Showing 159001 words to 162000 words out of 189984 words

Chapter 54 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15661

ne? To idan kana tunanin hakan ka daina domin wannan aikin da nayi daidai yake da saida rai domin za a iya kamani amma saboda yadda nake son kudi da yadda na yi tsawon shekaru ina farautarsu na amince da hanyar da ka kawo min domin samun mafita,yanzu dai babu abinda zanyi maka sai godiya", kar kiyi min haka bakya tunanin zan iya tona miki asiri? Bana tunanin haka Yusuf saboda na Fika wayo nasan takan iya shege kala kala shi yasa ban yadda na baka kofar da zaka san ko Ni wace ba", dan Allah karki min haka", ya fada cikin marairaice murya irin ta tausaya masa dinnan,dariya tasa tana cewa taimako daya zan iya yi maka shine zan iya sammaka wani abu daga cikin abinda na samu ma'ana dai kudin aikin da kayi min na samo min wadannan dukiya da nake ganin zasu yi matukar bani wahala gurin samuns.......muryarta ce ta katse saboda jin wani abu kamar bakin bindiga a saitin kunnenta,wani irin miyau ta haɗiya kafin a hankali ta juyo da kanta zuwa saitin da aka ritsata da bindiga,ido hudu ta yi da wasu manyan kattin jami'an tsaro kusan su shida zagaye da ita hannayensu dauke da manyan bindigu Dukansu sunyi mata saiti alamu dai ya nuna jiran kiris suke su sakar mata harsashi.




Dariyar da yusuf yake yi ce yasa hankalinta ya dawo kansa kallonsa take yi bakinta yana kasa motsi ta rasa wane irin kalar tunani zata yi bare akai ga batun furta wani abu,katse mata tunani ya yi da cewa inna maimuna kina tunanin kinci bulus ne? Zaro ido ta yi tana mai kuma cika da mamakin yadda akayi yasan ita ce", take wasu hawayen bakin ciki suka shiga zuraro mata, adaidai lokacin da take ji duniya ta dawo mata sabuwa a daidai lokacin ne kuma ƙaddara ta yi mata shammata tabbas Yusuf ya shammace ta, wai duk ma ta yaya akai hakan? Kamar yasan tambayar da take yiwa kanta ya bata amsa da cewa Kinga haziki fasihin da ya shirya wasan Ni kuma na aikataahi dai dai da yadda ya tsarashi ya fada yana nuna mata hoton wazer dake kan wayarsa ya cigaba da cewa Hajiya inna maimuna me wayo wato da ace wazer ba kwararre ba ne da tabbas kece zaki ci wasan domin kuwa kinyi kokari ta yadda kika dora surukarki a poster film din da yanzu ita ce a hannu bake ba,to da ke Allah yasan zuciyarta yasan alkhairinta akan danta shi yasa ya bawa Wazer fasahar tunani har ya gano shirinki ya kuma wargazashi,", kuje da ita kafin mu tunkudo keyar ragowar shedanun ya fada yana juyawa da barin gurin duk alokaci ɗaya.




_____________&&&&




A hankali yake kwantar da ita tamkar wata jaririya,dan motsawa tayi kamar zata tashi hakan yasa ya fasa kwantar da ita ya cigaba da rikonta a jikinsa a hankali yake shafa bayanta yana ɗan jijjigata,ita ko Raihan hannuwa biyu tasa ta kuma zagayeshi tana kuma lafkewa a jikinshi,numfashi take fitarwa a hankali cikin nutsuwa kallo daya za kayi mata kasan cewa ba karamin jin dadin Baccin take yi ba,wayarshi ce ta fara dan zumm zumm na baburashin kallon fuskar wayar dake saitin fuskarsa ya yi,sai da ya dauki sakanni kafin ya dan furzar da iskar bakinshi yana tunanin ta yadda zai kwantar da Raihan ya dauki kiran da Yusuf ke yi masa dan ya tabbata kiran me muhimmanci ne,cikin ainahin nutsuwarshi ya shiga kokarin kwantar da ita a wannan karon bata motsaba har sai da ya kwantar da ita ya daga dan mikewa kawai sai ji ya yi tasa hannu ta kuma janyoshi tare da tura karamin bakinta fuskarta akwabe alamun sakalci sai da ta janyo shi ya dawo jikinta sannan ta ci gaba da baccinta cikin kwanciyar hankali,wani irin kasaitaccen murmushin da ba a cika gani akan kyakkyawar fuskarsa ba ya yi tare da sa hannu ya shafa lallausar kumatunta,sai da ya dauki kusan mintuna biyu a haka sannan ya kara gwada tashi cikin takatsantsan din kar ta farka.




Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dan gyara jikinshi Allah yaso shi ba manyan kayane a jikinshi ba da ya sha tsiyar hajiyar agadex,rufeta ya yi da tattausan bargonta sannan ya bar dakin cikin dan hanzari yana danna kiran Yusuf da har ya gaji da kiransa ya kyaleshi.




Sai yanzu ka ga damar dauka baban SOYAYYA? Yusuf ya fada cikin dan kufula, lumshe ido Wazer ya yi kafin cikin deep voice dinsa ya ce", sorry man ina fata komai ya tafi yadda muke so?ajiyar zuciya Yusuf ya sauke sannan ya bashi amsa da cewa komai ya tafi daidai da ikon Allah", thanks ya fada yana fita daga tafkeken gate din gidansu Raihan.




Haka kawai zuciyarshi ta shiga raya mishi ya sake komawa asibiti wajen Abbie duk da cewa dazu ya je", wannan tunanin da ya yi yasa ya karya kan motarshi zuwa hanyar da zata maidashi asibiti.




Dady da Salim wajen aiki suka koma amma zuciyonsu cike suke da tambayoyi akan mutumin da ya dauki suryy,duk da cewa basu da damuwa akan ko wane motsi na Surry tunda sun riga sun gama dana tarkonsu akanta,Dady ne ya dubi Salim ya ce", bari na dan zaga dan wallahi cikina ya Murda ", dariya Salim ya yi tare da cewa kai fa zabone wallahi wasa_wasa abu kadan ke razanaka", naji din Dady ya fada yana nufar hanyar toilet dinsu na maza.




Shiga ya yi sai kuma ya fahimci kamar da mutum a toilet din kusa dashi,kasancewar toilet din irin me kashi_kashinnanne,tsugunne ya yi , sai dai kuma abinda yaji yasa shi kasa yin tsugunnen sai dai yana kai bai motsaba,waya ake yi daga katangar toilet din ta gefanshi, wannan ba Muryar abu Huraira ba ce? Ya tambayi kansa,kafin ya samo amsar tambayarsa ya kuma tsinkayar Muryar cikin rada rada yana cewa gaskiya OGA na kammala aikina dan haka kawai ka sallameni dama tun farko ba kai nazo yiwa aiki a gurinnan ba su shugaban jam'iyya nake yiwa aiki kai kuma ka siye Ni dan kawai na kashe maka OGA wazer", zaro ido Dady ya yi zuciyarshi na cika da mamaki da matsanancin tsoro,ɗan jim abu Huraira ya yi alamun ana magana ta wancan bangaren,ɗan numfasawa ya yi bayan ya gama sauraron me maganar sannan ya ce", duk nasan haka Nima ba dan ka kawar da Khalil din ba ai da yanzu ina garkame tunda shi ya ganni red hand na zubawa OGA wazer guba a lemunsa kuma ba tare da tsoro ba ya zubar da ita ya kuma ci alwashin tona min asiri, awannan lukacin da ban yi saurin turo maka test na gaya maka ba da tuni ya sanar da wazer,sai gashi kuma mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya saboda ina tsoran zai tona Ni ban tsira da aikin kowa daga cikinku ba,shi yasa nayi tunanin naje offece din Raihan neman videon su Dr sanater,to banga video ba kai kuma ka ɗauke khalil yayin da nake shirin guduwa, dauke shin da ka yi ne ya bani kwarin gwiwar zama saboda shirin da na yi na dora alhakin hargitsewar office din Raihan akansa to ashe ma shegiyar itama tana ankare da komai shi yasa ta ki aje videon a offece din a inda Allah yaso Ni shine bata gama gano waye acikinmu maci amanar ba," ya kare maganar da dan waigawa bayanshi saboda shi kanshi bai san dalilin da yasa ya shiga maimaitawa ogannasa abinda ya faru a baya ba,bayan kuma shima yasan komai.




