Showing 147001 words to 150000 words out of 189984 words

Chapter 50 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15624

su ba,kuma dole zata yi masa abinda yake so domin ta hakikance ba zai taba cutatawa rayuwarta ba.




Saida yaga shigarta sannan ya juyo, dai-dai lokacin Abba yahya ya baro gurin da HAJIYAR AGADEX ta tsaida shi da maganganunta da suke neman saka shi hauka,baima san cewa ba hanyar bangarensa ya ya nufa ba saboda tsabar yadda yake jin kwakwalwarshi na tsalle tana hargitsa duk wani tunaninshi,kicibus suka yi da wazer ɗin da yake takawa dan zuwa gurin da ya aje motarshi, kallonshi wazer ya tsaya yana yi saboda ganin gana daya baya hayyacinsa baima ga wazer ɗin ba,gyaran murya wazer ya yi Sannan cikin nutsuwarshi ya ce", Abba yahya Barka da War haka", a dan zabure Abba yahya ya dawo da hankalinshi bakinshi na rawa yana cewa lafiya lafiya me kike nufi da wanɗannan maganganun naki? Zuba masa ido Wazer ya yi kafin ya jefa masa tambaya ", Abba yahya lafiya kake kuwa", sai alokacin ya dan dawo hanya cikin rawar baki ya ce", lafiya umm umm sai kuma alokacin yaga inda yake nufa dan haka cikin hanzari ya juya ya nufi bangarensa jikinsa da komai nasa dake motsi rawa yake", binsa da kallo wazer ya yi kafin ya dan dage kafadunsa sannan ya shiga mota ya bar gidan.




Kamar anjefoshi haka ya fada falonsa,inna maimuna dake zaune tana jiran shigowarsa ta yi saurin mikewa tana cewa lafiya dai ABBAN Bashir? Bai kulata ba bare ta san ran zai bata amsa,wucewa ya yi kamar wata kububuwa yana shiga dakin ya rufo da key dan karma ta ce", zata biyo shi,cikin rawar jiki ya fara danna kiran BASHIR", kira daya ya daga daga dake su a lokacin dare baiyi sosai ba,Bashir duk yadda za ayi ka bar kasar nan ka dawo gida gobe a yanzu babu bukatar zamanka anan," to Abba me ya faru ne? Na ce maka ka dawo ko Bashir ya fada cikin tsawar da bai taba yi masa ita ba", to Abba An dawo amma ya zanyi da jeniper? Iska Abba yahya ya fesar sannan ya ce", ka ka taho da ita kasan dole muna bukatar ta dan ita ce last hope din mu gurin tsohuwa me jini barinta a nan hatsari ne," shike nan Abba yanzu zan fita na yi buking pilot ", daga haka ya sauke wayar ya shiga kewaye dakin kafin daga karshe ya dangana da toilet dan zubda ruwan da ya cika masa ciki.




Raihan dakin hajiyar agadex ta nufa kai tsaye,tana shiga HAJIYAR ta ce", dama nace mata kina hanya", zubawa HAJIYAR ido ta yi tana jin zuciyarta na kasa yadda da abinda ta ji kuma ta gani tun a wancan ranar, wannan abun yan daya daga cikin dalilan da suke hanata sukuni duk lokacin da ta tuna,hakan yasa ta juya ta bar dakin ba tare da ta tankawa HAJIYAR ba, murmushi HAJIYAR AGADEX ta yi tana cewa zaki fahimci ko mai in sha Allah,komai ya kusa zuwa karshe an kusa yin walkiya kowa ya ga fuskar munafukai ", daga haka ta kashingida a katifarta tana ci gaba da laziminta cikin tsarkake Ubangijin talikai wanda ya halicci zuciyoyi.




