Showing 96001 words to 99000 words out of 189984 words

Chapter 33 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15637

Turo shi cikinmu akai dan kawai ya dauke videon nan",dago kanta ta yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi, sannan cikin tunawa da wani abu wanda fuskarta ta nuna alamun hakan,ta ce",hamma wazeer to waye ya sace Haidar kuma saboda me aka sace shi? Idan har masu video ne me yasa zasu Turo wani dan ya sace musu videon? Da sauri ta zare jikinta daga nasa computer sa ta nufa ta shiga saita wannan abun da ta zaro daga jikin labulen office ɗinta,zama ya yi saitin computer hakan yasa ta koma ta bayanshi suka zubawa fuskar computer ido,dukkan su suna cike da mamakin wanda suka gani matsayin dan leken asirin su Dr sanate.




Wayyo hamma wannan fa khalid ne bashi nake zato ba,wlh abu Huraira nake zargi,to amma ya akai haka? Kanta ta shiga duka.cike da ruɗani da ake son jefa mata.




Da dan karfi ya janyota sai gata akan cinyarsa dabas,dubanta ya shiga yi yana son ta bari su haɗa ido,sai dai ina Raihan ta shiga ruɗani yadda take yi din tamkar wata zararra.




___________




Acikin safiyar dai momy Hanne ta yi kokarin ganin dukkan yaranta,Saida ta tabbatar da cewa lafiya suke sannan taja musu kunne akan cewa lallai suyi takatsantsan da kowa na gidan nan kar su yadda da kowa saboda koda yaushe za a iya cutar dasu,ta nuna musu cewa su ma suyi ɗamarar yin yaki da dukkan makiyansu da suka fara bayyana,duk dai da cewa bata sanar dasu sakon da aka turo mata dashi ba.




Abangaren ur exsellency da Abbie da kuma Abba yahya,sun hadu ne su uku dan tattauna matsalar da ki karewa saima karuwa da take da ɗa yi.




Cikin nutsuwa ur exsellency ya ce",ku yi hakuri babu wanda zan iya yin wannan maganar idan ba ku ba,saboda kune kadai mutanen da na yadda dasu a wannan kadamin", Abba yahya ya danyi murmushi kafin ya ce,ai ur exsellency babu wani abin yadda yanzu koda mu ɗin ne kuwa ina mai baka shawara cewa kar ka zurfafa yadda domin wanda kabawa amana da yadda shi yafi ci maka amanar,muskutawa ya yi kana cikin dan nuna girmamawa ya cigaba da cewa,bayan wannan ur exsellency ina da korafi akan ɗan uwana",duk zuba mishi ido su kayi kana ur exsellency ya ba shi damar magana,na gode Abba yahya ya fada sannan ya cigaba da cewa ur exsellency a ganina bai kamata idan za muyi tattaunawa ka dinga kiranmu gidan gwamnaty ba,sai nake ga kamar ka ture maganar dan uwana da tun kafin yau ya sanar da kai cewa baya bukatar shiga siyasa wanda hakan ne ya kaika kan kujerar da kake zaune akai,bayan wannan kuma hakan yana iya kawo mana matsala domin kuwa kowa yasan cewa duk wanda yayi motsi a cikin gidan gwamnati to tamkar yayi akan idanun mutanene,za a iya fassara zaman mu da wata manufa,kuma abin akan Nura zai kare saboda kowa yasan cewa bashi da sha'awar mulki mutane zasu ce to yanzu me ya sanya shi shiga,abu na biyu babu yadda za ai zaman da mu kayi ya buya sai dai maganar da muka tattauna itama kuma babu tabbas,dan haka ina rokon alfarma dan Allah duk sanda kake bukatar magana damu ko shi kaje inda yake kamar yadda kuka saba a can baya,za ka iya badda kama kaje gidansa amma shi ba zai iya ba domin gidan gwamnaty ba wasa ba.




Tunda Abba yahya ya fara magana ur exsellency yake jinjina kai wanda ke nuna cewa yana karbar maganar da Abba yahya ke yi,duk da cewa ya dan ji kalamansa akwai kausasawa a ciki ,to amma bai damu da hakan ba tunda yasan tun baya ABBA YAHYA shike yi musu fada akan duk abinda su kayi ba daidai ba,to yanzun ma haka ya dauka.




