Showing 90001 words to 93000 words out of 189984 words
Chapter 31 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
fidda camarar ta,kafin ya kuma yin wani abu tuni ta shiga recording yanmatan cikin sauri da nuna kwarewa,yana tabbatar da ta samu abin da take son samu ya kuma jan hannunta suka bar gurin ,barin su gurin ke nan su Dr sanate suka fito suna faman kyalkyala dariya alamun dai duniya ta yi musu da d'i,kafin su shiga motar ta yi saurin fuzgewa ta kuma saita camarar ta dauke su hoto dukan su a daidai lokacin da suke bude motar ana fidda yanmatan da suke kamar gawa.
Trouble girl ya fada can kasan makoshinsa yana janyo ta jikin shi suka shiga motar a tare,tura baki ta yi tana kokarin janye wa daga jikinshi,bai hana ta ba ya bata damar hakan,cikin kankanin lokaci y'ansanda suka yiwa wajen zobe,wasu kuma kai tsaye su kayi kan su Dr senate wasu kuma suka shiga ciki dan fitowa da sauran,Saida wazir ya tabbatar sun kamu dukan su sannan ya bawa Ramadan damar barin wajen.
Cike da rudani suke kallon junansu bayan duk an saka su cikin motar shiga ba biya fita Saida Allah ya isa,duk cikin su an kasa samun mai yin magana saboda yadda abun yazo musu a bazata,saidai kuma ba su wani tashi hankalin su ba saboda sun san duk cikin kankanin lokaci zasu fita daga tarkon da aka dana musu.
Gidado road abin da ya fadawa Ramadan ke nan ya ci gaba da danna wayarsa,Ramadan da shi kadai ya fahimci abinda ogan nasa yake nufi take ya yanke hanya ya dau hanyar inda ka bashi umarnin zuwa.
Ƙawataccen gida ne me hawa biyu wanda yake cike da kayan more rayuwa ,ba shi da wasu tarkace komai nasa a tsare yake kamar yadda me shi yake,babu wanda yasan da wannan gidan cikin jerin gidajen na wazir sai amintaccen drivan sa Ramadan,shi kansa securityn sa baisan da gidan ba dan haka sai ya yi tsammanin ko ziyara wazir din ya kawo,dan haka da ya ce", su ta fi bai kawo komai ba ya bi Ramadan suka tafi duk da cewa an bashi umarnin ya kasance tare da shi da duk wani motsinsa.
Sai da ta tabbatar da barin su Ramadan gurin kafin ta fara neman ba asin kawo ta nan din da ya yi,banza ya yi mata ya bude yar kofar da bata da wani girma sai azabar kyau,nuni ya yi mata da ta shiga amma sai Raihan ta yi tsaye a gun tana kin motsawa,idan baki wuce ba kin san dai ba gagarata zaki ba ko?bata fahimci abin da yake nufi ba dan haka sai ta kuma yin fuska tana neman hanyar gudu,dan ita a yanzu babu abin da take muradi kamar ya barta ta tafi ta kuma kwaso rahoton police,dan tasan i zuwa yanzu yan jarida sun fara cika ofishin y'ansanda,shima yasan me take so ta yi din dan haka ya taho da ita nan din,bata Ankara ba sai jin ta tayi a sama,daukar amarya ya yi mata ya shige tare da rufe kofar, a hankali ya fara taka matakalar upstairs din da ita,rufe idanun ta ta yi tana kananan hawaye tare da dan kai mishi bugu a kirji, wazir dai nunawa ya yi bai san tana yi ba,ba shi ya sauke taba sai a saman wata lafiyayyar shimfida cikin wani lafiyayyar daki me tsananin kyau da sanyi tare da kamshi me sa mutuwar jiki da ta zuciya.
Kamar daga sama shugaban jam'iyya ya samu wannan labarin,duk da cewa babu shi cikin wannan case din to amma fa yasan cewa tunda yaron nan ya iya dauko wannan hoton to kuwa tabbas yana gab da watsa videon nan,ba tare da bata lokaci ba ya fara shiri, abin ka da manya cikin awa daya ya samu ticket din barin kasar, wannan shine kawai abin da zai tseratar da shi da iyalansa,hatta da me gadin sa sallamar sa ya yi dan yasha alwashin ko ƙwaro ba zai bari a gidansa ba bare a samu hanyar kama shi.
