Showing 123001 words to 126000 words out of 189984 words

Chapter 42 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15655

dakin ta saka dogon hijab ta shimfida sallaya daga nan ta tada kabbara domin mikawa sarki zuljalalu kukanta,sam shi yasa RAIHAN damuwa bata cika zauna mata ba saboda da taji irin wannan mummunan tashin hankalin take saurin ƙara kusanta kanta ga Allah da izininsa kuma cikin ikonsa sai kaga ta koma kamar ba ita ba,yarinya ce da ta yadda Allah daya ne kuma shi zai magance mata dukkan wata matsala da take ciki.


Ba ita ta dakata daga kai kukanta ga Allah ba har sai da ta ji am fara kiran sallah,dan haka ta dakata ta yi addu'a da lazumi,tana zaune a ka tada sallah ,tashi ta yi tayi raka atanal fijr Sannan ta kawo farilla cikin nutsuwa da kushu'i.




Sai alokacin ta ji wani irin bacci me dadi yana dibarta,dan haka kawai tashi tayi ta cire hijab ta haye gadonta ta kwanta cikin salamar zuciya da ta gangar jiki.






Wayewar garin yazowa mutane da yawa ta hanyoyi dabandaban ,wasu farin ciki suke zasu gudanar da ayyukan alkhairi wasu mutuwa akayi musu wasu aure zasu yi wasu wani burinne zasu cika shi ,kamar dai yadda ta kasance a wannan familys kowa da yake da buri kyakkyawa ko akasin haka ya tashi da burin cika shi.






Tun daren jiya kallonsa kawai take tana saka abubuwa da yawa ,yadda taga ya tashi yana ta saurin shiryawa ya fice yasa ta kasa rike abinda ke ranta,cikin damuwa inna maimuna tace",wai Ni ko ABBAN Bashir meke dakuna ne? Na kula da kai tun jiya baka cikin nutsuwa da alama akwai damuwa a tare da kai",ba tare da ya karbi shayin da ta haɗa masa ba ya ƙarasa daura agogonsa sannan ya dubeta fuskarshi cakude duk sai ya wani sauya kamar ba shi ba,ya ce",maimuna ina cikin damuwa sosai kuma akan his excellency ne da yadda yake son kashe nurr a yau ko ta halin kaka, innalillahi wainna'ilaihi raji'un inna maimuna ta faɗa cikin tashin hankali tana faman zare ido,to yanzu me ye abinyi ? Ta faɗa muryarta kamar zata yi kuka,shine yasa nake ta sauri kada wani abu ya faru saboda na tabbata zai kira Muhammad nuur ɗin", kafin inna maimuna ta yi magana tuni har ya fice daga falon.






Tun adaren jiya Abbie ya samu kira daga his excellency shi yasa da sasafen ya shirya ya fice.




Sai bayan fitarsa hajiyar agadex ta tashi saboda bacci da ya dauke ta bayan sallar asuba,tana fitowa abinda ta fara tambayar mami shine ina Muhammad yake", cike da mamaki aunty amarya ta kalleta harma ta kasa boye mamakinta,ta ce", Hajiya lafiya? Baki bani amsa ba kina maida min da tambaya", hajiyar agadex ta faɗa ranta a hade,jinjina kai aunty amarya ta yi tana tunanin abinda ke damun hajiyarsu a kwanakinnan saboda dai ita a iya saninta akwai kunya tsakanin hajiyar agadex da Abbie din to amma yanzu abinda take yi ya fara damun aunty amarya dan tasan tunda ta ga haka to da kwai wani abu a ƁOYE.




