɗin nawa me gudun maza."
Tayi maganan cike da barkwanci,TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa take faɗin "Kai Anty Laurat."
Yadda tai maganan da salon shagwaɓar ta ba ƙaramin taɓa zuciyan Naseer da idanunsa ke kan TAIMIYYAN ya yi ba.Yayi saurin faɗin "Yauwa Anty nako gode da Allah ya jefo ki,dama na ga alaman sai ta wahalar da zuciyata sosai kafin abani dama.Ko tausayina ma ba'a ji sabida bata san yadda nake jinta a cikin zuciya da gangar jikina ba."
Naseer yayi maganan shi ma yana wani narke murya irin aji tausayinsa ɗinnan.Abinda ya baiwa Laurat dariya kuma nan take ta gane ɗanyi ne shi,irin sune ke saurin sace zuciyan mace.Don haka ta biye masa yana sake fallasa mata irin soyayyar TAIMIYYAN da yake ji.Ita ko TAIMIYYAH sai ta koma ƴar kallo tana jinjina rashin kunya irin ta maza da ake faɗi,da har ya iya zaƙewa yana sakin zance.Anty Laurat itace ta bashi Number ɗin TAIMIYYAH,wacce ta ji kaman ta sanya ihu don takaici.Sai kawai ta miƙe tana barin musu wajen bayan tai masa kallo ɗaya tana faɗin "Sai da safe ni zan shi ga daga ciki."
Ya ɗan ɗaga murya yana faɗin "To ranki ya daɗe amma zuwa anjima don Allah a daure a ɗaga wayata idan nakira.Don bana ji zan iya bacci ban sake jin golden voice ɗinnan ba,please Luv."
Gaba kawai TAIMIYYAH tayi tana faman taɓe baki,zuciyanta na wani irin bugu da bata san dalili ba.Sam ko da wasa ita bata son wani ya shigo rayuwanta,wanin ma wai da sunan soyayyah.Kuma bama gurgu irin ta ba,sam bata ji hakan abu ne me yiwuwa ma.Anty Laurat ne ta cinmata tana gab da shiga Sasan Iyah,suka ƙarisa jerawa tare tana faman zuzutawa TAIMIYYAH haɗuwan Naseer ɗin,tare da bata shawaran don Allah ta bashi dama aga iya gudun ruwansa.Idan har da soyayyan gaskiya yazo ita kam bata ga aibunsa ba, sai ma haɗuwansa.Har da cewa TAIMIYYAN bata ga yadda za su yi matching da juna bane ita da Naseer ɗin.Ita dai TAIMIYYAN jin Anty Laurat ɗin kawai take yi,ko da suka shiga ciki TAIMIYYAH wucewanta tai ɗaki tabar Laurat da Iyah a falo,ita a dole haushin Iyan take ji da ta sanya ta fita wajen Naseer ɗin.
Tana daga ɗaki amma tana jiyo Anty Laurat ɗin nawa Iyah zancen Naseer ɗin.TAIMIYYAH ta cika tai fam! Wani haushi na kamata,ta rasa meyasa ake son jajibu mata zancen aure tana zamanta lafiya.Wayanta ta janyo tayi saurin ɗauka ta kashe ta gaba ɗaya,don gudun karma ta manta ta bar ta a kunne ya samu halin kira don bazata ɗauka ba.Sai kawai ta nufi wajen da take aje littafan islamiyanta ta ɗauki wani littafi tana dubawa,sai da taji fitan Anty Laurat sannan ta fito ta nufi kitchen tana sake ɗebo furan ɗazu ta zuba madara tayo ɗakinta.Bata sake bi takan Iyah da ke zaman jiran ta fito tace mata wani abu game da baƙon ta ba,tana gama shan furan ta nufi toilet ta wanko baki,tare da ɗauro alwala ta fito tai shirin bacci tabi lafiyan gado........✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin