Showing 81001 words to 84000 words out of 189984 words

Chapter 28 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15629

kallonsa kake ba za ka taba cewa kallon nata yake ba.




Sai da ta fita ya samu nutsuwar yin abin da ya kamata.




Itama din ji ta yi ta samu kwarin gwiwar yin aiyukan da suke gabanta,duk da cewa ba wasu aiyuka ba ne saboda tana ragewa daga gida.




Su salim da abu Huraira sunji dadin dawowarta,dan haka kai tsaye suka fara gabatar da aiyukan dake gabansu.




Karfe biyu na bugawa ta tattara komai ta wuce office dinsa kamar yadda ya umarce ta.




Sai dai tana zuwa sakateria ta sanar mata cewa yana da bakuwa,turus ta yi tana duban sakateria wanda ita kuma sakateria ta yi hakan ne da biyu dan tasan cewa sanin yana da bako ko bakuwa ba zai hana Rahim shiga office din oga wazir ba,aikuwa ta samu abin da take so dan take a gurin yanayinta ya sauya zuwa wani sabon yanayin na bacin rai wanda kowa yasan ba ya boyuwa in dai akan wazir ne,sai dai kuma hakan bai hana ta shiga office din cikin nutsuwa ba.




Idanunshi akanta ya amsa sallamar da tayi akan labban sa,ta gefan idanunta takalli hamshikiyar matar dake zaune a gaban wazir,bata kula ta ba ta wuce cikin dakin hutu tana jin takaici duk da dai taga matar babba ce.




Sai da ta yi sallah sannan ta samu ta kashingida,tun tana jiransa har wani bacci me dadi ya dauketa ba tare da ta shirya ba.




Yin Baccin ta da wajen mintuna goma ya shigo dakin bakinsa dauke da yar gajerar sallama, cikin takunsa na nutsuwa ya karaso gabanta tare da tsuguno a gaban ta yana sawa kananun jajayen lip din ta ido,a hankali ya kai hannu yana shafa su kamar me tafiyar tsutsa,kafin ya ji duk wata laka ta jikin shi ta mutu,cikin wani irin abu dake janshi gareta da wani irin ƙarfi ya kai tattausan leban shi saman nata ya bata wata irin sumba da sai da ta ji ta har kwakwalwar kanta,dalilin da yasa ke nan ta bude idanunta da suka sauya kala na alamun Baccin da take yi,waro idon ta yi tana kallon fuskarshi da leban shi da har yanzu yake saman nata,tuni idanunta su kayi raurau sosai take jin tashin hankali a duk yinin yau din akan canjawar halin wazir wanda take ganin kamar auren da yayi ne ya ke neman fitsarar da shi, wannan tunanin daya shiga ranta ne yasa ta yi yunkurin miƙewa sai dai kuma kafin ta zartar da hakan ta ji lallausar harshen sa me sanyi da zaki cikin bakinta,wanda yasa ta hadiye maganar da ta so yi tana faman kakkarwa kamar me rawa,yadda yake yi da harshensa a bakinta ne yasa ta kuma jin wani irin tsoro da fargaban abin da ke shirin faruwa da ita.




Kukan da ta saki me karfi shi ya dakatar da shi daga nisan da ya yi wajen tsotse bakinta,a hankali ya janye fuskarshi yana mai kallon bakin da take ta gogewa tana kuma sakin kukan sakalci,bai kula taba sai miƙewa da ya yi tare da janyo hannunta ya mikar da ita tsaye,idan baki min shuru ba zan yi abin da ya fi haka",ɗuf ta yi kamar an dauke wuta sai dai zuciyarta batabar bugawa da razanin da ta shiga ba.




Fita su kayi kai tsaye wajen mota suka nufa,Samir yayi saurin buɗe musu bayan suka shiga,ko kallon shi ta ki yi babu abin da take rayawa aranta sai cewa wazir ya zama ɗan iska kuma yanzu ba abin yarda ne a gareta ba,dan abin da ya faru ya gama tabbatar mata da cewa ko mai zai iya yi mata,wani irin haushi da tsanarsa ta ji na mamaye zuciyarta,har suka je gidan magana bata shiga tsakaninsu ba,saima tsananin takurewa da ta yi a gefe kamar ace ket ta zura a guje,suna tsayawa ta fita da sauri ko waiwaye bata tsaya yi ba bare ya yi zaton samun sallama daga gareta,a hakan kamar hankalinsa baya kanta sai dai kuma ta can gefen zuciyarshi yake jin motsinta da komai nata.




