Showing 66001 words to 69000 words out of 189984 words
Chapter 23 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
da yasan yana faruwa da irin mu irinsu".
Khalid ya ce"maganar ka tana kan hanya,amma kuma kar ka manta da wani abu ,duk wanda ya mutu kwanan sa ne ya kare ,su kuma idan mun kasance mune karshen su Allah ba zai taba basu damar illata rayuwar mu ko wani abu makamancin haka ba,dan haka ka kwantar da hankalin ka ka sake mana record din muji ,dan musan ta ina za mu fara fidda bayanan mu",abin da ya kamata ke nan, Raihan ta faɗa ba tare da nuna karaya ko tsorata ba.
Playing din voice din ya saka musu,shuru suka yi gaba daya suna saurara.
Dr sanate yanzu kana ganin cewa yaron nan da ya dauki camarar nan ba zai samu dama ta tona mu ba,saboda bullowar wannan tree full Y trues din shine yake bawa yan jarida kwarin gwiwa akan ida nufin su akan mu,shi yasa nake tsoran ace yaron nan ya saki video nan,Gara tun wuri mu sauya tunani mu yi gaggawar kawar da shi",cewar shugaban jam'iyya ke nan da yake fitar da maganar cikin alamun tashin hankali da son karaya.
Alh sale ya ce" duk ba wannan ba, nifa yanzu gani nake a ko da yaushe asirin mu zai iya tonuwa ko da ba ta hanyar videon nan ba,tun da shi wannan tree full Y trues din shu Umi ne babba,mun kasa gane ta hanyar da yake samun wadan nan bayanan da yake fitarwa",ai ba za mu sani ba sabo bai fito ba sai da ya shiryawa ko wannenmu,su kan su wadan da suke tare da mu din ba ku ga tsoran sa suke ji ba,jami ai da yan jaridun,su kansu bakandamiyya da muke harallar mu tare da su,yanzu a tsorace suke",kawai yanzu abin da ya fi dacewa mu kawar da wannan dan Marayan zakin in yaso sai mu tunkari babbar giwar ba tare da tunanin baya ba.........
Dif maganar ta dauke alamun a nan ya tsaya da ɗaukar record ɗin,duk din su shuru su kayi kowa da abin da yake nazari a ransa,sai dai dukkan su sun zubawa Raihan ido suna sauraron abin da zata faɗa.
RAIHAN jaruma ce akan abin da ya shafi aikinta,dan haka babu wani alama ta firgici ko nuna alamun tasan video da suke magana a kai,ta yi nisa ne wajen yin wani zuzzurfan nazari wanda ita ka dai ta barwa kanta sani,abu Huraira ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa,Ni yanzu damuwa ta shine musan wane dan jarida ne videon nan yake hannun sa, Sannan a wa ce gidan jaridar yake?taya akai kuma ya samu video? Me video ya kunsa?duk da cewa wannan ina da tabbacin cewa wani sirrinsu ne da basa son ya fita a cikin videon ", Khalid ya tari numfashinsa da cewa , wannan fa babban aiki ne a gare mu,kawai Ni ina ganin mu yi aikin da yake hannun mu ba wai neman wanda video yake hannun sa ba", Rahim ba ka ce komai ba? Cewar abu Huraira,
Abun da Khalid ya fada shine abin yi",ta faɗa cikin rashin bawa maganar muhimmanci,abu Huraira ya ce" amma Rahim inaga kamar hakan baiyi daidai ba,saboda bamu sani ba ko acikin wannan gidan yake,nifa tunani na ya fara Bani cewa akan video nan aka kashe Halima kuma duk yadda akayi wanda yake dauke da record din videon a nan gidan yake,shi yasa hankalina ya tashi matuka",zuba mishi ido Raihan ta yi kafin ta maida kallon ta kan Khalid da shima yake wani dan nazari,ta ce" abu Huraira ko ma meye ba mu da hurumi da shi,maganar halima ta wuce Allah zai saka mata abin da aka yi mata,so batun mu barshi a nan idan kuma kana ganin kana da hanyar da za mu samu videon cikin sauki bamu da damuwa da hakan,sai muyi abin da ya da ce",yauwa Rahim ka fahimci abin da nake nufi, Khalid ya ce" amma fa Ni ina ga Gara mu fara wallafa wannan jaridar kafin binciken videon ya biyo baya kar muje tree full Y trues ya riga mu",ya fada da dariya a kan fuskarsa, su ma din murmushi su kayi daga nan suka yi sallama kowa ya wuce inda ya fi wayo.
