Showing 168001 words to 171000 words out of 189984 words
Chapter 57 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
dakin ba tare da kowa ya sani ba,Turus Bashir ya yi ganin dakin a kone kurmus da alama ma bai jima da konewa ba,kauri da yahakin da dakin yake yi yasa Bashir saurin fitowa daga dakin yana maida nunfashin da ya rike tun shigarsa dakin.
__________
Daidai lokacin da wazer yake yin fakin a harabar gidansa sakon su Dady da na Yusuf suka shigo a lokaci daya,bai duba ba ya bari har sai ya shiga gidan sai ya duba a nutse,daukar Raihan da bacci ya dauketa ya yi tare da rufe motar da gidan gaba ɗaya,sannan ya shiga falon dauke da Raihan a kafadarsa.
Kwantar da ita ya yi a nutse,sanan ya zauna a gefenta yana duba wayar da sakonnin suka shigo.
Na Yusuf location din inda haidar yake ne,sai na su Dady da yake dauke da ainahin Muryar ogan Surry.
Tashi ya yi zai bar dakin sai yaji hannun Raihan ta riko shi,juyawa ya yi yana kallon kyakkyawar fuskarta a tunaninshi ko cikin bacci ne amma sai yaga idanunta a bude tana kallonshi, akwai alamun bacci a idanunta hakan yana nuna cewa yanzu ta farka ke nan,dawowa ya yi kusa da ita ya zauna tare da daukar kanta ya dora kan cinyarsa,a hankali ya shiga shafa fuskarta zuwa wuyanta yana mata susar da tasa ta lumshe idanunta, kafin a hankali cikin sanyin muryarta ta ce", me kake boyen?.........✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page63 ```
,,,,,,,Babu abinda na boye miki don son raina,zan gaya miki komai amma da fari ki min alkwarin ba zaki tayar da hankalinki ba",in sha Allah ta faɗa cikin mutuwar jiki,gyara mata kwanciya yayi a jikinsa ,sannan cikin nutsuwarsa dake tare da shi ko da yaushe ya bude baki ya fara bata labarin komai da komai,salon da ya yi amfani dashi gurin bata labarinne ya hanata shiga wani hali akan lamarin yangidansu,babu labarin da yafi jijjigata kamar na inna maimuna domin kuwa har ga Allah tana son inna maimuna dan itama ta nuna mata so duk da cewa na karya ne,tasha mamaki da yakasance itace sanadin da yasa tayi rayuwa a matsayin namiji,me yasa duka suka kasance masu son zuciya? Me yasa ba a samu wani daga cikinsu ya zama na kirki ba? Tambayoyin da ta yiwa wazer ke nan idanunta na zubar da hawayen bakinciki,hannu yasa yana share hawayennata sannan yace", kaddararsu da rayuwarsu ce tazo a haka,son zuciyarsu yazo daya miji da mata,shi kuma da ya tsotsa wannan shine kawai, Raihan shi butulci wani abu ne da yake hade da son zuciya da kuma hassada,ma ana ,sai kana da son zuciya kake yin butulci shi kuma butulci ya samo asali ne daga hassada, Allah Ubangiji ya kare mu da wadannan abubuwa", Amin ta faɗa,yanzu saura mutumin da ya sace Mami jikina yana bani cewa hamma Affanne", karki saurin yanke hukunci wannan bincikene zai bamu tabbaci bamu da matsala tunda gashi an turo Muryarsa ta asali ya fada yana daukar wayar da su Salim suka turo Muryar,kunnawa ya yi tare da jingina bayanshi da makarin gadon dan kara samun nutsuwar fahimtar me Muryar.
BASHIR dai ya rasa inda zai saka ransa saboda ya gwada kiran tsohuwa yafi sau shurin masaki amma shiru babu ita babu hayakinta,tamkar zaiyi hauka haka yake ji,dole akwai abinda ke faruwa,ya faɗa yana gwada nomber ɗaya daga cikin abokannansu na ƙungiyar,sai dai abin takaicin ya kira wajen mutum biyar amma duka babu wanda yasamu, wannan dalilinne ya kuma tayar masa da hankali,zufa yake yi kawai tamkar yana cikin tukunyar gashi,bacci kam ranar babu shi a idon Bashir.
