Showing 33001 words to 36000 words out of 189984 words
Chapter 12 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
jininta ya ƙaru da ƙyar ta daidaita kanta ,ta ce" Banyi ba amma ina shirin yi"to ki kashe wayar ki kwanta"marairaice murya ta kuma yi wanda hakan ya bata wani amo me ratsa jijiyar jiki ,rintse idanun shi ya yi ba tare da yasan ya yi hakan ba,bai kuma san ma anar yin hakan ba,dan Allah ka barni wani sako zan duba kawai na kashe"kokawa ya fara yi da numfashin sa,ita kuma jin ya yi shiru yasa cikin wata irin shagwaba da ta riga ta ratsa jinin ta ,ta kuma cewa dan Allah fa dan Allah Hamma wazirrrrrr"wata yar ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki tare da sakin numfashinsa , sannan a hankali ya ce",wane irin sako zaki duba? Samun kanta ta yi da kasa fada masa gaskiyar cewa sakon kamar ya danganci halima ne,sai kawai ta ce"wani fans dina ne yake min ta aziya shine zan duba"ji ya yi kawai kirjin shi ya yi wani irin nauyi iskar shaka tana kokarin yi masa wuya,cikin son ƁOYE abin da yake ji ya ce"ok ki duba sai ki kashe kin san sammakon fita za mu yi,dan ya kamata ke da har yau ba kije ta aziya ba kije da wuri ,saboda kar hakan ya jawo hankalin mutane har su fassara hakan da wata manufa"shike nan insha Allah zan yi yadda ka ce" yana kokarin kashe wayar ta yi saurin dakatar da shi,da wani abu? ya fada a takaice, Hamma wazir jin ka nayi kamar ba a daidai ba,ji nayi ajikina akwai damuwa a tare da kai bayan wadda muka shiga ta rashin Halima da sauran abin da ya faru a tsukin nan?mamaki ne ya kama wazir chibado ya a ka yi Raihan ta fuskanci yaji damuwa akan ta? Duk da ya kasance me tsananin taka tsantsan da ƁOYE damuwar shi akan komai ,ta yadda mutane ba su taba fuskantar ta, Hamma wazir" ta faɗa cikin wata kasalalliyar Muryar da bata san ta yi ta ba,idan kowa zai kasa gane damuwarka ko walwalarka to kasa a ranka banda RAIHAN,ka kuma sa a ranka duk abin da kake yi da halin da kake ciki Raihan zata sani ta hanyar ji a jikinta da zuciyarta" daga haka ƙit ta kashe wayar tare da danne damuwar wazir.
Shuru ya yi tare da zubawa wayar idanu tamkar zai ga Raihan din ta cikin wayar,sai kawai ya samu kanshi da fitar da wani tattausan murmushi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciya.
Bata saurari sakon kowa ba kai tsaye ta tafi ga sakon da yaja hankalin ta tun farko,wato sakon Halima.
Wani irin bugu kirjin ta ya yi a yayin da ta ci karo da abinda Halima ta turo mata.
