Showing 30001 words to 33000 words out of 189984 words
Chapter 11 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
sauki,idan kuma kaddarar mu ta kasance wata iri babu yadda zanyi dan ban isa yin kokawa da ƙaddara ba."ita dai RAIHAN duban su kawai take amma gaba daya tunanin ta yana kan Halima shi yasa ma sam bata tsaya ta fuskanci inda maganganun nasu suka dosa ba,ko ta tsaya ma ba lallai ne ta fuskanta ba tun da har yanzu tunanin ta karami ne, RAIHAN"ta kuma maimaita kiran sunanta ganin duk hankalinta baya kansu,,,ɗago idanunta da suke cike taf da hawaye ta yi tana duban antyn,kimtsatstsiyar Muryar WAZIR ce ta ratsa kunnuwan ta har zuwa can wani sashe na zuciyarta wanda kai tsaye ba zata iya cewa ga wane sashe ba ne,da kuma manufarsa ta karbar sakon ba.kiyi hakuri ya fada yana mai yi mata wani irin lallashi da idanun sa da kuma dukkan zuciyarsa ,wanda take Tata zuciyar ta karbi sakon lallashin nasa harma tasa hannu ta yi saurin goge hawayen da suke ta tsere saman kyakkyawar fuskarta.
Ganin haka yasa ya saki wani dan tattausan murmushi wanda ko da can ita ka dai take iya ganin sa,yauwa ki nutsu gobe zan dawo muje gaisuwa gidan su Halima ,amma idan antyy ta sanar da Ni kin kuma yin kuka ba zaki ganni ba har nan da kwana haka"ya fada yana nuna mata yatsun shi biyar,zaro yalwataccen idanun ta tayi tare da cewa bazan yi ba"kinyi alkawari? Jin jina mishi kai ta yi tana murmushi irin na tsantsar yarinta,ok by sai kin ganni"daga haka ya fita da sassarfar takun shi wanda ya cude da nutsuwa da kamalar shi,bin bayan shi ta yi da kallo tana. Jin wani irin kewa na mamaye ta tare da wani irin nauyi da ya karu a kirjinta.
Antyy amarya ta tashi tabi bayan sa tana yiwa RAIHAN gargadin ta tashi ta kimtsa kanta ,dan ta samu nutsuwa yanzu zata dawo.
_______________
Duk inda zaku nemo camarar nan sai kun nemota,haba ace yarinya ta Shammace mu irin haka ba tare da mun sani ba"shugaban jam'iya ke nan da yake magana cikin yanayin tashin hankali,Dr ya ce"Ni abin da ya bani mamaki shine yadda aka yi Wazir ya mamaye mu har yasa yar jaridar su ta bibiye mu"Alhaji sale ya ce"kar ka yi saurin yanke hukuncin cewa wazir ne ya sata Ni nafi kyautata zaton cewa shige_shigenta ne ya kawo ta inda muke tun da binciken da mu kayi ya tabbatar mana da cewa yar jaridar sirri ce shi yasa ma bamu sanya ba", shugaban jam'iya ya ce"to amma lallai ta turawa wani video nan idan kuma ba haka ba ta turawa wani a cikin su sakon inda ta ajiye camarar kuma tabbas camarar tana cikin dajin nan da ƙwaro ya harbeta,yanzu abin da ya kamata mu yi shine ,bincike zamu yi mu gano wanda su ka fi kusa da ita a wajen aiki ko irin nasamanta din nan ko dai kawarta ko abokin da sukafi shakuwa,ina ga wannan ita ce hanya mafi sauki da za mu yi saurin gano wanda ta turawa sako"Dr ya yi saurin tarar nufashin shugaban jam'iya da cewa a'a zamu yi hakan amma fa Ni ina ga kawai wayarta za mu kai jago ya yi mana bincike nasan take zai gano wanda ta turawa sakon,ina ga bamu da lokacin da za mu tsaya yin wannan dogon binciken"Alh sale ya ce"tabbas wannan ita ce shawarar dauka mu duk mun ruɗe sam mun ma manta da saukakakkiyar hanya"jin jina kai kawai shugaban jam'iya yake saboda anzo gabar da zai iya yin komai dan samun rufuwar asirin sa da kuma dorewa kan mulkin da suke ta son hayewa a zaben da yake tun karo su.
