Showing 171001 words to 174000 words out of 189984 words

Chapter 58 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15615

gajiya RAIHAN ta faɗa tana rufe Tata computer, Allah yayi muku albarka amma dan Allah kar ku tsaya shiririta ku fito da wuri,in sha Allah Abbu wazer ya fada yana rufe kofar falon bayan fitar Abbu.


Yana zuwa ya dauke ta cak yana cewa kema ina da tarin tambayoyin da nake so ki amsa min na daga mikii kafa amma shine ɗan Kinga Abbu har zakulo min tambaya kike ko? Ya karasa fada tare da kwantar da ita saman kyakkyawan gadon da ya sha shimfidar alfarma.......✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page64 ```




.....Shima bin gefanta ya yi ya kwanta tare da janyota jikinshi,kafin cikin yanayinsa wanda ke cike da nutsuwa wanda har a kalaminsa take bayyana ya ce ", fada min ya akayi kika yi duk wannan ban sani ba? Kara mannewa ta yi a jikinshi tana shaƙar kamshinsa da bata gajiya dashi,sannan cikin kwantar da murya wanda ke fitowa da wani sanyin jiki da hakan ya kashewa wazer nasa jikin ta ce", lokacin da wannan kashe kashen ya fara faruwa ya faru ne tun bayan karbar kujerar da HIS EXCELLENCY yayi ne,hakan yasa nafi dora zargina akansa kamar yadda sauran jama'ar gari suke,ko lokacin da muka je wajensa tare sai da nayi wasu yan bincike ba tare da kai ka kula ba dan har muryarsa saida na dauka,tun daga wannan lokacin Ni kuma na dage akan lallai sai na samo wanda yake da hannu akan wannan matsalar da jahar mu take ciki,hakan yasa na shiga bincike ka in da na in har na samu na fara bibiyar mutumin da ban san ko shi waye ba,a hankali a hankali ina biye dashi har na fara samun bayanai masu muhimmanci akansa,kamar yaransa da yake sawa suna hada tarzoma a gari dan kawai a zubda jini da kuma mu amalarsa da matsafa a haka har na samu na tara vidoos da muryoyi masu dama, saida na tabbatar da cewa na hada hujjoji masu ma ana, sanan na tunkari haidar wanda nake da yakinin zai taimaka min a matsayinsa na jami'i me kishin kasarsa,abinda yasa ban sanarda kai ba a lokacin shine ganin yadda kake hanani irin wannan shige_shigen masu hadari,karshe dai ranar da haidar yazo na bashi Flash din da kuma na su shugaban jam'iyya washe gari aka saceshi,shi yasa kaga hankalina ya tashi ga kuma matsalar Khalil duk a cikin ranar,na tsorata da sace haidar matuka duk da cewa hasashena ya bani cewa sun jima suna bibiyarsa."




A hankali ta ɗan sauke numfashi tana jin wani irin daci a makoshinta.




Hannunsa ya dora akan lallausar sumar kanta yana mata tafiyar tsutsa, sannan a hankali ya bude baki ya ce", ya a kayi Flash din yazo cikin kayana? Itama ɗan jim ta yi kafin ta dago kanta ta kalli fuskarshi dake wani irin sheki na tsabar Hutu da jin dadi dan jan gemunshi ta yi tana cewa wannan amsar a wajen haidar za mu sameta dan Nima ban sani ba", kuma ka tashi mu tafi ka maida Ni gida kasan Abbu ya ce", kar mu tsaya shiririta mu tafi gida kafin sha biyu",




Yadda yake kallon bakinta ne yasa ta yi saurin rufe bakinta tana dan ƙunkuni akan mayen kallon da yake mata ko a gaban waye kuwa.