Shima abbien yaji dadin maganar da Abba yahya yayi duk da cewa ya dan ji nauyin wasu kalaman,amma dai duk inda aka je aka dawo maganarsa akan daidai take.




Cikin nuna girmamawar da ya saba yi masa ur exsellency ya ce",tabbas wannan maganar haka take kuma in sha Allah za a gyara kamar yadda muke son gyara al'amarin jihar nan",yauwaa cewar Abba yahya, Abbie ne ya dan kawo numfashi kana ya ce",to yanzu ta ina kuke ganin zamu fara? Ur exsellency ya ce",Ni ina ga kawai mu baza jami'an tsaro ta ko ina duk wanda suka kama da wani laifi makamancin wannan su kama shi,idan aka kama yaran zasu fadi manyan daga nan har a samu a cimma gaci.




Abba yahya ya ce", ban tari numfashinka ba amma kai kasan hakan baza ta yiwu ba,saboda anyi hakan sau ba adadi amma daga karshe sai kaji an sake su kuma a rasa daga ina hakan ke faruwa ,an canja Kwamishina ya kai sau goma amma duk bata canja zani ba,ina ga kawai mu ci gaba da addu'a musa malamai suyi ta sauka a ana sadaka domin sadaka maganin masifa ce, sannan mu je kowa ya zurfafa tunaninsa bincike koda ta sirrine mu samo masu yin taasarnan dan ina da tabbacin cewa acikin mu ne,kaga kuwa babu wadanda zasu iya gano komai sai dai a tsakanin namu mudinga kula da motsin kowa idanun mu ya zamana kullum a bude suke kan mutanan mu",tabbas wannan shawara tayi cewar ur exsellency har fuskarshi na fidda annuri na irin jin dadin shawarar da Abba yahya ya kawo,shima abbie ya ji dadi sosai..




Daga nan suka dan tattauna wasu al'amuran ,sai misalin ƙarfe hudu suka fito daga gidan gwamnaty, Abba yahya ya dubi abbie bayan sun hau titi ya ce",to gida ko Company wanne zaka? Duba agogo Abbie ya yi kana yace muje gida kawai lokaci ya tafi sai Allah ya kaimu gobe",daga haka suka dau hanyar komawa gida.




Abba yahya ne ya kula da wata ƙatuwar motar daf cike da simintyy tana bin bayansu da gudu kamar zata bi ta kansu, Abba yahya yace",Nura wannan motar kamar mu take so ta taka ga yadda yake tukyi kamar da hujja",kamar Abba yahya ya sani kafin ya rufe baki motar tayi kansu da gaske so take ta murkushesu,wani irin juya kan motar yayi suka gangara can gefan titi wanda hakan Saida ya jawo musu buguwa,wucewar su taki kadan babbar motar ta gifta su da wani irin gudu har na kusa da driver yana lekowa yana kallon su Abbie da suma kallonsu suke cike da mamaki,yatsa ya nuna musu alamar kashedi.




Baki sake Abbie ya ce", to me mu kayi musu waɗannan mutanen haka? Abba yahya yana gyara motar dan cire ta daga inda ta maƙale yace", turosu akayi wannan ba abin mamaki bane Allah ya shiga tsakaninmu dasu, Amin Abbie ya fada yana shiga motar bayan Abba yahya ya cirota ya gyara fakin,dan gurjewa su kayi ba mai yawa ba,har suka je gida ta ajjubin abin suke,ba su bari kowa ya ji ba gudun kawo tashin hankali da damuwa a wajen iyalannasu.






Bayan fitar su Abbie ur exsellency ya kira waya shi kadai yasan me suka tattauna da wanda yayiwa wayar amma dai alamu sun nuna cewa abune me muhimmanci a gareshi.




CHIBAƊO FM........


Sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya dago fuskarta da tayi jajur,dage mata gira ya yi tare da nuna mata fuskarta da girarsa,juyawa ta yi ta kalli fuskarta cikin mudubin dake gefanta ,anan taci karo da kanta saman cinyar wazeer CHIBADO dare dare,da wani irin hanzari ta mike tana lallubar hanyar guduwa,takaici kunya haushi duk sun dabaibaye ta.




