Showing 45001 words to 48000 words out of 189984 words

Chapter 16 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15613

ke ciki,wani irin washe baki yayi kai kace ba iya lamba aka samo ba har da mutumin,Dr ya ce" dakyau kyautar ka ta musamman ce,jagwal na gode me gida jagwal ya fada yana mai sakin murmushin jin dadin yabon sa da me gidan sa ya yi, Alh sale ya ce"to yanzu kuma me ye abu na gaba da ya kamata muyi? Jagwal ya yi saurin cewa idan kuna so a gano muku me lambar a daren nan zanyi trakin na samo muku shi"Dr ya ce"me yasa ba kayi hakan ba? Da sauri jagwal ya ce"sorry me gida bana son yin shishshigi akan aikin ka nafison ka bani umarni sai na aikata hakan sai ya fi daɗi"shike nan jagwal je kayi duk abin da ya kamata akan lambar nan Ni dai ina son cikakken bayani akan ko waye,to yallabai kar ka damu ka bani awa ashirin da hudu zan dawo maka da sakamako",Dr ne ya mika masa bondil din yan dubu dubu yana cewa jeka idan ka dawo da sakamako zaka ji alert"da rawar jiki jagwal ya karba yana faman zuba godiya tare da alkawarin cika aiki a kan lokaci,yana fita Dr ya kalli dayan saurayin ya ce"kai kuma shiga wancan dakin muna zuwa"ta shi yayi jikin sa a sanyaye kamar dai abin da ake shirin aikata masa dole a kayi masa,(to Ubangiji Allah ya shirya bayin sa masu shiryuwa).




_______________






.....Muhammad nurr hause..




Murmushi Abbie ya yi ganin yadda duk suka maida hankalin su kansa,kuma dukan su zaka iya hango tsananin tashin hankalin da zuciyoyin su suka shiga,tsaida idanun shi ya yi akan aunty amarya kafin ya maida idanun sa kan autan sa Rahim (Raihan)tsira mishi ido ya yi yana jin wata irin soyayya da kauna kai kace shi ka dai ne dan da ya mallaka a duniya.




Avangaren aunty amarya kuwa,da za a tsaga jikinta tabbas ba za a ga jini ko kadan ba,tsananin razanar da ta yi da kallon da Abbie yayi mata da wanda yake kan yiwa RAIHAN dinta,shi ya nemi sawa ta fallasa kanta tun kafin sanin ma anar kallon,bude baki yayi a nutse har yanzu idanunshi na akan Rahim ya ce"ina da R.........✍🏽




Fatima y Adam ✍🏽
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page14 ```






........tarin da ya sarke aunty amarya shi ya dakatar da shi daga abin da yake shirin fada,da sauri Raihan ta bude bottle din ruwa ta kafa mata a baki,sai da ta shanye ruwan tass, Raihan ta shiga goge mata zufar da ta shiga tsiyayo mata ta ko ina a cikin jikinta,sannu a ka shiga yi mata,idanun ta sun kada sunyi jajur,ji take kamar zata yi aman zuciyarta saboda tsananin tashin hankali,sai da Abbie ya ja wasu yan mintina kafin ya ci gaba da cewa,na bawa Affan asibitin bayan gari dama saboda shi na gina sa,tun da abin da ya karanta ke nan,ga takardun nan zan bashi a gaban shaidu kafin na kira lauyana,shi kuma Idris kamfanin takalma na gwarumfa,sai kuma kai rufa i tun da lauya ka karanta na baka gidan man City road,Amma zaka a jiye aikin ka ka kula min da babban kamfanin Raihan na shinkafa,shi kuma babana da shi da jami'lu da Hassan zasu rike kamfanin audiga wanda yake son na Kano sai yayi magana yaje can ya zauna da matar shi,tahowar biyun na nan sai ko wanne ya zaba wanda yake so.