Tuni fa gari ya dau dumi,gidan jaridu television rediyo kowa da nasa irin labarin,saidai kuma kowa yana jiran safiya ne dan jin cikakken bayani na gaskiya daga gidan jaridar chibaɗo.
Kafin lokacin tashinsa ya yi ya yi kokarin haduwa da dan leken asirinsu na gidan rediyon chibado,cikin tashin hankali shugaban jam'iyya ya bashi umarnin akan lallai kafin safiya yana so ya batar masa da wannan video,dan haka dole ne ya yi kokarin gano inda Rahim ya boye shi,ok sir zan yi kokarin hakan amma fa ina tunanin ba a office ya boye shi ba dan da anan ne da yanzu na gani ",cewar matashin saurayin da yake tsaye a gaban shugaban jam'iya cikin nuna girmamawa,shugaban jam'iya ya ce",to kuwa tunda kayi tunani cewa baya office to ina baka tabbacin cewa a office din zaka same shi dan haka ka yi gaggawar duba shi kafin wayewar gari ,idan ka ganshi ka sanar da ni kuma idan na samu isa zan kira ka,akan haka suka rabu kowa na tunanin abin da zai iya faruwa idan videon ya fallasa.
GIDAN GWAMNATI.........
Tun da labarin ya same shi yake kaiwa da kawowa cikin tangamemen falon da tsayawa bayyana tsaruwar shi da kyalekyalen shi ma bata lokaci ne,a hankali ya kuma kai hannu kan wayar shi dake kan d'an karamin senter table ya dauka tare da danna kiran shugaban jam'iya.bugu daya kuwa ya daga cikin girmamawa suka gaisa,Alhaji Garba ur exsellency ya dan numfasa tare da yin gyaran murya sannan cikin kamilalliyar Muryarshi ya ce", shugaban jam iya kana ina?ina son ganawa da kai a yammacin nan",da sauri shugaban jam'iya ya duba agogon da ke fuskantar shi sai ya ga yana da sauran awa ɗaya kafin jirgin su ya ta shi,dan haka cikin nuna girmamawa ya ce", shike nan ranka ya dade gani nan bisa hanya",daga haka suka katse wayar, Alhaji Garba ya ci gaba da dakon jiran shugaban jam'iya ba tare da ya koma ya zauna ba,saboda yadda abin da ke faruwa din yake tsinkulin zuciyar shi da saka shi cikin wasiwasin anya kuwa wannan tarzomar zata bar shi ya kuma hawa mulki,duk da cewa shi ba dan kansa yake kokarin komawa ba,sai dan al'ummar daya fuskanci cewa suna jin dadin mulkin nasa,to amma fa akwai ƙura indai wannan al'amari ya cigaba da faruwa a cikin jahar tasa.
Cikin mintuna goma kuwa sai ga sanarwar zuwan shugaban jam'iya,babu bata lokaci ur exsellency ya bada izinin shigowa da shi,bayan sabuwar gaisuwa cikin mutunta juna kamar yadda yake a tsakanin su,cikin nutsuwa ur exsellency ya sanar da shi abin da yake damun ransa, ya ɗora da cewa yanzu shawarar ka nake nema akan abin da ya kamata mu yi dan asirin kowa ya tonu wanda ta wannan hanyar ne kawai za mu wanku daga zargin da al'umma suka fara yi akan mu",dan jim shugaban jam'iya ya yi kafin cikin nuna alhinin sa ya ce",ai ina ga ranka ya dade kawai ka gayyato HAIDAR YAHYA RINGIM tun da kaga shine wannan al'amari yake hannun sa,dan haka nake ganin kamar da shine ya kamata ku tattaunaa abun da ya kamata domin kawo karshen al'amarin",dan numfashi ya fesar kana ya bawa shugaban jam'iya hannu su ka yi musabaha yana cewa na gode zaka iya tafiya",dan rissinar da kan shi ya yi cikin girmamawa tare da yin sallama ya bar falon da gidan ma gaba daya yana mai duba sauran lokacin da ya rage masa su bar ƙasar,wanda bai wuce mintuna ashirin da biyar ba,a wannan lokacin cike yake da dokin barin