Showing 24001 words to 27000 words out of 189984 words

Chapter 9 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15642

cikin ma'aikatan su, tare da tayin makudan kudade dan kawai tabar aiki da CHIBADO FM ,sai dai kash ba su san cewa Raihan ba dan kudi take aiki ba,dan da yawa basu san ita din ko yar gidan waye ba,sun san dai Rahim Muhammad nurr amma basu taba kawo cewa Muhammad nurr din da suka sani ba ne,dan tunanin su bai basu cewa Muhammad nurr zai bar daya daga cikin yaranshi su yi aiki a karkashin wasu ba,shi yasa kwata kwata hankalin su bai kai kan sa ba,hatta da Aminin mahaifinta gwamnan jihar Adamawa baisan cewa Rahim ya fara aiki tare da su chibaɗo's ba.




A gajiye Raihan ta koma gida saboda wasu aikyuka da suka ƙaran mata a office.sai da ta kimtsa sosai ,kana ta fito falo inda ta tarar da Antyy amarya zaune tana duban labarai a tashar ta su ta chibaɗo FM,zama tayi kusa da ita tare da kwantar da kanta a kafadar ta, cikin sanyin murya ta ce"antyy amarya na gaji sosai"shafa kanta antyn ta yi tare da cewa Allah ya baki lada ya kuma ci gaba da kare min ke ,Amma gaskiya Rahim ba zan boye maka ba wlh ban gamsu da wannan bangaren da aka baka ba, ƙasa ta yi da murya sosai ta ci gaba da cewa karfa ki manta da akwai raunin mace a tare da ke Raihan karfa nayi gudun Gara sannan nazo na haye zago,bana so duk tattalin rayuwar ki da nake akan makiyan da bamu san su ba,ya zamana kin karowa kanki wasu makiyan kin san fa harkar jarida jaridar ma irin bangaren da aka baki Raihan yana da haɗari sosai"ta shi zaune Raihan ta yi kafin cikin san kwantar da hankalin antyy amarya ta ce"antyy amarya wlh babu wata matsala Ni kaina naji abinda kika ji lokacin da na fara aikin to amma daga baya sai naga duk ashe ba haka ba ne,ita fa matsala sai ka kai kanka take samun ka,dan haka ki kwantar da hankalin ki ki mikawa Allah komai kamar yadda Abbie ya yi"murmushi antyy amarya ta yi kana ta ce" shike nan Raihan Ni dai kawai farincikin ki nake buƙata amma dai gaski,,,,,da sauri Raihan ta rufe bakin antyy tana cewa dan Allah antyy ki bari ki kwantar min da hankalin ki"dole antyy amarya ta yi shiru suka shiga wani zancen, tare da bawa RAIHAN ɗin abincin da me aikin ta kawo mata.




CHIBADO HOUSE




Tun daga farkon shigowa falon zaka jiyo fadan innawuro da hargowarta,duk da cewa shi wanda take yi saboda shi din ko kallon inda take baiyi ba,kai kace ma baya falon,ganin yadda yayi shakulatan ɓangaro da ita ya sa ta ɗauki jarkar ruwan dake gabanta ta wulla masa tana ci gaba da cewa, Ni zaka mayar mahaukaciya saboda ba uwar ka ba ce ke maka magana,to wlh na gaya maka na gama baka lokaci idan wata dayan da na ɗeba maka ta cika baka kawo matar da zaka aura ba,wlh sai na aura maka yar uwarka da kaƙi ta, duk da irin son da take maka"dawo da duban ta kan Ammi ta yi tana cewa ai kuna kallon sa yake yin duk abin da yake yi to in ku zaku iya Ni ba zan jura ba ehe"babu wanda ya tanka mata saboda sun san hali babu wanda yake shiga fadan innawuro da Ahmad idan ma ka shiga kai zata bari da jin kunya,dan take a gurin zata kunyata ka,shi yasa daga Abbu har Ammi basu tanka mata ba, shi kuwa gogan ko ajikinsa,karshe ma tashi ya yi ya bar falon ba tare da ya tanka mata ba,da ƙatuwar harara ta bishi tana ci gaba da yan guna_gunin ta.