A tare suka bude kofar da rabi'a ita zata shiga ita kuma Raihan zata fita,turus su kayi gaba dayansu suna kallon juna,kowacce ta gane yar uwarta, Raihan bata iya cewa komai ba saboda yadda zuciyarta ke wani irin halbawa da karfi ,ratsawa tayi gefan Rabi'ah ta shige,sake da baki rabi'a ta bi bayan Raihan da kallo,kallo tayi mata sosai wanda har sai da ta fara jin wani irin tsoro wanda ta kasa gane ko tsoran meye,da kyar ta daidaita kanta ta karasa shiga office ɗin,wai me wannan yaron yake nufi ne? kai ta bakin suryy fa wlh bata yadda da wannan yaron ba akwai wani ɓoyayyan abu dan haka dole tasa ido akansa.




A cikin nutsuwarsa ya juyo a tunaninsa Raihan ce ta dawo amma sai yaga saɓanin haka,tsaf fuskar ta kuma hadewa ta dinke kai kace wani mugun sakon aka aiko masa dashi.




Duk da cewa jikinta yayi sanyi amma hakan bai sa ta kasa karasawa ba.


Me ya kawo ki?


Turus ta yi jin tambayar da ya watsa mata amma kai ka ce bashi yayi maganar ba.




Yanzu Hamma WAZEER dan nazo wajenka sai ka tuhumeni?


Tunda baki da amsa jeki",


Wani abu ne ya tsaya mata,har ta kasa hadiyewa cikin fushi ta ce",amma shi wancan dan iskan yaron yana zuwa duk lokacin da yaga dama amma Ni da nake matarka kana kokarin samun get da shigowa inda kake",


Idan ba maganar aiki ce ta kawo ki ba kar na kuma ganin ki a nan',ya fada yana kuma kame fuskarshi wadda take kamar zata yi aman wuta.


Ganin babu sauki yasa dole ta juya ta fita cikin wani irin fushi da alwashi iri iri aranta.




BAYAN SATI ƊAYA.........






Shugaban jam'iya dai sai da ya tabbatar da cewa babu wata damuwa sannan yabar iyalansa a can ya dawo,yayi hakan ne koda zata kwaɓe sai yaji da kansa iya shi kadai.




Bai damu da tuhumar su Dr sanate ba saboda yasan shima ba haka ya zaunaba,dan haka ya bisu aka dora daga inda aka tsaya,dan kuwa babu abinda suka rage daga irin sharrinsu da kuma kulle kullensu duk akan kujerun da suke son hawa.




A bangaren su RAIHAN kuwa tun ranar da suka.gane Khalid har yanzu basu kuma sashi a idanunsu ba,bare kuma ya shigo da sunan aiki,duk da cewa Raihan har yanzu bata yadda cewa Khalid ne da Wannan aika aika ba,saidai ta dauki matakin tsayawa tsayin daka dan yin kyakkyawan bincike akan sarkakiyar da suke ciki ta kuma sha alwashin sai ta nemo inda Haidar yake a mace ko a raye.


Batun rabi'a kuwa tun ranar ta fara kafawa Raihan duk wani abu da yasan zata yi ya kuntata Rahim to shi zata yi ,ta dauki wata irin tsana ta ɗorawa Rahim ,yayinda ita kuma Raihan kallonta take a matsayin mahaukaciya duk da cewa tana jin wani irin abu me tsananin zafi duk ta tuna cewa rabi'a matar WAZEER ce.




A hankali ta gyara likaf ɗin dake sanye a saman fuskarta kafin cikin takatsantsan ta gyara zamanta tana mai fuskantar mutuminnata.




