Showing 174001 words to 177000 words out of 186776 words
Chapter 59 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ɗauka wani abin mu ke yi."
Maleek bai shirya yin murmushi ba amma sai da TAIMIYYAH ta sanya shi yin blushing,sabida yadda ta yi maganar kamar za ta saki kuka ba ƙaramin bashi dariya ta yi ba. Ya miƙa hannunsa ya kamo nata hannun tare da yin ƙasa da muryarsa ya ce, "Baby i luv u,please ki kula min da kanki daga nan zuwa anjima, kiss me please! Wife kin ji?"
Yadda ya yi maganar cikin wani irin salonda yadda ya wani miƙo mata fuskarsa, ya sanya TAIMIYYAH saurin rintse idanunta. Zuciyarta na cigaba da bugawa da matsanancin gudu,ga wani uban kunya da ke sake yi mata dabaibayi. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta ta dinga masa magiya akan ita dai ya buɗe mata motar ta fice. Maleek sai ya janyota jikinsa baki ɗayanta yana me kai bakinsa ya manna mata wani hot kiss a saman goshi, ya kamo ƴan yatsunta da zanen lallin da akai mata ya birgesa, su ma ya sumbacesu kafin ya sake ta yana me sake ƙureta da idanunsa da suka sauya kala,sabida zallar rigimar da ya ke ji akanta. TAIMIYYAH ban da rawa babu abinda jikinta ke yi, gani ta ke yi Yasmeen na kallonsu don sam ta manta ma da cewa tint ne glass ɗin motar. Maleek ya yi unlocking motar yana me yinƙurin sake kai hannunsa jikin TAIMIYYAH,amma sai ta yi saurin ɓalle murfin motar tana jefo ƙafarta zuwa waje. Yadda ta so fitowa da hanzari ya sanya ƙafar mara lafiyar gocewa, ta yi kamar za ta kifa sabida bisan da motar ke da shi. Maleek ya yi saurin dawo da ita baya yana cewa, "Haba wife saurin me ki ke yi haka za ki je ki jiwa kanki ciwo,don Allah ki rage wannan tsoron nawa da ki ke ji please!"
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana me saukowa a hankali daga motar,bayan Maleek ya sake furta mata kalamai na soyayya masu zafi,wanda yasa TAIMIYYAH sake narke fuska zuciyarta cike da mamakin lamuran da suka wanzu tsakaninta da Maleek ɗin.
Kallo ɗaya Yasmeen ta yi wa TAIMIYYAH ta ga yadda idanunta suka sha kuka. Fuskarta ta sake yin ja idanunnan sunyi wuƙi-wuƙi, Yasmeen sai ta ji wani irin dariya na son ƙwace mata,da ƙyar ta yi controlling kanta har su kai sallama da Maleek ya wuce,sannan ta dubi TAIMIYYAH da ke tsaye dafe da guiwar ƙafarta ta kwashe da wani irin dariya.
TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska cike da masifa ta ce, "Yasmeen wai mahaukaciya na zama ne da za ki tasa ni gaba kina faman tintsira dariya? Allah idan muka shiga gida sai na haɗaki da Ummie ta yi min iyaka daga iskancin ki."
Yasmeen ta sake kwashewa da dariya ta ce, "Really Matar Maleek Ado? Ke banda abinki daga ina dariyata sai ki ce da ke nake yi,haka ake yi a Zarian na ku dama?"
TAIMIYYAH ta ballawa Yasmeen harara tana me dafe ƙafarta, ta fara takawa don yowa gaba abin ta,ta bar Yasmeen a baya tana faman cigaba da kwasar dariyarta. Sai da suka iso bakin gate ɗin shiga gidan ne Yasmeen ta ce, "Sorry tawan wai fishi ki kai? Ki yi haƙury babyn Maleek idanunki ne suka bani dariya wallahi,sabida daga gani an san sun sha kukan luv ko ƴan matan Maleek?"
TAIMIYYAH ta dubi Yasmeen cikin ido tana ji tamkar ta saki kuka sabida takaicin kwasarta da Yasmeen ɗin ke yi.Ta yi magana cike da masifa ta ce, "Yasmeen don Allah ki bar ni inji da abinda na ke ji,bana son wannan iskancin wallahi. Banda ma sa ido ina ruwanki in ma kukan luv ɗin na yi?"
