Showing 93001 words to 96000 words out of 189984 words

Chapter 32 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15627

jin tsoran wannan rana,ki taimaka ki cigaba da bani haɗin kai har zuwa lokacin da zan gano waɗanda suke son kashe minke",ta ƙarasa maganar cikin karyewar zuciya da sanyin jiki,a hankali Raihan ta shige jikinta tana mai jin tsananin tausayin mahaifiyarta,anya kuwa ba za ta gaya mata abinda su Abbie ke ɓoye mata ba?ya za ai ta cigaba da rayuwa a matsayin matar WAZEER ba da sanin mahaifiyarta jigon rayuwarta ba?anya ko zata iya boyewa kamar yadda su Abbie su ka ɓoye?wasu siraran hawayene suka ɓalle mata na tsananin damuwar halin da auntynta take ciki,gaskiya dole tayi magana da Abbie akan wannan al'amari tana bukatar Umminta tasan halin da ake ciki hakan sai yafi kawo kata kwanciyar hankali.




Ɗago kanta ta yi tana kallon fuskar mahaifiyarta cike da ƙauna da wani shauƙi ta ce",karki damu ummina zanyi duk abinda kike so Ni dai buri na kiyi farinciki dan Allah ki daina damuwa kinji auntyna", ta kare maganar da goge mata yan guntun hawayen da suka fara ɓata kyakkyawar fuskarta,"jinjina kai aunty amarya tayi tare da cewa ba zaki je wurin aikin ba?.




Tura baki tayi cikin ƙunƙuni ta ce",Hamma wazir ya ce ",kar na fito sai ya nemeni", murmushi aunty amarya ta yi kana ta ce",ina jin dadin yadda wazir yake kokari a kanki shi yasa na bashi amana kuma na yadda dashi akanki dari bisa dari,tashi kije kiyi wanka ki ƁOYE jikinki ki dauko kayan da Dr Sabo ya kawo miki dan naga kara cika kike gwara ki fara saka su tun yanzu, sannan ki saka wular kannan dan itama naga kwana biyu bakya son sawa,bayan kin san wannan gashin naki ba ɓoyuwa yake sosai yadda ya kamata ba",


Kai aunty amarya duk wannan bayanin kamar kin same Ni da yin ba daidai ba cikin irin shigar da kike so nayi?


Ba haka bane Raihan naga yanzu kullum kara girma kike halittunki har sun fara kai munzalin da baza su ɓoyu ba shi yasa nake ƙara shiri akan hakan",Tom shike nan in sha Allah zanyi fiye da baya. komai nawa zai kasance a kimtse kuma a ƁOYE kamar yadda kike so my aunty,ta karasa maganar da shigewa bathroom dan tsaftace jikinta.




Tashi itama ta yi ta fita zuwa dakin hajiyar agadex,ji take duk a takure take saboda sun saba rayuwarsu free,amma yanzu tun dawowar Abbie da kuma zuwan Hajiyar agadex ta shiga cikin wata irin takura ,saboda kullum kaf_kaf take da Raihan gani take kamar duk wani motsinsu akan idanun Hajiyar agadex da Abbie yake,uwa uba kuma ga wani dan takurar da ƙarfi da yaji ya shiga jikinsu da kyawawan halayensa,(hamma idi) ga su inna maimuna duk da cewa su bata damuwa da kusancinsu dasu,dan tana da tabbaci akan Inna maimuna da Abba yahya hankalinsu kwatakwata baya kansu bare har su saka musu ido,shima Hamma idi bata masa wani zato to amma dai ya kamata ace kullum tana cikin takatsantsan,ita fa sam ta kasa ganin dalilin zaman Hajiyar agadex a gidan nan dan dai kawai bata da halin cewa bata bukatar zamanta ne.da wannan tunanin ta kai har dakin hajiyar agadex ɗin.




