Showing 117001 words to 120000 words out of 189984 words

Chapter 40 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15638

ba kowa ya jawo hakan ba sai uwarka dake boyeka tamkar wani sisin gwal", take ƙananan maganganu suka fara tashi da yawa suna ganin maganar goggo akan hanya take dan haka cikin lokaci kankani aka fara gulma,wasu da yawa abin yana cin ran su sai yanzu suka samu damar yada magana.




Aunty amarya dai tunda taga haka ta samu ta silale ta bar falon,Hajiyar agadex ma shiru ta yi bata ce komai ba,sai dai ragowar yan uwan aunty amarya sun bi bayan Hajiya goggo akan zancanta fa gaskiya ne.




RAIHAN kuwa tana can daki bata san wainar da ake toyawa ba,dan tun sa ilin da aka yi mata gaisuwa ta dau hanyar komawa daki Hajiya goggo ta fara sababinnata shi yasa bata tsaya sauraren abinda zai bata mata rai ba tayi shigewarta daki ta maida kofa ta rufe.




Duk hakurin da inna maimuna ke bawa Hajiyar agadex a banza , bata samu yin shiru ba sai da sallamar wazer da Idris ya katseta.




Cikin nutsuwa da Dattaku wazer ya kuma gaidasu da yi musu ta aziya,duk da yadda yaji na kasancewar samun mata a wajen to amma ya ya iya da zuciyarshi da take tamkar mayen karfe akan RAIHAN, Idris ne yaja shi yana masa iso zuwa dakin Raihan ɗin,a nan Hajiya goggo ta kuma sakin tsaki tana binsu da wata ƙatuwar harara tamkar idanunta zasu fado, kwafa tayi ba dai kuma cewa komai ba amma kana ganin fuskarta kasan cewa da kwai mugun haushi dake cin ranta.




Hajiyar agadex kuwa Murmushi ta yi bayan ta dauke idanuta daga kallon da take yiwa Hajiya goggo,ci gaba ta yi da ballar goranta ba tare da murmushin kan fuskarta ya gushe ba,wanda hakan yasa hajiya goggo tsarguwa.






A hankali Abban rabi ya dubi abbu ya ce",wai yaya da yaushe jirginsu Khalil zai sauka ne? Karfa mu sakankance suke su yi ta jira",Abbu ya dan numfasa tare da cewa har yanzu sunki fada min lokacin da za su sauka nara dalilinsu nayin hakan,kuma ina tunanin wannan tsarin yayansu ne WAZER ",wani dan dumm abban rabi yayi kamar irin ya shiga shock din nan,sai da abbu ya taba shi sannan yayi zunbur ya wayance da sakin Murmushi yana cewa kasan tun can baya ba ajin kansu shi yasa zasu dora daga inda suka tsaya,to Allah ya dai ya kara mana zumunci da kaunar juna", Amin ya rabbil alamin suka amsa har da su Abba yahya da suke tare a mazauni ɗaya.




Hamma idi yana yi masa nock din dakin Raihan ya juya ya bar gurin.a nutse wazer ya dan bishi da kallo kafin ya dawo da kallonshi kan kofar dakin da har yanzu bata motsa ba bare yasa ran wadda ke ciki zata buɗe,a maimakon ya kuma bugawa sai kawai ya zaro yar karamar wayarshi wadda Bama nom kowa ne a ciki ba sai wadanda suke da matukar muhimmanci a cikin rayuwarsa.dannawa ya yi sannan ya kara a kunnenshi ko sakanni biyar ba ayi ba ta daga,ba tare da ya saurari abinda zata ce ba ya bata umarnin bude kofar.




Da sauri RAIHAN ta kalli fuskar wayarta sai kuma ta kalli bakin kofar,tasan shi ba ma abocin wasa ba ne bare tayi tunanin wasa yake mata,a hankali ta zuro ƙafafunta kasa tare da zura silifas din dakin me tsananin taushi kai tsaye ta bude kofar tana mai sauke kyawawan idanunta akan ƙayatacciyar fuskarsa wadda ke ta fitar da wani irin haske kamar wata dan daren goma sha biyu,yadda ya kafa mata idanunsa masu kaifi da tasiri ga duk wanda ya ci karo dasu yasa ta matsa ta bashi hanya cikin sanyin jiki,shigowa ya yi ba tare da ya dauke idanunsa daga kanta ba,maida kofar yayi ya rufe sannan ya Murda key ɗin,sosai ya shigo tsakiyar dakin yana mai ci gaba da yi mata kallon kurulla wanda ya sa ta fara tura bakinta tana dan kakkawar da fuskarta gefe,to nikam wannan kallonfa? Ta tambayeshi cikin dan murguda bakinta gefe,bata Ankara ba taji ya yi mata zobe da dogayen hannayensa kana a hankali ya sunkuyo da kansa ta gefen wuyanta ya daidaita fuskarsa da Tata cikin wani salo me tafiya da hankali ya shaki daddaɗan kamshinta yana mai lumshe idanunsa a lokaci daya.