Baffa Ali ya ce"a'a kar kayi haka ka raba musu ko wanne ka bashi nasa kamar yadda kayiwa ragowar,saboda kar hakan ya zama rigima a tsakanin su"Hajiya goggo ta ce"wannan haka yake malam"jin jina kai Abbie yayi kana yace "to wannan sai mu bari sai sun dawo tun da basa nan,idan kuma dame wata magana yanzu ina sauraron ku, Affan ne ya jagorance su wajen mika godiyar su ga Abbien daga nan suma duk su kayi godiya,sai mama murja da ta ce"muma muna taya su godiya amma fa ba ka bamu amsar mu ta dazu ba, sannan kuma shi Rahim babu shi a yin kyautar cikin tawagar? sannan ina tunanin ba iya wannan ne dukiyar Raihan ba akwai wasu gidajen man a Kano da akwai gidajen haya sannan da akwai babban kamfanin auduga,duk su a hannun wa ka bari?ina ga ya'yan ka ne kawai ya kamata su kuka da wannan dukiyar tunda dai Yanzu kasan yadda amana ta yi ƙaranci?ba tare da Abbie ya nuna mata komai ba ya bata amsar ta ta biyu da cewa,har yanzu rahim yaro ne duk ranar da zan bashi tashi zan tara ku kamar haka"daga haka ya mike tare da yiwa baffan shi sallama,ya fita daga falon,hanne kuwa wata irin ƙwafa ta yi me cike da tsananin jin haushi da wani abu a cikin rai,wato ba zai sanar da su inda ragowar dukiyar take ba wanda ko rabin ta basa jin ya fada.




Aunty dai ta dan samu nutsuwa duk da cewa ,tambayoyi ne cike a ranta da tsananin rudani,anya kuwa Abbie bai gano ɓoyayyiyar RAIHAN ba?idan ya sani ta ya a akai ya sani? Tabbas yau abbin ya saka ta cikin rudani wanda zai yi wuyar fita,jiki a sanyaye ta bar bangaren baffan,ita kuwa RAIHAN zaman ta tayi sai zuwa anjima,kowa ya tafi sai ita da Hamma idi da Baffa Yahaya a ka bari suna ci gaba da taya baffa hira,a nan baffa yake kuma yi masa nasiha akan rike amana,ya ce"kasan dalilin da yasa aka baka amanar wannan babbar dukiya me tarin yawa,mahaifin ka ya yarda da kai da nutsuwar ka shi ya sa baka wannan amanar dan haka sai ka rike karka bashi kunya"Hamma idi ya ce"in sha Allah baffa ba zan baku kunya ba"yauwa dan albarka,a daidai nan wayar sa ta yi kara alamun kira,dagawa ya yi bayan yayi sallama,ok mama gani nan zuwa"abin da ya fada ke nan ya mike yana maida wayar aljihun shi,to baffa zan wuce mama na kira na sai mun hadu da asuba in sha Allah"kai kuma Rahim a nan zaka kwana na ne?miƙewa ya yi yana cewa a'a tare zamu tafi Ni kam Hamma ido ka taba gani na kwana a gurin da ba dakina na gidan aunty amarya ba? Ey ban sani ba dai ko bayan tafiya ta ka fara "cewar Idris yana kokarin fita daga falon, Abba yahya ya ce"wannan matsoracin ai ko a bangaren kakar ku bai taba kwana ba"dariya su kayi suna kara yi musu sallama.




Sai da Hamma idi ya raka ta har cikin falon su kana ya juya ya nufi bangaren maman nashi murja.