Turus aunty amarya ta yi lokacin da ta fito falo ita da Abbie taci karo da Hamma idi da matarshi rukayya a saman dining wai sun zo yin break a nan.kokarin saita kanta ta yi ,sai ɗan duban gefan da Raihan take da tayi, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta saki ganin Raihan ɗin cikin shigar da tafi bukata tayi editing ɗin kanta sosai dan yanzu ta kware a wannan fannin, ayanzu ko wata aka kawo mata akace ta yi editing ɗinta zuwa namiji tsaf zata iya..............✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page31 ```






A bangaren su Alh ja'e da su sanater kuwa ,wani abun mamaki ne ya faru ,tun kafin su shiga cikin station din dpo ya samu waya daga can sama na umarnin cewa ya saki mutanen da ya kama kuma cikin mutunci da mutuntawa.




Wannan lamari bakaramin tsoratar da shi ya yi ba,shi din bawai baya son sakin su ba ne, a'a kawai yana tsoran shiga list din treefull Y trues,babu yadda yaso haka ya sake su ba tare da ya bari cincirindon mutane da yan jarida sun Ankara ba,dakyar suka samu suka kori jama a da yan jaridar da suke son ganin ƙwaf.




Tunda ya shiga office dinsa yake sintiri cikinsa cike yake da zawo saboda tsabar tashin hankali,tunaninshi ta ina zai fara warware wannan matsalar mezaicewa mutane da suke ta murnar kama su sanater?idan tree full y ya gane hakan wane hukunci zai dauka akansu?to kai ba umarni aka baka ba,cewar wani bangare na zuciyarshi, wannan tunani da yayi shi ya dan bashi kwarin gwiwar ci gaba da ayyukanshi.




*SHUGABAN JAM'IYA*




YAna gab da shiga jirgi ya zaro wayarshi dan kashewa gaba daya saboda baya son wani abu da zai iya dakatar dashi daga barin kasar.tesx yaci karo dashi har zai share sai kuma ya shiga dubawa,(kar ka je ko ina ka dawo mun kashe maganar babu wata matsala)ita abinda aka rubuta ke nan, sannan ta email aka turo sakon bai san daga inda sakon yake ba,shigewa jirgi yayi yana tunanin cewa gasar zare ake son hada masa don ya dawo a kamashi,dan haka ba tare da bata lokaci ba ya hada kan iyalanshi suka shige jirgi suka daga.




___________




Su Alh DR sale ma dai mamakin wanda yasa aka sake su suke,tunda sun san cewa babu wanda su kayi wa waya dan sanar da abinda ke faruwa,duk wadanda suke tunanin sune suka sa aka sake su sunyi magana dasu amma abin mamakin sai suce basu bane hasalima basu san ankamasu ba, wannan lamari ba karamin sakasu a caji yayi ba.






*SHUDAA..........*






Wata irin dariya ce ke fitowa daga matsakaicin falon me kama da gurnanin zaki,sai kuma daga can wata murya me babban sauti da karfin amo ta fara magana,an gaya mu ku mu shashashai ne da za mu bari ku shiga prixin,idan muka bari kuka tafi a bayan wa zamu ci gaba da laɓewa muna aikata laifinmu ,Ni shuda bazan taba bari ku tafi ba saboda kuna mun amfani, kudin babban bango ne agareni bayan tsohuwa me jini",hhhahhhhhahh ya kuma ɓarkewa da wannan shegiyar dariyar da sam bata da daɗin sauraro,duban yaransa ya yi tare da cewa kuje idan ƙura ta ɗan lafa ku samo min idon zawarawa guda goma kuma da ransu zaku cire ba sai kun kashe su ba",mun bika ogah shuda zamu yi biyayya akan abinda ka ke so ,tsohuwa ta kara maka karfin iko",batare da yace musu komai ba yayi musu alamar jinjina da hannu kana ya basu umarnin tafiya .