kasar tun da yaga al'amarin ya kai ga ta shin hankalin Gwamna,to amma wani abu dake masa susa a rai shine me yasa ur exsellency ya neme shi shi daya ba tare da sauran ba kamar yadda suka saba,yasan cewa ba ne wanda ya cancanci da ur exsellency ya nema ba to amma me yasa ya neme shi? Ina Alh Yahya?ina dufuty?sannan me yasa ya kuma yi masa tambaya akan abinda suka riga suka shawarta tuntuni suka kuma sami mafita?kai gaskiya sam bai yadda da wannan zama nasu ba sai dai idan da akwai wata a kasa .....✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page32 ```
A daidai wannan lokacin da yake cikin zuzzurfan tunanin hanyar da zai kuɓutar da ahlin dan uwansa ,shi kuma ya danno masa kira,jikinsa babu kwari ya daga muryarsa a shake ya yi sallama,cikin girmama dan uwannasa Alh Muhammad nuurr ya ce ",yaya ku fito gaba daya idan muka yi sallar Isha sai muyi dinner ko?da sauri Abba yahya ya saita Muryarsa kana yace ok babu damuwa ganinan tawowa bari na sanar da maimunan, Rahim ɗin ya dawo ne yayi saurin tambayar nurr dan yaji yana kokarin aje wayar, Abbien ya ce",Rahim ya dawo gida tunkafin magrib,Tom gamu nan yanzu,a fito lafiya Abbie ya fada yana kashe wayar,ajiyar zuciya ya sauke ranshi duk a dagule,alwala ya daura ya fita dakin inna maimuna ya shiga samunta yayi itama ta ɗauro alwala ,cikin dan hanzari ya sanar da ita cewa idan ta kammala ta same shi a bangaren ƙaninnashi,amsashi ta yi tana kallon yanayin nashi wanda ko bata tambaya ba tasan tatsuniyar gizo bata wuce koki.
Mama murja ce zaune a falonta tana faman isa da takama gata matar me kudi waya take yi da ƙawarta akan oder kayan kiching da tayi wadanda take saidawa,tun kafin ta gama wayar taga wani kiran na shigowa bata damu ba harsai da ta kammala kana ta duba dan bin kiran da akayi mata,amma sai taga anyi hiding nomber ,tsaki tayi tana shirin ajiyewa aka kuma kira,sai da tayi shakara kafin ta daga,ko kin daga ko baki ɗaga ba hakan ba zai dakatar damu daga daukar rayuwar daya daga cikin 'yayanki ba,dan haka ki shirya samun sakon gawar daya daga cikin yaranki",kit aka.kashe wayar,wata irin zufa ce ta shiga keto mata ta ko ina.
Waye wannan yake min barazana da rayuwar yayana ? Waye wannan yake son kashe Ni da raina?'ya'ya na sune rayuwata sune kadarata,wai waye wannan din ta kuma tambayar kanta cikin tashin hankali,jummai jummai jummai ta shiga kwalawa me aikinta kiran mafarauta,da gudu jummai ta fito jikinta na rawa dan tasan halin uwar dakinnata,gani haj.......kafin ta karasa mama murja ta katseta cikin tsawa. uban me kike yi nake ta kiranki baki zo ba sai da kika ga dama?zata fara bata hakuri ta katseta a fusace tana cewa ki tashi yanzu kije sashen duka yarana ki duba min kowanne kitabbatar yana nan sai kizo ki fada min,Tom Hajiya ta faɗa tana mikewa cikin rawar jiki.
Sintiri ta shiga yi tamkar me jin zawayi ,ita sam ta ma manta da wata waya shi yasa hankalinta bai kawo mata cewa ta kira su ba,zuciyarta cike take da tunanika iri iri na wanda yake shirin yi mata wasa da rayuwar ya'ya,anya kuwa ba Hanne bace? Tabbas hakan zata iya faruwa domin bazata taba mantawa da cewa kowa ta ciki na ciki bace rashin mafita ne kawai ya sa suka hada kansu,lallai idan haka ta faru kuwa Hanne kin shiga uku dan wallahi bazan taba barinki ba.