Wuri wuri ta yi lokacin da ta shiga babban falonsu ta tarar da gaba dayan su aunty amarya har abbie,sannu da gida ta yi musu ta wuce kamar zata kifa,dan gani take kamar zasu gane abinfa ya faru da ita.aunty amarya na fakar idonsu ta mike kamar zata kiching amma sai ta yi kwana ta nufi corridon da dakin RAIHAN ɗin yake.


Da sauri ta tari auntyyn tana cewa aunty wai me yake faruwa ne ina ji kamar da akwai abin da yake faruwa wanda mu ba mu sani ba",colm down Raihan me yake faruwa nutsu ki gaya min komai",


Wani miyau ta hadiya kafin ta ce",aunty amarya wasu halayya ham......bata karasa ba aka turo kofar dakin kai tsaye, Abbie ne ya karaso yana cewa Rahim me ke damunka naga ka shigo cikin wani irin yanayi kamar da akwai damuwa ko?ey a'a dama kaina ne yake ciwo.......katse ta ya yi ta hanyar kama hannunta yana cewa muje Dr Sabo ya duba ka kawai",a'a abbie....shiii ya katse ta yana ci gaba da janta, da ido aunty amarya ta yi mata alamu akan ta yi shiru kawai su je.




Abbie yana kokarin tada mota wayar baffa ta shigo masa,hakan yasa ya dakata ya daga,daga can baffa ya ce",kazo ina son ganinka kai da Raihan ",Tom shike nan baffa gamu nan dama muna tare,kashe motar ya yi yana cewa zo muje baffa nasan ganinmu idan mun fito sai muje Asibitin,jinjina kai ta yi ba tare da ta ce komai ba saboda har yanzu akwai damuwar abun da ya faru akanta.




Shugaban jam'iya...........




Dr ne ya dubi shugaban jam'iya ya ce",har yanzu ba a samu wani sakamako ba,kuma nasan hakan ba yana nufin kyale mu yaron nan ya yi ba,idan ba ayi gaggawar kwace video nan ba ina tabbatar muku zai je wajen TREE Full Y TRUES hakan kuma da zai faru tamkar zuwan karshen mu ne", Alh sale ya yi saurin tarar shi da cewa duk kokarin da muke yi baka gani,sai ka dinga nunawa kamar ka fi mu damuwa da wannan lamarin,karfa ka manta saura kiris asirinmu ya tonu fa,idan har ba ma bin abun nan a hankali to tabbas za muyi kwabar da zata kwabe da mu,tun da dai munsa ana mana aiki akansa ana bibiyar sa cikin sirri mu dakata mu ga abin da zai biyo baya,tun da dai har yanzu a binciken mu babu wanda yasan da labarin video nan bayan shi kawai ina ganin mu saurara muji daga ɓangaren dan leken asirinmu",yafi dai cewar shugaban jam'iyya, wannan matsayar suka tsaya ko waye dan leken asirin na su? Ko a wane bangare yake?macece?namiji ne?mu dai mu bi su mu samo kan zaren.




BAFFA ALI...............




Sai da suka dan taba wasan jika da kaka kamar yadda suka saba idan sun hadu,duk da cewa yau RAIHAN bata cikin wannan yanayin,


Dan gyaran murya ya yi kafin ya maida dubansa kan Abbie ya ce ",yanzu AHMADU ya kira Ni ya kuma yi min bayani mai gamsarwa akan yana so a sanar da Raihan ko mai saboda hakki ne akan mu da ya zama dole mu sanar mata",


Wata irin zabura Raihan ta yi jin yadda baffa ya kira ainahin sunanta kai tsaye ba kuma tare da yanayin tambaya ko bugar ciki ba,kafin ta fita daga wannan mamakin abbien ta ya kuma jefa ta cikin wani mamakin,saboda shima kai tsaye ya amsawa baffan da cewa,nima nayi tunanin hakan bana so dai kawai nayi abinda baya cikin umarninka tun da ga akan yadda muka tsaida magana".