Shima Abba yahya tashi ya fara kokarin yi,yana cewa Baffa Nima zan wuce dare ya fara yi,dakatar da shi Baffa ya yi yana cewa ,tsaya ai ban gama da kai ba, akwai maganar da ɗan uwanka ya ce nasanar da kai,saboda yana ganin lokaci ya yi da ya kamata kasanin.komawa ya yi ya zauna yana mai kara maida hankalinsa kan baffan,Baffa ya cigaba da cewa ka dai ji tambayar da murja ta yiwa ɗan uwanka akan manyan dukiyar da ya bawa Raihan ko? Jinjina kai Abba yahya ya yi,Baffa ya cigaba da cewa to ɗan uwanka dai ya riga da ya bawa Amininshi Alh Garba gwamna namu na Adamawa hakkin kula da ita,kuma ba tun yanzu ba ne an jima da yin hakan a tsakaninsu,babu wanda yasan da haka daga Ni sai shi sai kuma lauyansa da lauyan shi Garba,ko mahaifiyarku bata san da wannan maganar ba.jinjina kai Abba yahya ya yi kafin ya dan ja numfashi ya ce ",Baffa hakan da ya yi abune me kyau kasancewar muhimmancin Garba da halaccinsa gare shi,tunda za mu iya cewa duk abinda Muhammad nuurr ya zama da akwai sa hannun amininshi Garba,dan haka wannan ba wata matsala ba ce,sai dai muyi fatan Allah ya bashi ikon ci gaba da rike masa dukiyarsa cikin amana da Gaskiya", baffa ya ce",Amin ya Allah baki dadin yadda kafahimce Ni,dan haka ka ta shi kaje Allah ya bamu alkhairi,Amin ya fada yana mukewa da fita daga sashen.




Kana ganin zaman da su kayi kasan na jiran sa ne,wani kallo maman ta wurga masa me cike da takaici,ta ce"yanzu kai dan rashin zuciya da sanin ciwon kai zama ka yi a can din kana surutu mara dalili bayan gashi mu nan muna jiran ka dan yin magana mai muhimmanci",zama ya yi yana cewa mama me kuma nayi daga dawowa ta? Kace me kayi mana kai yanzu baka ji haushin abin da ubanku ya yi ba?duba fa kowa zai zauna a kamfanin sa ya yiwa kansa kyakkyawan tanadi amma banda kai ,saboda kai an maida kai solobiyo ɗan solobiyo shine aka haɗa ka da aikin bautawa kamfanin gaibu, wannan kamfanin fa yana daya daga cikin manyan kadarorin Abbienku,akwai manyan kamfanonin da suke muhimmai wadanda ya boye su bayan ya mallakawa gaibu yarsa, sannan ya ƁOYE wanda ya bawa hakkin kula da su bare musan inda muka dosa,kai ba za kayi kishi da hakan ba bai hada ku da komai ba sai wasu ƙananun kadrori da basu taka kara sun karya ba?"momy hanne ta amshe da cewa yo kika san kyautar da za a yiwa wancan mata mazan ma kina ganin yadda aka ki bashi a gaban idanunmu kinga kuwa dole akwai muna furci cikin lamarin,dan haka tun wuri ku farka daga nannauyan baccin da ya kwashe ku,dan wannan kaɗai ya isa tabbatar muku da cewa mahaifin ku baya kaunar ku wancan gaibun da ba a haifa ba yake so da wannan mata mazan,dan haka yanzu ya rage naku ku kwatarwa kanku 'yanci ko ku tsaya kuna kallo ana wawashe dukiyar ku ana abinda aka so da ita" Affan cikin yanayin zuciya da alama dai an taso masa da abinda ya kwanta masa ya ce"wallahi mama ko da tsiya da tsiya tsiya sai mun karbi hakkin mu babu ruwan mu da wani kusanci ko ciki baya ku ka fito da mutum sai nayi duk yadda zanyi na kwaci hakkina"rufa i da yake ta huci kamar kububuwa ya zabura kamar zai kai duka ya ce" billahillazi ko me za ayi kai koda ya haɗa da shi mahaifin namu ne babu ruwan mu sai mun karba tun da shima ba kaunar mu yake ba,dan haka yanzu aiki ne babba a gaban mu dan dole sai mun san duk wasu dukiyoyi da ya tara wa Raihan tun daga lokacin da ya bata zuwa yau, dole ne mu binciko wanda yake riƙe da kadarorin,daga nan sai mu san hanyar da za muyi ƙwace su" Hamma idi ya dakatar da shi fuskar sa da wani irin yanayi na rashin jin daɗin abinda suke shirin yi ɗin , ya ce"amma ina ga abin da kuke shirin aikatawa ba daidai bane dan Allah ku yi hakuri da abinda kuka samu tun da shi din ma idan kuka jajirce watarana sai ya zama abin da baku taba zato ko tsammani ba, sannan ba hakkin ku ba ne kamar yadda kuke faɗa,idan da kuka duba duk abinda Abbie ya bawa Raihan ɗin da kuke magana akanta kuma ya baku sai dai kawai kuce ku baku juya naku ba har na waccan ɗin yake tsole muku idanu,da kunyi hakuri da naku watarana sai kufa kun samu abinda yafi wanda kuke son ƙwarya", dalla rufewa mutane baki wa yace maka abinda za mu yi ba daidai bane,?da kake kiran ba hakkinmu ba ne,to dukiyar ta uban waye aka dauka a ka bawa gaibu,ita fa wadda aka bawa dukiyar nan bata a duniya babu ita ko kadan,dan haka idan mun ci babu komai hakkin mu ne"cewar Affan ke nan da yake ta hura hanci zuciyar sa na kuma azalzala da kwadaituwa akan dinbin dukiyar da aka tarawa gaibun Raihan.