Cikin nutsuwa suka kammala cin abinci,duk da cewa dai Abba yahya dakiya kawai yake,yana boye halin da yake ciki,koda suka kammala inna mainuna da aunty da Raihan da dakin hajiyar agadex suka nufa dan tayata hira.
Gyara zama Abbie yayi bayan sun dawo falonsa,sannan ya dubi Abba yahya ya ce", yaya wai me yake damunka? Saboda na lura tun shigowarka kamar baka cikin nutsuwarka.
Wani Murmushi Abba yahya yayi me ciwo kana ya ce", Muhammad duk abinda zan fada maka baza ka yadda ba amma duk da haka bazan kasa tofawa ba,domin duk wanda ya yi sanadinka ba kowa yayiwa asararka ba sai mu,nuna mishi test din da akayi masa ta email dinsa ya fara yi,Abbie yana gama karantawa ya saki Murmushi wanda kai tsaye ba zaka bashi fassara ba,mika masa wayar yayi kana ya ce", yaya karka damu kanka babu wanda ya isa daukar rayuwarmu face Allah ya bai kawo lokacinmu ba ,duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi",zuba masa ido Abba yahya yayi kafin ya girgiza kanshi ya ce",wato nuurr har yanzu baka girma ba, na yadda da maganarka amma abinda nake so ka duba shine wahala ake gudu sannan da wadanda a kaiwa asarar wato iyalanka,dan haka Inaso nayi maka wani jankunne,dan shuru yayi sannan ya cigaba da cewa Nura mutane da kake gani basu da imani ba kowa ne yake da irin zuciyarka ba dan haka Inaso ka kula da mutanen da suke kewaye da kai,ba kowa ne yake da amana ba kai hatta da ɗan cikinka zai iya ci maka amana akan dukiya,dukiya da kake gani shu'umar abace kana cikin talauci baka huta ba arzikinma ba kasami kwanciyar hankali ba,dan haka ka kiyaye",bai saurari cewarsa ba ya tashi yana danna kiran inna maimuna dan ta fito su tafi saboda dare ya fara yi.
Abbie shuru yayi cike da tunani tun bayan fitar Abba yahya,nazari yake akan maganar Abba yahya,sai ya zamana kamar ya haska mishi wata hanya ne game da binciken da suke yi akan me neman rayuwar Raihan,sosai ya shiga tattara maganganunshi yana tarasu da ɗebewa,lallai ya kamata ya zauna da Dr Sabo da ur exsellency.
Cikin wannan tunanin aunty amarya ta sameshi,Abban Rahim me ya faru naga kamar kana cikin bad mood?
Murmushi ya kirkiro yana mai janyota jikinshi,bai bata amsa ba harsai da ya bata kyakkyawar sumba a gishi tukunna ya ce",wani labarin tausayi Yaya ya bani yanzu shi yasa duk kika ganni haka",oh to Allah ya taimaki bayinsa na gari Amin ya amsa yana mai lalubo tashar CHIBADO tv da remote din da ya dauka.
A bangaren mama murja kuwa bata samu nutsuwa ba harsai da ta samu tabbacin duka yaranta suna lafiya,daga nan ne ta fara saka yadda zata yi maganin Hanne da zuriarta dan tasha alwashin ko ciwon kai yaranta su kayi sai ta dau babban mataki me girma akan duk ahlin Hanne.
Wajen misalin biyu na dare mama Hanne na tsaka da bacci ta ji sautin karar wayarta da bata cika kashewa idan zata kwanta ba,cikin magagi ta daga wayar dan jin wane dan iskannee yake sharara mata kira cikin dare haka.
Ki tashi daga baccin da kike domin bashi ya kamace ki ba a yanzu,abinda aka fara fada kenan,babu shiri momi Hanne ta murtsike idanunta tana cewa to ubanme ya kamaceni gadin mutanen duniya a ka bani da bazan yi bacci ba? Ba gadin mutanen duniya aka baki ba,gadin 'ya'yanki zaki gwadayi ko hakan zai sa su tsallake mutuwar dake binsu,wata irin wuntsilowa Hanne tayi daga saman gadon da take sharara baccinta cikin jin dadi tayi tana cewa bana son irin wannan wasan kai waye?madaukin ran ya'yan ki ne", ya na fadar haka ya kashe wayar,kan bala'i Ni murja zata yiwa haka ,ai dama nasan wasan bai kare ba shi yasa Nima na daura damarata tun wuri,dan haka muje zuwa yanzu ne asalin wasan zai fara dan wallahi babu wanda ya isa ya taba 'ya'yana na barshi yasha ruwa adoran kasa.