Ta ce", na karanta duk bayananka da kuma kudurinka akan ahlin CHIBAƊO,tun lokacin nake jiran sakonka sai dai amma shiru kamar maye yaci shurwa,shin kana tunanin a wannan tafiyar wahainiyar zamu cimma burikanmu? Shima gyara zamansa ya yi tare da zaman fecemack dinsa kana ya ce", me lullubi duk abinda kike tunani ba haka bane,ina can ina shirya mana makaman yaki wadanda za muyi fita daya zuwa biyu dasu mu cimma kudurinmu,ke Raihan kike son ganin baya Ni kuma surukin Raihan da mijin Raihan Kinga kuwa dole mu cure waje daya tunda minti tarayya akan manufa daya,ba iya Raihan nake son ganin baya ba harda yan uwanta da mahaifinta kai da duk wani me ruwa da tsaki a cikin dukiyar Nura,ina son daukaka shahara shura sai dai kuma kash wadannan abubuwa basa yiwuwa sai da kudi Ni kuma bani da kudi,ina son shiga cikin manya a dama dani bazan iya kirga maka adadin burikana ba,wadanda kuma basa taba samuwa gareni sai da kudi.dan haka dole na kashe Nura da da Raihan dan na samu abinda nake so,yaransa su zasu zame min katanga domin kowa burinsa ya samu dukiyar da take a matsayin ta Raihan ",...


In tambayeki mana? Abokin cin mushenta ya tambayeta,ina jinka? Wai me yasa kowa keson dukiyar Raihan? Shin da ya bata dukiyar nan bai bawa Kowa daga cikin iyalansa ba? Kuma me yasa dukiyar Raihan tafi ta kowa yawa da haɓaka?




Wani dan Murmushi tayi kana ta ce", wallahi Allah daya kenan nur ya fita hakkin iyalansa domin duk abinda ya bawa ƁOYAYYAR RAIHAN sai ya fitar da na sauran iyalansa, sannan abinda yasa dukiyar Raihan tayi yawan da me zato bai taba zata ba tayi yawan da har tazo ta ninka ta ubanta sau dubu shine duk lokacin da ya cire wa Raihan wani abu adukiyarsa juya mata ake yi su kuma ragowar yaransa tunda sun kasance maza kuma suna nan sai yake warewa yana aje musu,duk wani Company da kaga Ni ko gidan mai ribar Raihan ce ta samar dasu,a lokacin da Nura ya dankawa yaransa dukiyoyinsu a lokacin tuni dukiyar Raihan ta kai inda me zato bai zata ba.




Sai dai cash ba kowa ne yasan wannan labarin da nake baka ba,domin duka yayansa kallon mahaifinsu suke a wanda baida adalci ya dauki hakkinsu ya baiwa gaibu dan haka dole kowa yanzu yake haƙilon yadda zaiyi ya kwaci dukiyarsa,ina mai kuma jaddada maka cewa babu wanda yasan wannan sirrin wato asalin sirrin dukiyar Raihan.




Ke ya akai kika sani?




Dariya tayi me dan sauti kafin ta ce ", haba abokina ba sai kaji wannan ba,iya wannan ma da na gaya maka ya ishe ka,yanzu dai wa kake ganin za mu fara aikawa uban ko yar? Ta bangarenka kuma wa za a fara kawarwa uban ko ɗan? Girgiza kai ya yi kafin ya ce", ta kananun za mu fara wato yaran Alh nur maza saboda sune suke kawo hari akan dukiyar Raihan idan an gama dasu sai uban",a bangarena kuma yanzu ya kan yaron zan fara saboda yafi uban wahalar sha ani nasan wanda zan tura ya yi min wannan aikin", dan jim ta yi kafin ta ce", ta wacce hanya zamu aika yaran sannan da wa za mu fara? Hoto ya nuna mata ba tare da ya bar hanyar da wani zai iya gani ba,dariya tayi kana suka mike gaba daya kowa yabi hanyar da ya bullo.






RAIHAN Kinga takanki........✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page33 ```




Aunty Rahim sannu da fitowa rukayya ta faɗa cikin yanayin girmamawa,yauwa rukayya ,Aunty amarya ta faɗa tana zama a kujerarta dake gefan Abbie, Hamma Idris ma gaidasu ya yi cikin girmamawa da wayewar da ke nuna cewa akwai fahimtar juna a tsakaninsu.


Cikin kwanciyar hankali suka fara karyawa,wayar Raihan ce ta dan kawo haske alamun shigowar sako,ɗan dakatawa ta yi da kai ruwan Lipton bakinta tana mai duban wayar,bata cika daukar waya idan tana cin abinci ba,kamar yadda iyayenta suka dorata kai.