Yauma Raihan bata hau office din wazir ba,kai tsaye fitowa ta yi dan daukar mashin dinta...
Barka dan uwa Rahim ", Raihan taji an fada daga bayan ta ,ya yin da take shirin hawa mashin dinta,juyowa ta yi cikin nutsuwa kafin ta ce" yauwa Barka amma da kin yi sallama ina ga sai yafi ko? Raihan ta faɗa tana kallon suryy dake ta faman murmushi jikin ta sanye da doguwar riga da dan madaidaicin mayafi kalar Les din dake jikinta, cikin lankwasa murya har da yin fari da ido ta ce" am sorry salamu alaikum",amsawa Raihan ta yi cike da gundura da tsayuwar,idan ba zaka damu ba ka bani nomber za mu yi magana saboda naga yanzu kamar ka tashi daga aiki",ey na tashi kamar yadda kika gani",ayya kayi hakuri amma dan Allah ka bani nomber ka,ganin macece yar uwarta yasa bata ja maganar ba kawai ta bata katinta,na gode,suryy ta faɗa tana bin RAIHAN da wani shegen kallo.
Ba tare da ta kuma tanka mata ba,ta haye mashin dinta ta fita da dan gudun ta irin na kwarewa.
Dariya suryy ta yi tana cewa yaro kazo hannun suryy,kuma nasha alwashin sai na gano ɓoyayyiyar dangantakar dake tsakaninka da Ahmad wazir chibado......................✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page22 ```
Abbie da aunty amarya ta samu a falon,babu hamma idi kamar yadda tafi samunsu, wasu lokuta,sannu da hutawa ta yi musu,ba tare da ta kuma cewa komai ba bayan haka,ta wuce dakin ta saboda yadda take hanzari wajen samun kebantuwa.duk da cewa antyy amarya na lure da ita,sai bata bawa hakan muhimmanci ba ganin abbie na wajen.
Tana shiga ta rufe dakin tare da sa masa key.bincike ta fara har sai da ta lalubo inda ta yiwa camarar nan boyo.zuba mata ido ta yi na wasu yan dakiku,tunda ta dauko camarar bata taba tunanin bude ta ba har sai idanun masu bin ta ya kau daga kanta,duk da dai a wannan lokaci bata da tabbacin zasu daina bibiyar Tata,to amma yanzu lokaci yayi tun da har taji tabbaci akan neman da suke mata,kuma tasan cewa camarar suke son karba amma da tuni sun kasheta,rintse idanunta tayi tana jin cewa gwara ta fitar da video kawai tun da dai basu daina neman ta ba,tasan koda ta basu camarar nan dole sai sun kashe ta tun da ta riga ta san kadan daga cikin sirrin su,amma fa duk da haka tana matukar jin tsoran fitar da videon kai tsaye ta jaridar su,badan kanta kawai ba,sai dan ragowar mutanen da suke aiki a chibado fm wanda ta sani cewa babu wanda zasu kyale ,kai hatta shi kansa Wazir bata da tabbaci akan zai sha.
Yaya zanyi na fidda wannan video ba tare da nayi sanadin rayuka da lafiyar wasu ba?
Ta tambayi kanta cikin damuwar da ta gama baiyana a kan fuskarta.
Duk da cewa ba ta yi wani mamakin sanin wadanda suka aikata kisan haluma ba,saboda ta riga tayi karatu me zurfi akan yanayin tafiyar siyasa.
Shi yasa ko alokacin da tasan komai bata firgita ba,duk da cewa ta yi mamaki ganin fuskokinsu a matsayin masu aikata wannan mummunan laifi.