Rahim duk yadda za ayi idan ƙurar mutuwata ta lafa kazo address ɗin nan ka duba wata alama a dai dai jikin bishiyar magarya ta baya a nan na ajiye camarar ,kuma duk abinda kuke so ku sani yana ciki,suna so su danganta abinda suke aikatawa da Gwamna wanda Ni kaji hakan da kunnena,dan haka ka kiyaye ko da zaka ji wata magana akan gwamna game da kisan da ake yi ,to ba haka ba ne sharri suke son yi masa,kai ka dai zan iya bawa wannan amanar, ina rokon Allah ya bar rayuwarka domin ceton al ummar da suke cikin tashin hankalin mugayen shugabanni,Rahim dan Allah kar ka dauki camarar nan yanzu sai bayan wani lokaci saboda kaima nasan zasu iya kashe ka idan suka gano camarar na hannun ka,amma zan gaya maka sunayensu koda baka samu damar dauko camarar ba domin ka sake yin sabon bincike akan su, Alhaji s......wayyo ga su nan sun biyo NI Rahim suna gab da cimma Ni,amma ka binciki D......a daidai nan sakon ya katse,,,,
A rude RAIHAN take cewa su waye Halima karasa baki karasa min sunan S ba kika dauko min D me s take nufi me D take nufi? Innalillahiwa'inna ilaihi raji'un take fada kai ka ce waya suke da Haliman a lokacin ,duk tambayoyin da take kai kace Haliman zata amsa mata su ne a lokacin,
Zubewa ta yi saman gadon kamar wadda babu laka a jikinta,kuka take son ta yi amma ji take kukan ma ya kasa fitowa ,wani irin zafi kirjin ta ke yi kamar ana gasa gurasa,cikin jan ajiyar zuciya ta fizgo kukan da wani irin ƙarfi,kuka ta yi sosai na ciwon mutuwar Halima da kuma rashin Makama akan takamaiman abin da Haliman take nufi da S da D,zabura ta yi tare da kara wawuro wayar ,sake duba address ɗin ta yi ,sai a lokacin ta dan samu nutsuwa tunda tana da tabbacin cewa ma anar S da D suna cikin camara.
Har wajen karfe biyu Raihan bata yi bacci ba,tana nan ko kwanciyar ta kasa yi bare idan ta kwanta baccin ya saɗado ya dauke ta. kamar daga sama taji sassanyan ringing din wayarta,ba karamin mamaki ne ya rufe ta ba ,ganin me kiran, cikin sanyin da jikinta ya gama yi ta daga kiran tare da karawa wayar a kunnen ta,a hankali ya dan furzar da wani zazzafan huci daga bakinsa, tare da kara lumshe idanun da suke cike da gajiya da tarin damuwa,murya can kasa kamar me yin mura ya ce"RAIHANNN yadda yaja sunan cike da kasalar gajiyar dake tare da shi ya haifar mata da wani irin jin sanyi me ratsa kasusuwan jiki da bargo,bata san sanda ta fara rawar ɗari ba,dan kuwa tabbas Muryar WAZIR ta haifar mata da zazzabin farat daya,baki bacci ba? Ya tambaye ta cikin ƁOYE mamakin rashin jin batayi baccin ba"umm ta ce ba tare da ta bude baki ta yi magana ba,me yasa? Ya kuma tambayarta"kai me yasa ba kayi baccin ba Hamma wazirrrrrr? Ta maida masa da tambayar itama cikin dan mamakin kiranta da ya yi a daidai wannan lokacin,rufe idanun shi ya yi yana kokarin nemo dalilin domin ya bata amsa tun da shima yana so ta bashi amsar abin da ya hana ta baccin,to amma me zai ce mata? Gaskiyar maganar bata da wani ma'ana bare ya fadeta,to rashin ma'ana mana,idan ba rashin ma'ana ba ta yaya zai ce ya kasa bacci ne saboda yaji a jikinsa ba tayi bacci ba dalilin damuwarta da yake ji a can cikin ƙasan zuciyarsa, Hamma wazirrrrrr "ta kira sunan shi jin ya yi shiru"cikin dakiyarshi dake nunawa a zahirinshi ya ce"naji kamar wani abu yana faruwa bayan mun gama waya "shine ya hana ka bacci? Ta tambaya tana mai son boye mamakin ta da kuma damuwar da bata son ta fallasa har Wazir ya san da ita ya kuma tambayeta ba'asi,zazzafan huci ya fesar tare da ƙara gyara kwanciyar shi kana ya ce" ina ga haka ne"ke fa me ya hana ki bacci Raihan?cikin yanayin ta na shagwaba ta langabar da kai kamar yana gaban ta ta ce"Hamma wazirrrrrr babu komai kawai ina tunanin yadda zan ci gaba da tafiyar da rayuwata a haka ne bayan kuma ina jin cewa Ubangiji babbar baiwa da Ni ima ya yi min na kasancewata mace kuma musulma" duk da ya ji cewar kamar ta ɓoye masa wani abu bayan wannan,sai ya yi kokarin kwantar mata da hankali,rufe idanun ta tayi tana jin cewar kamar bata da matsala idan Hamma wazirrrrrr yana kusa da ita kuma yana tare da ita,haka nan ta ji ta samu nutsuwa akan yanayin ta na baya.