Gaba daya maida hankalinsu su kayi kan Raihan ɗin da ta yi mutuwar zaune kallon su kawai take kamar bata taba sanin su ba,,baffa ne ya ce",raihanatu kwantar da hankalinki,yanzun nan za mu fidda ke daga duhun da kika shiga",yadda numfashin ta yake sama da kasa ne yasa dole Abbie ya janyo ta kusa da shi ya shiga shafa gadon bayanta yana cewa nutsu Raihan ban san ki da saurin rudewa kamar mamanki ba,pls ki nutsu kinji,gyada kanta ta shiga yi tana jin numfashinta na dan daidaituwa,sai da suka tabbatar ta samu kanta, sannan baffa ya zaiyana mata komi cikin nutsuwa kamar yadda Abbie ya sanar da su a wancan ranar,kara rungume abbin ta ta yi tana jin kamar yau tasan shi saboda yanzu tana tare da shi ne kai tsaye ba tare da muku muku ko fargaba ba,yau kai tsayenta take tare da abin ta amatsayin RAIHAN ɗinsa ba boyayya ba,wasu hawayen farinciki ne suka gangaro mata,duk da cewa har yanzu tsugunne bata kare ba,tun da auntyyn ta bata san komai ba,ke nan baza tacigaba da sakewa da abbien nata ba in dai har auntyyn na kusa,ɗago kanta ta yi daga kafadarsa ta dubi baffa dake mata kallon tausayi ta ce",Baffa me yasa ba za ku sanar da aunty amarya ba?aunty amarya fa tana da matukar rauni a kaina kar ku ga lefin ta Ako mai ita din jaruma ce a kaina ne kawai take raunannasam bata da juriya akan duk abinda ya shafeni,ina son aunty amarya fiye da yadda take so na",shafa kanta abbie ya yi cikin nutsuwa ya ce",ki yi hakuri raihanatu ki ba mu hadin kai kamar yadda kika bawa mamanki, muna sane da komai kuma ba munyi haka ne dan ramako ko wata manufa ba,munyi ne dan kawai mun san hakan shi ne zai bamu damar kama makiyan mu a hannu,ina fata kin gane?jin jina kai ta yi, tana share hawayen ta.




Baffa ya ce,"sai kuma abu na biyu da muka riga mu ka yanke shine aurar dake da mu kayi saboda wancan dalilin barazanar da aka yiwa mahaifiyarki akanki,ina fata zaki mana biyayya har zuwa lokacin da komai zai warware".


Aure kuma?


Ta tambaya cikin mamaki da tashin hankali.


Ey aure mana shi muka daura muki',


Abbie wane irin aure kuma?
Ya za ayi ku yi min aure kuma kudinga tunanin ba za asan ko Ni wacece ba?


Baffa ya ce ",ai ba wani bare muka bawa ba, AHMADU ne kuma ya san komai game da ke kin ga kuwa ba mu da wata matsala ke nan,


Wane Ahmadun kuma?


Yauwa gashi nan ma dan halak ya karaso dama tun dazu nace ya zo ayi komai agabansa shima,cewar baffa da ya karasa maganar tare da amsa sallamar wazir din.


Guri ya samu a kasa ya zauna yana gaida Abbie kafin ya juya ya gaida baffa cikin tsananin biyayya,amsawa baffa ya yi cikin kaunar wazir din da yake ji har cikin ran shi.


RAIHAN kuwa turbune fuska ta kuma yi tare da cusa fuskarta a bayan Abbie,baffa ne ya fara magana,yauwa to tun da gashi ya zo sai mu karasa magana danmu samu matsaya ko? Abbie ya ce", haka ne sannan ya juya kan Raihan yana cewa to yanzu kin gane wane Ahmad din ake nufi?to idan ma ba ki gane ba gashi nan wazirinki hammanki shi muka bawa auren ki", da sauri ta ɗago kanta dake bayan Abbie ta ce", amma shi ba ya yi aure ba?