Kai tsaye wazer main Hause dinsu ya wuce kasancewar dare yayi shi yasa bai shiga ko ina ba ya wuce bangarensu,har zai wuce dakinsa sai kuma ya dawo da baya ya bi ta kofar falonsa ya nufi dakin rabi a", kokarin murɗa hadle din kofar yake amma sai ya dakata saboda surutu da ya jiyo sama sama kamar ma hayaniya ce ta barke tsakanin masu tattaunawar,cikin fusata rabi a dake magana a yanzu ta ce", Surry ban fa kira ki kwana a gidana dan kici mun mutunci ba wai ya kike so na yi duk abinda muka shirya akan Raihan sai ya wargaje idan ban dauki matakin kasheta ba me zanyi? Surry ta ce", ba za ki fahimceni ba rabi a ba ina nufin ki rabu da Raihan ta ci bulus ba ne kawai so nake ki dinga bin abun a hankali idan ba haka ba kuwa kwabarmu zata yi ruwa ba tare da mun cimma abinda muke son cimmawa ba,dan haka nake so ki bar maganar kashe Raihan yanzu mu bi tsarin oga a karo na biyu", tsaki rabi a ta kuma yi a karo mara adadi sannan ta ce", wai rabi a waye wannan ogan dakike ta faɗa nifa bana son shigo da bare cikin aikina kar a samu sabani", dariya Surry ta yi sannan ta ce", Nima kaina so nake na san ko waye abinda kawai na sani a kansa shine yana da kusanci da RAIHAN harma na fara tunanin anya ba a cikin yayyayenta yake ba,abinda isa ban maida hankali kan sanin ko waye ba bashi ne a gabana ba cikar burina shine kawai abinda nake kallo", wani kallo rabi'a ta watsa mata kafin ta watsa mata tambaya,cikar burinki ko cikar burina,? Dubanta auri ta yi sannan cikin mamaki ta maida mata da tambaya", burinki ba nawa ba ne kawa? Ajiyar zuciya rabi'a ta sauke tare da cewa haka ne, Ni yanzu bani waɗan nan abubuwan na dan kora so nake nayi bacci sosai ko na dan samu nutsuwa,"




Barin bakin kofar ya yi yana dan dade kanshi,bai yi mamaki ba saboda dama yana zargin rabi a da kawarta,tunanin yadda zai bi takansu dan ya san komai cikin nutsuwa ya fara yi,tabbas ta hanyar Surry ne kawai zai gano dayan makiyan boyen da ya shige cikinsu yana basaja da fuskar muminai,talala zanyi muku gaba dayanku sai kuma shigo hannu ba tare da kunyi zato ko tsammani ba,ya fada yana shigewa cikin shaya bayan shigar shi bathroom dan samarwa kansa nutsuwa ta hanyar zubawa kanshi ruwa.






WASHE GARI __________






Cikin nutsuwarsa da kamala ya fito fuskar nan a gimtse kamar me", kamshinsa tare da takunsa shi ne ya karade gidan gaba ɗaya.




A bazata suka Ganshi sam basu san ya dawo gidan ba balle su yi tunanin yana cikinsa,zaune suke a falo sunyi baja_baja da kayan kari Surry a na ta zubi saboda babu a Hause,tuni lomar farfesun da take shirin kaiwa bakinta ta tsaya ita bata sauke ba ita bata kai bakinta ba, ruby kuwa kallonshi ta tsaya tana yi tana hadiyar miyan da ta babu ranar da zata daina hadiyarsa,bai kalli ko wacce daga cikin su ba,ya nufi hanyar kiching,basu san me ya shiga yi ba sun dai ga ya fito ya nufi hanyar fita falon gaba daya,sai da yazo gab da fita sannan cikin dakakkiyar Muryarshi me tafiya da wani irin amo ya ce", kar na dawo a same ki a gidannan tare da dan juyowa yana watsawa sury kallon da ya kusa sata datse harshenta,daga haka ya fice cikin sassarfar takunsa me cike da izza.




Yana ficewa Surry ta shiga hada kayanta tana cewa bari ki ga na bar masa gida tun kafin yasa a yi yaga yaga da namana,ko sauraren ruby ba ta yi ba ta bar gidan tana ayyana ranar dawowarta a matsayin matarsa dan tasha alwashi ko da tsafi sai ta aure WAZER.