Yasmeen ta gimtse dariyar da ke cinta a rai ta ce, "Afuwan Alarammiyar Maleek,haka ne babu ruwana wallahi kawai wannan bakin nawa ne da ba a gasa min shi ba,baya iya shiru bai tanka ba."
TAIMIYYAH ta saki dariyar da babu shiri tana faman zabgawa Yasmeen harara ta ce, "Allah ya shiryeki Yasmeen."
Daga haka suka cigaba takawa jere da juna har zuwa cikin part ɗin Ummie.TAIMIYYAH memakon ta nufi ɗakin da friends ɗinta su Zee su ke,sai ta nufi ɗaya bedroom ɗin Ummien da ta yi waya da Maleek ɗazu. So ta ke yi ta kaɗaice ko za ta dawo cikin nutsuwarta,sabida gaba ɗaya lamuran da Maleek ya gudanar akanta sun birkita nutsuwarta baki ɗaya.
Bisa kan gado ta zube tana me yaye lulluɓinta ta yi wurgi da gyalen akan gadon,ta sake gyara kwanciyarta tare da lumshe idanunta gam! Ta kai hannu ta shafa bakinta zuwa ƙirjinta,har lokacin jin hannuwan Maleek ta ke ji na yawo a jikinta. Ta sake rintse idanun wani maganaɗisu na sake zagaye jinin jikinta,ta buɗe idanun tana kai hannunta ta janyo gyalenta,wanda gaba ki ɗaya ya rine da ƙamshin jikin Maleek Ado. Ta kai hancinta kan gyalen tana shaƙar ƙamshin turaren AMOUAGE da ya gama kama jikin gyalen,tamkar Maleek ɗin ne a jikin gyalen sabida yadda mayafin ya kama ƙamshinsa. Wayarta ta fara tsuwwar neman ɗauki sai ta janyo wayar tana zubawa lambobinsa idanu,daf da kiran zai yanke ta iya ɗaga wayar ta kai kunni. Ba ta yi magana ba sai shine ya fara sanar da ita yadda ya ke jin kewarta me tsanani daga rabuwarsu. Ita dai TAIMIYYAH shiru ta yi tana sauraran manyan kalaman da ke fitowa daga bakin Maleek Ado,waɗanda gaba ɗaya suka girmi kwanyarta da tunaninta. Shi ko Maleek ko ajikinsa don wani irin fitinanniyar soyayyarta ce ke azalzalar zuciyarsa, ji ya ke yi tamkar ya rufe ido ya buɗe ya ga an gama duk wani bikin al'ada an barshi da matarsa don ya huta. Sun jima suna wayan kafin ya yi hanging up ya bar TAIMIYYAH da faɗawa duniyar tunanin yadda rayuwar aurenta da shi zai kasance,da irin tarin lamura masu girma da nauyin da za su biyo baya,don bata ga alamun cewa Maleek Ado ya san wani abu wai shi kunya ba. Ta maida idanunta ta lumshe tana sake gyara kwanciyarta,zuciyarta na cigaba da dawo mata da moment ɗinsu na ɗazu tare da Maleek ɗin cikin lafiyayyar motarsa, da irin bidirin da ya yi da jikinta da mouth ɗinta da ya sha tsotso. Daga wannan kwanciyar ne kuma bacci ya sace TAIMIYYAH sabida a gajiye ta ke, sam tunda aka fara hidiman bikin ba ta samun yin wani isasshen bacci.
__________
*GRA,Zaria.*
Suhailah ce kwance a kan gadon ɗakinta tana faman juyi tana kuka,idanunta sun yi asalin kumbura don tun daren jiya ta ke aikin kuka.
Duk iya rarrashi da ban baki haɗi da tarairayarta da Maleek ya dinga yi tun a daren jiyan,bai sanya Suhailah ta saki ranta ta daina kuka ba. Daga ƙarshema sai ta yi ƙaura daga ɗakin Maleek ɗin ta koma ɗakinta ta kulle kanta,dama kuma ta jima da daina bashi jikinta tun lokacin da aka fara maganar auren gadan-gadan, sai ta ƙauracewa shinfiɗarsa bisa ga huɗubar Jawahir da Suhailah ta hau kai ta zauna daram! Don gani ta ke yi duk duniya Jawahir ɗin ce kawai me ƙaunarta da tausayinta akan lamarin auren Maleek ɗin.
