Showing 84001 words to 87000 words out of 189984 words
Chapter 29 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
bata san yana yi ba,dan har yanzu akwai haushinsa me girma a ranta,duk da cewa ta kasa gane dalilin fushin nata akan aurensa da yar uwarsa rabi,wata yar kwallar da ta saba zubo mata a duk sanda ta tuna hakan ta cika idanunta kokarin sharewa ta yi tana mai daidaita kanta dan gujewa tambayar abokan aikin ta.
Yau din ma dai aiki su ka yi sosai, sun fitar da manyan labarai wanda kusan gaba daya sun danganci yan siyasa da kuma siyasar kanta, wannan shine ya dauke mata hankali har zuwa lokacin Sallah Sannan suka dakata da karbar sakonni tare da fitar da bayanan da a ka kawo mu su,a office dinta ta yi sallah, sannan ta fita suka wuce wajen da suka saba cin abinci ita da su salim.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kara lumshe idanunsa,yana mai kokarin dauke idanunsa daga kansu,wani abu yake ji yana taso masa akan fitar da su kayi ita da su salim,duk kuwa da yasan cewa ya bata umarnin zuwa office dinsa a wannan lokacin,kai ba ma wannan ba ai yanzun ya ci ace ta daina wannan mu amalar da su salim tunda dai tasan matsayinta ya sauya zuwa matar aure,idan su ba su sani ba ai ita ta sani,huci me zafi ya fitar tare da komawa saman kujerarsa ya kwantar da kansa tare da lumshe idanun sa,zarazaran gashin idanunsa suka yiwa idanunsa rumfa,numfashi kawai ya fesar ransa duk babu dad'i .
RAIHAN kuwa tana sane daga wajen cin abinci ta yi ficewarta,ba gida ta nufa kai tsaye ba,wani aiki ta fita ba tare da sanin kowa ba,saboda bata yadda da kowa ba dan a halin yanzu akwai wanda take tunanin yana musu zagon kasa a cikin group dinsu,shi yasa yanzu duk abinda zata yi takan yi da taka tsantsan tare da lura da dukkan su.
__________________
Alh sale da shugaban jam'iyya sai Dr sanate,da sauran membobin da suke kungiya daya,kamar su Alh ja'e da barrister yunus,da sauran kannanun ministoci.
Barrister yunus ne ya dan yunkura tare da yin gyaran murya ,ya ce",gaskiya Alh sale ya kamata mu daina wannan jiran gawon shanun,kunga har yanzu wanda muka sa ya yi mana aikin nan babu wasu manyan bayanai da ya samo mana, Sannan kuma gashi lokaci sai tafiya yake a kowane lokaci wannan shu'umin tree full Y trues zai iya bankado sirrikan da muka jima da rufe babinsu,zai iya binciko manyan sirrikan mu da muke fatan dauwamar su a rufe har kasa ta rufe idanunmu babu wanda zai san da su.to amma yanzu naga wankin hula nema yake ya Kaimu dare kuma duk laifinku ne,dan Bama gari bai kamata ku bari komai ya nemi lalacewa ba",tabbas maganar ka tana kan daidai, cewar Alh ja'e,ya cigaba da cewa dan ba ma nan ba shi yake nufin tunaninmu da hankalinmu baya nan ba,amma tun da ku kun gaza yin komai saboda kuna tsoran karamin yaro to mu za muyi duk abinda ya kamata duk da cewa ba mu shiga cikin video ba",wani irin kallo shugaban jam'iya ya watsa musu kana a dan fusace ya ce", haba Alh ja'e barrister me kuke nufi da irin wannan kalaman naku,shin ko kun manta mu din su waye a cikin wannan tafiyar?
