Showing 186001 words to 186776 words out of 186776 words
Chapter 63 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
Safiya kawai ta ke yi, amma zuciyarta sai faman bugu ta ke tunda Anty Safiya ta ambaci cewa wajen Maleek za ta kai ta. Kwakwalwarta ta shiga haska mata karon su da shi a ɗazu da rana, zuciyarta ta sake doka mata da wani irin tsoro da firgicin sake kaɗaicewarta da shi. Sai dai bata da yadda za ta yi don ba za ta iya cewa Anty Safiya ba zata ba,suka cigaba da takawa TAIMIYYAH na dafe da guiwar ƙafarta,gaba ɗaya ji ta ke yi da zata iya juyawa cikin gidan da ta juya,don ita yanzu tsoran haɗuwarta da Maleek ɗin ta ke ji, tun abubuwan da ya yi mata a ɗazu da nauyinsu da kunyarsu ba su bar zuciyarta sukuni ba har kawo yanzu.
Maleek Ado wanda ke zaune cikin motarsa idanunsa akan mirrow, yana hango tahowar su TAIMIYYAH xuwa wajen motarsa. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su akan su lokacin da suka ƙariso bakin motar, sai ya yi saurin buɗe side ɗin da ya ke zaune yana cewa, "Hey! Sis zo ta nan."
Anty Safiya sai ta nufi ɓangaren da Maleek ke zaune ta ce, "To gata nan dai na kawo maka ita,amma fa na sanar da Guggonta ba za ta daɗe ba zan maida ta,so ka yi sauri ka ganta mu wuce kada Hajjah ma ta zagaya yin patrol ta ga an ɗauke musu Amarya."
Anty Safiya ta ƙarisa maganar tana dariya cike da shaƙiyanci,Maleek ya ɗan taɓe baki ya ce, "Ni dai yanzu tunda kin cika aikin ki,komawa za ki yi ciki nan da minti talatin zan kiraki ki maida ta inda kika ɗakko ta,za ki ga alert kina buɗe wayarki, so za ki iya tafiya sai na kira ki."
Maleek ya yi maganar yana maida dubansa wajen da TAIMIYYAH ta yi tsaye, ƙirjinta na faman bugawa da tarin fargaba,ta dubi Anty Safiya lokacin da ta ce, "Amarya bari in shiga daga ciki idan kun gama zan fito mu koma ciki."
Daga haka Anty Safiyyah ta yi gaba tana sakin murmushi, gaba ɗaya TAIMIYYAH ta bata dariya yadda ta ke faman zare idanu kamar wacce ta yi ƙarya.
Maleek Ado ya zuro ƙafarsa ya fito daga waje, yana isa wajen da TAIMIYYAH ta yi tsaye ginjine da jikin motar,ya dubi fuskarta da ta sunkuyar ƙasa ya saki murmushi. Bai yi magana ba illah kamo hannunta da ya yi,yana zagayawa da ita ɓangaren me zaman banza, ya miƙa hannu ya buɗe mata ƙofar motar ya ce, "Wife shiga daga ciki."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta da suka haska da tarin tsoran da ke kan fuskarta ta ce, "Don Allah Yah Maleek ba sai na shiga ba,bacci na ke ji wallahi ina son in je in kwanta please!"
Maleek bai bi takan maganar da TAIMIYYAH ta yi ba, sai kawai ya ɗauke ta cak! Ya sanya ta cikin motar, ya maida murfin ya rufe yana saurin zagayawa ɓangarensa ya shiga ya dannawa motar lock. TAIMIYYAH sai ta haɗe kanta da guiwa tana sakin masa kuka me sauti,dukkanin jikinta na ɗaukar rawa don har ga Allah ita lamuran Maleek yanzu tsoro suke bata.
Maleek Ado kuwa gaba ɗaya ƙamshin TAIMIYYAH da ya fara cika motar ke motsa zuciyarsa, ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta yana sauraren yadda sautin kukanta ke fita a hankali. Ya buɗe baki cike da ƙasaita ya ce, "Zainab kina so in wuce da ke gidana ki kwana a can kenan ko?"
Ai bai ma kai ga rufe baki ba TAIMIYYAH ta yi saurin ɗago fuskarta tana sake sakin kuka ta ce , "No Please! Yah Maleek don Allah ka yi haƙury."
"To ki tsaida wannan kukan bana son jin sa okey."
Maleek ya yi maganar fuskarsa a miskile yana sake tsare ta da idanunsa da ke cike da zallar rigima, ganin yadda ya yi maganar babu alamun rahama akan fuskarsa,yasa TAIMIYYAH saurin tsaida kukan hawaye na cigaba da zirarowa daga idanunta.
Ya miƙa hannu ya zari tissue ya miƙa mata yana cewa, "Ungo ki share hawayen nan bana son kina min a sararsu,don lokacin zubansu bai yi ba ya dai kusa soon Baby."
Yana maganar ne idanunsa a kanta babu ko kiftawa,hakan yasa TAIMIYYAH miƙa hannu ta amshi tissue ɗin, ta fara share hawayen da ke sake sakkowa daga cikin idanunta. Da ƙyar ta yi nasaran tsaida hawayen tana faman zumbure baki da sauke ajiyar zuciya, wanda ya sanya Maleek sakin smile kaɗan yana cigaba da bin ta da wani mayen kallo. Ya buɗe baki cike da zallar ƙasaita ya ce.........✍🏻
_Hmmm! Maleek Ado ba dama ne,da alamu so ya ke ya gama gigitama Iyah jika da salon luv ɗinsa,shi baisan cewa Shaikha Alarammiyah TAIMIYYAH ya aure ba ne? Wacce ba ta saba da fitsaran kalar luv ɗinsa ba lol._ 😒
#Ɗansabo ce#