Showing 15001 words to 18000 words out of 189984 words
,kana cikin damuwa ta ce"to yanzu Dr ya zanyi da wadan da suke neman rayuwar RAIHAN,dole ta sa nake BOYE RAIHAN saboda gudun kar a cutar min da ita kuma kaima kafi kowa sanin hakan,yanzu idan na gaya mata ta ina zan ci gaba da ɓoye ta dan kare rayuwarta? Amarya rayuwar RAIHAN a hannun Allah ta ke ba a hannun mu ba kuma ba a hannun wanda yake son kashe ta ba,mu dai namu shine mu zama sanadin rayuwar tun da Allah bai kawo karshen ta ba,kuma ko a yanzu muka bayyana RAIHAN ina ga ba muyi aikin banza ba tun da ta yi girma ta yi wayo ta kuma fara sanin ciwon kanta,,,,katse shi Anty amarya ta yi da sauri tare da cewa a'a Dr Sabo har yanzu RAIHAN yarinya ce bata isa kare kanta ba,na yadda da maganar ka kuma Nima nasan haka,Amma kasan da cewa Allah da kansa ya ce ta shi in taimake ka,babu ta yadda za ayi kana zaune a inuwa Allah ya yi maka abu dole sai da sanadi,to rayuwar raihan tana hannun Allah amma mune sanadin dorewar rayuwar tata" jin jina kai Dr Sabo ya yi kafin ya dan numfasa ya ce"na fahimce ki amarya kuma nayi miki uzuri na kasancewar ki uwar da take matukar so da kaunar ɗan ta da kuma son ganin yayi rayuwa me tsayi,na fahimce ki a matsayin ki na uwar da bata da kowa sai wannan tilon dan da ake son ganin bayan sa,dan haka nayi alkawari zan ci gaba da taimaka miki har zuwa inda numfashi na ya tsaya da kuma bayyanar makiyan ɓoye"na gode Dr Sabo Allah Ubangiji ya sa ka maka da alheri Allah ya raya maka zuri'a Allah yasa ka gama da duniya lafiya"Amin ya Allah ya fada cike da jin dadin addua daga bakin wadda yake gani kamar y'ar uwar shi ta jini.
Cikin fesar da iskar da take bakin shi ya ce"amarya amma duk da haka bamu da wata hanyar bayan wadda na fada miki,dole sai dai mu sanar da RAIHAN ko mai,amma ba ina nufin Mu bude sirrin ɓoye ba,dole RAIHAN sai ta bamu hadin kai a wannan gaɓar"kamar ya ke nan Dr ? Anty amarya ta tambaye shi cike da zakuwar san jin manufar hakan,ɗan cizon bakin biron da ke hannun shi ya yi,kafin ya ce" dole RAIHAN zata ci gaba da zama a matsayin namiji bayan ta san ko ita din wacece" shi yasa nace miki dole sai mun samu hadin kanta, wannan ita kadaice hanya ,kin ga mun jefi tsuntsaye biyu da dutse guda daya,wato mun kawar da damuwar RAIHAN ta hanyar sanar da ita ko wacece,idan yaso sai muji da fara binciken makiyan RAIHAN " Dr Sabo ta yaya zamu gane wadan nan mutanen? Murmushi Dr Sabo ya yi sannan ya ce" amarya ba zamu iya gano makiyan RAIHAN ba dole sai ta hanyar ta" kamar ya ke nan,ta tambaye shi cike da mamaki,muskutawa ya danyi Sannan ya dube ta ,ya ce" amarya gane makiyi sai Allah,idan har ba bayyana RAIHAN wa duniya mu kayi ba to tabbas ina mai tabbatar miki da cewa sai dai muyi ta bulayi wato lalube a duhu,mu bar Raihan a ɓoye zuwa nan da wani lokaci wato lokacin da zata san kanta lokacin da ta zama cikakkar budurwa me shekaru goma sha tara zuwa ashirin,to mu kuma alokacin ne zamu bayyanar da ita ga kowa ,dan mu janyo hankalin masu san ganin bayanta,a yanzu raihan bata da wayo ko hankalin da zata fahimce mu da manufar mu,dan haka mu bar wa lokaci komai ,yanzu dai mu yi wannan matakin na gaba,amma shima kar ki sanar da ita kai tsaye sai nazo akwai hanyoyin da zamu bi mu sanar da ita ba tare da ta shiga tashin hankali da rudani ba,fata na dai kawai mu sanar da ita da kanmu,idan muka bari ta fahimta da kanta baza mu shawo kan ta har ta bamu hadin kai ba"ajiyar zuciya Anty amarya ta saki ,sai alokacin wani dan takaitaccen murmushi ya sibuce mata,tare da samun kwanciyar hankali,ta ce" to shike nan Dr Sabo na gode Allah ya nuna mana lokacin ya bamu a ran rai da lafiya,Amin ya Allah"ta shi ta yi tana cewa bari naje nasan yana can mota ya kumbura dan fushi ,saboda dakyar na lallaba shi ya zauna"ok tom shike nan amarya sai kin jini"daga nan ta fita daga office din tana mai jin yar nutsuwa a ranta.