A nan ne kuma ya samu sakon taron gaggawa da gwamna ya nema yan majalisar ta su da sauran membobin da abin ya shafa,dole ya katse tattaunawar da suke da su Dr sanate ya yi shirin tafiya.
______
Tun da Wazir ya tafi tunanika suka cika kwakwalwarshi,tausayin RAIHAN ne fal a ranshi ta yadda ƙaddarar ta tazama haka,to amma babu tsimi babu dabara abin da Ubangiji ya rubuta zai faru dole sai ya faru,yaji tausayin antyy amarya matuka ta yadda ya yi duba da matsanan cin son da takewa gudan jinin ta RAIHAN,tsoran kar ta rasa ta yasa ta kuma kawowa rayuwarta matsala wanda ita antyy amarya duk bata ganin hakan saboda idon ta ya rufe da SOYAYYAR tilon yarta,to yanzu ta yaya zata bayyanawa duniya RAHIM a matsayin RAIHAN,anya kuwa hakan ba zai zama wani babban kalubale ga Raihan din ba,tabbas ya kamata ya zauna da Anty amarya akan wannan batun,dan ya riga ya dauki alkawarin kare Raihan da taimakon zuljalalu Wal Ikram,da wannan tunanin ya karasa gidan makoki,inda yana zuwa jiniyar gwamna Alhaji Garba me fata ta karade baki daya anguwar ta su marigayiya Halima,take mutane suka fara turereniyar ganewa idon su asalin gwamna me zuwa gaisuwar talakawansa da aka zalunta,tuni mata suka fara leke ta soraye masu yi ta katanga na yi,kai harda wadanda suke fitowa waje ,ba don komai ba sai dan zuwan adalin gwamnan su.
Cikin mutunci da kamala su ka fara miƙa gaisuwa, abin mamaki a cikin tawagar gwamna har da shugaban jam'iya,shine ma kan gaba wajen mika ta'aziya da bada umarnin yin addu'a ,sosai gwamna ya yiwa WAZIR gaisuwa tare da jaje,daga nan aka fara shiga da manyan buhunan shinkafa da katon katon din ruwa , da kudi masu yawa da ya bawa iyayen Halima, wannan abu da gwamna ya yi ba karamin kayatar da mutane ya yi ba,tabbas ya yi abin da sauran gwamnoni basu taba yi ba,shi yasa baka jin komai sai addu'a da talakawa suke shararo masa tare da yi masa fatan sake komawa gwamnati kai harda masu fatan shugaban kasa,daga nan su kayi sallama, Wazir yana zaune inda yake bai motsa ba bare ya nuna wata alama na son yiwa gwamna rakiya,gaisuwar ma ya yi musu ita ne saboda Abba yahya da yake matsayin uba ga Raihan,ganin haka ne yasa gwamna Alhaji Garba me fata ya ya fito shi ,ba dan yaso ba ya ta shi ya karasa kusa da shi ,Wazir idan ba zaka damu ba ina son ganin ka idan ka samu lokaci dan ina son tattaunawa da kai akan kisan yarinyar nan duk da cewa har yanzu muna kan binciken nemo yan ta Addan da suke son ganin bayan mu"dan sassauta fuska Wazir ya yi kana ya ce"shike nan insha Allah zan samu na zo"idan zaka zo kayi min waya da fasinal layina saboda bana son ka biyo ta kan p.a dan maganar tana bukatar sirri"cewar gwamna ke nan da yake yin gaba dan tarar da mutanen da su kayi cincirindon a bakin motocin su,dan ma 'yan sanda suna yi suna korar su.
Shima wazir din bai dade ba ya yi sallama su ka wuce shida su Ishaq.
Sosai zuwa wannan jana isa ta kuma samowa Alhaji Garba me fata farinjini,kowa. Ya budi baki sai san Barka da fatan alkhairi yake yi masa (to muma Allah ya bamu shuwagabanni na gari Amin ya Allah) .