Uhm ina jinki", ya fada yana juyo da fuskarta da takawar gefe,cike da kuruciya ta bude bakin zata yi magana aiko caraf wazer dan Ammi ya cafe harshenta cikin bakinshi ya shiga juya shi yana binta da kallon har hanji,rufe idanunta ta yi tana jin wani irin yam tsigar jikinta na mikewa,samun kanta tayi da rike shi kam saboda ji ta yi kamar zata yi luxing temper nata,kai wazer karshe ne a fagen so da nuna so wadda bata samu soyayyar wazer ba tabbas bata samu soyayya ba,ita kadai take wannan surutun a ranta,sai da ya yi me isarsa ya gama cakudata sannan ya dauke ta cak ya yi toilet da ita.




Saurin rike rigarta da ya yi zipin dinta zata yi kasa ta yi,tana marairaice fuska tare da kankame jikinta,




Kallon ido cikin ido ya yi mata kafin cikin deep voice dinsa ya ce", me ne hakan? Ko bai da ce ba? Tura bakinta ta yi tana kara kankance idanunta tare da kif_kifta su kamar wata mara gaskiya,shi dariya ma ta bashi hakan ya sa shi ɗan murmusawa,zaro manyan idanunta ta yi tana cewa kai hamma wazer kaga yadda ka koma kuwa? Me na koma ya fada cikin sauraron jin serious zance amma sai ya ji ta ce", kyau mana murmushi yana maka kyau sosai ko dan baka fiye yinsa ba ne,dan Allah Ni dai hamma wazer kana yi min wannan murmushin ko da yaushe kaji", wani murmushinne wanda yafi wancan fadi ya kuma subce masa aiko Raihan bata san sanda ta saki rigar da ta ke rike da ita Katamau ba, tare da yin wani dan tsalle irin wanda yara suke idan a kayi musu abinda suka ji dadinshi, wannan ne ya bawa Wazer damar sakar musu shaya akansu a lokaci daya yana daukar shawa jel me azabar kamshi da tsada ya zuba a hannunsa ya soma gogawa ajikinta,take bakinta ya mutu mut, yanzu kam babu halin magana dan aikin gama ya gama.




Sosai wazer ya wanke Raihan dinshi tas,kafin ya zaunar da ita a kan kujerar bath ya shiga kokarin cire boxer din dake jikinshi,bata dakatar dashi ba tsayawa ta yi kallon gudun ruwanshi dan a tsammaninta ba cirewa zaiyi ba tsokanarta zaiyi,wani dan ihu ta saka tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta guda biyu jikiinta na wani irin bari dan kuwa sosai ta razana da ganin bazata da ta yiwa hamma dinnata, tsayawa ya yi da abinda yake yi yana kallon zallar haukan kuruciya gurin matartasa a ransa yake ji dama ya yi abinda ya yi niya a jiya da tuni ya yi maganin wannan sakarcin nata,bai ko kalli inda take ba ya shige cikin bathwash yana tunanin abinda ya kamata ya yi dan yin maganinta.




Shirun da taji ne yasa ta ɗan zame hannunta tare da kyalla ido guda dan ganin ko ya maida boxer dinsa,ai ko gwammacewa ta yi bata bude idon ba dan ko ta yi mugun gani a fadarta amma,kuka ta saka masa akan ya bude mata kofa ta fita ita ba zata iya wannan rashin ta idonba,kai ko kunya baka ji zaka cire kaya a gabana kai hamma wazer dama haka kake ana kallonka sumi_sumi", bude idanunshi da suke a lumshe ya yi kafin cikin wani irin zafin nama ya fizgota ta fado cikin ruwan da yake a lokaci daya yana hadeta da jikinshi,bude baki ta yi zata yi masa kwakwazo take kuwa ya hade bakin da nashi ta yadda babu wani harafi da zai samu damar fitowa daga matsiwacin bakinnata, Raihan bata san cewa muguntar wazer ta shahara ba sai da ta ji ya damƙi hannunta ya dora akan mararshi da ke wani irin harbawa da sauri da sauri, Raihan kam shidewa ne kawai bata yi ba amma Allah ya saka mata ta yi yafi sau shurin masaki,rantsuwa kuwa akan bazata kuma biyoshi gidannan ba ta yi babu adadi idanunta sunyi ja saboda kukan tsoro da tashin hankalin ganin abinda bata taba gani ba a rayuwarta,sai da ya mula dan kansa ya kuma tabbatar ta yi laushi sannan ya daurayesu ya daura towel itama ya daura mata suka fito yana kunshe dariyar dake ta cinshi a ranshi.