Ba zaki fada min inda ya je ba? Ta tambayi aunty amarya wadda tayi nisa a tunaninta,firgit aunty amarya ta yi sannan ta ce",tun ɗazu ya fita dan ko bakwai ba tayi ba lokacin da ya fita his excellency ne ya kira shi ina ga dai akwai abu me muhimmanci da ya taso", shiru hajiyar agadex tayi kafin ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba ta juya ta bar aunty amarya tsaye,




Raihan ma dake tsaye jikin kofarta tana hango su kuma tana jin abinda suke fada,ta juya ta shiga dakinta,bata jin zaman gidan aiki zata fita kawai tunda anyi uku idan ba haka ba zaman zai iya haifar mata da damuwa,shiryawa ta yi tsaf cikin shigarta ta basaja kai idan ka kalleta sai ka dauka namiji ne ,amma tabbas yanayinta na mace da salo na mace da yake jikinta sai wasu su dinga kallonta kamar dan daudu ,saboda da yawa a hakan ake kallonta a bayan idonta ana yin zundenta da hakan,ba ta yiwa hajiyar agadex sallama ba ta yi ficewarta aunty amarya ma a tsaitsaye ta yi mata sallama ta fice ,yau dai sabuwar motarta ta shiga ta tafi office,jikinta da zuciyarta duk babu dad'i hakanan take jin faduwar gaba da fargaba lokaci_ lokaci sai dai bakinta dake dauke da ambatan Allah yasa abin yayi mata sauki sosai cikin wannan yanayin ta isa office.






Shi kam Wazer bai yi tunanin Raihan zata iya fita ba yau,shi yasa bai tashi da niyar zuwa office ba,zama yayi a gidan zuwa lokacin da jirginsu Khalil zai sauka sai yaje ya dauko su da kansa.




Ruby kuwa bata san bai kwana gidan ba,ita ma din da wuri ta shirya ta fice zuciyarta fal farin ciki gani take kamar komai ya faru ya kare,har hango RAIHAN cikin tashin hankali take yi,idan ta tuna hakan har wani makirin murmushi ne ke subce mata,da wannan dokin ta isa office.






Gidan gwamnati.........




Duk sammakon da ya tafka haka yazo ya sami his excellency a falonsa na ganin baƙinsa masu muhimmanci,cikin mamakin kiran Abbie ya ce", ka tayar min da hankali meke faruwa ne haka? Murmushi his excellency ya yi sannan ya ce", to ka zauna mana idan yaso sai kaji ko ma meye", zama Abbie ya yi yana kallonsa zuciyarsa cike da tunani da damuwa,




Shiru falon ya dauka na tsawon mintina biyu kafin his excellency ya yunkura da kansa ya isa prige dake can kusurwar falon ta hannun hagu budewa ya yi , maimakon ya dauko lemon da yayi niyar dauka sai kawai ya tsaya yana kallon prige din tamkar wanda ke ƙirga yawan lemon dake ciki, Abbie dake kallonshi daga inda yake zaune ya kuma cika da mamakin al'amarin his excellency ɗin,kafin ya ce", wani abu his excellency ya dauko lemon kwali daya da ruwan kwalba ya nufoshi fuskarsa a sake,sai hakan ya kara saka Abbie cikin zargi da damuwa,yana zuwa ya mikawa Abbie lemon tare da cup din da ya dauko, Abbie bai ce komai ba ya karba ya aje ba tare da ya zuba ba,ɗan numfasawa his excellency ya yi sannan cikin raunin murya ya ce", abokina ka yafe min abinda zan iya cewa da kai ke nan saboda a halin yanzu baka da wani lokacin sauraren wani abu ko jin wani bayani dole ne na aikata abinda nake ganin shine zai fiddani daga ruɗani da kokonto,ka dauka cewa duk mutumin da ya mutu to wa'adinsane ya cika,,,,,karaf wannan kalma ta shige kunnen Abba yahya dake ta baya jikin window din falon,ɗan rintse idonsa ya yi cike da tashin hankali da fargaba,gashi ba damar shiga falon saboda an rufeta ta ciki,zufa ce ke kwararo masa ta ko ina.




Abbie kuwa samun kansa ya yi da kasa cewa komai sai bin his excellency da kallo yake cike da son jin karin bayani dan shi sam baya gane Yaren da yake masa magana dashi,muje mu yi karin kumallo his excellency ya fada yana mikewa tsaye.girgiza kai Abbie ya yi kafin ya samu ya iya daga harshensa dakyar ya ce",bana jin zan iya kai komai bakina idan banji dalilin wadannan maganganun da manufarsu ba", nan da nan his excellency ya haɗe ransa tamkar hadarin gabas ya ce", Nura dole ne kayi karin kumallon nan idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kar kayi kuka dani," cike da mamaki Abbie ya ke kallonsa harma baisan lokacin da ya tashi ya bishi zuwa dininng dinba, gaba daya sai yake ganin kamar mafarki yake saboda yadda abubuwa suke neman cakude masa a lokaci guda,da kansa his excellency ya zuba masa duk abinda yasan zai bukaci cinsa kafin ya ce",Bismillah ", a hankali Abbie ya dauki cup din shayin da his excellency ya haɗa masa ya kai bakinsa yana jin wani irin bugun zuciya tamkar zuciyar zata fito waje.