Inna maimuna.......
Tun tana daurewa zafi da sauro har abin ya fara cinta, ta shiga soshe soshe da fifita da hannu,zuciyarta da rayuwarta duka a ƙuntace,bata iya daurewa ba sai da ta fara zubar da hawayen bakinciki da kuncin da take ciki,duk da haka fa zuciyarta bata karaya akan daukar fansa ba,ji take ko yanzu ta samu dama sai ta ida karasa abinda ta fara,saboda wannan shine mafarkinta tun tana yarinya karama.
A cikin wannan daren Yusuf ya dauki jami'an tsaro suka tafi karshen gari inda gidan sirrin Abba yahya yake, take a ka kame Duka yaransa, suka dauko haidar da numfashinsa yake tsakanin rayuwa da mutuwa,kai tsaye asibiti ya nufa dashi Dr sabo da yake jiran karasowarsu ya karbe shi da taimakon sauran likitoci,cikin kankanin lokaci aka fara yunkurin ceto rayuwarsa.
___________
A bangaren rabi a kuwa kwana tayi da shirin zuwa gidan su Surry saboda a yanzu babu abinda take bukata sai wazer wata irin soyayyarsa ce ke dawainiya da ita,tamkar zata wuce da numfashinta,shi yasa ta bar batun kasheshi yanzu hanyar shiri take nema,zaman da tayi bata ganin ko gilmawarsa ba karamin azabtar da ita ya yi ba,ita bata taba sanin tana son wazer irin haka ba sai yanzu da basa tare ji take yi bazata iya rayuwa idan babu shi ba.
*Abba yahya.....*
Tunda hajiyar agadex ta rufe shi a dakin yake gwada siddabarunsa ko zai samu ragowar wani abu,amma ina tun yana sa ran zai iya fita daga gurin ta hanyar tsafinsa har ya fara sarewa,gaba daya ya rasa wane irin tunani zaiyi shin nadama ya kamata ya yi ko ci gaba zaiyi da gwada dabarunsa? Tsinuwa dai hajiyar agadex tasha ta babu adadi,mafita kawai yake nema ya bar gurin saboda yasan indai ya fita Bashir zai iya taimaka masa tunda shi har yanzu da sauran rufin asirinsa,gyangyadi ne ya fara dibarsa saboda rashin bacci da yake fama dashi a kwanakinnan,sai dai zunbur ya tashi saboda kukan yara da ya kaure dakin kowa da kalar nasa,kafin ya dawo daga gigitar da ya shiga sai ga inuwar mutane ta fara gilmawa bai gama tsorata ba sai da ya tabbatar da cewa fatalwar mutanen da ya kashece take tsorata shi,tun yana dakewa a matsayinsa na gogagge a cikin harkar tsafi da babu abinda ya isa tsoratashi,sai ga Abba yahya da mikewa tsaye yana rasa inda zai samu matsuguni saboda tsabar tsoro da yadda suke firgita shi,cikin kankanin lokaci ya firgice kunnuwanshi suka daina sauraron ko wane irin sauti idan ba kukan yara da jarirai ba,idan kuma ya bude idanunshi haka zaiyi gamo da mummunan fatalwar da suke mishi gizo suna razanashi.
WAZEER RAIHAN.......