........




Washe gari saboda kar innawuro ta kuma tada masa zancan aure ko bari ta fito baiyi ba , ya fice daga gidan, duk da cewa kowa yasan shi ɗin me zuwa da wuri ne mutum ne da yake matukar martaba lokaci shi yasa baya wasa da shi Ako wace gaɓa.




Tun da ya shiga office ya maida kansa busy dan duk ya cire tunanin da yake neman sarke zuciyarshi,a hankali aka bude kofar tare da shigowa kai tsaye wanda hakan yaja hankalin A Wazir,karaf idanun shi suka shige cikin nata,duk da ranshi ya ɓaci da yadda ta shigo masa kai tsaye amma sai ya dake ya dan saki fuska kadan,tare da kawar da kanshi daga kanta,Asiya Kabir ke nan abokiyar shi ta karatu,tun bayan da suka gama karatu ya rabu da shegen nacinta saboda tafiyar da ta yi wajen kakarta dake can Saudiya,sai kuma yau rana tsaka ya ganta cikin office dinsa.


A hankali a ka turo kofar tare da sallama, bayan sanar da shi cewa yana da bakuwa,amsawa ya yi can ƙasan makoshi,waje ta samu ta zauna ba tare da damuwa da yanayin na shi na gizago da ta fuskanci cewa a jinin sa yake,Barka da aiki ta faɗa idanun ta akan shi tamkar zata haɗiye shi,Barka ya kuma fada cikin dakakkiiyar Muryarshi dake fita da sautin rashin sassauci ko wasa,ji ta yi jikin ta ya kuma mutuwa yau din ma dai ba za ta iya fadin abinda ke ranta ba,wai shi wannan wane irin mutum ne haka me tsananin kwarjini)ta tambayi kanta.




Meke tafe dake?tambayar da ya yi mata ta katse mata tunani.kame kame ta fara domin ta rasa abin cewa, idan baki da abin cewa za ki iya tafiya?ya kuma fada fuskarshi na kan computer da yake ta latsawa tun shigowarta.


Asiya daya daga cikin fans dinsa ce,fasifar son shi take yi,amma babu fuskar nunawa bare sanarwa,baya daukar wayarta,dan bai ma san ita dince ba ko ta kira, ɗan yawan takura mishi da ziyara da take ne ma yasan ya dan shaida fuskarta.


Duk sanda zata zo da kwarin gwiwar sanar da shi abin da ke ranta take yi,amma da zarar ta zo gaban sa ko mai sai ya kufce mata,kamar dai yadda yanzun ya faru.




Turo kofar aka kuma yi tare da siririyar sallama,wadda lokaci daya Muryar Rahim ɗin ta shiga kunnen sa,asiyar ce ta amsa,shi ko motsawa baiyi daga abin da yake ba,hakan yasa zuciyar Raihan ta sosu,kallon Asiya ta yi idanun ta cike taf da ruwan masifa,sai dai ba tace ko mai ba,ta kuma duban wazir din da har yanzu dai bai ko kalli inda take ba.




To yallabai Ni zan wuce sai na dawo",cewar Asiya da ta ɗan samu kwarin gwiwa bayan shigowar Rahim,jin jina mata kai ya yi ba tare da ya ɗago ya kalleta ba.


Tana fita daga office din Raihan ta matsa kusa da shi idanunta akansa ta ce",Hamma wazir ina zata dawo?yanzun me tazo yi?kuma wacece ita?