Abba yahya,kuwa tunda ya samu labarin nan ya shiga cikin zuzzurfan tunani, hankalinshi ba karamin tashi ya yi ba,duk sanda aka ce wani abu ya faru a cikin jahar nan ba kowa yake tunawa kuma yake hangeba sai dan uwansa,a cikin wannan yanayi inna maimuna tazo ta sameshi,zama tayi gefansa tana mai cire masa tagumin da yayi,cikin taushin murya irin na matar dake son kwantarwa da mijinta hankali ta ce",abban Bashir,dan Allah ka daina wannan zurfin tunanin kar fa kaje ka hadu da wata cutar ,me yasa baka son bin abu a sannu?janye tagumin ya yi tare da sakin wani kakkarfar huci kana ya dubeta ranshi duk a jagule ya ce", maimuna wallahi ina tsoran shu'umancin ur exsellency ina tsoran irin abinda yake shiryawa ɗan uwana", Inna maimuna ta ce",to ai dama dole a ji tsoran irin waɗannan mutanen da suke rufe ainahinsu ,wato a zahiri su din mutanen kirki ne amma a baɗini halinsu ko kare ba zai ci ba",jinjina kai ya yi yana ɗan rufe idanunshi da buɗewa a lokaci ɗaya, mainuna tunanina kullum bai wuce ta yadda zanyi na kuɓutar da ɗan uwana daga kaidin mugun aboki ba,yanzu bani da aiki sai na gadin rayuwar Nura,kai harma da ta iyalansa dan ina da tabbacin cewa rayuwar Rahim tana cikin hatsari,amma nasan abinda ya kamata nayi wallahi ba zan bari ya halaka dan uwana da iyalansa ina ji ina gani ba, Inna maimuna ta ce",nifa shi yasa sam bana son wannan aikin da Rahim yake saboda za a iya samun dama da mafaka a cutar da shi ta dalilin aikin",kar ki damu maimuna zan yi duk abinda ya dace indai akan ɗan uwana ne",ya fada yana tashi daga gurin,binshi ta yi da kallo cike da tausayinsa shida dan uwannasa.




____




Duban sa Raihan take kamar zata fashe idanunta sunyi ciki saboda tsabar tunzura,ƙunkuni ta shiga yi tana rufe idanuwanta da tafukan hannayenta saboda yadda yayi wata tsayuwar sarakai yana binta da wani shu'umin kallo wanda yake shiga loko da sakon jiki da jini yana bin ƙwaƙwalwa tare da direwa cikin zuciyarta,wani sanyi sanyi ta fara ji a jikinta saboda yadda kallon yake tasiri a gareta,ganin yadda tayin sai kawai yanayin ya tafi dashi,a hankali ya shiga takawa cikin wannan takunnashi na nutsuwa da nuna cewa shi ɗin me aji ne,yana karasowa ya yi wani irin sunkuyowa samanta yayi mata rumfa da faffadan ƙirjinshi yana ci gaba da yi mata kallon da take neman haukatata.


Cikin tura baki da kifkifta idanuwa ta ce",nikam ka rabu dani gida zanje,idan Abbie ya neme Ni me zance masa?

Kice masa kina tare da mijinki?yayi maganar yana mai kawar da fuskarshi gefe tare da zama daf da ita tamkar bashi yayi maganar ba,zaro manyan idanunta tayi baki bude cikin yanayin mamaki cike da yarinta ta ce",kanbu Abbie zancewa haka?to ai ko Baffa da hajiyar agadex da Hajiya goggo bazan iya fada musu haka ba",bai tanka mata ba sai tashi da yayi ya fita daga dakin,binshi ta yi da kallo tana kebe baki.






A hankali ya fesar da wani zazzafan huci yana mai dan murza goshinsa cikin yanayinsa na kullum da ba a gane ainahin zuciyarsa,zubawa wayar ido yayi yana mai jin ɗacin sakon da aka sanar dashi yanzun,wai an sake mutanen da Raihan tayi sanadin kamasu,numfashi ya kuma fesarwa ,kafin kuma cikin saurin da kazarkazar dinsa ya koma dakin da yabar Raihan.


Da sauri ta mike tsaye tana kallonsa ,duk da cewa babbar wata alama da zai nuna yana cikin damuwa ba,amma hakan bai sa Raihan ta kasa gane cewa da akwai wani abu ba,mu tafi yace mata yana juyawa,dan jim tayi sai kuma tayi saurin bin bayansa dan ttasan kadan daga aikinsa ya tafi ya barta a wannan gidan.




A kofar katon gate dinsu ya ajiyeta ba tare da yace mata komai ba,ganin haka yasa itama ta kuma kama kanta yadda bai tanka mata ba haka itama bata tanka mishi ba, tasa hannu ta bude kofar hatta zura kafarta daya a waje taji kamilalliyar Muryarshi yana cewa kar ki sake fitowa sai na nemi hakan zaki iya tafiya,wai me mutumin nan take nufi da ita ne?tambayar da tayiwa kanta ke nan tana mai ficewa daga motar tare da rufowa cikin dan yanayin tunzura,bai bar wajen ba sai da yaga me gadi ya bude mata karamar kofa ta shiga sannan ya ja ya tafi.