Tunda wazer ya wuce Hajiya goggo ta tsurawa kofar dakin Raihan idanu tamkar wadda take son ganin abinda ke wakana a dakin ata cikin kofar.


Inna maimuna da ke daga can dan gefe da Hajiya goggo akan kujerar dake fuskantar Hajiya goggon ta zuba mata ido tana son karantar ko ta ce gano ma'anar kallon da takewa kofar RAIHAN,da dai taga abin ba na kare ba ne,sai kawai ta yi gyaran murya tare da cewa Hajiya goggo ya dai naga kamar kinyi zurfi a tunani?firgita Hajiya goggo ta yi tamkar wadda aka tasa daga barci cikin yan kame_kame har da cire dankwali ta gyara ta ce", ey ah ahhhh ina tunanin halin yaronnanne wlh sam bana jin dadin kuntata kansa da yake", Murmushi inna maimuna ta yi kamar dai bata gamsu da abinda Hajiya goggo ta ce ba,to amma ya ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru tunda bata da halin cewa bata yadda ba suruka sukutum guda.






Abban rabi kasa daurewa ya yi wazer ya fito saboda abinda ke cin ransa,tashi yayi daga cikin mutane yayi can baya ta wajen bangaren surukan gidan,wayarshi ya dauko daga aljihu jikinshi har rawa yake wajen neman sunan wazer,danna masa kira yayi ya tsaya yana sauraren ringing din da ta fara.




*RUBY*




Duk da yadda zuciyarta ke kuna akan lamarin haka ta daure ta shirya dan zuwa yiwa Raihan gaisuwa wadda ba wai dan Allah zata ba sai dai abinda take kullawa a ranta domin kuntatawa RAIHAN.




Lokacin da taje bangaren innawuro, innawuro kallonta tayi kafin ta dan tabe baki ta ce", saboda gulma da za muje baki bimu ba sai yanzu zaki wani shirya wai zaki gaisuwa,hmm Tom sai kin dawo Allah bada sa a", dan tura baki rabi ta yi tare da ficewa tana maganganu kasa_kasa,kai tsaye mota ta dauka ta fice daga gidan.




*WAZEERRAIHAN*




A hankali ya kai bakinshi cikin kunnenta tare da hura iska kadan wanda hakan yasata kankame jikinta, tana dan mutsu_mutsu ganin kamar tana son ƙwacewa yasa shi ƙara ƙarfin rikonsa gareta sosai ta hadu da jikinsa ƙamshin turarensa da nata ƙamshin ya haɗe ya sakar mata wata irin kasala me tsananin sanyi tamkar ana hura mata iska cikin bargonta.




Juyo da ita ya yi tana fuskantarsa, ƙasa ta yi da kanta dan kaucewa kaifafan idanunsa masu sata taji wani irin kunyarsa,cikin wani irin deep sound ya ce", kina jin me wancan kakarnaki ke fada? Jinjina kai ta yi idanunta na kawo ruwa kafin yace", wani abu tuni ta fara ruwan hawaye, ɗan ware idanunshi ya yi akanta sai kuma yasa hannunshi me taushi saman kuncinta ya dauke hawayen ya daga yatsan yana kallo kamar wanda ke kirga yawan hawayen,sai kuma ya kalleta tare da daidaita fuskarshi da Tata yana kallon hawayen da suke ƙara saukowa da gudunsu, a hankali ya matsar da bakinshi daf da fuskarta bata yi aune ba saijin ɗumin bakinsa tayi saman idanunta wani irin ajiyar zuciya ta saki sai kuma samun kanta ta yi da ƙamkame shi saboda tsananin zummm din da taji har cikin kwakwalkwarta,a hankali cikin ajinshi da iyawarshi ya ci gaba da lashe hawayen da duk wani abu dake gangarowa daga idanunta,gangarowa ya cigaba da yi zuwa kan dan ƙaramin bakinnata........✍🏽