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivat the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page54 ```




*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page55 ```






Tana fita ta samu wani me a daidaita yana ɗan kakkabe nafef dinshi da alama dai wani ya aje ya tsaya yana ɗan tsaftace nafef din da alama kuma irin gayun nan ne masu tsafta, tafiya za kayi? Ta tambayi me nafef din da sai alokacin ya juyo yana kallonta hannunshi rike da duster ya ce", haba Hajiya tafiya zanyi mana Ni da na fito neman kudi har a tambaye Ni tafiya zanyi",ina zaki je? Ya dora Mata tambaya bayan ya gama bata amsa,shiga nafef din ta yi tana cewa muje zan nuna maka inda zani,haba Hajiya ya za ai na dauke ki bamu yi tsada ba," ko nawa ne zan baka muje kawai", ok Hajiya dama irinku muke son dauka wannan shi ake kira dauka daya yafi yawon awa Biyar ", ya fada cikin irin muryarsa ta gayun samarin erea,shiga ya yi yana shirin tada Babur din wani saurayi ya ƙaraso gurin da sauri yana cewa kai haba dady da wucewa za kayi ka barni dan rashin amana? Dariya wanda aka kira da dady ya yi yana cewa kudi na gani ya za ai na tuna na daukoka dalla shiga mu wuce kana batawa Hajiya lokaci",ita dai Surry har yanzu bata ce komai ba sai wayarta da ta dauko ta danna tare da karawa a kunnenta ta ce", oga a ina zan sameka? Ban san me aka ce mata daga can bangaren ba ta dai kuma bada amsa da cewa ey ban fito da mota ba yanzu haka ina cikin a dai-daita, ko me ya ce mata da yasa ta ɗan kalli me a daidaitan da wanda ya dauka daga baya dake gefanta sai kuma ta maida hankalinta kan wayar ta cigaba da cewa banga alamun matsala a tare da su ba amma tunda baka amince da zuwana a nafef din ba bari na sauka sai ka turo a dauke nin kamar yadda ka ce ", tana kashe wayar ta dubi me adaidaita da aka kira da suna dady ta ce", yauwa bari na sauka a nan kawai", ok Hajiya ba damuwa ya fada yana gangarawa bakin hanya,daidai lokacin da wanda ya dauka daga baya ya dan sunkuya kamar zai dauki wani abu bai fi sakan goma ba kuma sai ya dago ya cigaba da sha'anin gabansa,kokarin bude jakarta take yi ta bashi hakkinsa amma sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa jeki kawai Hajiya ai ba mu yi tafiyar da zaki bada kudi ba", fasa bude jakar ta yi tana cewa shike nan na gode amma da ka bari saboda na yi niyar yi maka kyauta",,no maind Hajiya ya fada yana jan Babur din da dan gudu.




Tabe baki Surry ta yi kafin cikin bayyana murya ta ce", ka huta.






Sai da suka tabbatar sunyi mata nisa sannan dady ya dubi abokinsa yana cewa ka tabbata ka ɗauke wayar kuma ka makala mata wannan madaukar? Dariya Salim ya yi yana cewa kasan bana wasa da aikin oga baya goya marayuya fada yana nuna masa wayar sury", haka ne cewar dady yana ɗorawa da cewa Wallahi salim har yanzu Ban yadda cewa Khalid ya ci amanar oga ba gani nake kamar akwai wani abu a kasa ",tabbas tunanin mu ya zo daya kuma Ni ba kowa nake tunani ba sai abu Huraira", exactly tunaninmu iri daya ne", to idan haka ne kuwa salim lallai ya kamata bayan wannan aikin muma ya kamata mu bada tamu gudummawar domin sakawa wazer da RAIHAN hidimar su a garemu duk da cewa ba za mu iya sakawa Wazer abinda ya yi mana a rayuwa ba",sanan shi kansa Khalid ya kamata musan wani abu akan shurunsa dan ko da ace ya aikata wannan laifin ba za mu kasa haduwa a wani waje ba in dai yana garinnan",ɗan jim Salim ya yi sannan ya ce", gaskiya dady dole mu binciki abu Huraira dan gaskiya ina matukar zarginsa kuma ta wajensa ne ka dai za mu san inda Khalid ya ke", dady ya ce in sha Allah za mu yi abinda ya kamata,yanzu dai yi sauri ka karasa copy din wayar nan mu mayar mata kar ta gano mun dauka bare tunaninta ya kai kan mun canja mata", ai har na gama ya fada yana maida wayar aljihunshi.