Sosai Raihan ta tsorata da lamarin duniya jin muryar wanda bata taɓa tsammanin zai iya cutar da wani ma ba ita ba,kukan ta ne ya kasa rikuwa dole ta sakeshi ya taho da karfinsa,wani irin nauyi take ji a kirjinta na tsananin damuwa da tsoran lamarin mutanen duniya ,wani irin imani da tsoran Allah ne ya ke kuma shigarsu saboda yadda Allah yake ta karesu akan makiyansu da suke tare da su suke kwana dasu bangare da su sun sansu ba,wazer bai hanata kukan ba sai dai bai yadda hawayenta sun zuba a kasa ba hakan yasa shi tara hannunshi suna zuba cikin tafukanshi,sai da ya tabbata ta samu salama saboda yin kukan sannan ya dagota gaba dayanta ya zaunar akan cinyarsa tare da juyo da fuskarta tana fuskantarsa,idanunshi ya lumshe sanann a hankali ya kai harshensa saman idanunta ya shiga lashe ragowar hawayen bayan ya shanye wanda suka zuba a hannunshi,sai da ya lashe fuskarta Tas ya tabbata babu ragowar digon hawaye sannan ya maidata cikin jikinshi yana cewa shike nan wannan shine na karshe bana son ki sake wani ko nan gaba in dai ba na farincikin ganin maminki ba",samun kanta ta yi da murmushin maganarsa sannan a hankali ta ɗora hannunta kan fuskarshi tana shafawa kafin cikin muryarta da ta dan dashe ta ce", ina sonka hamma wazer ina fata na ci gaba da sonka har karshen numfashina", lumshe idanunsa ya yi saboda jin dadin kalmar kafin ya budesu a kanta bai jira wani abu ba ya shiga sumbatarta ta ko ina,wata irin soyayyace me zurfi da wahalar misali yake mata shi yasa bashi da bakin fadin ina sonki sai dai ya fada dan rage radadi, wannan hanyar ita kadaice hanyar da zai iya nuna mata tsagwaran son da yake mata wanda ke tafiya da numfashinsa,zip din rigarta ya zuge tare da saka hannunshi cikin jikinta yana aika mata da wasu zafafan sakonni wadanda suka fi karfin karamar ƙwaƙwalwarta, Raihan dai tun tana alkunya har abin ya fi karfin iyawarta ta fara maidawa malaminnata amsa amsa cikakkiya da ta wargaza duk wani lissafinsa,sosai take maida masa martanin Koyarwarsa koyarwar da ita kanta bata taba sanin cewa tana daukar darussan ba sai a yau,ey dole ta ce", haka domin kuwa malaminnata kwararre ne in dai amfanin soyayyarta ne.
Kuka ta saka me karfi saboda jin ya karanta addu'ar haduwa yana daidaita abinshi a cikin jikinta,jin kukanta yasashi dakatawa daga kokarin zamar da ita mallakinshi ta har abada,shiru yayi yana ɗan maida numfashi kafin ya mirgina gefe idanunshi a rufe yana ƙoƙarin maida kwadayinsa,ey shima ya ga hakan bai dace ba saboda har yanzu Raihan bata gama samun nutsuwa ba saboda rashin maminta a kusa,zuciyarshi ta ainayana mishi da yayi hakuri zuwa akawo masa Raihan har gida ko shi din sai yafi samun nutsuwar maidata matarshi,jin shirun da ya yi ,duk sai ta ji babu dad'i a tunaninta fushi ya yi,hakan yasa ta matsa jikinsa tare da dora kanta a kan kirjinsa hannunta zagaye da cikinsa,sannan cikin karamar murya ta ce ", sorry ba zan kuma ba," shiru bai tanka ba,sai ta kuma shiga damuwa tana cewa hayatty ba zan kuma ba kayi hakuri", tausayinta ne ya kamashi hakan yasa ya kuma manneta ajikinshi yana cewa wa yace miki fushi nayi? Raihan ko zan yi ta zama dake ba tare da wani biyan bukata ba wallahi bazanji haushinki ba kuma ba zan damu ba,ke din nake so ba wani abu naki ba,nifa hasalima ban san ina da wani peeling ba sai akanki so kar ki damu banyi fushi ba", dago kanta ta yi tana cewa ka tabbata ba za ka kwana da fushina ba? In baki tabbaci? Ya tambayeta lumsassun idanunsa akanta,gyada kai tayi tana karamin murmushi,ok ya fada yana maida hannunshi cikin jikinta yana shafawa, dan zaro ido ta yi jin a inda ya tsaida hannunshi,shima zaro idon ya yi yana cewa ashe yarinyar tana daukar darasi yadda ya kamata anya ko RAIHAN nan gaba ba zaki karasa cinyewa Ammi Ni ba? Ihun kukan shagwaba tasa tare da hayewa ruwan cikinshi tana kai mishi kananun duka har da yan guntayen hawayenta,sai da ya barta ta yi san ranta ta gaji sannan ya rungumeta yana ci gaba da bawa junansu farinciki ta hanyar yan lalube_lalube.asuba ta gari raihanwazer.
Ƙarfe shida daidai....