RAIHAN ki nutsu ki yi bacci kinji"ya fada cikin lallashi da tausasa murya,to kaima za kayi? Ta faɗa a sangarce,lumshe idanun ya yi kafin ya bude, sannan ya ce" ba kince kina jin komai nawa a jikin ki da zuciyar ba? Ey mana ta faɗa da sauri kuma cikin tabbatarwa,yauwa to idan na yi bacci gobe za ki gaya min Nima idan kin yi zan gaya miki,duk wanda ya fada ba daidai ba to abin da ya fada na cewa muna tare da juna a cikin ko wane yanayi ba haka bane"cikin farinci ta ce"na yadda"ok to Allah ya tashe mu lafiya"ta amsa suna mai kashe wayar a tare,jin motsin antyy amarya yasa ta yi saurin kashe wayar ta rufe kanta tare da rufe idanunta ,saboda da gaske ta ji tana son ta yi baccin ko dan Hamma wazirrrrrr.
Sai da aunty amarya ta zo ta bude ta ta tabbatar da lafiya sannan ta fita daga dakin,bayan ta kuma tofa mata addu'a (Ubangiji Allah ya sakawa iyayen mu da alkhairi Allah ya sa su gama da duniya lafiya,wadan da suka mutu Ubangiji ya yi musu rahama).
Wazir ma dai ya samu ya yi baccin ,dan har sai da ya dan makara zuwa Sallah.
Ita kuwa RAIHAN Saida aunty amarya ta shigo ta tayar da ita saboda yadda babu zato bacci me nauyi ya sureta,ko da ta tashi cikin sauri ta shirya ta fito falo su ka karya,itama antyy amarya a shirye take ,amma ba tare zasu tafi ba,ita za su tafi tare da goggo Rahma da jiddo, da kuma inna maimuna, Raihan ta dubi aunty amarya lokacin da take miƙewa daga saman dininng ta ce"wai aunty sun je kuwa? girgiza kai aunty amarya ta yi tare da dan haɗe fuska sannan ta ce" ba su je ba kuma bana tunanin zasu je" daga haka itama ta mike ta wuce bedroom dinta Dan dauko mayafi da jaka.taɓe baki Raihan ta yi tana mai gyara ƙatuwar jaket din da ke jikinta ,ta wuce daki ita zata dauko wayarta tana mai ɗan gyagygyara shigar ta wadda ta rufe kyakkyawar surarta ta me shirin zama cikakkiyar budurwa.
Tsaf ya fito cikin shigar manyan kaya wanda su kayi masa matukar kyau ko dan bai cika saka su ba ne oho,hakan sai ya kara fiddo da kamalar sa dake nuna tsananin nutsuwar da yake da ita,tuni rabi a ta saki baki da hanci tana kallon tsayayyan namiji me cike da baiwa daban daban, innawuro dake saɓa mayafi ta dube shi tare da cewa ,kai irin wannan shiga kamar me shirin zuwa daurin aure ,anya kuwa mutanen nan ba za su ji haushin ka ba?tsalaf rabi'ta saka baki da cewa ke kuwa innawuro kin san cewa duk kayan da hamma wazir ya saka sai sun fidda kyawun shi da kwarjinin shi,dan haka ma ko ya canja sai ma dai kiga ya fi da yin kyau"innawuro ta ce"hakane maganar ki rabi,sai ka wuce muje"duban ta ya yi cikin haɗe fuska ya ce"ba tare zamu tafi ba"to saboda me"innawuro ta faɗa a harzuke,saboda zan biya wani wajen kafin na karasa can gidan addu'ar"to da wa za mu tafi? Da su Abbu zaku tafi na gaya masa"to shike nan amma ka tafi da rabi dan mota daya ba zata ishe mu ba"innawuro ta faɗa cike da kumbura fuska dan karma ya Musa mata,to ko bata yi hakan ba ma dama baiyi niyar magantuwa ba dan ya gaji da maganar,hakan yasa ya wuce cikin sassarfar takun shi me matukar birgewa,sosai Rabi'ah ta ji dadin abin da innawuro ta yi ,dan haka cikin sauri ta bi bayan shi dan ta san yana iya fecewa ya barta.