Comments


Comments


Comments


Yawan comments yawan post..
Pg43






Haɗe bakinshi da nata ya yi kafin a hankali cikin salon kwarewar da baya sanin yana dashi sai kanta, ya shiga tsotse harshenta tamkar wanda ya samu alewar da yake matukar so,yadda yake yi din dolene ya tsaya a yar karamar ƙwaƙwalwarta da zuciyarta harma da gangar jikinta.salon na dan gidan Ammi jikan innawuro dabanne da na kowa harma dana 'yan Indiya inji Raihan,cikin nutsuwarsa da kamewa ya cigaba da bata wani zazzafan kissess,a hankali ƙafafunta suka fara rawa saboda yadda take jin abin har can maƙurarta,wani irin sha yakewa miyanta wanda yake jinsa tamkar wani zuma.




Ganin yadda ƙafafunta ke neman lanƙwayewa saboda yanayin da yanayin da dan Ammi ya jefata ciki ,yasa shi tarairayota gana dayanta tamkar jaririya ya wuce da ita zuwa saman tattausar shimfidar gadonta,zama ya yi da ita yana kallon fuskarta da yake jin tana matukar ɗebe kishi kewar kadaicinsa na nunkufurci da yake dabiarsa,ajikinta take jin kallon dake mata wanda yake wucewa kai tsaye yana shiga ko wace kafar sadarwa dake da rai ajikinta, sosai ta rintse idon rana kasa budewa,shi kuwa kallon fatar idon yake da wani irin burgewa saboda yadda take dan motsi tana dagawa gashin idon na wani irin kwanciya hakan ya bashi sha'awa matuka har baisan lokacin da ya kai hannunshi saman idanunta ba,ita kuma hakanne yasa ta bude idon da sauri zuruf kuwa sai acikinnasa idon.




Wayarshi da ta yi kara a karo na uku ya dan kalla bayan ya zarota daga gaban suet dinshi kashe wayar ya yi duk da yaga sunan me kira domin baya son damuwa ko wace iri ce ta gitta masa a daidai wannan tsukin.






Wani irin kwafa tare da cije yatsa Abban rabi yayi, Ni wannan yaron zai kashewa waya", lallai Wazer kullum idanunka kara tsauri suke lallai ya kamata nasan abin yi tun kafin guri ya ƙure min", juyawa ya yi dan barin gurin sai dai kuma cak ya maida numfashinsa ya tsayar saboda ganin mutum bayanshi ba tare da ya yi zato ba.






Dai-dai lokacinne kuma Hajjaju rabi ta danno da motarta cikin gidan,duk da cewa da yawan jama a a gidan amma bazaka taba gane hakaba saboda girman gidan da yawan dakuna da bangarori,shi yasa ko bangaren aunty amarya babu wasu mutane sai iya danginta wanda basu wuce mutum biyar ba,sai kuma Hajiya goggo da tayi kaura ta bar sashenta tazo nan ta kasa ta tsare bayan kuma yan uwanta da suma suna can bangaren nata ta barsu,shi yasa inna maimuna ta sa mata ido saboda haka nan taji bata yadda da motsin surukartasu ba.




Ganin maza hakan bai sa rabi taji nauyin isa gurin ba,haka ta karasa ta zube ta yiwa su Abbie gaisuwa da su Abba yahya sannan ta kuma karasawa wajensu Baffa suma tayi musu gaisuwa daga nan ta tashi ta nufi cikin gidan tana tunanin inda WAZER yayi dan duk iya hangenta ta hanga bata ga ko kyallinshi ba,da wannan tunanin ta shiga falon da yar gajeriyar sallama,kasancewar falon yana girma dan kujerun cikinsa set uku ne sai ya yi kamar ba falo daya ba,shi yasa idan ba da karfi kayi sallama ba bakowane zaisan ka shigo ba,Hajiya goggo da inna maimuna sune suka amsa mata saboda sune a set din farko,zama ta yi cikin nuna ladabi tana gaidasu tare da yi musu gaisuwa,inna maimuna na cewa sai dai bamu shaidaki ba", sai ga aunty amarya ta ƙaraso zama ta yi itama tanawa ruby kallon rashin sani.