Fada yake wa securitys din tamkar zai ari baki,dan me zaku barshi shi kadai babu drever babu ku? Me ye amfaninku indai zaku dinga barinsa yana yawo shi kadai,to wallahi duk abinda ya sameshi Hasan rabu daky ba",abban rabi a ke nan idanunshi har wani ja suke saboda masifa,Abbu ne ya dakatar dashi ta hanyar dafa kafadarsa yana masa magana cikin lallami.




Haba Mustafha WAZEER fa ba ƙaramin yaro ba ne dan Allah ka rabu dasu zai dawo gida lafiya, innawuro da hayaniyar ta fito dasu gaba daya ta ce",wai Mustapha kana nufin kafini son wazeerin gida da kake wannan haƙilon? Wannan wane irin makahon so kake yi masa haka? Shuru ya yi yana muzurai kamar wanda aka ce masa wazir din ya yi hatsari,Abbu ne ya kamo hannunshi yana cewa rabu dashi innawuro don da yake masa ba matsala ba ne kawai dai ya dinga control dinsa ta hanyar da ya dace.






Juyawa rabi a ta yi tana zuba tsaki,duk komai akan idanunta ya faru,wani abu me kama da kishi taji yana yawo a zuciyarta,tun ba yanzu ba ta fahimci cewa abbanta yana Bala in son WAZEER don ko aurenta da shi da andaka ta abban nata da ba ayi shi ba,wai me yasa kowa yafi son WAZEER ne ? Dame yafi sauran ya'ya? Da abinda kika gani a tare da shi kema kike sonshi ,wata zuciya ta bata amsar tambayarta,tsaki tayi tana kuma jin kishin na karuwa aranta.






Innawuro ta dubi abban rabi a ta ce",bana son sakarci Mustafha daga yau kar na kuma ganin kasa yaran mutane a gaba kana musu fadan ba gaira babu dalili,su ba uwaye ne suka haifesu ba? Idan yace su taho ya zasu yi dashi? Kai baka san halin dannaka ba,sam wannan ba tarbiya bace su sauran yan uwanka haka kaga suna yi? .


Kiyi hakuri innawuro baza a sake ba in sha Allah,yana rufe baki suka fara shako ƙamahinsa da sautin nutsatstsan takunsa,a hankali ya yi sallama,bai shigo ba har sai da innawuro ta amsa masa kana ya ƙaraso tsakiyar falon inda iyayensa ke zaune.


Sannunku da gida,yauwa cewar su baki daya, innawuro ta ce",ina kaje ka tayarwa da abbanka hankali tamkar wani karamin yaro ya fita?ɗaga lumsassun idanunsa yayi waɗanda bakin gashi yayi kwance luf asamansu ya dubi gefan da Abban rabi a yake sannan a hankali ya ɗaga fatar leɓbansa ya ce",ina bukatar pravency ne,daga haka ya mike yaɗan rissinar da kanshi alamar biyayya sannan ya wuce saman shi.innawuro dawo da kallonta kan abban rabi tayi ta ce",to yanzu ka gamsu ko kuwa da sauran magana? Girgiza kanshi ya yi yana dan guntun Murmushi na jin kunya.




Yana ɗaukar abinda zai dauka ya kuma saukowa yayi musu sallama,bangaren Amminshi ya nufa,can yaci abinci suka ɗan tattauna kafin ya tashi ya yi mata sallama ya wuce bangarensu.




Lokacin da Raihan ta shiga falonsu , babu kowa,har zata wuce dakin aunty amarya sai taji alamun su a kiching,hakan yasa ta fasa shiga koridon da zai Kaita dakin aunty amarya.kichin din ta shiga da sallama,inna maimuna ce ta amsa tana cewa Barka da dawowa Rahim yau dai da alama kayi nisan zangon",karasowa Raihan tayi da murmushi kan fuskarta tana cewa inna maimuna yau kam nashiga rububi,sannunku da aiki ta faɗa tana dan bawa auntynta sumba a gefan fuskarta, yauwa kawai aunty amarya ta ce ta cigaba da tuƙa tuwon semon da take yi,ina hajiyar agadex ta faɗa tana duban inna maimuna?kaima ka san inda zaka sameta ai,cewar aunty amarya,inna maimuna ta ce",tana bangaren Hajiya goggo,ok bari naje na dan watsa ruwa na fito",a fito lafiya.


