Showing 63001 words to 66000 words out of 189984 words
Chapter 22 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
gaida innawuro dake yi mata kallon tsaf kafin ta amsa babu yabo ba fallasa,duk kuwa da cewa suryy ta yi shigar mutunci dan sanye take da katon hijab dinta har jan kasa yake,cikin sauri rabi ta janye ta su ka haura sama dan gujewa baranbatamar da innawuro zata iya yi mata.
Suna shiga dakin suryy ta yaye hijabin shedaniyar shigar ta ta bayyana,tana cewa gaskiya ruby dole kiji tsoran wannan tsohuwar kin ga wani kallon kurilla da take min kamar tana son ganin kayan dake jikina",rabi a ta ce"shi yasa nayi saurin janye ki dan wannan matar da kike gani bata da sauki.
Sai da suka nutsu sannan rabi ta korawa suryy bayani akan wazir ,ta ɗora da cewa suryy ki bani shawara meye mafita? Ɗan jim ta yi kafin ta ce",yanzu matakin da ya kamata mu fara hawa shine samun tabbacin baya son kowa"kamar ya? rabi ta tambaya cikin rashin fahimtar zancan na suryy. suryy ta ce" ina nufin Mu fara bincike mu tabbatar da cewa babu wadda ta kama zuciyar shi da mahaukaciyar SOYAYYA,idan har babu to ina tabbatar miji da cewa duk irin taurin kan Ahmad wazir sai ya saurare ki akan tarkon da za mu dana masa,amma fa idan a ka samu akasin cewa yana da wata a zuciyarshi to shike nan ke da samun soyayyar sa har abada domin son waccen ba zai taba barin sa ya saurareki ba harma ya fahimci zuciyar ki, wannan shine hikmata".
Shuru ne ya ratsa dakin na wasu yan dakiku,kafin ruby ta yi wani dan murmushi wanda kana ganinsa kasan na yake ne,ta ce" suryy maganar ki na kan hanya,sai dai kuma ina kokwanto akan zuciyar wazir,tabbas ina da shakku akan cewa zai iya son wata har haka,to amma mu jarraba mu gani".
Murmushi suryy ta yi,kana ta ce" rubyy baki san irin su wazir ba,wuyar sha ani ne da su ,irin su baka gane takamaiman abinda ke cikin ransu,sun iya boyon SOYAYYA,ke karewa ma ko wadda suke so ba lallai ne ta fahimci hakan ba,dan haka.nace miki aiki ne a gaban mu babba,saboda kafin zuwan lokacin bikin ya kamata muyi wannan binciken,shi kuma auren Kinga lokaci kadan ya rage tunda baifi sati biyu ba".
Haka ne maganar ki Surry , nifa yanzu wlh har kin sani cikin fargaba saboda bamu san wane irin sakamako zamu samu ba,wlh suryy duk na gano da akwai wadda wazir yake so wlh sai na kashe ta ko wacece.
Sai daf da magriba rabi ta sauko daniyar yiwa suryy rakiya,a nan suka ci karo da kyakkyawar fuskarsa wadda ke gewaye da siririyar saje wanda ya kuma kawata fuskar tare da kamewar shi me saka mutum kama kai ko bai shirya ba,sanye yake cikin doguwar bakar jallabiya yar asalin Saudiya me matukar sheƙi,yana zaune a dinning yana cin tuwon farar shinkafa da miyar agushi wadda taji ganda da Nama,cikin nutsuwar sa da kamewar sa yake cin abincin kai ka ce wani sarki ne,ko yadda yake cin abincin wani abun burgewa ne da kallo wajen yanmata,tun daga nesa yake jin idanu akansa wadda hakan yana daya daga cikin dabiar da ya tsana,duk da cewa bai ɗago ya kalli ko da bangaren da suke ba,hakan bai hana shi gane cewa su biyu ba ne.
Cikin mutuwar jiki suryy ta gaida shi,wanda ko motsi bai yi ba bare ta sa ran zai amsa,cike da jin haushi rabi a ta ce" hamma ƙawata na gaida ka fa",goge bakin shi ya yi da tisue ya mike cikin dan hanzari saboda kiran sallar magrib da aka kwala a Masallacin chibaɗo,ficewa yayi cikin nutsatstsan takunwanda yake gauraye da 'yar sassarfa me nuni da cewa sauri yake yi ya bar su da shaƙar mayataccen ƙamshin sa.