Runtse ido Abba Yahya ya yi yana jin tamkar numfashinsa zaibar jikinsa ,cikin rawar baki ya fara kiran sunan nuran a jere har sau uku tamkar dai nuran zai ji shi,sai dai ina tuni Nura ya kai shayin bakinsa.






Ruby na zuwa kai tsaye ta wuce sashen buga jaridu,babu wanda ya hanata shiga saboda ansan wacece ita duk da sun san ba bangarenta ba ne,tana yi tana share gumi ganin kamar zata samu matsala saboda rashin kwarewa yasa ta yi amfani da Google nan da nan kuwa ta samu abinda take so cikin kankanin lokaci ta yi rubutu akan wacece RAIHAN ta sigar jan hankali,ta yi rubutun ne a matsayin labari kamar yadda aunty amarya ta sanar da wazer daga karshe ta ce ", na nemi na fallasa sirrinnanne saboda makala min ita da aka yi matsayin mata alhalin bana sonta ina da wadda nake so harma anyi mana baiko.




Tana gamawa ta fita bayan ta yi copy kusan dubu,sai da ta tabbatar babu kowa ta bangarenta sannan ta kira Surry ta ce",tazo ta kammala.




Cikin mintinan da basu wuce ashirin ba Surry ta ƙaraso da ƙatuwar bakko suka ɗure jaridar suka fita da ita ba tare da tsoro ko tunanin komai ba.




Karfe biyu WAZER ya gama shirinsa tsaf ya fito cikin kamalarshi, ya shiga sabuwar motar da yasa aka kawo masa ita a jiyan,kaitsaye filin saukar jiragen sama na Yola ya nufa dan dauko kannensa da babu wanda yasan ranar zasu dawo bayanshi,wanda shi ya san dalilinsa na yin hakan.




RAIHAN kuwa ji ta yi gaba daya bata jin dadin zuciyarta,haka kawai take jin faduwar gaba,hakan yasa ta nufi office din WAZER, tana kokarin shiga kamar yadda ta saba sactariya ta dakatar da ita tana mata wani kallon kin shiga uku,sannan ta ce", oga yana ciki ya ce", kuma baya bukatar ganin kowa expicialy ma kai Rahim ya ce", kar na Barka ka shiga , a wannan lokacin matarsa ruby kadai yake da bukatar gani dan halin yanzu ma tana ciki", wani irin miyau Raihan ta haɗiya me matukar daci kafin ta samu damar yin magana am fara kokarin bude kofar, ruby ce ta leƙo kanta babu ɗan kwali gashin kanta kuma duk a jiƙe,cikin yauƙi ta dubi sactariya ta ce", me yake faruwa ne anan? Cikin biyayya sactariya ta ce", kiyi hakuri ranki shi dade dama Rahim ne yake son shiga shine na ke fada masa sakon oga", a yatsine ta dubi Raihan sannan ta ce", Rahim sorry ka je sai zuwa anjima yanzu miji yana ganawa da matarsa ne so dan haka yana bukatar privency", daga haka ta juya ta rufo kofar da karfi.




Yadda kofar ta yi ƙara haka zuciyar RAIHAN ta yi ƙara har da ƙoƙarin tarwatsewa, idanunta har wani dishi dishi suke saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai,a duniya babu wanda zai wulakantata taji tashin hankali me tsanani kamar wazer,a hankali ta juya ta fara tafiya tamkar zata kifa saboda yadda jiri ke dibarta,a haka ta samu ta sauka motarta kawai ta nufa ta shiga,sai da taja sama da mintina goma kafin ta ja motar a hankali ta fice daga buldin ɗin.