Dukanku ya aura", baffa ya yi saurin bata amsa,kuka kawai tasa har da gunji,Ni wlh baffa bana sonshi kuma Ni banzan yi aure yanzu ba har sai duniya ta sanni amatsayin mace", Abbie ya ce", raihanatu wannan fa duk ba matsala ba ne,shi kanshi wazir din ba tare da sanin shi ko neman shawararshi mu kayi hakan ba sai daga baya muka sanar da shi,dan haka tun da bakwa so gaba daya nayi muku alkawarin duk ranar da muka cimma manufarmu,komai ya warware zan sa ya sake ki shi yaje ya yi rayuwa da matarsa ke kuma ki samu wani ki aura,bashi ke nan ba ",ya fada yana kallon wazir da tun da Abbie ya fara magana ya samu kansa da zubawa bakin shi ido har ya kai aya,jin jina kai kawai wazirr ya yi ba tare da ya iya cewa komai ba,sai dai kuma yadda yaga baffa ya danyi murmushi shima abbien ya yi yana masa wani kallo yasa ya gane cewa wayo ake son yiwa RAIHAN ɗin ,shima samun kansa ya yi da ɗan sakin murmushi ba tare da Raihan ta lura ba.


Shike nan na amince ta faɗa cike da wauta.


To tashi kije an sallame ki,ta shi ta yi tana dan satar kallon wazir da ya yi tamkar bai san tana wurin ba,kwafa ta yi ta fice daga falon.sai yanzu ne ta gane dalilin da yasa yake mata abubuwan iskanci saboda yasan ya bada sadakinta ke nan?tabe baki ta yi tana jin farincikin da bata san na menene ba,nauyin zuciyarta kuma na raguwa.


Ko da ta shiga Aunty amarya ta samu da hajiyar agades,zuba mata ido Aunty amarya ta yi tana dan mamakin yanayin nata na yanzu,to amma ganin cewa da Abbie suka fita sai ta danganta walwalarta ta da hakan,dan. Haka kawai sai ta share suka cigaba da hirarsu har Raihan din da take jin zuciyarta fresh,ko ba komai yanzu zata fuskanci aikinta ne kai tsaye ba tare da wani babban kalubale ba.(hmmm raihanatu ke nan kalubale kam da akwai shi saidai fatan sauki).






______________________




Ko mai akan idanun ta da kunnen ta ya faru, ba tun wannan lokacin ta kware a leke ba,shi yasa har ta gama naɗar komai babu wanda yasan tazo bayan window din,tun tana zama har ta zo ta kasa kaiwa kawai take tana kawowa, tashin hankalinta a bayyane yake damuwarta a bayyane take.


Yanzu dama RAIHAN ɗin da suke tunanin gaubuce ba gaibu bace da akwaita?
Dama tsinanniyar matar nan mace ta haifa?
To wai ya akayi lamra ta shammacesu haka da yawa?
Lallai yaki ne sabo me haɗe da guguwa ya tashi,domin kuwa ba zata taba barin burinta na tsawon shekaru ya mutu ba,kuma wannan abu zai zama sirrinta ne ita kadai, bazata taba bari ya'yanta da kishiyarta su san wannan al'amari me daure kai ba,ita kadai da zata ci gaba da yin yaƙinta har zuwa ranar da zata cimma nasara,idan haka ne kuwa tabbas aunty amarya ta yi ganganci a maimakon ta kashe labarin da yakin sai kawai ta yi masa rai ta hanyar yi masa kyakkyawan ginin da makiyan labarin zasu samu hanya me bullewa,shekewa ta yi da wata shakiyar dariya kafin ta yi saurin rufe bakin tana dan leke leke dan kar wani ya ji ta,inna ta ko ke ba zaki san ko mai akan wannan Labarin ba,a wannan karon yakin na murja ne ita kadai,a wannan lokacin boyayyan halin murja zai yi amfani,a wannan lokacin ko mai zai bayyana zan tayar da tsohuwar ajiya domin samun nasarar rayuwata....................✍🏽