*TSOHUWA ME JINI*
Hhhahhhhhahh .........shuda aikinka yana kyau,cewar tsohuwa tana maganar bakinta na fitar da wani irin hayaki me tsananin zafi kai kace wuta ce ke ci a cikin bakin,shuda dake durƙushe agabanta kansa a sunkuye ,cikin tsananin biyayya ya ce",jini ya temaki TSOHUWA muna tare dake duk runtsi umarninki nake jira naki fada nawa cikawa,hahhhhh ta kuma ɓarkewa da wata mahaukaciyar dariya har kogon na girgiza kamar zai rabe biyu,sai da tayi me isarta sannan kuma ta haɗe yamutsatstsiyar fuskarta me kama da an dama fura,ta ce", lallai jini na bukatar karin jini daga jikin ahlin wancan mutumin ka tafi kayi hanzari kar jini yayi fushi,jinjina kai ya yi kafin ko mai ya shafe kamar babuu wata halitta da ta ke zaune a gurin.
*WASHE GARI*
Cikin farin ciki yau rabi'a ta tashi saboda fara shigarta office,cikin gaggawa ta kammala shirinta dan duk a tsammaninta tare zasu tafi,
Har abun kari tayi kokarin yi masa duk da cewa tasan ba ci zaiyi ba,zaman jiran fitowarsa ta yi na tsawon mintina goma sha biyar,kafin ta fara shako sihirtaccen ƙamshinsa wanda duk ƙwaƙwar mutum bai isa gane turaren da ya ke amfani da shi ba sai dai hasashe,zuba mishi ido ta yi tamkar zata cinye shi danye,tafiya yake tamkar wani saraki cikin hanzari irin wanda ke nuna cikakkiyar lafiyarsa.
Ina kwana hamma WAZEER,tayi saurin gaidashi ganin yana neman ficewa ba tare da ya kalli inda take ba,lafiya,ya amsa cikin ƙasaitacciyar muryarsa ,idan kun shirya habu driver ya kawo ki",bai saurari abinda zata ce ba ya yi ficewarsa.
Kwafa tayi kafin ta figi jakarta tabi bayansa,bata taɓa tunanin zaice ta tafi ita kadai ba,dole ta bi umarninsa badan ranta yaso ba sai dan tasan ko shiɗin waye.
*RAIHAN*
Ke Raihan ki tashi daga wannan baccin ko baki san lokaci yaja ba?juyi tayi asaman gadon tana kuma kanannaɗewa cikin tattausan dovet ɗinta.
Hajiyar agadex zata kuma yi mata magana aunty amarya ta shigo bakinta ɗauke da sallama,dole hajiyar agadex ta sauya salon tashin Raihan ɗin da cewa, kai kuwa Rahim wannan wane irin bacci ne kake ko baza ka je office ɗinba yau?jiki a sanyaye aunty amarya ta karasa bakin gadon,tana cewa Hajiya kije zan tasheshi ina ga yau baza shi office din ba",mele baki hajiyar agadex ta yi kana ta juya tabar ɗakin ,cikin zuciyar ta kuwa fadi take , yau naga wani abin al'ajabi ,idan banda abin ramla ai zuwa yanzu yaci a ce ta daina boye min Raihan tunda dai tasan muna tare waje daya kuma dole duk ɓoyonta wata rana idanuna su gane min wacece Raihan,tunda bata da dabarar sauyawa Raihan ɗin halitta a karo na biyu,jinjina kai ta yi tare da cewa zan biki naga inda rainin hankalinnaki zai tsaya.
Sai da ta tabbatar hajiyar agadex ta yi nisa da barin ɗakin, sannan ta shiga jijjiga Raihan tana cewa,ke Raihan tashi bana son sakarci da irin wannan sokoncin naki ne zaki janyo hankalin Hajiyar agadex har ta fuskanci me muke ciki,dan Allah Raihan ki rufa min asiri kar na rasaki wallahi ina matukar