Surry da ruby da komai ya faru akan idonsu suka juya suka tafa da hannu biyu,kafin Surry ta ce", ruby komai fa yana tafiya dai-dai da yadda muka tsara,to amma abinda ya bani mamaki ya akai kika san wazer baya nan har kika hada baki da sactariya? Dariya ruby ta yi sannan ta ce", ai na shigo office din lokacin da naga banga motarsa ba,da har nayi tunanin ko suna tare da RAIHAN ɗin to sai kuma naga shigowarta,hakan yasa nayi saurin samun sactariya na shaka mata kudi na kuma shirya mata duk abinda nake son ta yi min", tafawa suka kuma yi tare da shekewa da dariya,cikin sauri suka bar office din dan kar oga wazer ya dawo ya samesu.




Dakyar take tuƙin har Allah ya dawo da ita gida,ko key ɗin motar bata tsaya cire ba ta faɗa bangarensu, bata samu kowa a falon ba hakan yasa ta shige daki ta saka key, dan bata son cin karo da kowa a wannan yanayin da take ciki,so take ta yi kuka ko yaya amma hakan ya gagara hadiyar zuciya kawai take tana dafe kirjinta dake yi mata wani irin suya kamar ana soya fanke,wani irin zafi take ji a dukan jikinta hakan ya sa ta kuma ficewa zuwa gading dinsu.




Cak ta tsaya daga inda take tana kallon bayan matar da ta juya sanye da a baya ta lullube kanta sosai bata ga fuskar matarba,abinda matar ke cewa ne yaja hankalinta.


Lallai ina so kafin yau ɗin nan ta kare ku batar min da Yahya ku kaishi inda mutum bai taba zato ba ku boye shi har sai sanda na neme shi",domin tabbas idan na bari yayi nasarar kubutar da Muhammad nuur to fa babu shakka zai samu nasarar rayuwarsa dan haka Inaso ku bishi har cikin gidan gwamnatin ku batar da shi....tamkar iska haka maganganun matar suka dinga shiga kunnen RAIHAN,da sauri taga matar ta kashe wayarta ta cusa cikin jikinta kafin ta fara waige dan tabbatar da cewa babu wanda ya ganta....


A yadda take waigen yasa RAIHAN taso gane wacece", wani irin duka kirjinta ya yi saboda gane matar da ta yi waro ido ta kuma yi ta kasa ko da motsi har matar ta bace daga idanunta.........✍🏽




Tofa wa kuke tunani a cikin matan gidan?


Burin rabi zai cika?




Me his excellency yake kullawa?




Ya zata kaya tsakanin ABBAN rabi da wazer?




Kai rikita rikitar fa da yawa ku dai ku tabbata kunyi comments masu yawa domin hakan shi zai bani damar fede muku biri har wutsiya...


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page46 ```




Cikin daukewar numfashi ta janye ƙafafuwanta da su kayi mata matukar nauyi ta koma dakinta,shigewa ta yi cikin bargo jikinta na wani irin karkarwar sanyi wanda da alama dai zazzaɓi me karfi ya kamata.




A hankali yake tafiya bayan ya dauko su Khalil daga filin jirgi,tun bayan gaisuwar farin cikin ganin juna da su kayi bai kara shiga cikin surutunsu ba,to dake dama sun san hali shi yasa ba su wani damu ba.




Kai tsaye family house dinsu ya nufa,hon daya ya yi masu gadi suka wangale babban gate din da ya cinye rabin unguwar,shiru gidan kasancewar tsakiyar rana ce, kowa yana can ya kule a daka daga me bacci sai me kallo,hakan yasa babu wanda yaji alamun shigowarsu.




Shine a gaba suna baya hakan ya hanasu yin kwarafniyar dawowa gida cikin ahlinsu,sallama su kayi suna saka kai cikin tafkeken falon kakartasu,ita kadai ce a zaune akan kujerarta tamkar ta gado,zuba musu ido ta yi bayan ta amsa sallamarsu, tabbatar dasu dinne yasa ta mikewa cikin tsananin farin ciki tana cewa Masha Allah marhabin da dawowar jikokina jabbama jabbama ta koma fada da filanci,da sauri duka su biyun suka rungume ta cike da farin cikin samunta lafiya.