Ko da ta samu Rahim a mota ya cika taf din kamar yadda ta faɗa,shafa kanshi ta yi tana murmushin samun nutsuwa, cikin tausaya wa ta ce,"sorry my friend na jima ko? Ɗan karamin bakin sa ya tura kana ya dubi a gogon dake daure a siririyar tsintsiyar hannun shi,sannan ya sube ta a shagawabe ya ce" Anty amarya kin san tun dazu akayi sanarwa A Wazir zai yi hira da Alh Ibrahim mangal shahararren ɗan kasuwar nan kuma fitaccen dan siyasa ,akan dalilin sa na komawa jam'iyar adawa wato jam'iyar su Alhaji Garba
Me fata" rike baki Anty amarya ta yi cike da mamakin yadda Rahim ya iya zaiyano wannan lissafin,kafin ta ce" to Rahim kai meye damuwarka da siyasa da ka damu sai kaji hirar?ta tambaye shi Daidai lokacin da take harba motar bisa kwalta bayan fitowa daga harabar asibitin,karyar da wuya Rahim ya yi cike da sangartar da ke nuni da tsananin gatan sa,ya ce" Anty ke ma kin san ba wannan nake son ji ba,A Wazir chibado kawai nake son gani" to shike nan my Love kar ka damu kayi hakuri zaka samu ji tun da har yanzu da sauran awa daya a gaba" da wannan hirar su ka karasa gida,sai da Anty amarya ta tabbatar ta bawa Rahim magungunan sa sannan ta shiga sabgar gida, ta bar Rahim da jiran lokaci.
Ba Rahim kadai ba,zan iya cewa gaba daya kusan daukakin mutane jiran wannan hira suke,wadda ita ce damar su ta farko da suka samu dan ganin fuskar wazir chibado,a zahirin gaskiya da yawan mutane ba ta hirar suke ba ,ta yadda kawai zasu ga fuskar WAZIR CHIBADO ne,dan da yawa basu san ainahin fuskarsa ba,sai daddaɗar muryasa da ta gewaya birni da ƙauyuka harma da wasu kananan jahohi,ƙalilan ɗin mutane ne wadan da siyasar ke tsakiyar kansu suke daukin jin makasudin abin da yasa Alhaji Ibrahim mangal sauya sheka.
Yanmata kuwa bazan iya kirga adadin su ba,ko wacce ka kalli fuskarta sai kaga annuri da farincikin ganin gwarzan matashi me farinjini a duniyar matasa,
To a dai-dai wannan lokacin ma Hajiya innawuro ce zaune a hamshaƙin falonta ita da jikarta wadda ta samu bakuncin zuwan ta safiyar yau ɗin,gaba daya sun zubawa ƙatuwar tv flaxuma ido ,tare da ɗan satar kallon a gogo,zuciyar rabi a cike take da dokin yin tozali da fuskar dan uwanta yayanta kuma rabin ranta wanda kullum take mafarkin ya zama angonta,duk da cewa ita din fuskarshi ba bakuwar ta ba ce,to amma sai taji yau ta zamar mata bakuwar kasancewar jimawar da tayi bata ganshi ba,dan lokacin da ya dawo daga karatu ita kuma suna jarrabawar karshe shi yasa bata samu zuwa ba,shi yasa suna kammalawa ta hado kayanta ta yiwa gidan tsinke,axewarta bata barin gidan sai da igiyar auren A Wazir.