Da sauri rabi a dake zaune a falon ita da innawuro tana tausa mata kafa,ta mike saboda shigowar da
Wazir ya yi,duk da cewa
yanayin shi ya nuna a matukar gajiye yake hakan baisa Rabi'ah ta hakura da kokarin tarrar shi da take yi ba,sai dai kafin ta kai ga inda yake har ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,shigewa yake kokarin yi innawuro ta dakatar da shi cikin nuna kulawa ta ce"wazirin gida ya kamata ka zauna ka huta ka dan saka wani abu a bakin ka,tun shekaran jiya fa in dai ban ɓata lissafi ba rabon ka da saka abinci acikin ka,a gajiye ya dube ta da lumsassun idanunsa da suka kuma lumshewa har rufewa suke saboda gajiya da damuwa kai harma da yunwar da bai kula da ita ba, a hankali ya bude baki kamar me ciwon baki ya ce"innawuro zan bari na kimtsa tukun amma bana son abu me nauyi ki hada min Koda salad ne"to shike nan Allah dai ya jikan wannan yarinya ya kuma tona asirin masu yi mana wannan aika_aika"Amin ya Allah ya fada a saman harshen sa,da sauri rabi a ta ce" bari na hada maka salad din kafin ka fito" bai ko kalli inda take ba ya haye sashen sa.
Sai da ya sakarwa kansa shaya ya wanke jikinsa,tare da ɗauro alwalar magriba sannan ya ji nutsuwar sa ta fara dawowa,doguwar blue din jallabiya ya saka tare da fesa turarukan sa masu sanyin kamshi.daga nan ya zura tattausan silifas dinsa ya dauki wayoyin sa ya fita.
Kusa da innawuro yaje ya zauna tare da dora kansa a kafadar ta ,shafa kanshi ta yi tana cewa rabi a kawo masa salad din nan zai fi ci a.gabana".
Ba dan yaso ba sai dan rabuwa.da mitar innawuro ya karba ya fara ci a hankali,yana yi yana duba sakonnin da suka.tarun masa,bai wani ci da yawa ba duk dan saboda ba innawuro ce ta haɗa masa da kanta ba,dan haka a darare ya ci wannan din ma,ta shi ya yi tare da duban innawuro ya ce"zan shiga gurin Ammi sai anjima zan dawo"Tom shike nan sai ka dawo,rabi a najin haka ta mike tsaye,ganin tana kokarin fita , Wazir ya kara haɗe fuska kafin cikin miskilalliyar Muryar shi ya ce"ki zauna da innawuro"daga haka yasa kai ya fita,babu yadda ta iya dole ta hakura da bin nasa, innawuro ta dube ta tare da zabga mata harara ta ce"wannan rawar kan da kike shi zai hana ya yi miki duban Rahma bare na soyayya ,dan haka idan zaki nutsu ki kama kanki to ki nutsu kin dai san halin sa sarai bai san hayaniya"tura baki gaba ta yi ta koma ta zauna tana saƙa yadda za ayi ta cusa kanta cikin zuciyar Wazir .
________
Tsaf antyy amarya ta dawo ta samu Raihan,dan haka sai ta koma ta debo mata abinci ta zo ta zauna kusa da ita,cikin rarrashi ta shiga yi mata nasiha har ta samu ta fara karbar abincin.koda ta gama bata abincin bata barta ita kadai ba,zama ta yi tare da ita tana ɗebe mata kewa, cikin hakan da kuma dabara ta dinga jin damuwar RAIHAN har taso ta dan fuskanci wani abu akan mu amalarta da A Wazir,sosai antyy amarya ta bawa Raihan lokacinta ,wanda dama tana yin hakan lokaci lokaci tun can farkon tashin Raihan din ,ko dan ganin yadda ta kuntata rayuwar ta ta hanyar hanata mu'amala da mutane,yanzu kuwa da ta fara girma tana zama da ita ne saboda bata son kusancin yarta da kowa idan ba ita ba,bata son yarta ta yadda da kowa idan ba ita ba,bata son 'yarta ta kaiwa wani damuwarta idan ba ita ba,haka ba ta so 'yarta ta zama me yi mata nuku_nuku akan lamarinta. Aiko dai aunty amarya ta yi nasara dan kuwa ta yiwa RAIHAN ja a jikin da bata iya boye mata damuwarta.