[12/21, 12:40]: *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




Page28

Washe gari Raihan ta fito cikin shirinta na zuwa office,yau jin ta take kamar wata sabuwar mutum ,fuskarta cike da walwala ta nufi gurin abbien ta dake zaune saman dinning shida su aunty amarya harma da hamma idi da ya dawo daga tafiya yau da safen,Barka da safiya ta yi musu tare da ba su sumba kamar yadda ta saba,Hamma idi ya ce",Rahim anya kuwa bata samu ba?cikin sassanyan murmushinta ta dube shi kana ta ce"hamma idi ka dawo lfy gidan duk babu dadi kwana biyu da baka nan",ta faɗa tana dan spin ruwan Lipton da aunty amarya ta mika mata, murmushi ya yi yana miƙewa ya ce a'a kanina ban da dadin baki kai dai ko ka samu wani abun dadin ne kawai kake cikin nishadi",dariya ta kuma yi har kumatunta na lobawa,matsawa ta yi dinnin ta ajiye cop din sannan ta juyo tana cewa Hamma bari na wuce idan na dawo ma yi magana ta faɗa tana kallon a gogon diamond dake sakale a hannun ta,shima miƙewa ya yi ya ce",ok muje sai na sauke ka nima hanyar gidan na ku zanyi,sallama su kayi da su Abbie suka fita a tare.




Sai da ya sauke Raihan ya ga shigar ta sannan ya juya ya tafi.




RUBYY..............




Cikin fargaba ruby ta tura kofar dakinnasa ta shiga,dai dai lokacin da ya fito daga wanka jikinsa sanye cikin rigar wanka wanda ta tsaya iya gwiwarsa,tsayawa ta yi tana kallonsa ba tare da ta iya koda yi masa magana ba bare kuma magana akan batun da ya kawo ta,bai kalli inda take ba,a haka har ya gama shirinsa tsaf kai kace wani dawisu ne saboda kyawu da cikar kamala,sakaro ta yi da hanci da baki tana kallon tsagwaran kyau da kwarjini sai tsananin kamewa da take halittarsa,sai da ta ji ƙamshin sa da alamun takun sa me cike da nutsuwa sannan ta farga ,cikin in inar baki ta iya furta ina kwana Hamma AHMAD",lafiya ya fada yana mai cigaba da takawa cikin yanayinsa na gozago,bin bayanshi tashiga yi kamar wata escort dinshi,bata iya yi masa magana ba tana gani ya fice daga falon ba tare da ko kallo ta ishe shi ba bare ya tambaye ta dalilin bin nashi da take yi.




Yana fita ta zube a gurin tare da sakin kuka me tafe da zallar nadama,sai da ta yi mai isar ta sannan ta rarrafa ta shige dakinta,ta janyo wayarta ta saka kiran suryy,bugu daya kuwa ta daga, kuka kawai ruby ta saka mata tana cewa suryy ki taimaka kizo aure na da birina na zama har abada a zuciyar wazir yana neman rushewa,da sauri suryy ta katse ta da cewa yi shiru gani nan zuwa baki da damuwa in dai ina numfashi.




CHIBADO FM.........




Kusan a tare suka isa gidan,duk da cewa shi ya tsaya ta gidan su Raihan din masu gadi suka tabbatar masa da cewa ko minti biyu ba su cika da fita ita da Hamma idi ba.


Hannu su kayi shi da hamma idi kafin hamma idi ya mu su sallama ya fice daga building din.ko kallon shi ba tayi ba ta fara takawa dan tafiya office dinta,da Wani irin kallo ya bita kai kace zai cinye ta ne,cikin takunshin nan me cike da ginshira ya bi bayanta yana mai ci gaba da kalleta tamkar zai hadiye ta,duk da kuwa babu wanda zai ce ya ma san da ita a gabannasa bare a shaida kallon kurilla da yake mata.tana gab da shigewa bangaren su ta ji kamammiyar Muryarsa yana cewa nan da awa biyu kizo office,tana jinshi amma sai ta yi kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login