To idan kun manta ya kamata kuyi gaggawar tunawa,ku sani cewa mu duk abinda za mu yi sai munyi tunani mun gano makomarmu da abinda hakan zai haifar mana,babu irin tunanin da ba mu yi ba,karfa ku manta idan muka kashe yaron nan ba ku san in da ya kai camarar nan ko wanda ya bawa ba dan haka mun kashe maciji ne ba mu sare kansa ba,ko na ce mun bar baya da kura, sannan kuma idan ba mu yi takatsantsan gurin bibiyyarsa ba shima za mu kwantowa kanmu kura kasancewar shigowar wannan hatsabibin tree full Y trues,dan haka Ni ina ga ku yi hakuri da matakin da muka dauka sai dai idan da akwai wata shawarar makamanciyar matakin da kuke kai ku kawo saboda karawa aikin sauri",jin jina kai Dr sanate da Alh sale su kayi suna duban juna alamun dai kara tabbatarwa da yan uwansu abin da shugaban jam'iyyar ya fada haka ne babu kuskure,a nan dai yan cece kuce suka balle daga baya kuma duk suka nuna gamsuwar su akan matakin da aka dauka din tare da kawo wasu yan shawarwarin da zasu karawa dan leken asirin su kaimi da saurin samun nasara,daga nan kowa ya watse da yar faragabar abin da zai iya biyowa baya.
RUBYY........
Da sauri ta rungume sury tana ci gaba da kukan da har yasa Muryar ta dashewa,kamata tayi suka zauna kafin ta dubeta cikin nuna tausayawa ta ce",rubyy me kuma ya faru ina tunanin komai ya wuce tunda kinriga da kin zama matarsa ko ba haka ba?da saura wlh suryy da sauran rina a kaba komai ya kuma dagulewa Ni da nake neman soyayya amma sai ga shi san zuciyata ya jawo min na rasa damata gaba ɗaya,a nan ta bawa suryy labarin abinda ya faru a daren jiya a ya yin da wazir ya sameta ba cikakkiyar mace ba.
To sai me dan ya same ki ba a cikakkiyar mace ba?, da sauri rubyy ta kalleta idanunta shabeshabe ta ce", suryy ko dai baki ji abin da nace miki sosai ba?tabe baki Surry ta yi kafin ta ce", Ni ko naji abinda kika ce dama abinda hakan yake nufi sai dai kuma wannan ba shi ne zaisa mu karaya har mu fara tunanin faduwa ba, rubyy ki kwantar da hankalin ki tun da kika sako Ni cikin rayuwarki to kuwa tabbas Saina tabbatar da farincikinki ta hanyar samo miki mafita akan damuwarki,shi yasa kika ji na ce sai me,saboda Ni wannan ban dauke shi a komai ba,shi din kika san me yake yi a waje ai shi namiji me kyau da aji ba a shaidar sa,dan kuwa ko shi bai bi su ba su zasu bishi kuma komai ajinsa sai ya sauke kai agaban mace,bare kuma ke da kike matarsa ina tabbatar miki da cewa wazir sai ya zo hannunki kinyi yadda kike so dashi ba kuma da boka ko Malam ba,ke dai kawai ki bani lokaci ki kuma kwantar da hankalinki, sannan ina so ki sa shi ya baki aiki a gidan tv ku dan hakan shi zai bawa shirinmu damar tafiya daidai yadda muke so",ajiyar zuciya rubyy ta sauke tana jin damuwarta na raguwa,cikin nutsuwar data fara samu ta ce",to sury ta ya zan nemi aiki a wajensu bayan ba abin da na karanta ba ke nan, sannan kuma ba magana yake min ba duk ta yaya zanyi hakan?
Murmushin samun nasara suryy ta yi kana ta ce",haba Ruby ta inda aka hau ai tanan ake sauka ki samu Abbanki ki sanar da shi idan bai yadda ba sai ki nemi Abbun nashi nasan shi ba zai ki yadda ba,ina tabbatar miki da cewa ba karamar nasara zamu samu ta wannan hanyar ba,dan haka sai ki yi kokari kuma dan ba abin da kika karanta ba ne wannan ai duk me sauki ne karfa ki manta a bu naku ne dan haka babu abinda zai gagara ke dai ki gwada kar ki tsaya sanya", ta faɗa tana saba jakarta tare da miƙewa tsaye, rubyy ta yi dariyar farinciki ta ce shike nan ƙawata zanyi duk yadda kika tsara kuma nasan ba zan sami matsala ba".daga nan Surry ta fita ruby na bin ta tana dan raka mata har sai da suka dangana da kofar falon sannan su ka rabu.