Nan ta barsu suna ci gaba da aikinsu saboda yau anan bangarennasu zasu yi dinner gaba daya har Abba yahya.




_________




Yana shiga ya ci karo da rabi a zaune a kujerar farko,ga dukkan alamu jiran shigowar sa take yi,tana ganinsa kuwa tayi saurin mukewa bakinta na rawa tace sannu da zuwa Hamma WAZEER ",yauwa ya amsa a hankali wanda ba daban tana kallon fuskarshi ba bazatasan cewa ya amsa ba ,dan Allah Hamma ka saurareni mintinan da zaka bani basu da yawa",ki fadi abinda zaki faɗa ina abunyi masu muhimmanci",ya fada ba tare da ya daina takun da yake yi ba,wani kakkauran miyau ta hadiya kafin cikin in inar da tazo mata alokacin ta ce",dama maganar aikine ko abbu ya yi maka maganar?gobe ki same bi a office", daga haka ya wuce tabbarta tsaye kamar wata kunki.


Har zata sa kuka sai kuma tayi saurin hadiye abinta ,tare da cewa WAZEER Hasan ƙara yi maka kuka ba sai dai kai kayi bazan ƙara bari zuciyata ta yi wahala akanka ba sai dai taka zuciyar ta yi ,nasha alwashin ko da baka soni ba to tabbas kaima bazaka samu abinda kake so ba, wannan alkawarinane.






*ABBA YAHYA*




Wata irin zabura ya yi bayan gama karanta sakon da aka turo masa ta email address,wata irin zufa ce ta shiga karyo masa duk kuwa da cewa bayan fankar dake kaɗawa a dakin har da na urar sanyaya guri wadda ke fitar da sassanyar iska me dadi ,dafe goshinsa ya yi yana mai zubawa fuskar wayartasa ido tamkar zai gano wanda yaturo sakon ta ciki.




Ka fara tanadar likkafanin da zaka rufe gawar dan uwanka da kuma ta iyalansa abu mafi soyuwa agareka,zaka fara dan dana ɗacin rashin ɗan uwa me zumunci kafin ka dan ɗani taka,dan wallahi nayi rantsuwa da Allah babu wani majibincinsa da zan bari a doron duniya balle ya kawo min cikas gurin kwatar hakkina. Da ɗaddaya saina ƙarar da duka ahlinsa domin nadan kowa idanunsa nakan abinda ya tara, dan haka ka shirya lokacinku ya fara mutuwa ta biyo ta kanku......






Waye wannan?anya kuwa ba wani ne daban ba bayan ur exsellency? Asanisa yasan cewa ur exsellency ne kawai yake da wannan burin a ransa shi ma kuma bai gama tabbatarwa ba yana yin bincike ne kawai dan san tabbatarwa ,dan yasan inhar bai tara hujjoji ba kaninsa bazai taba yadda ur exsellency zaici amanarsaba,lallai ashe yaki ne babba a gabansa dole ya farka daga baccin da ya tafi dan lalubo ta inda zai fara kare iyalan dan uwannasa,domin yasan duka yayansa babu wanda zasu kyale tunda sune masu dukiyar da koma waye yake tunƙahon zai ƙwace.


.to wai ma ta ina dukiyar Nura ko yace ta Raihan ta zama hakkinsa? Kai shi da kansa ya kulle dole yana bukatar nazari me kyau......✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page34 ```








A hankali ya shiga bubbuga bayanta batare da ya iya cewa da ita komai ba,memakon shiru sai wani kukan da ya kuma gocewa kamar dai dama jiran inda zata sauke shi take yi.


Bai ce komai ba har sai da ta yi ta gama dan kanta tayi shiru,cikin tura kanta ƙirjinshi ta fara magana,hamma akwai wanda nake zargi cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login