Aje ta yayi ya gama shiryawa sannan itama ya shiryata ya sa mata kaya,duk tana jinshi ta kasa haɗa ido dashi bare ta tanka masa,dubanta ya yi lokacin da ya ganta tsaf cikin doguwar rigar leshin da yake ta ajiyarsu a gidan duk saboda ita,dan kanne idonsa ya yi tare da rissinawa a gabanta ya ce", tuba nake matar wazer,banza ta yi da shi saima ƙwallah da suka kuma cika idanun, da sauri ya mike yana cewa haba tawan ki yi hakuri da duk wannan alwashin da kike dauka da rigimar nan sai ranar, dan idan suka kare baki da nayi wannan ranar me zuwa,saboda haushi da kunya ko tambayarshi wace rana yake magana bata yi ba ta fita fuuu daga dakin tana cewa nayi gaba sai ka taho", dariya yayi wadda bai taba yin irintaba kafin ya bi bayanta yana aiyanawa a ransa idan suka tare RAIHAN wace irin dariya zata dinga saka shi,tabbas ke ce farincikina ya fada yana zama a kujerar dereba,a kunnenta wannan tsadaddiyar kalma ta sauka hakan yasa ta ji duk wata fushi da damuwarta sun kwaranye sai wani irin so me sanyi da kauna me sanyi saboda samun abinda kake so a kusa da kai,da wannan shaukin suka bar gidan.






RABY.. SURRY......






A safiyar yau da Surry ke tsammanin daurin aurenta da mutumin da ko sunanshi bata sani ba ne, aka tashi da wannan hatsaniya, yayin da a bangarenta take jin kamar an sauke mata wani kaya, ji take yi a jiya kamar ba ita ba,sai kuma gashi yau din abinda ke jikiinta ya sake ta,ey tabbas ta san cewa jiya ba kalau take ba,take duk bojet dinta suka dawo ta dawo cikin walwalarta da lissafin mallakar wazer mijin aminiyarta, waya ta kuma dauka dan kiran oganta wanda a safiyar zuwa yanzu ta kira yafi sau ashirin amma wayar akashe,ke Surry anya ko wannan mutumin ba yaudararki ya yi ba kamar yadda kike yaudarar kawarki? Zuciyarta ce ta yi mata wannan tambayar aiko take ta dura wani uban Ashar da yayi sanadiyar dakatar da rabi a dake shirin shiga dakin,abinda ya biyo saura daga bakin suryy ne ya tsaida duka ruwan jikin rabia .




Wallahi ko da yayi nadama mara amfani,ai Ni babu wanda ya isa ya yaudareni saboda Ni ba sakarya ce kamar rabia ba,ko rabi a idan tayi wani abun haushinta nake ji,to wai me yasa wasu suke kamar galahanga ne gurin sakarci?kai gaskiya na sha da rabi a wato ita nan saboda sakarci sakin baki ta yi na kawo mata mafita ko? To zata ga mafita kuwa , wallahi sai ta yi da ta sanin wannan sakarci da ta yi,dadinta ma babu abinda nayi masa bayan tozarcin da aka yiwa Raihan,Ni kuma yanzu da kaina zanyiwa kaina maganin rabi a da RAIHAN,saboda sune matsalata kai ko da su in dai har wazer zai aureni bani da wata damuwa,dariya ta sheke da ita tare da buga cinya tana cewa da nice rabi a bin Raihan zanyi sau da kafa dan na kama kafa da ita na zauna da mijina lafiya amma dake sakarya ce tayi watsi da a binda ya kamata tabi shawarata,gaskiya rabi a mahaukaciya ce"...... Gaki nan babbar mahaukaciya maha'inciya maci amana", rabi a ta faɗa tana shigowa cikin dakin idanunta na zubar da hawayen bakinciki da nadama,gaskiya ne da ake cewa kayi abota da mutumin kirki aiyukanka zasu gyaru,da ace nayi dace da kawa ta gari tabbas ba zan aikata kuskuren da na aikata ba,Surry kije na barki da Allah idan har zaluntata kika yi zaki gani",, daga haka ta fita daga gidan tana sharbar kuka kamar ance da ita iyayenta sun mutu.