Da sauri suryy ta shige dan sahun da ta barshi yana jiranta,fuskarta tarwai kana kallonta zaka san cewa tana cikin farin ciki,tana sane ta haɗawa ruby hanyar haduwa da ciwon zuciya,dan ta tabbatar da cewa idan rubyy ta fara aiki a inda zata dinga ganin Raihan da yanayin muamalarta da wazir to kuwa tabbas zata gane ko mai daga nan kuma wasan zai fara , Ruby ba zata taba iya jurewa Raihan ba shi kuma wazir ba zai taba iya jurar wulakanta Raihan ba,zata lalata komai idan ta lalata muamalar auren ruby da wazir sai kuma ta dawo kan Raihan wanda take ganin ba zai mata wuya ba,saboda Raihan ragowar maƙiya ce zagaye take da yan farauta dan haka bata da matsala da wannan.
Sai misalin karfe biyar Raihan ta koma gida,sam ta ki bari tunanin laifin da ta yiwa wazir ya kashe mata jiki,hakan yasa tana shiryawa ta bi hajiyar agades bangaren Hajiya goggo dan debewa kanta kewa da kuma tunanin wazir din da ya hana zuciyar ta sakat.
Shima sai wajen karfe biyar din ya koma gida,dan abinda ya hana shi tafiya Raihan din ce a tunanin shi zata dawo amma har ya taho baiji duriyarta ba,dan tsuka ya yi yana jin damuwar hakan aran shi,ji yake kamar ya hana ta aikin gaba daya sai dai kuma idan ya tuna burinta da aikin da tuna irin damuwar da zata shiga sai ya ji tsoron hanatan,to amma fa tabbas zata ci gaba da irin haka ko mai zai iya faruwa da aikin nata,da wannan tunanin securityn sa ya bude mishi kofa tare da sanar da shi karasowar su gida.
____________________
Kai wanene?kuma me yasa ka nemi zama da Ni?matar da take zaune fuskarta sanye da facemask da bakin glas ta faɗa tana mai tsatstsare mutumin dake gabanta da ido, murmushi ya yi tare da cewa me kike ci na baka na zuba tun da na neme ki ai kin san cewa Ni din abokin tafiya ne na hakika kuma Ni din me nasara ne wata kila ma nasarar dake tare da Ni tasa nasarar ki ta ta shi daga suman da ta yi",zuba mishi ido tayi kafin ta kyalkyale da wata muguwar dariya nuna shi ta yi da yatsa tana cewa amma wlh ka bani dariya to amma dai ba zan katse maka hanzari ba ina sauraron ka inji da abinda kazo",
Jinjina kai ya yi yana mai ɗan kara duba wajen da suke, sai da ya tabbatar da tsaron gurin kafin ya yi gyaran murya ya ce",ina so ki bani dama mu hada hannu domin kawar da mutanen da suka zama shamaki ga burikanmu na son zamowa shahararrun masu arziki wadanda duniya zata dama da su",sosai take kallonshi tare da al'ajabin shi da tunani akan shi barkatai.
Nasan tunanin da kike kuma bana so ki wahalal da kanki gurin tunanin yadda aka yi nasan cewa ke ce kika nemi kashe Raihan tun tana yarinya ,kuma.kece sanadin da yasa uwar Raihan ta boye halittarta ta mace ta bayyanawa duniya ita a matsayin namiji",yanzun ma duban shi take yi kamar idanunta za su fado ranta fal mamaki,sannan kuma tana jin cewa lokaci ya yi da dama tazo mata a karo na biyu wadda ba zata yi wasa da ita ba................✍🏽
[12/21, 12:40]: *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page29 ```
Kallonta yake shima cike da son fahimtar yadda zancan sa ya karbu a wajenta,sai dai bai gano komai ba sakamakon baya iya ganin fuskarta a bayyane.