Karfe biyar dai-dai ƙatuwar tv flaxuma dake girke a bangon falon Anty amarya ta hasko kyakkyawa kuma kamilalliyar fuskar A, Wazir chibado a tashar nan ta su me farinjini wato CHIBAƊO TV.
Wata yar zabura Rahim ya yi,yayin da zuciyar shi ta yi wani irin mahaukacin bugu,wanda ba zai iya cewa ga dalilin hakan ba,Anty amarya ma zubawa fuskar a wazir idanu ta yi,haka jiddo da ta gudo nan ta bar Hajiya goggo itama ta zubawa wazir chibado ido zuciyarta na bugu da ganin wani irin kwarjini da haiba tare da kamala a fuskar wazir, a hankali sassanyar Muryar shi me cike da wani irin amo wanda yake tafe da tsananin kamewa ta fara karaɗe kunnuwan masoyan sa da masoyan Alhaji Ibrahim mangal,idan kaga yadda yake fitar da kalaman sa abin zai matukar birgeka ya kuma kayatar da me kallon sa,tabbas mutane sun shaida baiwar da Allah Ubangiji yayi wa wannan bawa nasa,hira ce ta kasance tsakanin sa da baƙon sa cikin hikima da sanin makamar aiki ga kuma iya sarrafa harshe,hirar mintina talatin da yayi da bakonsa ta kuma janyo masa yawan mutane da shi kansa Ibrahim mangal ɗin wanda tun kafin ya bar gidan tv ya fara amsa sakon masoya wanda suke goya masa baya dalilin hirar sa da A Wazir ,hakan kuwa ba karamin farinciki ya sanya shi ba.
To bare kuma mai gayya mai aiki ,dan har sai da kansa ya fara daukar ɗumin ciwo saboda amsa sakonnin masoya,da ƙyar ya takaita karbar sakonnin da dalilin gabatowar lokaci wanda hakan ne ya kwace shi ya baro dakin tattaunawar cike da gajiya da kasalar da ta rufe shi.
Ko da ya koma gida bai tsaya wajen Innawuro ba bare ya amshi bakuncin rabi a,kai tsaye ya wuce sama inda anan bangaren sa yake,bath ya fada tare da sakarwa kanshi shaya,sai da ya ji dan dama kana ya yi wanka tare da ɗauro alwalar magriba.
A masallaci suka ci karo da mahaifin sa,daga nan suka yo sashen innawuro,kasancewar duk dare a nan suke haduwa gaba daya suna yin dinner,a nan suka samu Ammi da shukrah,gaida Ammi ya yi kana ya koma kusa da innawuro ya zauna tare da jingina kansa a kafadar ta,alamun shi ya nuna gajiyar da yake ciki sosai, shukrah ce ta fara gaida shi kafin rabi'a ta dora tata gaisuwar cike da kisisina ko kunyar su Ammi ba ta ji ba,kamar yadda ya amsawa shukrah haka ita ma ya amsa mata,duk sai taji jikin ta ya mutu na rashin nuna halin ko Inkula da ya yi da ita,duk da cewa ta san halinsa amma sai tayi tunanin wannan aikin da yake yi ya canja shi,to ashe har yanzu dai yana nan a miskilin sa,Ammi ce ta fahimci yadda gwiwar rabi a ta saki,hakan ya sa ta danyi gyaran murya tare da cewa babana rabi a dai an gama karatu ya kamata ka taya ta murna"ɗan duban Ammin ya yi idanun shi kamar masu jin bacci kana a hankali ya ce"nayi mata murna, Allah yasa ya amfani al'umma "take kuwa fuskar rabi a ta washe har sai da kowa ya fahimci farincikin ta a fili,kowa ya fara cin