Ita ko sury wani uban tsaki taja tana cewa baki ga komai ba rabi a sai ranar da kika ganni matsayin matar tsohon mijinki dan nasan lokacin tuni ya jima da baki red card,hada kayanta ta yi ta dauki jakarta tana kuma duba adireshin wajen bokan da aka bata,fita ta yi ba tare da ko sallama ta yiwa mahaifiyarta ba,ita dama mahaifiyarta ta saba shi yasa ko ajikinta ta cigaba da sabgoginta a ranta tana cewa surayya da ke kadai na haifa da tuni kin kasheni.




Muhammad nur House....


Lokacin da Aunty Amarya ta shiga falon bakinta dauke da sallama babu kowa,hakan ya bata damar wucewa dakinta kai tsaye,turus ta yi ganin Abbie kwance ya rungume wata rigar baccinta idanunsa a rufe,hawaye ta ji sun fara zubo mata saboda tsananin tausayin kansu,wai shin wace irin rayuwa muke yi a yau? Me yasa san zuciya da rashin adalci su kayi mana yawa? Shin ina zamu kai kudi ko zamu tafi dasu lahira ne? Anya ko mutane suna tunawa da mutuwa bare kuma hisabi? Jin wata irin runguma da kayi mata ne ya tsinke mata tunaninta,ba tayi wata_wata ba itama ta rungumeshi suka hadu suna kukan farinciki da bakincikin abinda ya samu zuriarsu dan ko ba komai Abba Yahya jininsu ne.




Wazer bai tsaya a ko ina ba sai cikin gidansu Raihan inda suka samu duka jama'ar gidan suna jajantawa junansu,sai alokacinne wazer ya bayyana musu wanda ya yi garkuwa da mami da ma duk abinda ya aikata a baya,akan son samun dukiyar Raihan,sosai suka shiga shock da wannan labari,mama murja kuwa sumewa ta yi saboda tsananin razana dan ko a mafarki bata taɓa kawo Idris dinta cikin masu son dukiyar Raihan ba saboda yadda ya nuna musu rashin goyan baya lokacin da suke kan ganiyar son zuciyarsu,ga kuma yadda ya dinga nunawa RAIHAN da Aunty Amarya soyayya kai gaskiya mutum mugun icce ne,cewar hajiyar agadex tana kuma jinjina lamarin dan ko ita ta girgiza.




Baffa Ali kuwa sai da zazzaɓi me zafi ya kamashi jin abinda Abba yahya ya aikata,ba karamar girgiza ya yi ba,dan har ya fi Hajiya goggo shiga damuwa,dan ita cewa ta yi wallahi ta yafe shi kuma ita bata da wata damuwa tunda tana da kamar Muhammad nur,uwa ke nan tsabar ɓacin raine yasa ta fadin wannan kalaman amma tabbas can kasan zuciyarta Allah ka dai yasan irin damuwar da take ciki.



Momy Hanne kuwa hamdala ta dinga yi da bata samu damar cutarwa ga kowa daga cikinsu ba,tabbas sunyi nadama tuba irin wanda ake so,babu komai a zuciyarsu sai tsananin tsoran Allah da gujewa duniya yanzu kowa fatanshi ya samu ya cika da imani.


________




Sha biyu daidai videon bannar da Abba yahya ya dinga shukawa ya fara trending a ƙafafan labarai da social media,kafin kace me gari ya dauka kowa da irin abinda yake tofawa, HIS EXCELLENCY kuwa tuni ya tsufa a gida cikin iyalanshi,yan jarida babu abinda suke son ji daga bakin HIS EXCELLENCY sai yadda a kayi Abbie yaso mutuwa a hannunsa da yadda gubar tazo gidan har cikin abincin his excellency wanda Abbie yaci kuma shi baici ba", wannan tambayoyi ne da mutane suke buƙatar jin amsarsu daga ciki har da ahlin nan guda biyu.