Karfe shida daidai ita ce tayiwa Raihan da wazer a gurin da me garkuwa da aunty Amarya ya yi dasu zasu aje kuɗi,aje kudin Raihan ta yi tare da komawa cikin motar,tare da barin wajen kamar yadda suka umarceta.
Cikin sanda da yan dube dube wanda zai dauki kudin ya fito,sai da ya tabbatar babu kowa a gurin sannan ya duka ya dauki kudin yana dauka ya juya dan barin wajen amma sai yaji numfashin mutum da bakin bindiga akansa,cak ya tsaya yana ɗan juyowa a hankali. ido biyu yayi da jami' in tsaro na farar kaya fuskar nan yawa an aiko masa da mala ikan mutuwa,ina take? abinda jami' in ya fara tambaya ke nan yana kuma saita shi da bindigarsa,cikin tashin hankali mutumin ya ce", tana can gidan da muka ajiye t.....kafin ya karasa fada wayarsa ta kama ringing,cikin tsawa jami in ya ce", dauka wayar kace ka karbi kudin yanzu zaka taho", haka ce ta faru yana dagawa ya basu tabbacin cewa kudi suna hannunsa harma ya kusa.karasowa maboyarsu,dariya na cikin wayar ya sheke da ita sannan ya ce maza ka kawo kudin sannan na aikata sun dauka zan basu ita sai kace mahaukaci bayan nasan zata iya tona min asiri duk da cewa bata ga fuskata ba,maza ka kawo ina jiranka",
A gaba jam'i an tare da motar Raihan da wazer suka saka shi har zuwa gidan.
Bai taba zato ba kawai sai ganinsa ya yi zagaye da jami'an tsaro.
Bai gama fita daga razanar da ya shiga ba sai jin saukar hannun Raihan yayi a fuskarsa ta zuba masa wani lafiyayyan mari kafin cikin kumar zuciya ta nuna shi da
Yatsa.
Wallahi HAMMA IDRIS ban taba tunaninka cikin masu ha inci da yau dara ba, ban taba kawo ka cikin muguyen mutanen da basa sonmu ba,ka bani kunya Allah ya isa tsakaninmu da kai wallahi Abbie ma ba zai yafe maka ba saboda kaci amanar haihuwarka da ya yi anya kuwa ba Abba yahya ne ya haifeka ba? Gaskiya ina tantama,ta faɗa tana goge hawayen da suka kasa daina zuba,wazer kuwa shi yaje ya kunce Aunty Amarya daga daurin da su kayi mata ya taimaka mata ta tashi.
Da sauri RAIHAN ta rungumeta tana jin damuwarta na raguwa cikin kaso dari babu tamanin saboda samunta lafiya, murmushi Aunty Amarya ta yi sannan ta ce ", kaga abinda nake fada maka ko Idris kai zatonka ban gane ka ba ko? Girgiza kai ta yi tana cewa Wallahi nasan dole sai karshenka yazo bakin azzalumi ta bakin Raihan ɗin wata ƙilma Yahya ne ya haifoka bakin iri kawai", kada keyarsa jam'i an tsaro su kayi ba tare da ya iya cewa komai ba saboda ji yake bashi da abin cewar,tun daga cikin motar ya fara zubda hawayen takaici da nadama tun kafin ake ko ina.
Raihan wazer Aunty Amarya kuwa gida suka wuce suka kai aunty Amarya,basu shiga ba amma basu tafi ba sai da suka tabbatar ta shiga falonta,sanann suka bar gidan saboda akwai aikin da zasu gabatar dashi a cikin wannan safiyar
WASHEGARI.......
Wannan safiyar an wayeta ne da tarin abubuwa na ban mamaki,tree full y trues ya bankado abubuwa masu tarin yawa daga ciki har da videon su shugaban jam'iyya wanda shi ya fara bayyana, jami'an tsaro basu yi wata wata ba suka dangana da gidan shakatawarsu suka kamesu suna kan aikata Masha arsu,su Dr sanater basu taba zato ko tsammani ba saboda yadda labarinsu ya shude acikin masu aikata laifi shi yasa suka ci gaba da cin karensu babu babbaka hankali kwance ba tare da sun tuna ranar nadama na zuwa ba.