Ɗan lumshe idanunsa ya yi saboda yadda Muryar take shiga ko wace kafa ta jikinsa,sai dai kuma sam ya kasa amsa mata tambayoyinta,saboda baisan me zai ce mata ba,






Ganin yadda yayin hakan sai ya kuma harzuka zuciyar RAIHAN,sai kawai ta fashe da kukan da yake ta yakushin ranta,tun ganin Asiya a office din nasa wanda ita kanta bata san dalilin jin zafin ganin nata ba.cak ya tsaya da abinda yake yi,babu wani abu da yake saurin karya lagwan A Wazir sai kukan Rahim babu wani abu da yake saurin sashi damuwa irin damuwar Rahim,idan ka cire iyayen sa to Rahim ne na biyun su a matukar muhimmanci a rayuwar A wazir,a hankali ya ajiye keyboard din dake hannun shi yana sarrafa computer,ya juyo inda Rahim din yake tsaye a tagefan shi yana wani irin
Kuka me sosa zuciyar me sauraro,kana jin kukan za kasan cewa yana fitowa ne da wata irin damuwar dake can cikin ƙasan zuciya,cikin wata irin sassanyar murya A Wazir ya ce" Rahim me aka yi maka meye damuwarka? Ya fada cikin damuwar da kukan
Rahim din ya jefa shi a ciki,dan sai ya ji ma ya manta da duk wata damuwa da ya shigo da ita da kuma wadda tazo ta tarar da shi,janyo hannun RAHIM ɗin ya yi yana ƙoƙarin rarrashinsa cikin yanayinsa n rashin son hayaniya.meye damuwar? Ya kuma tambayarsa cikin kwantar da murya, a hankali Raihan ta ɗago idanunta da suka sauya daga ainahin su na farare masu sirkin zaiba,tambayar da ta yi mishi na amsa ta ba ita ta kuma maimaitawa. wacece waccen da ta fita yanzu?" Nima ban sani ba kawai dai daya daga cikin fans ne“ya bawa Raihan din amsa cike da son jin abinda asiyar ta yiwa Rahim ɗin,jin Rahim din ya yi shiru yasa A wazir ya kuma tambayar sa da cewa wani abu tayi maka"girgiza kai Raihan ta yi tare da barin office din tana cewa lokacin aiki ya fara sai an jima oga" cike da mamaki yabi bayan Rahim din da kallo, zuciyar shi tana mai son gano mishi dalilin Rahim din na damuwa da zuwan Asiya ko kuma tarayyar sa da ita wanda tuntuni ya fahimci ba wai a kan Asiya ne Rahim ya fara wannan ɗabi ar ba,yawanci baya son huldarsa da mata ko abokanan aiki ko kuma waɗanda suke zuwa musamman danshi,dan sau da yawa yana gani Rahim din ne ke yi masa maganin tarin yammatan da suke addabar shi,ajiyar numfashi ya yi tare da komawa ya zauna,ci gaba ya yi da aikin shi dan son kawar da tunanin abun a ranshi............... Fatimah y Adam.......✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page8 ```




Yanzu murja haka zaku zauna ku zuba idanu dukiyar mijin ku kuma uban ya'yan ku tana ta zama ta gaibu,kun zauna sakoko da baki kun kasa tsinana komai,cewar innar murja ke nan kuma kanwar goggo Rahma,cikin takaicin da yake cin ran murja ta buɗe baki ta ce" wallahi inna na fi ki shiga halin bakin ciki da ruɗu akan wannan lamarin,amma ba komai ne yasa nayi shuru ba illa so nake yarana su taso saboda mu hadu mu kwatarwa kan mu yanci,to kuma alhamdulillah tun da yanzu dukkan su sun yi wayo sun mallaki hankalin kansu,jira nake kawai su dawo gaba dayan su ,domin mu ɗora daga inda muka tsaya" tsaki inna ta yi tare da cewa to wane tabbacin ne dake na cewar zasu baki haɗin kai tun da dai kin san mutumin nan mahaifin su ne babu yadda za ayi su yadda a cutar da shi" dariya murja ta yi kafin ta haɗe fuska ta ce" inna tun yarana ba su san komai ba bare wata aba ƙiyayya na riga na cusa musu tsanar yan uwansu da ganin baƙin su karma wannan Rahim din ya ji labari,shi kuwa mahaifin su na riga na saka musu a ransu cewar baya kaunar su,dan haka da wannan damar yanzu zanyi amfani su bani hadin kai domin kwatar dukiyar RAIHAN wadda a yanzu nake kyautata zaton zata iya zama ta Rahim saboda mugun son da na fuskanci nurr na yi masa,duk kuwa da cewa yana kokarin boye hakan a gaban idanun mu da idanun yaran",ajiyar zuciya inna
Ta yi fuskarta ɗauke da murmushin samun nasarar karya yar uwarta a ta dalilin muguwar hassadar dake cin ranta ,na iya tsawan lokacin da Allah ya ɗaukaka Muhammad nurr.na gode y'ata kuma nayi miki alkawarin cewa da Ni za ayi wannan yakin dan haka duk lokacin da kuka shirya ki sanar da Ni dan karo makaman yaƙi.da wannan batun suka rufe hirar ta su,inna ta tashi ta koma bangaren yar uwar Tata wadda acewarta ita ta kawowa ziyara.