Juya a daidaita sahun Dady ya yi suka koma wajen da suka aje Surry ,daidai lokacin ne wata bakar mota ta yi fakin a gabanta,da sauri Salim ya fita yana cewa Hajiya dan tsaya", tsayawa ta yi tana kallonsa cike da mamaki,kafin ta yi magana ya mika mata wayarta yana cewa ina ga garin sauka ki ka yar da wayarki", da sauri ta karba tana cewa kuma wlh ban Ankara ba amma gaskiya na gode sosai", abubuwan da suke dauke a wayar nan suna da matukar muhimmanci na gode sosai ta kuma fada cike da jin dadi", kar ki damu Hajiya", ya fada yana shirin komawa cikin nafef din,da sauri ta dakatar da shi tana cewa ko zaku bani nomber ku duk sanda nake bukatar zuwa wani wane na kira ku,kasan karfen nasara ba tabbas gare shi ba", haka ne hajiya kawo na saka miki", mika masa wayar ta yi ya saka mata nomber sannan ta kuma yi masa godiya ya koma cikin adaidaita suka wuce,ita kuma ta shige motar da oga ya turo mata suka tafi.






Tafawa su kayi salim ya ce ", aiki ya tafi dai-dai yanzu mu wuce office kawai mu fara takan abu Huraira muga shi kuma dame za mu same shi", haka za ai Dady ya fada yana kuma bawa nafef din wuta.






__________




Sury na fita daga gidan rabi a ta nufi kiching jikinta har rawa yake", saliha me aikinta ta gani tana wanke_wanke,ke salaha me wazeer ya shigo ya yi a kiching dinnan? Cikin dan mamaki salihar take duban ruby kafin cikin rashin sanin abinda uwar dakinnata ke nufi ta ce", yaushe ya shigo ai Ni tunda na shigo babu wanda ya shigo kiching dinnan", ke dalla rufewa mutane baki,ruby ta faɗa cike da hasala,bata kuma cewa komai ba ta bar kiching din.
Binta da kallo saliha ta yi kafin cikin sanda ta fidda kananun madaukan da wazer ya bata har guda uku,ya ce", daya ta tabbata ta saka a dakin ruby daya kuma a falo dayan kuma tasa a kiching ɗin,dan haka cikin sauri ta nemi guri mafi sirri ta makala ɗaya,sannan ta cigaba da wanke_wankenta kafin kuma ta samu damar makala na falon da dakin tunda tasan ruby zata fita aiki".






Cike da matsanancin mamaki inna maimuna take kallon dannata tare da matarshi,murza idanunta ta kuma yi dan tabbatar da abinda idanunta ke gani ba mafarki ba ne", fitowar Abba yahya da jin Muryarshi yasa ta kuma tabbatarwa ba mafarki take ba,me ya kawoka gidana? Tambayar da Abba yahya ya jefawa Bashir ke nan bayan shigowarsa tsakiyar falon,diri_diri Bashir ya shiga yi irin na marasa gaskiyar nan sannan cikin nuna nadamarsa ya shiga bawa ABBANnasa hakuri ,dan Allah Abba kayi hakuri ba zan iya jurar rayuwa babu ku ba shi yasa na tattaro iyalaina na dawo gida", da sauri inna maimuna ta ce", dan Allah abban Bashir kayi hakuri hannunka fa baya rubewa ka yanke kayar yaron nan shi kadai Allah ya bamu to me zai sa mu sarayar da abinda Allah ya bamu", kamo hannunsa da na matarsa ta yi tana cewa muje ku huta kuci abinci daga baya ma yi maganar", wani irin duba dan da uban suka yiwa juna tare da murmushin da yake dauke da manufofi masu tarin yawa.