To yau tun safe ta sake kafa wani sabon babin kukan, akan kunnuwanta Maleek ya dinga knocking yana rarrashinta akan ta buɗe masa ƙofar ɗakin amma ta yi biris da shi. Haka ya gaji ya fita a sabgarta ya je ya yi shirin zuwa ɗaura aurensa ya bar mata gidan,abinda ya sake ɗaga hankalinta kenan tare da jefa zuciyarta cikin matsanancin baƙin ciki,sabida akan idanunta motar Maleek ya fice daga gidan. Tana daga tsaye tana leƙensa ta window ɗin bedroom ɗinta,da ke kallon harabar parking space ɗinsu ta waje.
Ta ɗaga idanunta ta kalli a gogon ɗakin lokacin da ya buga ƙarfe goma sha biyu na rana. Ta sake rushewa da wani irin kuka me cin rai,sabida kwakwalwarta ta gama sanar da ita cewa, zuwa yanzu Maleek ɗinta ya sake zama mallakin wata mace ba ita ba.
Ta sakko daga kan gadonta tana jin yadda wani irin jiri ke neman kayar da ita,sabida yunwar da ke ɗawainiya da ita don bata sanya komi a bakinta ba tun safe, har kawo yanzu ɗin da agogo ke nuna sha biyu na rana. Haka ta dinga takawa tana rangaji har ta isa inda jakarta ta ke,wacce ta zo da ita daga Abuja randa suka iso tare da Maleek ɗin.
Ta ɗauki jakar tana me komawa kan gado ta zauna,tare da buɗe jakar tana ciro wani ƙullin leda ta warware shi. Ta ke wasu layu guda biyu suka bayyana,Suhailah hannunta na rawa ta ɗauke su tana juya su a tafin hannunta. Zuciyarta na sake shiga cikin matsanancin ruɗani,tana jin wani matsanancin tsoro na lulluɓe zuciyarta. Maganar da Jawahir ta gaya mata sanda ta kawo mata layun na dawo mata cikin kwanyarta,tamkar a lokacin jawahir ɗin ke furta kalaman in da ta ke cewa,
" _Suhailah da zaran an ɗaura auren ki yi gaggawar birne waɗannan layun, kafin cikar awa ashirin da huɗu da ɗaura auren,idan har ya wuce waɗannan awannin baki rufe su ba,to shikenan kuɗinki ya tafi a banza,don ko kin birne bayan cikar awa ashirin da huɗu babu tasirin da hakan zai yi, don haka da zaran an ɗaura kawai ki san yadda ki ka yi suka shiga ƙarƙashin ƙasa._ "
Suhailah ta sake damƙe layun a cikin hannunta,hawaye masu tsananin zafi da ƙuna na sake biyo fuskarta. Maganar da Jawahir ta yi akan tasirin birne layun na haskawa a cikin kanta,
" _Da zaran kin birne layunnan Suhailah,shikenan zai ji ya tsaneta ba zai iya rayuwar aure da ita ba,don suna haɗuwa da juna zai dinga ji tana masa wani irin wari,wanda hakan zai jefa ƙiyayyarta me tsanani a cikin zuciyarsa,kuma ba zai yi sukuni ba har sai ya sake ta.Don haka ki cire duk wani tsoro da fargaba Suhailah,da zaran kin yi yadda aka ce shikenan kin gama da matsalar kishiya,ni kuma daga baya zan kai ki inda za ki mallake zuciyar Maleek,ta yadda ba zai iya sake kallon kowace mace ya ganta a mace ba ma, bare har ya ji cewa zai iya sake aure._ "
Suhailah ta ƙurawa layun idanu bayan ta dawo daga duniyar tariyo kalaman Jawahir ɗin. Ta dinga jin wani irin courage na shigarta akan ta aiwatar da wannan aikin kawai,don ba za ta iya zuba ido ta ga Maleek ɗinta tare da wata mace bayan ita ba.