RAIHAN aunty ta fada tana shafa kan Raihan din dake kan cinyarta,na am aunty Raihan ta amsa cikin siririyar muryar ta me cike da yarinta,ki daina damuwa akan mutanen da suke son mu amala da Wazir saboda idan kina yin haka zai dinga jin haushin ki,musamman ma akan kokarin ki na raba shi da duk wata budurwa"tura karamin bakinta ta yi, sannan ta ce"auntyy nifa ba hana shi na yi ba,kawai dai bana son suna kula shi ne sai na dinga jin wani irin bugu a kirjina,aunty nifa ko tunawa nayi sai naji damuwa ta lullube Ni"ta karasa maganar tana jin damuwar tunawar da gaske tana lullubeta,shuru aunty amarya ta yi tana nazarin maganar Raihan din,dama ta yi haka ne dan ta san dalilin da yasa Raihan din ke korar yammatan ko dan ta yi tunani me zurfi akan hakan, shafa kan Raihan din ta ci gaba da yi tana cewa ki dai dinga daurewa bana so yazo yana jin haushin ki kinji ko"gyada kai Raihan din ta yi daga haka suka tashi dan yin alwalar magriba,duk da cewa Raihan din ba yin sallar zata yi ba.
Wazir yana shiga falon Ammi aka kira sallar magriba,hakan yasa ya gaidata a gaggauce su ka fita sallah shida Abbu.
Koda suka dawo daga masallaci bayan sallar Isha, wajen Ammin ya koma ,sun jima tare Ammi da Abbu na yi masa nasiha akan abinda ya faru,daga nan Ammi ta tilas ta masa cin abinci ,yana ci suna yi masa hira har ya ci da dan yawa bai sani ba, sosai yaji nutsuwa atare da shi, cikin murmushin da bayan su da innawuro da Raihan ba kowa ne yake samun sa akai akai ba,ya ce"Ammi kunyi min wayo dai kamar wani karamin yaro"dariya Abbu ya yi tare da cewa to ai dama mu kullum kamar jariri kake a wajen mu,kaima kuma nasan haka kake ji ko? Sassanyar dariya ya yi tare da ƙara lumshe idanun shi da dama suke kamar na me jin bacci,haka nan ya dinga jin nishaɗin kasancewa tare da iyayen nasa ,haka nan sai kuma RAIHAN da damuwarta suka fado masa,tashi ya yi yana duban agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa,ya ce"Abbu dare ya fara yi ni bari na wuce na kwanta na huta,ga kuma sammakon zuwa sadaka"to shike nan Allah ya tashe mu lafiya,Abbu ya fada ,har zai fita sai kuma ya dakata tare da juyowa ya ce"Abbu tare zaku tafi da innawuro saboda Ni zan bi ta gidan su Rahim na dauko shi"fadar sunan Rahim da ya yi sai yaji kamar ya yi sabo,Abbu ne ya katse shi da cewa Tom shike nan idan ka shiga sai ka sanar da ita"jinjina kai ya yi ya fita yana ci gaba da sauraren addu ar da Amminsa ke yi masa, da haka har ya fice gaba daya daga falon yana mai jin kaunar iyayen sa na kuma nunkuwa a zuciyarsa da dukkan rayuwarsa.
_______________
A bangaren gwamna kuwa sai da suka dawo daga ta aziya, sannan su shiga dakin taro,
Alh Garba ya so ace Amininsa na wajen ,to amma duk da haka bata ɓaci ba,dan yasa Abba yahya joining din shi ta video call.sosai suka tattauna akan matsalar karancin tsaro wanda kuma duk wannan yana daga manyan mu wadanda su suke aikata laifin shi yasa ba a daukar wani mataki akai,to amma wannan karon sun shirya yaki da wannan matsala da ta riga ta zama kamar annoba a cikin garin nasu.