Wani kallon kurilla suryy ta kuma binsa da shi ba tare da ta kula da wulakacin sa ba,ruby ce ta dube ta tana cewa kin gani dai da idon ki ba,?wannan yanzu a ce a haka Da kwai wata mace da zata zauna a zuciyarsa,wani irin murmushi suryy ta yi me cike da manufofi. Kana ta ce",za muyi yadda na sanar dake kar ki damu,da ga haka suka fita.
A cikin wannan dare kuma shuda da dudu suka ziyarci tsaunin tsohuwa inda ta kuma basu sa a da tabbatar cikar burin kowannen su idan har suka kara dage damtse wajen habbaka fitinu da zubda jini kai dama duk wani aiki da za ayi Allah wadai da wanda ya aika,da kuma la.antar Ubangiji.
A cikin kwanakin Raihan bata kuma bari sun hadu haduwa ta daga Ni sai kai ba,ita da wazir, sai kuma aiki da ya fara rincabe musu saboda yawaitar fituntinu da kashe kashe da ake ta yi.
Abangaren Haidar ma tuni ya tasamma aiki da zuciyarsa da kuma ƙwanjinsa,(to sai dai muce Allah bada nasara malam Aliyu)
Haka ta wajen Abba yahya sosai ya da 'yandabarunshi da kuma matsayinshi ya kuma samun shiga jikin gwamna da niyarshi ta rufe duk wata hanyar cutarwa da ake shirin yiwa ɗan uwanshi ko kuma a kayi masa.
A bangare daya kuma wani shahararren masani akan iya aikin sirri kuma dan jarida me kwana aikin marasa gaskiya ya baiyana a cikin jahar ta su,a inda ya fara yiwa marasa gaskiyar yan kasuwa tone tone da ma yan siyasar da suke ta kokari gurin ganin cewa sun haye kujeru takarar su ta wannan shekarar.
Hankalin manyan kasa marasa gaskiya ya fara tashi akan wannan dan jarida da yakewa shafinsa ko nace jaridar sa lakabi da tree full Y trues,wasu irin bayanai ne suke bayyana ta shafukan sa boyayyu wanda ko kafi kusa naci baka isa yi masa kutse ba bare har ka canko wane ne,babu wanda yasan shi,
Macece?
Namiji ne?
Mutum ne?
Aljan ne?
Musulmi ne?
kafiri ne?
A ina yake?
Duk babu wanda ya sani, ba su san komai ba sai tonen sililinsa.sirrikan yan siyasa da manyan shegun masu dukiya yake tonewa,su kuma jam'i ai kwashe su kawai suke yi ba tare da jan zance ba,domin su kansu akwai shafin da yake tsoratar da su akan muddin basu dauki mataki akan su ba,to suma yana gab da tona asirin su, wannan dalili ne yasa basa jinkiri wajen kame su,hatta lauyaoyin da zasu zauna a kotu da su sai anbisu da nasu kashedin.
Lokaci kan Kani duniya ta san da zaman tree full Y trues talakawa sun sami abinyi kullum fatan su Allah ya bawa wannan bawa sa a akan masu sheke musu ya'ya da jikoki,
Ita kanta Raihan yanzu burin ta tasan waye wannan,shi yasa ta dukufa bincike ita da abu Huraira.
A bangaren Ahmad wazir chibado ba za ka san komai ba,dan sanin kansa sai Allah babu yadda za ayi ka gane halin da yake ciki akan wani abu,lamarinsa da halinsa daban suke da na sauran mutane,ko da a kallo ze yi wuya ka fahimci ainahinsa,
Muje zuwa yanzu ne za a fara wasan ku gyara zama dan jin wannan cukurkudaddan al'amari me matukar tsayawa a rai,shin rabi zata cimma binciken ta na gano wadda ta mamaye zuciyar Ahmad?
Aunty amarya fa?makomar Raihan fa?
Yaya batun bidiyo dake hannun RAIHAN?
Wanene shuda da dudu?