Halima ce tsaye a bakin wani katon shopping moll, sanye take cikin doguwar rigar a baya fuskarta kuma sanye da facemask,fitowa ta yi daga gurin aiki saboda siyayya da take son yi, dan yau sai ta tsaya ta gabatarwa da Rahim rahotanni da suke hannun ta na sirri,shi kuma Rahim din sai ya gama gabatar da shirin siyasarmu a yau.shi yasa ta yi tunanin ta fito ta gabatar da uzurinta,idan yaso tana ta shi gida kawai zata nufa babu batun tsaye tsaye,tun da dama yau bata da fitar aikin sirri.


Kamar ance ta kalli saman barandar hotel din dake opposite da shopping moll din da ta ke tsaye a gurin, gani ta yi wani mutum me sanye da cot ya ritsa wani saurayi da bindiga,ga dukkan alamu a boye mutumin ya nunawa saurayin bindigar bai kuma yi tsammanin ta yi fitowar da har za a ganta ba,sai dai kuma kash ido biyu Halima ma'aikaciyar jarida wadda ke aikin sirri a gidan rediyon CHIBADO FM,ta yi da wannan bindiga,zaro idanunta tayi sosai dan tabbatar da abinda idanun nata ke gani,gani tayi mutumin ya boye bindigar sun kuma jero shi da saurayin da ya nunawa bindigar kamar wasu abokanan aiki,har kafadar saurayin mutumin ya dafa suka sauko daga saman barandar hotel din,cikin wani irin hanzari halima ta tare me mashin din a daidaita,kokarin saita kanta ta yi a matsamayinta na sirrintacciyar 'yar jarida tare da ƙara bawa kanta ƙwarin gwiwa,ta ce"da me nafef din malam dan Allah wannan motar da zata tafi yanzu nake so ka bi min cikin nutsuwa bana so su gane cewa muna bin su"to Hajiya kar ki damu wannan aiki na ne" me nafef ɗin ya faɗa yana tada mashin ɗin da sauri saboda yadda motar ta zo ta wuce su da gudu,shi ma me nafef din da gudu ya bi bayan su.




Sakon da halima ta turawa Raihan ta sanarwa da wazir shi ya tilasta mata zuwa office din Wazir badan ranta ya so ba,sallama ta yi tana ta faman ciccin magani saboda ganin sakatariya da ta yi tsaye ta zuba masa ido kamar ta samu tele,shi kuwa da alama bai san ta na yi ba,dan gaba daya hankalin shi na kan takardar da yake saka hannu zai bata,harara Raihan ta zubawa saude kafin cikin jin haushin da bata san dalilin sa ba bare kuma wanzuwar sa da sanin muhallin sa,tace to Malama cinye shi zaki yi ne kin wani ƙwalalo masa ido kamar zaki cinye shi ɗanye"ta ƙarasa faɗa tana mai tura karamin bakinta da yiwa Wazir din kallon ƙasa ƙasa,tun da ta fara maganar ya bar abin da yake yi tare da maida hankalin shi kan ta,amma ba zaka taba gane hakan ba,mikawa saude takardar da ya gama sa hannun ya yi tare da yi mata alamun ta fita,babu yadda ta iya haka ta karba ta fita ba tare da ta samu damar tankawa Rahim ba,tunda ko ta girme shi yana matsayin samanta ne,ko ba haka ba ma wazir ba zai taba daukar hakan ba.