Dady kuwa wata irin zufa ce ta shiga kwaranyo masa,ji ya yi ba zai iya ci gaba da zama a kan toilet din ba, cikin sauri ya dannawa recording din da tayi save, kasa jurewa ya yi kawai ya fita a zuciye ya yi gaba da gaba da abu Huraira wanda ya yi matukar razana da ganin dadyn,kafin ya yi wani tunani yaji wani irin kakkarfan naushi a fuskarsa wanda take yasa shi suma, bayan jini da majinar da yake fitarwa ta hanci da baki.jansa Dady yayi tamkar kayan wanki ya fita dashi har faffadan filin gidan jaridar.






Surry dai tunda suka fara tafiya tayi tsuru_tsuru ga baki dai amma ba halin magana,duk lokacin da ta kalli Bashir dan ta ce ya sauketa sai taji ta kasa,sai da suka yi tafiya me nisan gaske kafin su isa inda yake son su isa ɗin,fita ya yi ya kulleta a mota kai tsaye ya nufi bakin ruwan da suke kiran tsohuwa me jini shida abbansa,yana zuwa ya shiga karanta ɗalasumansu na tsafi bai saurara ba har sai da tsohuwa me jini ta baiyana cikin mummunan suffarta.nunashi ta yi da sandar tsafinta sannan ta ce", ka gama aikinka kaje gobe a daura maka aure da ita da kaje gidansu za a baka babu jinkiri,hahhhhh ta shiga babbaka dariyarta mara dadin sauraro kafin ta bace cikin hayakinta na tsafi.




Har gida ya maidata sannan ya yi magana da babanta akan cewa zai turo magabatansa gobe a daura musu aure,baban Surry kuwa yana jin wanda zai aure masa marajin yarsa ya amince ba tare da wani dogon nazari ko bincike ba.




__________




Kamar yadda yake ka ida duk wanda yazo sai securitys sun bincike shi,to haka ta kasance ga wazer.




Kai tsaye dakin da Abbie yake ya nufa,duk da yana dan jin nauyin haduwa da Aunty Amarya saboda yau girkinta ne kuma Raihan ta ce masa ta taho nan din tun dazu,ga mamakinsa bai samu securitys a bakin kofarba,bai kawo komai a ransa ba yasa hannu ya Murda handle din kofar tare da yin sallama can kasan makoshinsa,cak ya tsaya yana kallon mutumin da ke tsaye kan Abbie da wani jan kyalle a hannunsa sai kwarya ga kuma wasu yan tarkace nan a gefe ko wanne da amfaninsa.




Innalillahi wainna'ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fil musibati wakalufni Khairan Minha", addu'ar da wazer ya shiga maimaitawa ke nan akan harshensa,yayin da Abba yahya ya ke can yana ci gaba da aikinsa ba tare da ya san me ke faruwa ta bayansa ba.




Abba yahya aji tsoran Allah, Allah Ubangiji ka tsare mu daga bin sharrin zuciya ka yaye mana son kai irin na hassada,kasa mufi karfin zuciyarmu,ka bamu ikon zama lafiya da makiyanmu Allah kar ka bamu ikon cutar da ko makoyinmu bare masoyi ya rabbil alamin 🙏


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page60 ```




HAIDAR........




A hankali yake buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi saboda yadda suka yi matukar kumbura,laluben inda zai ga kwanon abincinsa ya fara yi,dan dama kullum haka yake sai yaga yunwa tana neman kasheshi yake daukar abincin da suka kawo masa yaci,a maimakon ya taba kwanon abinci sai kawai yaji hannunsa yana shafa karamar wayar Tecno me madannai,cikin wani irin rawar jiki ya danko wayar a hannunsa yana fata ace ta gaske ce ba fanko ba,abin kamar almara ko mafarki yana kunnawa sai ga haske ya kawo sa hannu ya yi ya rufe bakinsa saboda ji yayi kamar zaiyi ihu saboda dadi amma sai ya yi saurin nutsar da kansa tare da yin hamdala ga Ubangiji da ya kawo masa mafita cikin sauki ba da wayo ko dabararsa ba,cikin sauri ya shiga tafa nomber WAZER hannunsa na rawa kamar wayar zata subce.