A can wajen su Raihan kuwa tuni ta fito harabar gidan tana jiran wazir ,saboda antyy amarya ma da goggo Rahma sun fito,har zasu ta fi sai goggo ta dubi jiddo ta ce"ke ki tsaya Rahim kun taho tare dan kar a barshi ya yi jira shi kaɗai,da sauri Raihan ta dubi goggo ta ce"Ni zan iya jira abin da gidan da mutane ga yan aiki da masu gadi"goggo ta ce"a'a ta dai tsaya ku tafi tafiyar ta fi muku daɗi " jiddo ta ce" shike nan goggo sai mun taho ɗin"to sai kun taho"goggo ta fada tare da shigewa motar da har antyy amarya ta tayar da ita.har suka fita idanun Raihan akan motar yake ,ji ta yi ranta ya ɓaci da wannan shishshigi na goggo,ita kuwa jiddo murmushi ta yi tare da cewa Allah na gode maka yau zan zauna gani ga wazir abin da na dade ina son yi ban samu dama ba" ta karasa maganar tana kunshe bakin ta saboda dariyar hararar da Raihan ke ta zuba mata,ta sani sarai Rahim baya son hada ta da wazir tun da tasha nuna mata tana son raka ta aiki amma sai ta kufcewa hakan,ita dai jiddo bata kawo komai a ranta ba tun da ganin ta babu abin da zai sa namiji ya yi kishin namiji in dai ba akan wata harkar banza ba,wanda kuma ta yi yakinin cewa ko a mafarki ba zata saka Rahim a wannan jerin ba.
A cikin hakane me gadi ya wangale katon gate din gidan nasu, kyakkyawar mota baka me tsananin kyau da sheƙi ta shigo farfajiyar gidan,duk da bata taba ganin shi da wannan motar ba amma ta ji a jikinta Wazir ne,ko da yake ita har yanzu bata gama tantance yawan motocin sa ba,har gaban su ya zo ya yi parking, cikin kamewarshi da gizagon dake ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa ya zuro kansa tare da zuba mata narkakkun idanun sa wanda kullum suke kamar na me jin bacci, Rabi'ah dake gefan sa sakin baki ta yi tana kallon sa,ban da kara birgeta da ya yi har da tsagwaran mamakin ganin yadda lokaci guda duk cin maganin da suka taho yana yi mata ya gushe ya maida gurbinsa da nutsutstsan murmushi mai matukar wahalar samuwa gare su da duk wani da ya yi masa farin sani.
Ba sai ka fito ba bandirawo wazirrrrrr mu wuce kawai,ta faɗa tana zagawa bangaren daman sa wato kujerar me zaman banza,da sauri jiddo ta wuce ta bude gidan baya ta Wada dan kar ma tsautsayi yasa a fasa tafiyar da ita damar da take nema ta kufce mata.
Wani irin jan burki RAIHAN ta yi ganin Rabi'ah zaune a gidan gaban bata da alamar motsawa,duk da cewa tun tahowar su wazir ya umarce ta da idan sun zo zata koma sit din baya,kafin kace me idanun RAIHAN sun ciko da kwallar da batayi mata wahala,cikin kosawa da lamarin Rabi'ah ya ce"fita "da sauri ta dube shi kafin ta ce"amma ina ga Ni ce ya da ce"na zauna kusa da kai tun da ina matsayin yar uwar ka kuma matar da zaka aura ko?"tamkar walkiya haka suka ga Raihan ta bar wajen da wani irin fasifar gudu,ya yin da take jin duniyar na wani irin juya mata tamkar fanka,cikin ɓacin ran da ya kasa ɓoyuwa a ran shi kamar yadda ya saba ya ce"me kika yi hakan? Cikin mamaki ita ma rabi a ta maida masa tambaya da cewa me nayi kuwa ai Ni ban ga abin jin haushi a kalamai na ba? Jiddo ta yi tsalam ta ce" ke ce baki ga abin bacin ran ba ,tun da baki san matsayin Rahim a wajen wazir ba kuma baki san matsayin wazir a wajen Rahim ba",ta karasa maganar cike da jin haushin rabi ar da take yiwa kanta ikirarin kanta a matsayin wadda wazir zai aura,cikin nutsuwa wazir ya fita daga motar ya bi bayan RAIHAN zuciyar shi fal damuwa da tsananin haushin rabi a da ta bata masa ran Raihan.