abinci cikin nutsuwa, kamar yadda ɗabi a kuma ya kasance koyarwar ma aiki,idan suna cin abinci babu me yin magana har sai sun kammala,to yanzun ma haka ce ta kasance,A Wazir bai ci loma sama da biyar ba wayar shi ta fara haske alamun kira,ɗan zubawa wayar idanu ya yi ,duk da cewa wayar pasinal din shi ce ,hakan bai hana shi mamakin me kiran a wannan lokaci ba,har zai share sai kuma ya yi tunanin ba ko wane yake da wannan layin nasa ba,dan haka ta iya yiwuwa kiran yana da muhimmanci, a hankali ya kai hannu ya dauki wayar tare da danna ok,haka kawai ya samu kanshi da wani irin faduwar gaba har bai san lokacin da ya kwantar da kanshi jikin makarin kujerar dinning din da yake zaune ba,tare da rufe idanun shi duk a lokaci guda, a hankali kuma a nutse sanyin Muryar Rahim ta cigaba da cewa Assalamu alaikum A Wazir ne akan layi? Ta fadi haka saboda jin ba a amsa mata sallamar ta ta farko ba,Muryar shi a ɗan shake ya ce" I'm ,dariya Rahim ya yi wadda ta yi gudun fanfalaki ta shige kunne har da jijiyoyin jikinsa,a wani irin bazata Muryar tazo masa,sai kuma ta saukar masa da wani irin yanayi da kara masa kasala da gajiyar da yake ciki,Rahim ya ce"Ni fand ɗin ka ne kuma masoyinka,sunana Abdul Rahim Muhammad nurr,kuma muna gari daya jaha daya,ina fata zaka karbe Ni a matsayin a boki na musamman kuma ƙani,wani kayataccen murmushi Ahmad ya saki wanda tun shigowar sa gidan babu wanda ya ganshi a saman fuskarsa sai yanzun,shi kuwa ba komai ne ya sashi murmushi ba sai jin yadda Rahim ya dage yana introduced din kansa ,babu kwama bare full stop,duk da cewa bai cika son mutum me surutu ba,amma sai yaji Rahim ya burge shi yanayin yarintar shi ya kayatar da shi,dan haka cikin Muryar shi da a yanzu ta dan saki ya ce" thanks Rahim Nima Ina sonka kuma na karbe ka a matsayin abokina kuma amini dama bani da amini abokin shawara,dan kwabe fuska Rahim ya yi kamar yana gaban shi sannan ya ce" to bandirawo wazir amma fa wannan ba waya ta ba ce wayar Anty amarya ce ,Abbie na ya ce zai sai min waya ita kuma ta hana ,amma yanzu dole a saimin waya tun da nayi aboki".
Wazir ya kuma ƙawata fuskarshi da murmushin da yake matukar wuyar samuwa a kan fuskar shi sannan ya ce" na gode Rahim zan ajiye nomber antyn ka,kafin lokacin da zata bari a siya maka",yeee Rahim ya fada yanayin murna wadda ke cike da yarinta,daga nan suka yi sallama kowa ya ajiye wayar, innawuro ta ce"wai har ka koshi ne wazirin gida? Shafa shafaffen cikin sa yayi har yanzu kuma fuskarsa a washe take duk da cewa ba murmushi yake ba,amma kana gani kasan yana cikin nutsuwar zuciya,ya ce" I'm ok granny kar ki damu an jima ki hada min fruet da hannun ki zan sha"yauwa to shike nan yanzu naji zanje,Abbu ya ce" ina zaune kirkiri an kawacemin uwa" gaba daya falon aka sa dariya,wazir kuwa lumshe idanun shi ya yi kawai.