Da sauri cikin tsananin ladabi rabi'a ta zame daga kujerar da take kai ta gaida aunty amarya saboda ta shaidata dan sun taba haduwa gidan gaisuwar Halima marigayiya,amsawa aunty amarya tayi tana dan tuna rabi ar kaɗan,cikin sunkuyar da kai rabi a ta ce", baku game Ni ba ko? Bata bari sun amsa mata ba ta ci gaba da cewa", rabi a ce matar WAZEER ",yadda ta faɗa matar WAZEER din cikin kunya sai ka dauka ko haɗa ido da surukatar bata yi,Hajiya goggo ce ta ce", ayyo sannunki da zuwa bari a kira Rahim ɗin shima Wazer ɗin ai yana ciki tare da Rahim din""" wani irin duka kirjin rabi a ya yi har wani jiri_ jiri ta fara gani,sai dai kuma ba zata iya bayyana komai ba yanzu saboda abinda take shiryawa ya tafi dai_dai,ayya to Allah ya kara hakurin rashi ta faɗa tana ƙaro murmushi kan fuskarta,Hajiya goggo na shirin tashi aunty amarya ta riga yunkurawa saboda karfin jikin ba daya ba", dole ta koma ta zauna ba dan taso ba.




Inna maimuna kuwa Murmushi tayi dan kuwa taji dadin hakan da mamin RAIHAN ta yi.




Ƙur rabi'a ta zubawa aunty amarya ido tana jin kamar ta yi musu duka gaba dayansu,to amma me abun duka kissafine dole sai ta nuna musu ita din ta Allah ce kafin ta aiwatar da shirinsu saboda ko da maganar ta fallasa ta kuma batar da tunaninsu akan ta koda kuwa daga baya sun gano ta san sirrin da suke boyewa.






Duk da cewa sai anbi corridor dogo za a isa dakin Raihan ɗin to amma tunda kofar dakin na kallo falon na farko dole zaka iya ganin me shiga da fita, a hankali aunty amarya ta kai hannunta dan yin nocking din dakin zuciyarta kuwa kamar zata wantsalo saboda tunanin abinda yake wakana a dakin,kwankwasawa ta yi cikin taraddadi.




Acan cikin dakin kuwa tunda Wazer ya kashe wayar da Abban rabi yayi masa,sai kawai ya kwantar da jikinsa kan gadon tare da RAIHAN dake jikinsa kamar jaririya,tunda suka kwanta ta samu ta cukyikyiyeshi tana shaƙar ƙamahinsa me dadi yana shigewa kofofin hancinta,a hankali ta fara lumshe ido cikin kankanin lokaci Wazer ya fara jiyo tashin numfashinta cikin nutsuwa tamkar ba me bacci ba,dan dago kanta ya yi yaga tabbas dai baccin take yi, kawai sai ya tashi ya kwantar da ita sosai yasa bargo ya rufeta ya koma kan kujerar dakin ya zauna,zamansa baifi da minti ɗaya ba aka kwankwasa dakin.