TREE Full Y TRUES shine abin da ya fado ƙwaƙwalwar ta da tunaninta,shin ta yaya zan same shi? A ina zan ganshi?ya za ai na bashi wannan video?
Zagaye dakin ta shiga yi cike da tsananta tunani,ya rufe komai nashi ,bai bar wata alama da za a iya tura masa ko dan guntun sako ba,shin ta yaya ne wai?
DSP.Haidar ne ya wado mata,cikin sauri ta lalubo lambar wayar sa,bugu biyu ya daga,kana ina abin? da ta fara tambayar shi ke nan.ina hanyar zuwa gida,ok idan baza ka damu ba ina son magana da kai ka karaso gidanmu idan ba zan takura ka ba",No ba damuwa yanzu zan karaso.kashe wayar ta yi ,sai a lokacin ta dan samu nutsuwa har ta fita falo dan kar ta janyo hankalin iyayen ta su Ankara da abin da ke damunta.
Magana su kayi me dan tsayi ita da Haidar wadda sam ban samu jin ko daya daga abin da suka tattauna ba.sai dai daga dukkan alamu shima ta samu wasu bayanai daga gare shi wadanda suka kara mata karfin gwiwa,ragowar kuwa sai nan gaba za mu sani.
..........
Cike da farincikin fara samun kusanci da Rahim suryy ta kira kawarta rubyy ta sanar mata komai,daga nan ta ce" ta bata nan da kwana hudu duk abin da ya kamata su sani zasu sani akan Tsakanin Rahim din da Wazir.
CHIBAƊO'S HAUSE......
Sosai shirye shiryen biki ya kankama ta bangaren iyaye da amarya,shi kan wazir da yake amsa sunan ango bai ma san anayi ba,hasalima bai san ranar aurenba, babu abin da ya dame shi da hakan ,sai dai kuma duk ya tuna auren idan ya ga wata alama sai ya tuna Raihan da abin da zai faru idan ta ji auren, gashi shi kuma miskilanci ya hana shi sanar da kowa,saboda yana jin sanarwarsa ga mutane yana nuna cewa ya na sane da auren ne ko kuma ya damu da maganar auren.
Washe gari ma'aikatan yan jarida da jama'ar gari su ka wayi gari da sabon labari a shafin jarida ta tree full Y trues,labarin daya girgiza yan siyasa da su kansu 'yan jaridu, zuwa kan al'ummar gari wadanda kusan abin yafi shafar su.
A shafin nasa ya bayyana wani babban al'amari me taba zuciya akan lamarin yansiyasar mu.
A shafin nasa yake cewa akwai wani boyayyan sirri akan mutanen da bai gama gano su ba,wanda ya tabbatar da cewa idan ya tsaya bai bayyana wannan labarin ba har sai ya gano ai nahin masu ruwa da tsaki cikin al'amarin to tabbas abin zai ci gaba har ma ya fi na baya,saboda shirin da suke kuma yiwa lamarin.
Ya ce" ya gano a cikin manyan mutanen mu akwai wadanda suke tada tarzoma a yi kashe kashe a zubda jini,bayan sunyi hakan kuma daga baya sai su bi kabarurruakan gawarwakin su tone su cire wasu sassa daga jikin gawarwakin.
Ya ce" wannan abu ba karamin girgiza shi ya yi ba,shi yasa ba zai iya tsayawa har sai ya kammala binciken gaba daya ba,daga karshe ya ce"yana mai umartar jami an tsaro su yawaita su kuma saka idanu akan ko wane lungu da sako , su kuma saka idanu akan manyan kasa da yan siyasa,saboda yana da tabbacin wata babbar tarzoma da suke shirin kara tayarwa duk akan kudirin su.
Daga nan ya ɗora da yi wa al'umma alkawari akan in sha Allah in dai yana raye da lafiya, sai ya binciko wadan nan mutane Sannan sai ya bincika a salin abin da suke yi da wannan sassan jikin gawar,amma yana mai yiwa jam'i ai kashedi da babbar murya kan su kula, su tsaya su yi aikin kare hakkin dan Adam kare al'umma shine aikin su ba kare dukiyoyi da rufawa marasa imani asiri ba.