Bani wayata Sarkin surutu,kayi sa a ma da ya daga wayar taka,,langabe kai Rahim ya yi tare da cewa dan Allah Anty ki barni nayi waya, komai kin hanani karatu waya da duk wani abu da zai sa na samu farinciki"ya fada idanun shi na cika da hawaye kuma hakan shi yake nuna raunin sa da tsananin damuwar da yake ciki a kan haka,da sauri ta dawo kusa da shi tare da kama shi ta kwantar da kanshi saman kafadunta,cikin damuwa ta ce" No Rahim bana so ka tuhume Ni a matsayin uwar da bata son farincikin danta duk abin da ka nema zan yi maka kuma duk wata walwala da ka rasa zan dawo maka da ita zan sa a kai ka University joda ka karanci media zan cika maka burinka na zama cikakken dan jarida,da wani irin farin ciki ya rungume antyn yana cewa da gaske kike Anty amarya duk abin da kika fada zaki yi min? Zan yi maka Rahim amma da sharaɗi"ta faɗa tana mai ɗago fuskarsa dan tana son ya gano gaskiya a cikin idanun ta,meye sharadin Anty amarya? Sharadin shine zaka ci gaba da ɓoye mana kanka ta yadda babu wanda zai fahimci kaiwaye kuma wane jinsi ne,dole sai kayi mana wannan alkawarin tare da yiwa mahaifiyarka biyayya akan hakan"Dr Sabo ke nan da ya shigo akan gaɓa ya bawa Rahim amsar tambayar sa ,wanda zaman na jiran zuwan sa ne.
Fateemah y Adam.......... ✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page6 ```
....Da sauri Anty amarya ta tashi ta duba waje ta leka ko ina, sannan ta gyara contain ɗin falon ,zuwa ta yi gaban tv ta kara volum,shi dai Rahim kallo yake bin ko wannen su da shi,dan kwakwalwar shi ta kasa hasaso masa komai,iya kacin sa jiran tsammani,zama Anty amarya ta yi a gefan sa yayin da Dr Sabo yake fuskantar sa.
Kama hannun sa Anty amarya ta yi idanun ta cike taf da hawaye,ta ce" Rahim nayi maka babban laifi wanda ban sani ba ko har da Ubangiji na nayiwa saboda nayi shishshigi cikin lamarin sa,duk da cewa so ne ya rufe min ido da kuma neman mafita,dan haka nake kyautata zaton cewa idan ma nayi laifi gurin Allah insha Allah zai yafe min,haka kaima ina saran yafiya daga gareka ,duk abin da nayi saboda kaine saboda kar na rasa ka nayi kuma har yanzun ina kan baka na saboda Allah ya ce tashi na taimakeka,kuma ina so na zama uwar da ta zama sanadin kyakkyawar rayuwa me nisa ga danta,dan haka kafin na gaya maka komai kuma na cika maka alkawarin ka, sai Nima kayi alkawarin yi min biyayya akan abin da na umarce ka" duk da cewa Rahim ya shiga ruɗu amma ya aiyana cewa mahaifiyarsa baza ta taɓa cutar da shi ba,dan haka kai tsaye ya ce" Anty amarya nayi miki alkawari ko da baza ki cika naki alkawarin ba,Ni ya zamarwa wajibi da nayi miki biyayya dan haka babu sharadi a tsakanin mu akan abin da kike so nayi miki" da kyau yaron kirki wanda ya samu tarbiyya ta gari,cewar Dr Sabo ke nan da kalaman Rahim su kayi matukar birge shi da bashi mamaki a matsayin sa na yaro karami,sai dai kuma idan ya yi duba da cewa Rahim ɗin ya samu ilmi me zurfi da kuma ingantacciyar tarbiyya ,abin ba wani abin mamaki ba ne,dan haka ya dan yi gyaran murya tare da kara gyara zaman sa,ya ce" Rahim nasan ko baka fada ba akwai tarin tambayoyin da kake da su akan ka da kuma rudani da kake shiga na yanayin halittar ka" da sauri Rahim ya ɗago kansa yana zuba idanunsa masu sheƙi cikin na Dr Sabo,duk da cewa bai ce komai ba amma Dr Sabo ya kuma fahimtar yadda al'amarin yake matukar damun Rahim ɗin,wanda har hakan yake gab da shafar lafiyar sa,ci gaba ya yi da cewa Rahim kayi hakuri ka kuma gafarce mu,kai ba namiji ba ne macece mahaifiyarka ta haifoka kuma sunan ki shine RAIHAN" a wani irin zabure da matukar rikicewa RAIHAN ta mike tsaye tana mai nuna kanta bakin ta na wani irin karkarwa komai ya kasa fita daga bakinta,da sauri Anty amarya ta janyo ta ta rungume ta tare da sakin wani Marayan kuka me cike da ban tausayi,cikin kukan ta shiga bawa RAIHAN