Ganin aunty amarya baisa shi diriricewa ko shiga halin kunya ba ,dama Abbie ya fada masa aunty amarya yasan komai shi yasa baiji wani damuwa dan yagantaba,ita aunty amaryar ce ta kasa kallonsa kai tsaye kamar yadda take yi a baya,cikin nutsuwa ya gaidata yana kaucewa daga hanya, a'a ina Rahim din", ta faɗa tana dan leka dakin ba tare da ta shiga ba, cikin kamewarsa dake nuna biyayyarsa cikin lafazinsa ga manya ya ce", ta yi bacci", aunty amarya ta ce", to aiko a tasheta matarka ce tazo mata gaisuwa", luuu yayi da idanunsa kamar zai lumshesu sai kuma ya budesu fes akan hanyar falon,kafin cikin dakewarsa ya kuma cewa sorry Mami ki barta ta samu bacci zata iya tashi da headeach yanzu aka tasheta,aunty amarya da abin da wazir din ya yi yaso burgeta da kuma dan sata jin kunya ta fita daga dakin tana cewa shike nan kai sai ka fito kasan abinda zaka ce mata nikam ina jin kunya", wani sassanyan Murmushi ne ya subce masa wanda ba kowa ne zai lura da hakan ba,komawa ya yi dakin ya kuma gyara Raihan ɗin yana jin kamar ya zauna yayi ta gadinta har ta yi baccinta ta tashi ,zubawa ɗan ƙaramin bakinta idonu ya yi sai kuma yaji ya kasa jurewa tamkar wanda ake ja haka yaji ya kai bakinshi samannata da niyar sumba ɗaya ya fice,sai kuma ya bige da lasar lips din kamar alewar da baya son karewarta,ɗumin harshensa da ya sanar da ita bakuncin bakinshi yasa ta bude ido a hankali idanunsu ne suka sarke,da sauri ya zaro idonsa na mamakin ya akayi ya tasheta,dan langabar da kai yayi alamun hakuri,amma abin mamakin yaki dagata dan yanzun gaba daya nauyi shi ya sauke akanta,marairaice fuska ta yi idanunta sukayi narai narai kamar zata yi kuka se alokacin ya Ankara, maimakon ya tashi sai kawai ya mirgina da ita ya koma kasa ita kuma tana samanshi,ƙaramin bakinta ta tura kafin cikin alamun baccin da bai gama sakinta ba ta ce", Hamma WAZEER bacci nake ji", wani irin yamma yaji har tsigar jikinsa na tashi lumshe idanunsa ya yi tare da kuma sarketa cikin jikinshi tamkar zai hadiyeta,bai ce komai ba saboda baya jin zai iya cewar dakyar yake iya control din kanshi in dai yana tare da RAIHAN tun can baya ma bare yanzu da ya gane me yake ji ya kuma fahimci nisan da yayi cikin azabar so,so da yawa yakan yiwa kansa tambaya wai dama haka so yake idan ka samu abinda zuciyarka ke so? RAIHAN ko sunanta na musamman ne a gareshi wani irin zuzzurfanso ne wanda bai taba jin irinsa ba a wannan zamanin namu.




Hamma WAZEER ta kuma fada ganin yadda ya zuba mata ido ko kiftawa ba yayi,tashi ta fara kokarin yi saboda tasan idan ya fara wannan kallonnasa zai iya daukan awowi a haka ba tare da ya gajiya ba,bai bata damar hakan ba sai janyota da ya yi ya maida ta gefe ya ja duvet ya kuma rufeta sannan ya tashi ya subaci idanunta wanda take ta ji baccin da take ya kuma dawowa hakan yasa tunda ta lumshe ido bata kuma budewa ba har ya fita daga dakin ya rufo mata.




Tun bayan fitowar aunty amarya suke dakon bullowarsa sai dai shiru,sai da aka cinye mintina ashirin kafin su Ganshi ya fito cikin takunshinanna, idon rabi a kanshi tana jin zuciyarta na babbaka da wuta tana ci ,ji take kamar ta kashe su shida Raihan ɗin ,shin me suke yi a daki shida RAIHAN ɗin? Yadda tale kallon idanunshi kai tsaye yasa ta fahimci wani irin so me zafi wanda shi kansa Wazer ɗin ba zai iya ƙididdigeshi ba,wani irin tashin hankali ta kuma shiga ji take kamar ta yi hauka anya kuwa zata iya raba WAZER da RAIHAN? Ai ko ba zan iya ba sai na gwada idan hakan ya gagara na kashe kowa kowa ya huta,ta faɗa hakan cikin ranta tamkar tayi aman zuciyarta.




Aunty amarya kuwa da tun fotowarta tace gasu nan bata kuma cewa komai ba,mikewa ta yi ta bar gurin saboda kumyar Wazer ɗin da taji ta lullubeta,dan kallon rabi a ya yi Sannan ya dauke kansa yana ci gaba tafiya dan fita daga falon ya ce ", Rahim tun ɗazu ya yi bacci baya bukatar hayaniya yanzu", daga haka ya zura dogayen kafafunshi waje bayan ya bude kofar ta zallar zaiba ya ciewarsa ba tare da ya damu da abinda yace din ba.


Dakyar rabi a ta hadiye abinda yake taso mata sannan ta dubi inna maimuna da goggo ta ce", shike nan Ni zan wuce idan ya tashi a yi masa gaisuwa", inna maimuna ta yi saurin cewa bari a rakaki can wajen mahaifiyar me rasuwar ki mata gaisuwa", itama rabi'a cikin dakiya ta ce", ai can na fara zuwa Allah kara hakuri", daga haka ta fice daga falon kamar zata kifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login