Sai ta aje layun bisa kan bed ɗinta tana nufan hanyar bathroom, don ta yo wanka sabida ta ji ƙarfin jikinta kafin ta zo ta nemi abincin da za ta sanyawa cikinta. Har ta murɗa handle ɗin ƙofar shiga bathroom ɗin ta saki ta juyo ta dawo cikin ɗakin, tana nufar hanyar ƙofa ta buɗe ta fice. Direct kitchen ɗinta da ke nan up stairs ta shiga,ta nufi wajen fridge ta buɗe tana ciro kwalin Hollandia milk me matsakaicin sanyi. Ta aje bisa saman island ɗin kitchen ɗin tana matsawa zuwa in da ta ke aje kayan su Bread da su cookies wanda Maleek ya jido su da yawa daga wani Bakery. Ta ɗibi cookies ɗin cikin plate ta haɗa da kwalin Hollandia milk ɗin ta fito,ɗakinta ta koma ta aje bisa saman bedside drawer, sannan ta wuce zuwa bathroom ɗin don sallo wanka. Gaba ki ɗaya ta manta cewa bata sake kulle ƙofar ɗakin da key ba,burinta kawai ta yo wankan ta fito ta sanyawa cikinta wani abu, kafin ta aiwatar da aikin birne layun nan biyu,wanda aka bata tabbacin da zaran sun shiga ƙarƙashin ƙasa shikenan aiki ya ci ya gama..........✍🏻
_To masu karatu ga dai Suhailah ta samo layar tarwatsa wannan auren luv na Maleek Ado da gurguwarsa TAIMIYYAH. Shin ita ke da nasara ko su TAIMIYYAH wanda suka dogara ga Allah? Ku cigaba da bin labarin sannu a hankali har ya zo ƙarshe.....Kar ku da mu da ayi rushing domin bana buƙatar gintse labarin._
_Ina godia da tarin ƙaunar da ku ke nunawa wannan labarin,i really really appreciate it my guys! Ɗansabo ta yaba, kuma tana ƙaunar ku domin Allah_ 😍
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*68*
Anty Safiya da Anty Radiya ne suka iso gidan Suhailah bisa ga umurnin Hajjah,sabida tunda ta tambayi Maleek ya sanar mata cewa har ya fito daga gidan, bai sanya Suhailah a idanunsa ba hankalin Hajjah ya kasa kwanciya. Musamman da ta kira wayar Suhailah amma bata ɗaga ba,shiyasa ta yanke shawaran turo babbar Ƴar Inna Dije Yayar Hajjah me suna Anty Safiya, tana aure ne a can Katsinan nasu da yaranta har huɗu, waɗanda bata samu xuwa da su bikin ba duk suna skull. Sai Anty Radiyar wacce ta ke matsayin Guggon Suhailah don ƙanwar Baban Suhailah ce uwa ɗaya uba ɗaya,aure ne ita ma ya kawo ta Zaria sai kuma ta yi kyan kai suna zumunci da Hajjah sosai, tana zaune ne a cikin Tukur-Tukur da yaranta Uku da kishiyoyi har biyu amma kowacce na zaune a Flat ɗinta daban ne.
Anty Safiya ta dubi Anty Rady bayan sun yi ta rafsa sallama daga downstairs ɗin, amma shiru babu wanda ya san ma suna yi,don ko Mai aiki ɗaya basu gani ta leƙo ba da alamu suna can ciki ne.
"Radiya mu wuce zuwa saman kin ji mu ga wani hali Ƴar banzar Yarinyar can ta ke ciki."
Anty Rady ta jinjina kai ta ce, "Hakane kam tunda muna ta sallama shiru,ni wallahi da Hajjah ta bar ni tun shekaranjiya so na yi in bubbugeta,iskan cin nata ya yi yawa kamar akanta za a fara yin kishiya,ni da ke da har biyu ashe sai na faɗi na mutu,su kuma Hajjah da Maleek ɗin kansa lallaɓata suke yi ba sa so ai mata tsiya-tsiya,shiyasa ta ke zuba iskancin nan sabida ta ga ana nuna tausayinta sosai."