Rashin abin da zai cewa Rahim ɗin yasa shi ci gaba da wasu aiyukan.tura baki Raihan ta yi idanuwanta na cika da hawayen rashin dalili,jin damuwar Rahim din a cikin jikin shi ya yi ,hakan yasa shi ɗago manyan idanun sa masu saurin kashe jikin duk wata lafiyayyar mace, ɗora Mata su ya yi tare da cewa, Na kasa gane komai akan abin da kake yi,sai dai kuma na fahimci abu daya shine kamar kana kishi da duk wani da yake son tarrayya da Ni,ragowar ne ban fahimta ba dan haka sai ka fahimtar da Ni"ya fada yana ta shi daga saman kujerar sa kai tsaye ya nufi bathroom dan dauraye hannunsa.




Haka nan Raihan ta samu kanta da jin bakin cikin kasancewar ta a matsayin namiji,bakin cikin da bata taba riskarsa ba,haka nan take jin matsananciyar damuwa akan ɓoyewa Wazir kanta da ta yi,to amma ya ta iya wannan alkawarin mamanta ta yiwa shi,kuma ya zama dole ta cigaba da riƙe shi,wani irin kuka wanda ke tafe da wata irin damuwa ya kufce mata,wanda ya sa ta fita daga office din ba tare da ta isar da sakon da halima ta turo mata ba,nata kuma bashi amsar tambayar da ya yi mata ba,ba ta tsaya ba kai tsaye office ta nufa ta fara gabatar da shirin siyasarmu a yau.




Ko da wazir ya fito yaga bai same Rahim ba,duk sai ya kuma jin damuwa ta lullube shi,bai san me ya sa ba sam baya son abin da zai taba ran Rahim , yana matukar jin shi a zuciya da gangar jikin shi,kai duk wani motsin shi ma sai ya ji Rahim a tare da shi,dan lumshe idanun sa ya yi tare da furzar da huci.




Alhaji sale anya kuwa kana ganin wannan hanyar da muka dauka zata bulle inda muke so ta bulle kuwa? Cewar Dr sanate ke nan, ɗan numfashi Alhaji sale me shanu ya furzar kana ya ce"Dr kar ka damu wannan hanyar da muka ɗauko ita ka ɗaice mafita a gare mu dan samun damar tarwatsa gwamna"kafin Dr ya bude baki sai ga mutumin nan da wannan saurayi ya tunkuɗo shi cikin falon kamar wani kayan wanki,oga an kammala wancan aikin saura wannan kawai shima umarnin ku nake jira na isar da sako"kafin su samu bakin bashi amsa wani gurnani ya fara fitowa daga can karshen falon wanda ga dukkan alamu dai daki ne,kuma gurnanin bana komai bane sai na irin alamun ana jin dadin fitar hayyaci,tsit falon ya yi kamar ɗaukewar wuta ,su Dr da mutumin nan dai da alamu sun san me ke faruwa a cikin dakin,sai dai kuma tuni suka bar ƙwaƙwalwa da gangarjikin halima kyarma,domin kuwa tagar da ta samu ta laɓe tana gab da jikin dakin da wannan gurnanin yake fitowa,gyara camarar ta ta kuma yi sosai dan tana son komai ya fito tar.




Dr ne ya dubi wannan basamuden mutumin ya ce"kwaro mu dukan mu bamu da damar yin komai har sai shugaba ya fito daga dakin hutu kuma kaima ka sani dan haka sai ka dakata mu jira fitowar sa,yana rufe baki ma sai ga shi nan ya fito shida wani matashin saurayi sai sakin murmushi suke kamar wani saurayi da budurwa, ko da yake kusan hakanne su a wajensu.




Zaro ido halima ta yi saboda mamakin mutumin da ta gani da kuma gane dalilin jin gurnanin nan,wa iya zubillah Allah ka tsaremu daga sharrin masu fuska biyu, ta faɗa tana kara dai-daita camarar ta,dan ji take kamar karshen su ya riga yazo tun da har Allah ya tona musu asiri ta hanyar ganin su da ta yi,ba kowa ba ne wannan mutumin da halima ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login