Suna shigewa Abba yahya ya mike yana cewa Finally Bashir ya dawo dan haka ba zan taba bari abinda yake shirin faruwa ya faru ba indai na cika Ni din jinin babana ne", daga haka yasa kai ya bar gidan gaba ɗaya.




____________




RAIHAN tana gama shirinta ta fito tsaf kai baka ce ita ce wannan Raihan ɗin dake shigar maza ba,sanye take cikin doguwar rigar a tamfa me zaiba kalar Koriya wadda ta yi matukar amsar dirarran jikinta fuskar nan tayi fes da ita danma akwai alamun damuwar yanayin da suke ciki a tare da ita ", sama_sama ta sha tea da dan chips da maminta ta tsareta taci duk da cewa cike take da Raihan ɗin akan Wazer", Raihan dinma na sane da hakan amma sai ta basar taki bari ma su haɗa ido da mamin bare tasha tuhuma ta ido tunda babu damar magana HAJIYAR AGADEX na kusa ta tsare gaba ta tsare baya.






Tana fitowa suka hadu da hamma Affan da Idris zasu fita tare", cikin mayalwaciyar fara'a wadda a yanzu take bawa Raihan mamaki hamma Affan ya ce", kanwa har kin fito? Aje mamakinta a gefe ta yi itama tana marabtarsa da ƙayataccen Murmushin dake karawa fuskarta kyau", ta ce", ey wlh hamma Affan na fito ai yau ban fito da wuri ba ma",Barka da safiya", ta faɗa idanunta na komawa kan yamma idiris da yake kallonsu cike da jin dadin yadda yan uwannashi suka fara gane Gaskiya ", HAMMA IDRES Barka da safiya ? Barka dai my sis", za ki biya ta asibiti ne ko sai kin dawo? Hamma Idris ya tambayeta", a'a sai dai idan na dawo yau da akwai aiki da dan yawa a office", ok mu can zamu fara zuwa mama Hanne tun da sassafe ta wuce( kasancewar yau girkinta) ok RAIHAN ta faɗa tana shiga motarta.




A tare suka bar gidan kowa ya nufi inda zashi.




A tare suka shigo buldin din da rabi a ,ita Raihan bata kula da ita ba ,amma ita rabi'a kaf hankalinta na akan Raihan ɗin,cikin nutsuwa ta kashe motar ta fito cikin kamshinta dake dauke hankalin mutum duk da cewa kuwa kadan ta saka saboda dokar wazer amma saboda yadda ya kama jikinta yasa baya buya,tana bayyana a guri shine zai fara isar da sakon zuwanta,ga karin cabbasa da tun fil azal take matukar sonshi idan maminta na yi amma sai ta hanata ta ce", na mata ne,shi yasa yanzu da ta yi free kullum cikin turara jikinta da kayanta take yi.




Wani kallon uku saura rabi a ta yi mata tana wani yatsina fuska da hanci saboda yadda kamshin RAIHAN ɗin ya bugeta, Allah wadaran naka ya lalace matar shige dai ba daraja take yi ba", sai a lokacin Raihan ta kula da ita dan haka ba tare da ta kalli inda rabin take ba ta wuce zuwa office dinta dan ita kallon mahaukaciya takewa rabin yanzu dan haka bata da lokacin sauraren ta.




Wannan abu da Raihan ta yi ba karamin cin zuciyar rabi'a ya yi ba dan haka tasha alwashin kafin a tashi saita saka Raihan kuka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login