Wannan lamari ba karamin jijjiga zuciyoyin jama a ya yi ba,ya yin da bayanan tree full Y trues ga jam'i an tsaro ya yi matukar sa su cikin firgici da gudun tonan sililin da ya dauki hanyar yi musu,hakan yasa ta ko ina garin ya dau wuta da jiniyar yan sanda, wanda hakan yake nuni da sun tsorata za kuma su yi aiki ko dan Allah ko kuma dan gudun tsira da mutunci da rayuwarsu,wasun su kuma dama dole a ka yi musu,dan haka yanzu sai suke jin kansu a free su ka samu karfin ɗorawa daga abin da suka yi niya tun asali aka dakushe su ta hanyar barazana da rayuwarsu.
Dsp,Haidar yana daga cikin masu karawa abin armashi ta hanyar kama wasu masu laifi da tun farkon zuwansa ya binciko su tare da taimakon su Raihan...
RAIHAN na gama duba labarin ta ɗago kanta, ta dan zubawa su Khalid da abu Huraira da salim idanu na wasu yan dakiku,kafin cikin jan numfashi ta ce"gaskiya wannan ko ma waye ya cancanci girmamawa,ya kuma cika jarumi,ina tare da kwarin gwiwar shi da yake bamu ta hanyoyin da shi kansa bai zato ba,ina ga kawai mu yi rubutun mu akan su shugaban jam'iya kamar yadda mu ka tattauna a jiya", Abu Huraira ya ce" a'a bai kamata mu fidda labarin nan yanzu ba,a ganina za mu janyo hankalin su ya dawo kan mu har ma su yi tsammanin cewa da hadin bakinmu akan wannan Labarin,karshe ma su yi tunanin tree full Y trues yana cikinmu,kun ga tamkar mun janyowa kanmu masifa ne muna zaune kalau",wani banzan kallo Raihan ta yi masa kafin cikin jin haushin abinda ya fada din ta ce" wlh abu Huraira kana bani mamaki,wai shin ba aikin jarida ka karanta ba ne? Dan me yasa zaka dinga kawo mana tsoro a cikin aikin mu,idan ba za ka iya ba ka ajiye aikin a maimakon mu ka dinga sarayar mana da gwiwa,shi fa me aikin al umma kullum kwarin gwiwa yake so,amma kai kullum baka da batu sai na tsoro ",ganin yadda ran Rahim din ya ɓaci sai kuma duk ya ji kunya da nadamar abin da ya yi din,Salim ne",ya ce"gaskiya ne maganar ka Rahim ,abu Huraira duk ma'aikatan da ka gani a chibado fm chibaɗo tv chibaɗo daily trues to ina tabbatar maka da cewa ba gama garin mutane ba ne,shi yasa kullum muke aiki cikin nasara Allah yake daukaka mu,akwai amana a kwai gaskiya sannan akwai sadaukarwa,idan zaka iya shike nan idan kuma kana jin tsoron nan ma bamu da damuwa zaka iya bari",Salim yana ajiye wa Khalid ya dauka da cewa me yasa kaga duk lokacin da aka yi kisan dan jarida sai ka samu a wannan gidan nan,saboda kawai mana tsaye kan gaskiya ne,ko halima da sauran wadanda suka gabata yan sanda da 'yan jarida duk sunyi shahada ne saboda sun mutu ne akan hanyar Allah wato yaki da zalunci da aikata munanan aiyuka kamar dai irin wannan da aka baiyana yau, sannan mu da ka ganmu nan ,muna kara samun kwarin gwiwa ne daga uban gida Ahmad wazir chibado da matemakinsa RAHIM,kai ma ya kamata ace zuwa yanzu ka samu kwarin gwiwa da irin salonsu na aiki,duk da cewa kuwa Rahim shine yaro mafi kankanta da yake cikin wannan ma aikata,amma kwazon sa da himma ya sa ya zama babban kowa ,hatta da shi kansa oga wazir ya sakar masa da yawan ragamar aikin gidan nan,dan haka duk abin da Rahim ya ce ",mu yan bada shawara ne ba'yan dunkufar da shi ba".