Shin me su shugaban jam'iyyar suke shiryawa Raihan dake amatsayin Rahim? Abba yahya zaiyi nasarar kare dan uwansa daga cin amanar da yake tsakiyar tunanin gwamna nayi masa?Abun da yawa fa ku dai ci gaba da bina sannu dan warware kullin dake kulle.....✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page21 ```
Wannan al'amari ne yasa gaba ɗaya gari ya ɗauki ɗumi,ko wane gidan jarida burinsu su gano waye tree full Y trues,sai ya zamana gaba daya yanzu 'yan jarida da shi suke kishi,sai ya lamarin ya koma tamkar ya yi musu allura,sai ya kasance ko wanne gidan jarida bincike suke akan masu kuɗi yan kasuwa da uwa uba yan siyasa,saboda basa son tree full Y trues ya riga su fidda labari.
Chibado's hause
Kaiwa kawai take tana kawowa kamar wadda ke jin zawo,shigowar suryy ne ya dakatar da ita,nufota tayi da sauri tana saurin rufe kofar tare da sa key,suryy kin tayar min da hankali tun da muka yi wayar nan najiki ba daidai ba hankalina ya tashi", zama suryy tayi tana dan goge fuskarta da hannunta, sai da ta ja yan sakanni duk rubyy ta damu da jin sakamakon binciken da tayi akan A wazir,duban rubyy ta yi sannan ta ce" rubyy akwai matsala fa"zabura rubyy ta yi cike da tashin hankali tana cewa gaya min kawai wacece? a ina take? Yar uban waye?.
Calm down mana rubyy ki saurareni nayi miki bayani", shiru ta yi tana saurarenta,suryy ta ce" babu abin da bincikena ya samo min sai sunan Rahim ,a yadda labari ya zo min wazir bashi da wani na kusa da zuciyar sa kamar Rahim ,babu dan adam din da yake kallo da idon kauna kamar RAHIM,to rubyy hakan yana nufin Rahim ne ya hana wazir ya saki a zuciyarsa kome? Idan ba haka ba meye dalilin? A yadda na samu labari Ma cewa a kayi Rahim shi yake fada da duk wata mace da ta kawo soyayyarta ga Wazir",wani miskilin murmushi ruby ta yi,kafin ta ce" duk nasan wannan suryy,me ye ya hada binciken mu da Rahim? Karfa ki manta Rahim namiji ne ba mace ba,dan haka ki cire shi daga cikin lissafinmu,duk wannan abun da Rahim yake kuruciya ce" kuma SOYAYYAR su da wazir Allah ne ya hadata,so muyi abin da yake gabanmu bani da damuwa da wannan Rahim ɗin ".
Wani kallon baki da hankali suryy tayi mata,kafin ta yi Murmushin da ke nuni da cewa akwai fa ƙura,ta ce"rubyy ba zaki gane ba,amma insha Allah kafin zuwan satin bikinku sai na binciko gaskiyar abinda ke akwai,sai na gano abinda ke tsakanin wazir da wannan Rahim ɗin,saboda naga ke ƙwaƙwalwar ki baya aiki,idan har abin da nake tunani shine yake tsakanin su to ki tabbata Gara wazir ya yi soyayya da mace akan SOYAYYA da namiji,wadda ta fi ta mace Bala i",daga haka ta mike tare da ɗaukar jakarta ta bude dakin ta fice,kusan mutuwar zaune rubyy ta yi tana maimaita kalaman suryy cikin ƙwaƙwalwar ta tare da tace su dan son gano manufarsu.
Alh Muhammad nurr hause....
Abbie Ni dai ka barni da mashin wlh nafi jin dadinsa,bana son mota, Abbie ya ce"haba Rahim kabar mashin din nan mana ka fara tuka mota amma ka dage kai sai mashin",hamma idi dake zaune yana aiki a laptop din sa ya ce"abbie ka rabu da shi mana tunda yafi jin dadin mashin din,ina tabbatar maka nan da wani dan lokaci zai nemi motar da kansa ko dan ya burge budurwarsa,cak aunty amarya ta tsaya daga kofar kiching din da ta sako kai dan fitowa hannunta rike da jog din da ta hadowa abbie lemon zobo, Raihan ma jikin ta ya so ya nuna alamun sanyi ,amma sai tayi hanzarin basarwa ta hanyar taya hamma idi din da cewa,kai Hamma Ni kam bazan yi budurwa ba ina kusa da auntyna da Hajiya goggo da abbie", hamma idi ya yi dariya tare da cewa to shike nan abbie kayi mana sheda duk ranar da yazo yana yar murya akan na ara masa mota zai je zance bazan bayar ba",na rike wannan cewar abbie yana yiwa aunty amarya sannu da hada zobon da ta yi, murmushi kawai ta yi ba tare da ta nuna musu taji kan hirar da suke yi din ba.