Aunty Amarya........




Tunda ya kawota gidansa da yake aikata Masha arsa yasa yaransa suka daureta ajikin kujera ta yadda ko motsi bazata samu sukunin yi ba,kujera suka aje masa a gabansa ya zauna yana kare mata kallo kafin ya basu umarni su bashi ruwa,da sauri suka bashi robar faro bayan sun bude masa murfin,babu imani ya shiga tuttulawa aunty Amarya ruwan masu sanyi a fuskarta,wata irin sheshsheka ta yi tamkar zata shide tare da bude idanunta a gigice a lokaci daya tana yunkurawa dan tashi amma sai taji ko ina a daure,ɗaga kanta ta yi dan ganin a inda take dan sai yanzu abinda ya faru ya dawo mata,zare idanuwa ta shiga yi,kafin ta tsaida idanunta akansa idanunsa take kallo tana son gane inda tasan wannan kalar idon,katse ta ya yi cikin shakakkiyar muryarsa da cewa waike jaruma ko? To yanzu ina jarumtartaki da wayonki suke?kin boye RAIHAN na nemo ta yanzu kuma kin biyoni saboda kisan ko ni waye sai kuma gashi reshe ya juya da mujiya ke kika zo hannuna ba tare da na shirya hakan ba,enyway dama Raihan na shirya kwamushewa amma tunda ke kin rigata samuwa zanyi amfani da hakan wajen cimma burina,nasan zan cimma nasara tunda ke dinma Raihan na sonki dan haka duk abinda nace ta bani zata bani koda bata san inda dukiyarta suke ba nasan zata nemo su ta kawo min dan ta fansheki", ya kare maganar yana zukar sigarin da yaronsa ya mika masa bayan ya kunna masa.




Tuf yaji kakkauran miyan da ta kasa hadiyeshi akan fuskarsa cikin idanunsa dan saida ta daidaici inda babu facemask sannan ta tofeshi,shafo gurin ya yi yana kallonta yana kallon miyan,kafin ya samu abin cewa ta riga shi cikin kakkausar murya da bushewar zuciya ta ce", tur tur wallahi da masu mugun hali irin naka kuma in sha Allah wannan shine sanadin karshen zaluncinka, Allah na tuba fir auna ma fa ya yi ya gama bare kuma kai karamin alhaki dan haka ina shaida maka da babbar murya wallahi wannan abun da ka yi shine sanadi, fitowar da nayi banyita a banza ba,Kum......kafin ta karasa ya wanke farar fuskarta da wani mahaukacin mari tuni jini yayi tsartuwa ta hanci ta baki,duk da haka bakinta bai mutuba ta ce", kasa a ranka Raihan sai ta yi maka mafiyin wannan dan wallahi sai ta rama min", dariya ya saka cikin izgili ya ce", har yanzu lokacina baiyi ba dan babu wanda ya isa ya hana min cikar burina ke din nan baki isa ba kuma kinyi kaɗan", idan Ni ban isa ba ai wanda ya halicceka ya isa dan haka shi zai isar mana", shiru ya yi yana mamakin karfin halinta,bai sake cewa komai ba ya mike tare da bawa yaransa umarnin su kula da ita kafin zuwa gobe su shigar da bukatarsu gurin Raihan.






Wani irin ihu inna maimuna ta saka lokacin da ta ganta cikin wani tsukakken daki baki kirin wanda koda tafin hannunka baka isa gani ba,ko zama ta kasa yi saboda kankantar gurin hatta da taga yar karama a kayi itama saboda kar a mutune,kuka take yi amma ba kukan nadama ba,kuka ne irin na wanda bai samu abinda yake so ba,babu abinda take shiryawa a kwakwalwarta sai hanyar da zata tsere domin daukar fansa akan wazer da Yusuf,sai ina duk wani tunani da zata yi tayi karshe ma kasa tunanin ta yi saboda yadda kuncin zaman gurin ya fara damunta.