So sorry ku yi min gafara,amma in sha Allah bazan kara ba,kuma zanyi amfani da shawararku",ganin nadama sosai a tare da shi yasa Raihan tace "so babu damuwa mu ma ba a san ranmu mu kayi maka haka ba,kawai dai munga kamar kana son maida mu baya ne akan nasarar da muke samu ko nace ake samu a gidan nan tun kafin zuwan mu,Salim ya ce",ya kuke ganin za mu yi kenan? Shin za mu fitar a yau ko kuma mu bari zuwa gobe, idan yaso yau sai Rahim ya kaiwa oga,daga hannun oga koma sai mu bawa Xulaihah ta fara aikin,"Raihan ta ce",hakan ya yi Allah ya Kaimu goben",da Amin suka amsa.
Salim ne ya dakatar da su da cewa kun san kuwa bikin oga baifi saura kwana bakwai ba,amma har yanzu ya ki sanar da kowa a cikin mu?Khalid ya dan zaro ido tare da cewa kai ma kasan ba zai gaya mana ba sai dai kawai muga katin gayya",dariya su kayi har da tafawa, Abu Huraira ya ce"ka ce su oga an kusa shiga daga ciki",suna maganar su ka fita ba tare da sun lura da mutuwar tsayen da Raihan ta yi ba,wanda su sam basu kawo cewar bata sani ba,dan shi Salim ma har da cewa ai laifin Rahim ne da bai sanar da su da wuri ba.
Suna karasa fita ta koma jabar ta zauna,sam ta kasa gane wane irin yanayi ne take ciki,wani irin numfashi me azabar huci take fitarwa,kirjin ta har sama yake yana kasa,idanunta tuni suka koma wata kala,miƙewa ta yi tana ganin duhu a cikin idanunta ,ba tare da ta kula da yanayinda take ciki ba,ta fita daga office din,da lalube ta karasa inda mashin din ta yake,a hankali tasa hannu ta ciro key ɗin,duk da yadda take ganin bibbiyu hakan bai hana ta jan mashin din da wani irin speed ba.....
Wani saurayi sanye da facemask ya fito daga bayan ƙatuwar bishiyar dake jikin buldin din da waya a kunnen shi ,oga ya fito kuma naga kamar yana a yanayin da za mu iya aikin mu cikin sauki,ok sir saurayin ya fada yana kashe wayar,da sauri ya shiga wata bakar mota suka ja da gudu suka bi bayan RAIHAN dake ganin titin na rabe mata huɗu.
Wazir ya na ganin lokacin da Raihan ta fita,duk sai yaji hankalin shi ya tashi,cikin nutsuwa da boye abin shi a zuciya ya fito ba tare da ya saurari security n shi dake binshi kamar jela ba,ya fada mota kai tsaye bayan raihan ya biyo wadda cikin kankanin lokaci ta bace a titin kamar ma bata bi ta hanyar ba,ci gaba da tafiya ya yi cikin gudun da yake dan karawa da yakinin cewa zai same ta a gida.duk kuwa da cewa zuciyar shi na wani irin bugu da shiga yanayi me wuyar fassara akan fitowarta Raihan.
Luf kake ji tun fitar labarin sun kasa yin wani motsi wanda zai sa a yi zargin su,duk wani me fada a ji ko dan takara yanzu yana cikin halin kaka nikayi ne,akan labarin da tree full Y trues ya fidda, zuciyoyin su cike suke da tsoran budewar ballin duk da cewa basu san komai akan lamarin ba ba kuma su san ta inda wannan shegen ya samo labarin nan ba,to amma duk da haka sun tsorata saboda ganin su da kuma tunanin su shine kan me uwa dawabi za ayi.
Hatta gwamna sai da ya tara mittin din ujila,
Cikin nutsuwar shi da