Jiddo ta ce" ka ce zama ya ganmu tun da an tabo dan lele,ga shi rarrashin Rahim yana da wuya idan har a ka sake ranshi ya ɓaci Gara ma kai kana iya shawo kanshi da wuri" ta karasa maganar tana gallawa Rabi'ah harara tare da gwalo duk a lokaci ɗaya,ƙwafa kawai rabi a ta yi tare da fitowa daga gaban ta koma gefan jiddo,jiddo ta ce" a to mutum ya yi abin da Rahim ya ke so ko mu tafi mu bar shi"duk da haka dai rabi a bata tankawa jiddo ba saboda ba ita ce a gabanta ba yanzu tsananin kishin wazir ne kawai ke cin ranta da kuma son gano dalilin wannan kakkarfar alakar dake tsakanin wazir da Rahim.
Kwance ya sameta tana faman kuka kukan da yake daukar shi na tsantsar shagwaba,dan ware manyan idanun shi da suke alumshe ya yi yana kallon yadda take ta kukanta babu abin da ya dameta,cikin sassarfar ya karasa bakin gadon tare da kiran sunan ta, RAIHANN, ya fada cikin jan sunan ta yadda yake shiga can cikin jini da bargon ta,shuru ta yi ba tare da ta amsa ba sai dai ta yi shiru da kukan,sai jan numfashi da take yi a hankali,zama ya yi tare da kamo hannun ta ya rike cikin tafin hannun shi, sannan a hankali cikin taushin murya ya ce" baki ji na ce ta fita ba? Me yasa kuma zaki damu kanki? Tura karamin bakin ta ta yi tana kokarin kwace hannun ta cike da yanayin shagwaba,mai makon ya sake mata hannun kawai sai ya jawo ta ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna,maida kanta ta yi kasa tana mai kin hada ido da shi,umm baki bani amsa ba"ya fada yana rintse hannun ta cikin nashi,cikin san fashewa da wani kukan ta ce"ba ita ce ba"ai nasan ita ce ki gaya min abin da ya bata miki rai saboda na ja kunnen ta kar ta sake"kai tsaye ta ce"ta daina cewa kai zata aura bana so"lumshe idanun ya kuma yi tare da fidda wani dan gajeren murmushi kana ya ce"Tom zan gaya mata kar ta kuma saboda Ni Raihan ce zata haifo matar da zan aura ko? Da sauri ta toshe bakin sa tana zaro manyan idanunta ta ce" yi shiru Hamma wazir kar ka fada a harshen Mala'iku" dariya su kayi gaba daya,janta ya yi zuwa bakin madubi yana cewa gyara fuskar kar su yi kiki dariya,shi ya dau abin shafa fauda ya gyara mata fuskar ta yi tass kamar ba ita ce ta yi kuka ba.
Sai da ya tabbatar bata da sauran damuwar rabi a sannan ya ja hannun ta suka fita,bude mata gaban ya yi ta shiga sannan ya koma mazaunin sa ya shiga tare da tada motar,sai da suka fita daga gidan sannan jiddo tai magana cikin son turawa rabi a haushi ta ce" dama na gaya miki rarrashin Rahim sai Hamman sa wazir, sannan sanin matar wazir sai Allah wata kila ma Rahim ne zai zaba masa matar da ta da ce da shi dan haka ina ga ki shafawa kanki lafiya" a fusace rabi a ta ce" tunda Rahim din ne magabatan sa ai dole ya sama masa mata,kuma Ni da kike