Miƙewa tsaye idiris ya yi fuskar shi babu walwala ya ce,Ni dai babu hannu na a cikin wannan lamari dan haka idan ta kwaɓe muku kar kuce da Ni, kuma Allah ya ganar da ku"daga haka ya fice cikin sauri yana jin damuwa me tarin yawa akan abin da suke son aikatawa din.


Bin shi su kayi da kallo,kafin momy hanne ta ce"ai dama har yanzu kana nan baka canja ba,na dauka girma yazo ka fara sanin ciwon kanka ashe dai har yanzu da saura"mama murja ta ce" rabu da shi mu za mu yi duk me yiwuwa dan samar da farinciki a cikin rayuwar mu,a haka suka ci gaba da tattauna matsalar da suke ganin ta Addabe su har zuwa tsawon wani lokaci kana kowa ya wuce makwancin sa.




CHIBADO's hause.......




Ko da rabi ta ji batun saka ranar auren su ita da wazir,farinciki tamkar zata yi hauka dan kowa sai da ya shaida hakan,maman ta ta fara kira ta sanarwa sannan kawayen ta da sauran duk wanda yasan kaunar da take yi wa wazir din,dan har sai da innawuro ta yi mata fada dan ita macece da sam bata son rawar kai da rashin aji ga koma waye.




Shi kuwa wazir da kyar ciwon kan da ya addabe shi ya bar shi ya runtsa,saboda tsabar tunani da damuwa,wani sam baya barinsu su yi tasirin da zasu bayyana saman kyakkyawar fuskarsa bare har a gane abinda yake ta bunnewa.




Muhammad nurr hause.....




Sai yanzu da ta kebe dan kwanciya sannan damuwar wazir ta dawo mata sabuwa,dan tsuka ta yi tana mai shigewa cikin tattausan bargon ta,tare da rintse idanun ta,so take ta yi tunani akan camarar nan da videos din dake cikinta,duk da cewa lokacin da ta shirya dan fara bibiyar lamarin baiyi ba,a Haka bacci ya kwashe ta me cike da mafarkin wazir me dadi da mara daɗi.





A bangaren aunty amarya kuwa ko da ta samu Abbie a daki cikin shirin bacci,kasa ce masa komai ta yi,amma tabbas zuciyar ta na cikin wasiwasi akan sa,da kuma dinbin tambayoyin da suke bakinta,sai dai tana tsoran fara tarar shi da maganar kar taje kuma abin da take tunanin ba haka bane,ta tunawa kanta asiri,shi yasa kawai taja bakin ta ta yi shiru ,harma ta yi kokarin daidaita nutsuwar ta duk dan kar ya fahimci a razane take,sai ma kulawa da ta yi kokarin bashi kamar yadda ta saba duk lokacin da yake wajen ta.