Dariya da shewa kawai kake ji a sashen na mama murja, gaba dayansu ne a sashen banda surukansu,saboda suma idan zasu yi tattaunawar sirri ba sa bari su biyo su sashen iyayen nasu,Affan ne ya ce" wlh mama ina jin dadin yadda abi ya bamu wannan damar kamar yasan shirin mu akan su,Hassan ya yi ƙwafa tare da cewa" bibiyar yaron nan nake sosai kuma ina gaf da cimma nasara,wataran sai dai kawai a shigowa da amarya da yan koranta gawarsa,daga nan kuma ta ubansa ta biyo bayansa ba,cewar momy ke nan ta faɗa cike da karsashi,shigowar hamma idi ne ya sa gaba daya suka yi shiru sai harara da suka fara binsa da ita,girgiza kai kawai yayi tare da yi musu fatan shiriya,gaida iyayen nasa ya yi ya juya ya fita,dama abun da ya kawo shi ke nan,yana fita suka dora daga inda suka tsaya,babu komai a kalaman su da fatan su sai sharri da mugun nufi.
________________
Wai waye wannan tree full Y trues din? Shugaban jam'iya ya za ayi mu sani? honorable sani dan ƙusa ,ya ce"gaskiya ba mu ga ta zama ba,dole ne tun kafin mutumin nan ya biyo ta kanmu mu san yadda za ayi mu yi maganin sa",to ta yaya za mu yi maganin nasa bayan ba mu san ko mai akan sa ba,cewar shugaban jam'iyya da yake cikin taron yan jam'iyar su ta gwamnatin dake ci a yanzu,(idan baku manta ba Alh sale da Dr sanate ba jam'iyyar su daya ba a jam'iyyar adawa suke,kuma boyayyar alaka ce tsakanin shugaban jam'iya da su, kuma kamar yadda suke zaman sirri da su Alh sale da Dr haka suke yi shida yan jam'iyar ta su wadan da suke macuta masu ha intar gwamnati da kuma son cutar da gwamna a ta bayan fage).
Alhaji Hamza ya ce" duk wannan surutun bashi da ma'ana,dan garin surutun ne bamu Ankara ba sai dai muji mu a fursuna,kawai yanzu abin da za ai shine mu gayyato manyan masana na'ura me ƙwaƙwalwa su yi mana kyakkyawan bincike ko za mu da ce" take kowa ya yi naam da shawarar sa,nan suka bar maganar akan gobe zasu tattaro yaran dan yi musu bicike a sirrance.
CHIBADO FM.........
Raihan na dakin daukar rahoto,bayan ta isar da sakon ta na yau,tattara komai ta yi ta fito,kai tsaye office dinta ta nufa,anan suka yi kicibus da abu Huraira shida Khalid,yauwa Rahim dama wajen ka muka nufa, Allah yasa lafiya Raihan ta faɗa idon ta akan abu Huraira dan ta fahimci ko ma meye daga wajen sa ne,dan yau kusan sati ke nan yana son su zauna su yi magana kamar yadda ya fada amma hakan bai samu ba,saboda aiki da ya dan cushe musu kwana biyu,lafiya kawai magana ne me muhimmanci zamu tattauna dan idan aka yi magana da kai kamar anyi da oga ne,idan ma kaje wajen sa cewa zaiyi muzo wajen RAHIM, Khalid yace mu shiga office din mana dan jarida uban zance", dariya su kayi gaba dayan su kana suka bi bayan RAIHAN.
