Showing 189001 words to 189984 words out of 189984 words

Chapter 64 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15632

ba a hannunmu take ba.


Raihan na bata miki rai ko?


Bakya son kishiya ko?


Kin fi so nayi Miki alƙawarin zama dake ke daya ko?


Girgiza kai ta yi sananan cikin sanyin murya ta ce," a'a idan son zuciya zamu bi haka nake so ,amma idan muka ture batun son zuciya ba haka nake so ba,Nima banson wannan kishin nawa yana takura min hayatty bani na sawa kaina ba ina kokarin dannewa amma hakan ya gagara kayi hakuri bazan kuma ba",


Rungumeta ya yi cikin so kauna da wani irin tausayi sannan ya ce", no habebty ba laifinki na gani ba,kawai nayi abin da ya kamata ace ko wane namiji ya yi ke nan,akwai manyan dalilan da suka saka na rabu da rabi a daya daga ciki shine wallahi Raihan duk na sake na hadaki da wata mace to tabbas zan iya tashi ran alkiyama da shanyayyen barin jiki domin bazan iya adalci ba, wannan bayanan ina yi miki su ne saboda ba a hannayenmu kaddarorinmu suke ba,Kinga bamu san abinda gobe zata yi ba,tunda komai yana wajen Allah assamadu lamyalid walam yulad," hayatty na fahimce ka maganarka gaskiya ce ko Nima zan iya samun sauki ta hanyar wannan kalaman naka da kuma addu'a daga bakinka", in sha Allah habebty,ya fada yana daukarta da cewa muje na bada tukuicin wannan kwalliyar,dariya tayi me sanyi zuciyarta na yin sanyi da samun miji irin wazer alhamdulillah ta fada a fili, ya amsa da Masha Allah daidai lokacin suka rufo kofa.






Washe gari aka yankewa abban rabi hukunci shida makarrabansa,sa arsa daya angano Khalid da ya gudu saboda shi,shi yasa ya samu sassauci ta hanyar yin shekaru ashirin a gidan yari suma yaran nasa haka duka aka yanke musu hukunci, suka tafi suna kukan nadama da rokon yan uwa gafara.




Su Abba yahya kuwa sai dai muce Allah kyauta makwanci domin kwanansu biyu suka ce ga garinku nan,


Surry ma ta samu sauki ba laifi, sun dawo gida a nan ne mahaifinta ya bada ita ga wani almajirinsa wanda shi da kansa ya ce yana so, dan haka ya bashi ba tare da wani ja ba,ita ma haka ta hakura saima godiya da suke masa saboda taimakonta yayi,rayuwa ke nan Allah yasa mu dace",




Rabi a kuwa haka ta gaji da naci ta hakura dan daga karshe hanata shiga gidan yasa a yi har office dinsa saida ya hana a hanata shiga,dole taga uwar naki ta samu ta daidaita da wani dattijo me mata uku ita ce ta hudu aka lallaba aka kaita ta fara zaman hakuri,(kin kasa yin hakuri da daya gashi yanzu kin kare da uku) dama haka rayuwar take.


Yusuf ma tuni ya kai kudinsa aka sa masa rana da shukra duka za a hada auren da yayyayenta, jiddo khalil zai aura abu ya koma auren gida Masha Allah,zumunci dai ya kuma kulluwa tsakanin gidajen biyu,sai fatan Allah ya dorar da zumunci Tare Da farin ciki.




Su Raihan sarakan soyayya tunda ta samu ciki take shan tarairaya Baga wazer ba Baga innawuro ba Baga Ammin da maminta ba,kai hatta hajiyar agadex sai da tazo ta zauna wai renon ciki,amma ko kwana uku bata yi ba ta tsere saboda taɓarar Raihan da yadda yake biye mata ko kunyarta basa ji dole ta bar musu gida.




Komai yayi farko yana da karshe,daidai lokacin da aka yi bikin su shukra a lokacin ne kuma Raihan ta sunkuto kyawawan tagwayenta masu kama da wazer kamar an tsaga kara,ba sai nace muku komai akan shagali da murnar da akayi ba,yara sunci sunan Abbu da Abbie saura Ammi da mami cewar wazer,


Anyi zabe kuma his excellency ya lashe sai dai fatan nasara a rayuwa,dama duk wanda ya rike gaskiya zai ta ganin daidai a rayuwarsa Allah ya bamu ikon kwatanta gaskiya.




Gidajen uku sun hade sun zama tsintsiya madaurinki daya babu mai jin kanmu,tamkar wani mummunan abu bai taba faruwa ba.




Raihan kam ta kama wazer yadda ya kamata,ta hanyoyi masu dama wa'danda na lissafa kadan daga cikinsu,tare suke tarairayar junansu suke tattalin junansu ,ko fada su kayi basa nisan zango suke shiryawa saboda sun san kansu kuma sun fahimci junansu sun san halin junansu,ga yaransu abin sha'awa suna tattalinsu ta hanyar da ta dace duk da cewa basu cika zama gidan ba.




Tsaye take bakin madubi tana gyara dogon gashinta,shigowa yayi cikin kamalarshinnan da sallama bakinshi,amsawa ta yi tare da mika mishi brush din da take gyara kan", karba yayi fuskarshi cike da wani irin Murmushi dake nuna cewa yana cikin farinciki,ya ce", yarinya tasa komai na iya kamar wata mace harda su girki,kasancewar daga kiching yake", tura karamin bakinta ta yi tana cewa ai kaine kace babu abinda zanyi saboda kar yayanso su jigata Bama Ni ba", zagayeta yayi da hannayensa yana shafa dan cikinta da ya fara tasawa insha Allah yan biyu zaki kuma haifa Ammi da mami ke nan", Amin ta amsa tare da juyowa ta kama fuskarshi ta sumbaci labbanshi sannan ta ce", tunda Ammi ta kwace wadancan dole muyi addu'a mu samu wasu", su dinma na Mami ne", ya fada yana kissing bakinta, ok haifa musu za mu tayi muna basu? Arzikin ke nan my angel nets kuma sai mu rike ko?


Bai bari ta amsa ba ya dauke ta cak ya dora bisa gadon yana cewa zo kiji wata magana sirrice bana so Fatima y Adam ta ji bare ta je ta cigaba da bazamu a duniya mu rufe kofa lada ya isa haka ,a barmu mu huta,daga haka ya rungume matarshi yana cewa Allah ya yi miki albarka RAIHAN alhamdulillah da samun mace ta gari,Masha Allah da samun miji na gari ta fada tana rufe su da bargo,


Nima fitowa nayi cikin jin kunyar kamani da su kayi ina satar labarinsu,to nima dama na gaji alkur,an




Masoyan ɓoyayyiyar Raihan ko nace masoyana ina yinku ina muku sonso alherin Allah ya kai muku a duk inda kuke.


Alhamdulillah


Alhamdulillah


Alhamdulillah


Allah ya yafe mana kurakuren da mu kayi ya bamu lada akan daidai sai mun hadu netx book WASU ALƘALAN...✍🏽

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login