CHIBADO FM......




Dukansa suke kamar Allah ne ya aikosu,duk wanda yazo jin ba asi da zarar Dady da Salim sunyi masa bayani,zakaga shima ya fara tattare hannun riga an shiga fafatawa dashi,dakyar wasu daga cikin manyan dattijan staff suka kwace shi tare da bada shawarar su kulleshi har sai wazer ya zo,da wannan shawarar su kayi amfani suka kulle shi a daya daga cikin dakunan da ake aje tsofaffin jaridu babu ruwansu da abinda zai cije shi suka kulle suka kama gabansu, kowa da abinda yake fada akansa dan kuwa sosai suka ji ciwon yadda yake son kashe me gidansu da suke samun na rufawa kai asiri a karkashinsa.




___________




Dr Sabo dake kokarin shigowa shima tsayawa ya yi cak yana leken abinda ke faruwa wanda ya hana wazer ci gaba da takawa zuwa cikin dakin,zaro ido ya yi shima cikin wani irin al'ajabi da tsananin tsoro,kallon Wazer ya yi sai yaga bakinshi na motsi daga dukkan alamu dai addu'a yake yi,a tsaye yake kyam fuskarshi babu alamun tsoro ko razana tun shigowar da yayi yaga abinda Abba yahya yake yi ya fara innalillahi tare da jero addu,o'in karya sihiri, hakan da Dr Sabo ya gani shima kawai sai ya bi wazer ya shiga karanto nashi addu'ar.




A bangaren Abba yahya kuwa har yanzu bai san abinda ke faruwa ba,hankalinshi kwance yake tsafinshi akan Abbie saboda tsohuwa me jini ta bashi tabbacin cewa babu wanda ya isa ya shigo ko da an shigo ma babu wanda zai Ganshi idanunsu makamcewa za suyi daga kansa,shi yasa ko a mafarki baiyi zaton wani zai shigo har ya Ganshi ba,ya yadda da tsohuwa fiye da yadda ya yadda da Ubangiji (subhanallah Allah kasa mu fi karfin zuciyarmu Allah ka karemu daga aikata shirka komai kankantarta ka karemu daga yadda da waninka, Allah mun yadda kaine Allah mahaliccin sammai da kassai mahaliccin duniya da lahira wuta da aljanna muna rokonka ka rufe idanunmu daga kallon wani a matsayinka ka toshe kunnuwanmu daga yadda da kalmar waninka,ka kuma rufe zuciyoyinmu daga jin Dar akan ikonka da kudurarka tare da buwayarka ya arhaman Rahimin).




Cikin mamaki yake taba kayan tsafinshi yana kuma maimaita ɗalasuman tsafin sai dai kuma har bayan wasu sakanni babu motsin komai,hannu yasa ya kuma taba saitin zuciyar Abbie yaji ko dai aikin ya kammala ne ba tare da ya nuna masa wata alama ba,sai dai kuma kudura ta Ubangiji da buwayarsa wanda ke dayawa da kashewa a maimakon yaji zuciyar Abbie ta daina aiki sai kawai ya ji tana bugawa a hankali kallon fuskar Abbie da zaiyi sai kawai suka haɗa ido,kallonsa yake ido cikin ido,da sauri Abba yahya yasa hannunshi ya taba kwayar idon Abbie wai ko mutuwa yayi sai kawai yaga Abbie ya juya kwayar idonsa har ma da guzurin hawaye, a matukar razane Abba yahya yaja baya yana nuna Abbie kafin cikin rawar murya ya ce", a'a sam hakan ba zai yiwu ba saboda tsohuwa ta ce", ba zaka taba tashi ba har abada saboda ita ta kwantar da kai ba wai coma kashiga ba dan haka ba zaka tashi ba har sai mun gama aikinmu akanka wanda cikin dayan biyu zaka yi daya ko mutuwa ko tashi ga hauka",




To Allah da rayuwa da mutuwa ke hannunshi bai nufa ba", ya ji an fada daga bayanshi,a razane ya kuma juyawa sai kuwa karaf suka haɗa ido da wazer sai Dr Sabo dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login