Alhji Muhammad nuurr dake kallon su ta ƙatuwar laptop bai ce komai ba , saboda shi sam baya son yawan sako shi da gwamnan ke yi cikin lamarin siyasar su,saida Abba yahya ya nuna masa alama da ido akan ya ce wani abu, sannan ya danyi bayani a takaice daga nan aka rufe taro da addu'a kowa ya kama gabansa.
_________
Aunty amarya na tsaye ta gama shirinta na bacci,idan da baya ne tare da zasu kwanta ,to amma saboda yanzu raihan ta fara zama budurwa yasa Aunty amarya ta fara barinta ita kaɗai amma fa duk farkawar da zata yi sai ta zo ta duba Raihan din da safaya key din da yake hannunta,duk da cewa Raihan a matsayin namiji duniya ke kallonta ,hakan bai sa aunty amarya ta yi sake da baki akan tilon yarta ta ba,sosai Raihan take karuwa da mahaifiyarta ta fannoni da dama,ta ɓangaren ilmi da kuma zaman takewar rayuwa,idan goggo Rahma ta shigo taga Raihan a kiching sai ta yi ta faɗa akan wai aunty zata maida yaro dan daudu,dama a hakan ma ya aka cika yana yin wani abu kamar mace bare kuma tana sa shi girki,antyy amarya takan ce kiyi hakuri goggo ai ko namiji ana so ya koyi aiyukan mata saboda baka san inda rayuwa zata kai ka ba"goggo kan tabe baki ta ce"ke dai fi'ili kawai da kuma takurawa yaro,to duk irin wannan tuni antyy amarya ta riga ta gina rayuwar RAIHAN da shi,sam Raihan bata da ƙyuya irin ta wasu sangartattun ya'yan masu kudin,da wannan tunanin antyy amarya ta gama lura da shirin Raihan din da duk wata tsafta ta kwanciya da ya kamata ta yi,ta kuma tabbatar babu wata matsala sannan ta yi mata addu'a bayan ta rufe ta cikin tattausan bargon dake malale a saman gadon,shafa kanta ta yi ta ce"kema kiyi addu'a kinji Allah Ubangiji ya tashe mu lafiya, murmushi RAIHAN ta yi sannan ta langabar da kanta ta ce"ina son ki mamina "Nima Ina sonki autata"auntyn ta faɗa tana sumbatar goshin Raihan din,marairaice fuska Raihan din ta yi tare da cewa dan Allah aunty zan dan bude data na,yau kwana biyu ke nan ban ga sakonni ba,nasan a na ta yi min ta aziya"dan jim aunty amarya ta yi kafin ta furzar da numfashi ta ce"to amma kar ki dade Kinga idan Allah ya kaimu za muje gidan sadaka dan haka ban so ki makara dan ma ba zaki yi tashin sallah ba"promise aunty bazan jimaba, Raihan ta faɗa a marairaice"shike nan Allah ya tashe mu lafiya"daga nan ta fita tare da rufewa Raihan kofar.
Tana fita Raihan ta janyo wayarta ta kunna tare da kunna data,cikin kankanin lokaci sakonni suka fara rige_rigen shigowa,a shigowar sakonnin ne wani sako ya ja hankalinta saboda sakon daga Halima ne.....ɗiiiiiiiii
Muje zuwa pg na gaba dan ganin sakon da Halima ta turowa Raihan me sakon ya kunsa kuma me sakon zai haifar?
Kuyi min share tare da zazzafan comments din da zai kara min karfin gwiwa kar ku manta littafi na ɗaya kyauta ne,idan ba ku yi comment yadda ya kamata ba zan maida shi gaba dayan shi vip arewabooks 😌
Fatima y Adam ✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page10 ```
Kafin ta bude sakon wayar ta shiga fidda wani dan karamin sauti me dadi wanda yake nuni da cewa kiranta a ke yi,ganin wanda yake kiran yasa ta fasa abin da ta yi niya wato share kiran, ɗagawa ta yi tare da karawa a kunnenta,sallama ta yi cikin Muryar ta da tayi can ƙasa saboda alamun shirin bacci,amsawa Wazir ya yi tare da ɗora Mata da tambaya,ba kiyi bacci ba? Ji tayi gudun