Murmushi ta yi wanda yake kunshe da ma anoni masu tarin yawa, sannan ta ce",na amince da bukatar ka sai dai har yanzu baka sanar da Ni manufarka da dalilinka ya yasa kake so mu hada kai da kai dan cimma burinka ba, sannan kuma ban san yaya aka yi muka hada tarayyar da har zamu cimma nasara a kan sa ba",ba tare da ya ce mata komai ba ya zaro hoton da yake rike da shi a hannun sa ya nuna mata,duk da cewa tana cikin facemask hakan bai hana shi ganin irin razanar da ta yi da ganin hotan ba,nuna hotan take da yatsanta har yana rawa ,cikin rawar baki ta ce", wannan din shine dai da na sani ko wani me kama da shi ne?,shi ne dai wanda kika sani,mayar da hotan ya yi sannan ya ɗago yana dubanta a lokaci daya kuma fuskarshi na sauyawa da wani irin fushi da ya fara tasowa tun daga kasan ransa, ya ce",kar ki tsaya tunani ko mamaki kamar yadda nima ban tsaya tunani da mamaki ba a lokaci da na gano ke ce makashiyar Raihan,dan haka ina so ki rufe bakin ki kawai mu dora daga inda kowannen mu ya tsaya,bai saurari cewarta ba ya ci gaba da cewa,zamu fara shirin mu kamar haka ya nuna mata wata doguwar takarda tare da dage girarsa guda daya irin dai na yan duniyar nan mara sa imani, jinjina kai ta yi tana bin shi da kallo,shi ke nan zaki iya tafiya ya fada yana shigewa cikin wajen kamar ba da shi ne suka gaba tattaunawa ba.
Dan jim ta yi tana kallon takardar da ya bata da jerin sunaye da cikakken bayani akan ko wane tsarin sa,wanda kallon su kawai take yi ba tare da tana fahimta ba dan kuwa har yanzu bata fita daga shock din abin da ta ji kuma ta gani ba,da kyar ta samu ta yakice tambayoyin da ke ranta ta fita daga wajen cikin takun da take yin sa da rashin laka.
Hhhhhhhh.katuwar dariyar da ta cika duhuwar dajin ke nan,wanda sautin ta yake fita da wani irin amo me karfi mara dadin saurara,bayan shudewar mintuna biyar sannan dariyar ta tsaya hayakin da ya turnuke wajen ya fara washewa a hankali har Saida ya gushe gaba daya,sai ya zamana wutar da ke ci ce kamar ana babbaka mutum ta fito tarwai a tsakiyar mutum biyar da suke gewaye da ita,cikin wata irin murya me tsananin girma da karaji tsohuwa ta bude wangamemen bakinta wanda hucinsa ke fita da wani irin hayaki kamar me shan shisha ta ce",ba komai ne yasa na kira ka ba dudu fa ce na sanar da kai cewa ka samu masu yi maka yakin sunkuru a bangaren duhuwar da idanun mu ke gani,duk da cewa har yanzu jini bai gano ko mai ba,to amma ina tabbatar muku da cewa an samu manyan shu'uman da suke da cikinsu tun tsawon shekaru,kuma su zasu yi muku yakin fili,mu kuma sai mu cigaba da yin duk abin da ya kamata akan siyasar ku da ta yadda abin zai ta fi ba tare da mun samu tangarda ba,dama wannan matsalar ita ce ta tsaida komai akan aikin mu na karbar kasar nan,to yanzu tunda muna da masu ɗauke mana hankalin su ba mu da matsala ta bangaren aikinmu ,mu dai kawai abin da za mu iya shine idan mun gano wata matsala mu yi saurin kauda ita.
Cike da tsananin biyayya suka rissinar da kawunan su ,suna cewa mun gode ya shugaba,mun san cewa inda ke ba za mu fadi ba,kuma ba za mu tagayyara ba,mungode tsohuwa me share mana kuka,(a gidan banban ku ta zama me share muku kuka, Allah dai ya shirya wadan da suka bata Amin).