Yadda mutane suke tururuwar jifansu kai kace jifan shaidan suke yi,fadi suke Allah ya tona muku asiri kamar yadda ya tonawa his excellency.....
A daidai lokacin da ake wannan zanga zanga ta kama su shugaban jam'iyya,a lokacin karfe tara na safe daidai,Abbu Chibado ne da RAIHAN da WAZER zaune a gidan wazer da suka kwana.
Gaba dayansu ko wanne da computer a gabansa ga kuma tv da suke kallon abinda ke faruwa a cikin tashar Chibado tv.
Finally Abbu mun fitar da videon su shugaban jam'iyya saura uwa uba Yahya ", jinjina kai Abbu ya yi idanunshi akan fuskar computer ya ce", mu dan jira wannan ƙurar ta lafa dan idan muka saki wannan videon garin zai kuma hargitsewa dan haka mu bari zuwa anjima idan HIS EXCELLENCY ya ƙaraso kamar yadda muka shirya muna bukatar hirarsa da jama a ko dan ya kuma wanke kansa ", Abbu ai wannan videon ya isa wanke Abba Garba dan haka ina ga ba sai yayi magana ba yau mu bari ya dan samu nutsuwa da ahlinsa shima in yaso daga baya sai mu bukaci hira dashi ko? Raihan Ta faɗa cikin tsananin nuna biyayya ga surukinnata,shike nan wannan ma shawarace me kyau, dan haka Ni bari na saita komai anjima karfe sha biyu zan sake shi ta shafin tree full y trues,ya fada cikin dariya yana kallon fuskar wazer da shima yake wani ƙayataccen Murmushi bai ce komai ba dai, Raihan ce ta ce", Abbu gaskiya mun ɓatar da hankalin mutane akan wannan tree full y trues din dole kayi dariya", wazer ya ce", ke baki ga rainin hankalin da kika dinga yiwa ma'aikatanki akan son sanin waye tree full y trues ba? Rufe fuskarta ta yi tana dariyar da har sai da kumatunta suka loba", kafin ta bude tana kallon Wazer cikin son ya bata amsar tambayar da zata yi masa ta ce", dan Allah hamma wazer me yasa ka cire ai nahin karshen sunayenmu ka maida shi y bayan naga babu y a sunanmu? Abbu ya ce", Nima dai ina bukatar wannan amsar dan da farko Nima sai da kayi wasa da hankalina na", a hankali wazer ya kawar da kansa daga kallon da yake jifan Raihan dashi, shiru ne ya ratsa falon kamar ba zai tanka ba sai da ya mula dan kansa sannan cikin deep voice dinsa da ke fitowa a nutse ya ce",
Nayi tunanin mutane irin su shugaban jam'iyya da Abba yahya zasu yi saurin gano ko su waye masu wannan sirrintacciyar kungiyar jaridar, shi yasa na dauke wancan sunan na maida shi tree full y trues saboda batar da hankalin masu bin kwakkwafi dan da ace ban yi hakan ba da tuni wadanda muka yi nasara akansu a baya sun ganomu hatta su shugaban jam'iyya da tuni sun gano mu saboda binciken da suke yawan yi akan son gano tree full y trues,kuma nayi la akari da yadda Abba yahya yake da matukar wayo yake shiga jikin mutane yana amfani dasu dan ko su shugaban jam'iyya shine ya dinga fito dasu daga sel da zarar an kama su saboda yana buya a bayansu yana aikata bannarsa son ransa,duk da cewa lokacin bamu san waye me laifin ba.
Salut dinshi suka yi a tare kamar sun shirya yin hakan sai hakan ya bada wani irin salo me burgewa, Raihan ta ce", batun inna maimuna fa za mu fitar ko zamu rabu da ita? Abbu ya ce", rabu da wannan kawai yanzu ta wadannan muke kafin kuma mu gano wanda yasa abu Huraira ya baka guba,tsugune fa bata kare ba", ya fada yana rufe computer shi", murmushi kawai wazer ya yi ba tare da ya ce komai ba,saboda Abbu bai san komai akan gwagwarmaya da yakin da yake akan dan uwanshi Abba Mustapha ba,shi yasa kawai ya yi masa shiru idan ya gama tabbatarwa shima asirinsa zai tonu kamar yadda na sauran ya tonu.
Abbu Allah huta