Sosai Raihan ta fuskanci maganar da yake so su tattauna din me muhimmanci ce,shi yasa ta bashi hankalin ta kacokan,ina sauraren ka abu Huraira,ta faɗa tana kallonshi,dan gyara zaman shi ya yi tare da yin gyaran murya kana cikin nutsuwa ya fara magana,Rahim magana ce akan wannan tree full Y trues din ,dan gaskiya ya tsaya min a raina sosai,gani nake kamar ya kamata mu danyi wani kokari dan mu gano shi,gano shi da za mu yi ba dan ko mai ba ne sai dan samun cigabanmu da kuma kwarin gwiwarmu,domin na fahimci manyan kasar nan sunyi matukar shiga firgici da tsoro a akan sa,shi yasa nayi tunanin mu zauna mu yi tunanin yadda za ayi mu samo shi",zuba mishi ido Raihan ta yi na wasu yan dakiku kafin taja dogon numfashi ta fesar,cikin kaifin basirar da Allah ya bata ta ce" abu Huraira me ye ribar mu na san lallai sai mun sami wannan mutumin? Khalid ya ce" Rahim maganar abu Huraira abin dubawa ce,sai dai Ni kuma ina ganin a me makon mu tsaya bata lokacin mu akan neman sa dan mu hada hannu da shi,ina ga Gara mu kara himma mu dage damtse domin ganin cewa muma munyi aiki kamar shi,saboda idan har muka ce sai mun neme shi to sai nake ga kamar bamu cika burinmu na kawar da miyagu ba, kuma ba muyi amfani da karsashinmu da kwarin gwiwarmu ba,tun da munyi amfani da basirar wani ne can da ban da kuma aikin sa",dan tafi Raihan ta yi tana duban Khalid ta ce" Khalid kamar ka shiga zuciyata ka debo abin da yake cikin ta,dubanta ta mayar kan abu Huraira tace" abu Huraira banƙi shawarar ka ba,shawararka me kyau ce domin na fahimci abinda kake nufi,saboda nima da farko hankalina ya tashi da bullowar wannan mutumin dan har na fara kokarin bincike akansa,sai dai kuma ban samu komai ba baya ga dinbin takaici na rashin samun nasarar hakan,daga baya kuma sai nayi tunani irin na Khalid da fatan ka fahimce mu?jinjina kai abu Huraira ya yi fuskar shi cike da gamsuwa.
Sai magana ta biyu,ya faɗa idon shi akan Raihan da itama ta kuma bashi hankalinta, ya ci gaba da cewa akwai wani kokari da nayi akan wasu yan siyasa da suka yi badda kama a matsayin mutanen kirki,na samo kadan daga cikin bayanansu, wannan shine makasudin zaman namu",da sauri Raihan ta ce"su waye daga cikinsu?Dr sanate da Alh sale sai kuma shugaban jam'iyyar dake ci a yanzu,wanda abinciken da nayi na gano ɓoyayyar alakar dake tsakaninsa da yan jam'iyar adawa,hakan ya nuna cewa yaudarar gwamnan yanzu yake yana cin dunduniyarsa ta karkashin kasa",wani kayataccen murmushi Raihan tayi kafin ta ce"ashe ka fara aiki me kyau amma kake son mu bi ta kan wani? .
Girgiza kai abu Huraira ya yi kana ya ce"Rahim wlh tsoran mutanen nan nake ji kai kan ka kasan cewa duk wani dan jarida ko jami i ko wani da yake son gaskiya,basa tsira da rayuwar su a wajen mutanen nan,idan ka duba abin da ya faru da a s p jatau da d p o Kasim,da sauran irin su harma da halima,duk abin da ya faru da su ke nan sun rasa rayukansu ne ta hanyar san tabbatar da gaskiya",tabe baki Raihan ta yi sannan ta ce"abu Huraira tsoro ba na mu ba ne tun da har muka ji muka gani muka ce za muyi dan haka tun wuri ka cire tsoro domin aikin mu ba na matsraci ba ne",na sani Rahim amma zaka ce haka saboda kai baka ji abinda naji ba,kuma wannan dalili ne yasa na fara kawo shawarar mu nemo tree full Y trues,saboda mu bashi bayanai ya fitar tunda shi boyayye ne,kuma shi kansa tree full din ya boye kansa ne saboda abin