Alhamdulillah haidar ya farfaɗo da taimakon Allah da na Dr Sabo,takanas Abbie yasa aka je aka ɗauko masa yan uwansa da matarsa da dansa harda mahaifiyarsa,kai kana ganin murnar da suke kasan cewa suna matukar son haidar ɗin.


Jama ar gari fa sun gama shan alwashin Abba yahya a hannundu zai mutu dan wallahi sai sun dauki fansar jinin yan uwansu dan haka su kayi mummunan shiri akan kisansa,dan baza su taba bari akaishi kotu ba dan basu da tabbacin za a iya zartar da hukunci bisa adalci,karshe dai ayanke masa hukuncin son zuciya wanda ba zai musu dadi ba.........✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page65 ```


Duk abinda ke faruwa BASHIR yana cikin gidan kuma ya ga komai sarai,amma tsananin tashin hankali da kunya ya hanashi fitowa,tuni wannan tashin hankalin yasa shi mantawa da wata suryy da aurenta,yadda zaiyi ya fidda mahaifansa su gudu kawai yake tunani,to ta yaya inna maimuna tana hannun yan sanda ABBAN kuwa babu wanda zaice ga inda yake dan har yanzu hajiyar agadex bata ce musu ga inda yake ba.




A bangaren rabi a kuwa gidan innawuro ta nufa kai tsaye tana ruwan hawaye,ko kallo bata ishi innawuro ba,bare ta tanka mata,hakan yasa dole da taga uwar naki ta magantu ta hanyar tsuguno a gaban innawuro tana faman bata hakuri akan abinda ya faru", wani kallo innawuro ta watsa mata kafin ta ce", duniya ta koya miki hankaline ke da ubanki shine kika zo bada hakuri? To maza ki tashi ki bani guri ba zan karbeki ba har sai ubanki da ya tafi dake ya tako gidannan rike da hannun ki ya ce min ya dawo dake tare da bada hakuri ga wadanda ya batawa,dan haka fita ki bani guri", innawuro ta faɗa cikin tsawar da ta razana rabia ta mike ba tare da ta shirya ba,da harara innawuro ta raka ta tana jin takaicinsu ita da mahaifinta,ai ko dan ta kona musu rai kamar yadda su kayi mata dole ta yadda da wannan yarinyar Raihan a matsayin matar wazer,ana gama wannan hatsaniyar wani satin zata basu dama su kawo ta kowa ya huta.






Suryy tun tana ganin tafiyar me karewa ce har ta sare ta fara gajiya,duk tayi wani figai figai da ita abinka da ba a saba ba,tana shirin cewa a sauketa ta shiga motar komawa gida sai taji ana kiran sunan garin wanda hakan ke nuna cewa sun iso,hamdala ta yi ta sauka ta kuma hawa dan acaba dan shiga da ita cikin ainahin kauyen da bokan yake", nan ma wata tafiya ce mikakka wadda Surry ta fara danasanin zuwa.




Bayan share doguwar tafiya suka karaso gurin sa arta daya babu layi hakan yasa ta shiga kai tsaye bayan an yi mata iso,kafin ta yi magana bokan ya katse numfashinta ta hanyar sanar da ita abinda ke tafe da ita, wannan abu ba karamin burgeta ya yi ba,take ta ji duk gajiyar da ta kwaso ta gushe,ya tabbata zai yi mata aiki amma shi ladan aikinsa ba kudi ba ne,to me Nene? Ta tambaya cikin jin kwarin gwiwa akan kome nene zata yi in dai bukatarta zata biya,gyara zamanshi ya yi tare da cewa ladan aikinmu shine za mu mu'amalantu da baiwarki ta 'yaa mace kuma muddin mace ta shigo gurinnan dole sai ta amince damu idan ba haka ba zata fita cikin hauka tuburan babu ita babu gida sai bin bola,"dafe kirjinta ta yi tana kwalalo ido waje bakinta har rawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login