Kankace me gida ya rude da dawowarsu Nasir falon innawuro take ya dau haramar yan uwan junan,hatta da umma rumana ba a barta baya ba sai da ta halarto gidan duk da tsohon cikin dake jikinta,kowa yana gidan idan ka cire rabi a da Abbanta,dan hatta da wazer bai kuma fita ba yana can sashensa na bangaren innawuro,tunda ya shiga yake faman kiran wayar RAIHAN amma bata dauka ba,tun yana jinta a kunne har yaji an kasheta,cike da mamaki yake duban wayar,sai kuma yaji hankalinsa yana neman tashi, bai tsaya wani tunani ba bayan wanda yayi na zuwa gidan ya gano ko lafiya,hakanne yasa ya yi saurin yin wanka ya sanya ash din jallabiya ya feshe jikinsa da turarukan da na kasa tantancesu,no wonder mana idan ya fito ake kasa gane kalar ƙamshinsa,manyan turarukane na alfarma kusan kala goma kuma ko wanne sai ya fesa shi yasa ba ka isa tantance kamshinsa ba.




Dai-dai lokacin aka fara kiran sallar la'asar,a kuma lokacinne Abban rabi ya dawo sai kawai suka rankaya gaba daya zuwa Masallaci.




Gidan gwamnati..........




Tun bayan gama karin kumallonsu suka koma falon,zaune shiru su kayi his excellency bai bawa Abbie damar tafiya ba shi kuma bai nemi tafiyar ba saboda son jin abinda abokinnashi ke shiryawa,suna nan har aka kira zuhur a nan suka yi sallah, daga cikin gida kuku ya shigo ya shirya musu abinci,a nan ma Abbie yaso yin gaddamar cin abincin amma sai his excellency ya nuna masa idan fa baici ba to babu abinda zai ji daga gareshi,haka nan ya hakura ya tsakuri abincin..




Shi kuwa Abba yahya ganin zaman bana kare ba ne kawai sai ya tafi da niyar aiwatar da shirinsa na tonawa his excellency asiri tun kafin ya kashe masa ɗan uwa.




Cikin tashin hankali Abbie yake kallon his excellency fuskarshi dauke da wani irin mugun mamaki,tunda yake a rayuwarsa bai taba ji ko ganin makirci da cin amana irin wanda aka yi masa ba,kafin ya samu abincewa tari ya sarƙeshi ya fara shi kuwa babu kakkautawa tun yana yi daga zaune har takai shi da faduwa kasan cafet hannunshi dafe a kan ƙirjinshi dake yi masa wata irin suya,jinin da ya fito daga bakinshi da wani farin abu yasa ya yi saurin kallon his excellency, wannan shike nuna alamun cewa gubar ta fara aiki a jikinshi,kai tsawon lokacin ma ya isa ace ta gama dagargaje kayan cikinshi tunda sau biyu yana cinta,magana yake son yi amma ina tuni ya fara kokuwa da numfashinsa dake son kufcewa daga makogaransa.




Dai-dai lokacinne kuma motar yan sanda ta shigo gidan gwamnatin sakamakon kiran gaggawar da Abba yahya ya yi musu akan cewa su zo gidan gwamnatin domin an samu mutumin da ake nema ruwa a jallo.




HAMMA IDRES.......




Traffic ne ya tsaida shi akan hanyarsa ta dawowa gida kasancewar yau ya tashi da wuri saboda har yanzu ana zuwa musu gaisuwa shi yasa ko da suka koma bakin aiki basa kaiwa dare suke dawowa gida,me saida jarida ne yazo jikin glas din window motar yana tura masa yallabai ga sabuwar jarida me dauke da abin mamaki ka siya kaji kanun labarin na tabbata zaka ƙaru", dan tsaki Hamma Idris ya yi shi sam ba ma' bocin karanta jarida ba ne,to amma jin abinda me sayar da jaridar ya fada ya dauki hankalinshi har ya karbi jaridar tare da bashi kudinsa,a lokacinne kuma aka basu hannu,


Bai kalli jaridar ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login