_______________




Washe gari da wuri ta tashi ta yi shirin zuwa office saboda yau din akwai aiki sosai agabanta,tsaf ta fito cikin shirinta na kullum as a male,sai kamshi take zubawa wanda ya ke ta shi a hankali,a dinning table ta samu Abbie da aunty amarya suna karyawa,waje ta nema ta zauna bayan ta gaida su cikin kauna da soyayya, Abbie ya ce"manyan yan jarida yau za Afita aiki ke nan,an gama ɗokin dawowar abbie ne?dariya ta yi har fararen haƙoranta suka bayyana tare da lotsawar kumatun ta,zuba mata ido Abbi ya yi,yayin da shi kuma aunty amarya ta zuba masa nata idanun tana jin wata irin fargaba akan sa,ba komai ne yasa bata son Abbie ya san komai akan Raihan ba sai dan tasan idan ya sani din ba zai taba yadda ya ɓoye RAIHAN ɗin ba,dan soyayyar da yake mata ba zai bashi damar yin hakan ba, Abbie ya ce" Rahim me yasa wasu abubuwa naka suke yanayi da na mata ne shin kana sane kake yi ko kuma haka Allah ya yi k....kofin kunun tsamiya da ta kai bakinta tuni ya dawo tari ta fara sosai na alamun mummunan kwarewa,da sauri Abbie ya shiga shafa bayan ta yana mata sannu,aunty amarya kuwa mutuwar zaune ta yi saboda tsananin razanata da tambayar ta yi,ashe dama bai sani ba Gara da Allah yasa bata yi masa maganar ba jiya,tabbas da ta tonawa kanta asiri,to amma jiyan me yake so ya fada ya kuma fasa fada,daga karshe ma share tambayar ya yi,me ye manufar yin hakan,me yasa yayi wa Raihan tambayar da bai taba yi mata ba,ko dan yanzu ya samu nutsuwar zama da su ne yanzu ne hankalinsa ya dawo kansu?,idan kuwa haka ne aiki ne agaban ta ja,dan wlh baza ta taɓa yadda asirinta ya tonu ba,dan hakan yana nufin rasa tilon yarta ne.




Dakyar tarin da Raihan take yi ya tsaya, amma idanun ta sunyi ja sun kuma kankance,sannu Abbie yake ta jera mata yana shafa bayanta,cikin tausayawa da nuna kulawa,kallon aunty amarya ya yi ya ce" ko dai asibiti zamu tafi a duba shi?kafin aunty amarya ta ba shi amsa, Raihan ta yi saurin tarar shi ta hanyar miƙewa tana tattara kayan ta,ta ce" haba Abbie daga kwarewa kuma sai asibiti kaga Ni na wuce office sai na dawo"to Allah yayi albarka ya dawo dakai lafiya ya kuma kare ka daga sharrin mahassada" Amin abbiena na kaina,ta faɗa da bashi sumba a hannun shi,haka tayiwa aunty amarya ta nufi kofar fita aunty amarya na raka ta da Tata addu'ar,a bakin kofa suka ci karo da Hamma idi,wai har ka fito broder? Me zan zauna yi, bari na gaida su Abbie na zo na sauke ki a office din,ya fada yana shigewa falon,yauwa Hamma ido na,bari na jira ka a waje amma kayi sauri dan yau din akwai aiyuka da yawa.






CHIBADO's hause






Fuskar nan babu walwala kamar ko yaushe, a haka ya sauko daga saman cikin takun shi na nutsatstsu kuma zaratan maza,bai ko kalli inda innawuro ta sa aka jere masa kayan karin kumallo ba ya nufi kofa kai tsaye,sai da ya kusa kaiwa kana ya dan dakata tare da juyowa inda innawuro ke hakimce tana bin sa da kallo,a hankali ya bude bakin sa kamar wanda a kayiwa dole ya ce" Barka da safiya Ni na wuce office" bai jira tankawarta ba ya fice cikin sassarfar tafiyar shi irin ta wanda yake son barin guri da gaggawa,amma ba kowa ne zai gane hakan ba saboda shidin komai nasa yana gabatar da shi ne ta cikin nutsuwa,ƙwafa innawuro ta yi tare da cewa duk tsiyar da zaka shuka ka yi ka gama aure ne dai babu fashi,kawun naka Mustapha ma yayi ya gama bare kai karamin jariri".






Chibaɗo FM.......




Kamar tare suke suna tsaida motar su ,shima tasa ta tsaya a wajen da aka tanadasa masa dan ajiye mota,sam Raihan bata kula da shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login