______________
Tsaf ruby ta shirya ta nufi bangaren Abbu, cikin ladabi ta gaida Ammi suka dan taba hira ita da shukrah ,kafin nan ta dubi Ammi cikin dan jin nauyi ta ce",Ammi Abbu fa?cikin sakin fuska Ammi ta ce",yana falonsa kuje shukrah ki rakata sai ki dawo yanzu na baro shi idansa biyu ",to Ammi shukrah ta faɗa tana yuunkurawa....
Da sallama suka shiga falon,yana zaune yana kallon tasharsu ta chibaɗo tv,amsa sallamar ya yi yana fadada fuskarshi da fara a,rabi a ce ku shigo mana",ya fada har yanzu fuskar shi da murmushi,juyawa shukrah ta yi ita kuma rabi a ta shiga ta samu gefan shi ta zauna,kanta a kasa ta gaida shi,amsawa ya yi ya kara da tambayar ta yadda zaman na su yake,har zata saki baki sai kuma ta tuna a gaban wanda take dole ta hakura ta maida maganarta in da ta fito,dole ta maye gurbin maganar da ba shi tabbacin suna lafiya babu wata matsala.
Wajen mintuna biyu ta kasa cewa komai,fuskantar hakan da Abbu ya yi ne ya sa shi maida hankalinsa kanta yana cewa rabi'a da wata matsala ne naga kamar da magana a bakinki ko?jin jina kai ta yi kafin cikin taro karfin hali ta fara zaiyana masa dalilin zuwanta cikin tsari kamar yadda kawarta suryy ta tsara mata.
Dariya Abbu ya yi irinta dattijon kirki kana ya ce",haba rabi akan wannan maganar ne kika tsaya kina dta nuku_nuku?
To indai wannanne kar ki damu in sha Allah idan AHMAD din ya shigo zamu yi magana sai asan bangaren da ya kamata a baki tunda ba bangaren ki ba ne aikin jarida,kar ki damu ba zai gagara ba",wata ajiyar zuciya ta saki a boye kafin ta shiga godiya cikin nuna girmamawa,cike da farin ciki ta koma bangarenta , dan ko bangaren innawuro ba ta je ba,sauri kawai take ta sanar da suryy wannan kyakkyawan albishir.
CHIBADO' FM......
Ganin har lokacin tafiyarsa Raihan bata dawo ba shi ya bashi tabbacin cewa tana sane ta yi hakan,tabe baki ya yi cikin rashin nuna damuwar hakan.
Yana shiga gida bai ko kalli inda rabi take da wani kwalliyarta ba,ya shigewar sa daki....
Sai da ya Shirya cikin doguwar ash din jallabiya me bin jiki,ya fito yana takun nan na shi me cike da kasaita,waya ce a hannun shi yana yi, amma ba za ka taba cewa waya ya ke ba saboda yadda ya yi shiru yana sauraren wanda suke wayar da shi,yanzun ma da kallo rabi ta bishi tana hadiyar yawu,yadda ya yi kyan nan ji take kamar ta kwana tana juyi a kirjin shi,hadiyar yawu ta kuma yi tana kallon yadda jallabiyar ke wani kwanciya a jikin shi tana bin fatar jikin shi.
Yana fita ,ta saka kuka tana jin duk wata tsiga dake jikin ta na tashi,babu abin da take so take muradi a yanzu irin ta ji ta a duniyar da wazir ya saka ta a daren jiya,shin yanzu lefinsa zata gani ko kuma laifinta?me yasa bata taɓa tsayawa ta yi tunanin wannan rana ba?me yasa bata taɓa bin maganar innawuro na karantar halayyar wazir ba?tabbas da ta yi hakan watakil ta gano cewa yana da matukar tsantsanin mazinaci da kaucewa hada guri da shi bare kuma shinfida ,ta sani cewa yanzu abu ne