Anty Radiya ta kai ƙarshen maganar cike da sababi,suna fara taka stairs ɗin benen ne Anty Safiya ta ce, "Hmm! Ke dai bari kawai Radiya,ai shiyasa aka ce idan gata ya yi wa mace yawa tafi hauka da iskanci. Suhailah tabbas ta bani tausayi don kishiya ko ta buzuzu ce bata da daɗi,kuma babu macen da ke so tana cikin zamanta da mijinta cikin so da ƙaunar juna ya ce zai yo mata kishiya,to amma idan har Allah ya ƙaddara hakan ai sai mutum ya sallama ya rungumi ƙaddararsa,amma Suhailah ta kasa fahimtar hakan gani kawai ta ke yi Maleek ya daina sonta ne shi da Hajjah,sabida ta samu matsala bata haihu ba. Kar ki so ki ga huɗubar da na yi mata jiya a gidan Hajjah akan ta kwantar da hankalinta, ta baiwa marar ɗa kunya amma kin ji wai tun safe ta kulle kanta a ɗaki tana faman kuka."
Anty Safiya ta kai ƙarshen maganar lokacin da suka isa matakalan ƙarshe,Radiya na cewa, "Ai ki bar ni da ƴar banza idan bata shiga hankalinta ba bubbugeta zan yi,in bi kishin da gudu in tattake shi babu ko takalmi,tunda ita shashashar Yarinyar ce mara lissafi. Kishi ai ba hauka bane da za ta bi ta addabi kanta,duk ta fita hayyacinta ba wannan gayu da kwalliyar duk ta zubar sabida shirme da wauta,ko an gaya mata hakan shi zai sa ya fasa yin auren oho!"
Anty Safiya ta saki murmushin takaici ta ce, "Hmmm! Allah ya ganar da ita gaskiya,ina ne ɗakin nata don kin san ban taɓa hawo mata sama ba,duk zuwan da na ke yi a gurguje kawai mu ke gaisawa in wuce."
Anty Radiya ta nufi hanyar ɗakin Suhailar tana cewa, "Nan ne ɗakin in ba kuma ta sauya wani ba."
Suka tura ƙofar bakunan su ɗauke da sallama suka shiga, jin shiru babu motsinta sai tray da suka hango a saman drawer ɗin bedside,da kuma jakarta da ke yashe bisa kan gado,hakan yasa Anty Safiya ta dubi Anty Rady ta ce, "Kin ji ɗakin shiru hala ta ga dama ta shige wanka ne,bari na ƙarisa daga bakin gadon in ga miye a cikin jakar ja'irar."
Ta yi maganar tana isa bakin gadon Suhailah ta zauna,Anty Rady ta nufi wajen Sofa ta zauna tana cewa, "Wanka yanzu da rana tsaka sabida shashanci."
A ɓangaren Suhailah da ke cikin bathroom kuwa,tunda ta ji muryoyin su Anty Safiya hankalinta ya yi mummunar tashi. Musamman da ta tuna cewa jakarta da layun da ta ciro suna zube akan gadonta bata kwashe su ba,sannan kuma sai lokacin da ta ji shigowan nasu ne ta gane cewa ashe bata saka key a ƙofar ba lokacin da ta shigo ɗakin. Cikin wani irin sauri ta gama watsa ruwa a jikinta,ta yayo towel ta ɗaura tana me nufo ƙofar fitowa banɗakin a gaggauce,cikin zafin nama ta fito tana addu'ar kada Allah ya basu ikon isa bakin kan gadonta. Sai dai tana ƙarisa fitowa ta yi turus! A tsaye ganin Anty Safiya zaune a bakin bed ɗinta hannunta na ƙoƙarin kaiwa kan jakarta. Ai sai Suhailah ta ƙariso da mugun gudu tana faɗawa kan bed ɗin, tare da saurin damƙo ledar da layun suke ciki,hakan da ta yi sai ya razana su Anty Rady duk suka bi ta da ido,Anty Rady na cewa, "Ke lafiya za ki fito a guje ki yi wannan uwar sufan a gado kamar mahaukaciya,wai meke damun kanki ne Suhailah,uban me kike ɓoyewa da baki son a gani?"
Suhailah sai ta ɓata fuska tana ɗagowa ta dubi Anty Rady ta ce, "Anty Rady bakomi fa kawai sirrina ne ban son a gani."
Anty Safiya ta riga Anty Rady yin magana tana cewa, "Ki rabu da ita Rady ni kuma sai na ga wannan sirrin da ake wa wannan sufan don ɓoye shi. Oya bani in gani miye sirrin? Idan na maganin mata ne kin ga muma sai ki sammana mu gwada anfani da shi."
Yadda Anty Safiya