Sai dai kuma haka nan taji bazata iya jurewa har ta kammala kafin ta ɗaga wannan sakon ba,sai da ta fakaici idanun Abbie Sannan ta yi saurin daukar wayar ta bude inbox.


Zaro manyan idanunta ta yi,kana cikin mamaki har bakinta na rawa ta ce", what? Duk kuma sai hankalinsu ya dawo kanta,cikin fargaba da tsoran da ya riga ya zauna mata aunty amarya ta ce",lafiya me ya faru?cikin wani irin takaici da tasowar tsohon miki Raihan ta ce", Abbie wai kaji an sake mutanen da aka makama jiya,a yadda labarin yazo min ance ko shiga station din ba su yi ba aka bada umarnin sake su.




Jinjina kai Abbie yayi yana mai jin ɗacin hakan a ransa,Hamma idi kuwa zabura ya yi cikin nasa takaicin ya ce",gaskiya Abbie ya kamata a dakatar da wannan abun haka,ya za ai ana tufka wasu shegu na warwarewa gaskiya da sake,Ni wallahi na fara zargin gwamnatin nan kamar yadda da yawa mutane suke zargin da sa hannunta a kan duk abinda ke faruwa", Abbie ne ya dakatar da shi cikin rashin jin dadi ya ce",Idris ka nutsu bana son rashin ɗa a", kayi hakuri Abbie Hamma Idris ya fada yana kallon yanayin fuskar abbien da ta nuna rashin jin dadin kalamin da ya yi akan gwamnati.






Cikin damuwa Raihan ta dubi abbien ta ce",Abbie kayi hakuri da abinda zance,ta cigaba da cewa Abbie ko Ni ina zargin gwamnatin nan da rashin gaskiya idan ba haka ba Abbie ya za ai ace an kama mutane kuma ansa an sake su ba tare da ko cikin station din sun shiga ba?kuma babu me karfin hakan sai gwamnatin da ke kan mulki,Abbie mutanen nan fa duka bakinsu daya. a idanun duniya ne suke makiyan juna amma a bayan fage kansu a hade yake ,yarjejeniya ce a tsakaninsu,wallahi Abbie yau sai nayi rubutu akan haka sai na fidda abinda suke boyewa duniya dan naga idan ba muyi da gaske ba mutanen nan so suke su halaka mu baki daya",wani irin kallo aunty amarya ta yi mata kafin ta ce", Rahim kar naji kuma kar na gani babu ruwanka da abinda suke yi,bana son ka jawowa kanka wani bakin jinin bayan wanda kake ciki dan Allah kabarmu muji da wanda yake damunmu",duk zubawa aunty amarya idanu su kai suna kallon fuskarta da idanunta da suke cike da fargaba da tashin hankali,Abbie ne yayi gyaran murya sannan cikin nutsuwa ya ce", duk me ya kawo wannan batun? Dan Allah ku kwantar da hankalinku yanzu fitar da zanyi ur exsellency ne ya kirani nasan kuma ba zai wuce wannan maganar ba,idan ma da sa hannun wani a gwamnatin duk za mu bincika kuma za a kamasu a yi musu hukunci daidai da laifinsu",daga haka ya mike yana shirin fita, Raihan ma mikewa ta yi dan ji ta yi sam ba za ta iya bin umarnin Hamma wazir ba,dole ne taje office ta gabatar da abinda ke ranta, ranar bude video ce yau Allah ya kawo,tunda su basu san zuru ba,to duk yau zatai maganinsu,tana ganin fitar da videon nan ne kawai zai iya kawo karshen mutanennan.




Abbie tsayani mu tafi tare",tafada tana yin hanyar dakinta dan dauko wasu muhimman abubuwa.




A'a kuje idiris ya kaika,saboda tare za mu fita da yaya Yahya", Allah ya kiyaye su kayi masa, ya fita yana amsawa, tare da kokarin lalubo wayar Abba yahya.




Anty amarya dai ranta baiso ba ta bari Raihan ta fita, a hakan ma ji take kamar ta bi sawunsu ,gani take kamar wani abun zai iya samun Raihan ɗin,sai dai da ta tuna Allah sai tayi istigfari ta yi mata addu'ar kariya.




Ruby.........




Tana ganinta a cikin kyakkyawan office din da ya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login