Showing 135001 words to 138000 words out of 189984 words
Chapter 46 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
haka dole komai mu bishi a sannu in dai ba so muke rayuwarmu ta kare a gidan bursuna ba", kallon kallo suka shiga yi kafin duk su jinjina kai alamun dai sun gamsu da hujjojin shugaban jam'iyyar yan adawartasu...
___________
Tunda suka samu suka Ganshi aka umarce su da su barshi saboda ba ason yawan hayaniya akansa, Raihan dai dakyar baffa ya rarrasheta suka fita amma cewa ta yi babu inda zata tana kusa da Abbie dinta,
Abun bakaramin mamaki ya bawa Aunty amarya da Hajiya goggo ba ganin mama murja har da ita a lallashin Raihan, wannan abu ya mugun dasa ayar tambaya a zukatan wadannan mutane ukun,Aunty amarya momy Hanne HAMMA IDRES,da kuma hajiyar agadex......✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page50 ```
50
.....Sam mama murja bata kula da irin kallon da suke mata ba zuciyarta daya take rarrashin RAIHAN.
Tana tsaka da kukanne hancinta ya fara shako mata ƙamshin da a duk inda take ba za ta kasa gane shi ba,kanshin da bata taɓa jinsa a tare da kowa ba sai wani mutum daya da ya zama wani babban jigo a rayuwarta,ɗif kukanta ya tsaya kamar daukewar wuta", kafin a hankali ta dago kanta dake jikin inna maimuna,idanunta da su kayi ja basu sauka a ko ina ba sai kan WAZEER da yake takowa zuwa garesu cikin wani nutsatstsen taku tamkar wani Basarake me iko da birane goma", samun kanta ta yi da kasa dauke idanunta akansa saboda wani irin kyau da taga ya mata,sai take ganin yadda take jinta daban shi dinma haka take kallonsa a daban saboda yau ne rana ta farko da ta Ganshi a Raihan dinta ba wai ƁOYAYYIYAR RAIHAN ba.
Yana karasowa daf dasu ya rissina gaban baffa da Abba yahya ya mika gaisuwa cikin nutsuwarshi dake hade da wani irin girmamawa. Hamma Idris da Hamma Affan dukkansu hannu ya basu su kayi masabaha,kafin ya gaidasu hajiyar agadex yana musu jaje da fatan samuwar lafiyar Abbie,duk abinda yake idanunshi da zuciyarshi na kan Raihan,wani irin kyawu ta yi masa me tsayawa a rai gani yake kamar yau ya fara ganinta ,eh zai iya cewa yau din ya fara ganinta amma a cikin shigarsu ta mata yaune ta fito masa sak kyakkyawar mace matashiyar da ta fi ko wacce mace a idanunsa da kuma zuciyarsa.juyowa yayi da nufin gaida aunty Amarya amma sai wayam babu ita a gurin, ɗan lumshe idanunsa ya yi yana maida kallonsa kan RAIHAN da idaunshi suka kasa daina zagawa a kan jikinta da duk wani motsinta,yayin da ita kuma ta yi zukudi tana kallon inda mamin ta yi,sarai yasan saboda shi tabar gurin RAIHAN ma tasan haka,ragowarne dai basu fahimta ba,saboda ba kowa ne ma ya kula da tashin nata ba.
Shigowar Dr Sabo reseption dinne yasa suka maida hankalinsu kansa, hannu ya bawa Wazer yana cewa surukinmu Barka da zuwa",yauwa Dr ya jikin Abbie fatan babu wata matsalar? Babu in sha Allah zai tashi normal kamar komai bai faru ba", Allah yasa zan iya ganinsa? Wazer ya bukaci hakan daga wajen Dr Sabo ", ey me zai hana yawan hayaniya ne kawai ba a so anayi akansa shi yasa muke hanawa",, ok thanks wazer ya fada yana nufar dakin", da sauri RAIHAN ta mike bata saurari komai ba ta bi bayanshi dan har ga Allah so take ta kuma ganin Abbie din...da kallo suka bi ta cike da tausayi.
Rabi'a dake makale tana kallon duk abinda ke faruwa ji tayi zuciyarta kamar zata fito waje,kallon da taga wazer yana yiwa Raihan ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba ita kadai ta san me ta hango cikin wannan kallon duk kuwa da cewa tana dan nesa da su,to amma dake hankalinta yana kansu babu abinda bata gani, da da yadda za ta yi ta bi su dakin da sai ta bisu ko dan ta Korewa kanta shakkun result dinta,tunawa ta yi a kwai window ta can baya yasa ta yi a zamar juyawa ta fita daga reseption din,motar gidansu ta hango ta shigo da alama su Abbu ne suka zo dubiya ta aiyana hakan a ranta.tsayawa ta yi dan ganin dawa dawa suka zo,sai dai bata bari sun ganta ba.
Abbu Ammi da su salim shukra har da umma rumana,gaba daya dai family din wazer innawuro ce bata gani ba da alama har yanzu bata yi amanna da auren ba,ji ta yi idanunta suna wani tsaki tsaki saboda azabar bakinciki,ganinsu da ta yi gaba daya ya bata tabbacin cewa suna tare da RAIHAN ke nan, ganin suna kosanto in da take yasa ta yi saurin barin gurin ta nufi inda zuciyarta ke tunzurata zuwa.
Hasashen rabi a ya yi daidai dan kuwa lokacin da wannan sirrin ya fasu,Abbu bai yi wani nuku nuku ba gurin fayyace musu komai ba,sai dai fa innawuro ta yi tsalle ta dire akan ita fa sam bata yarda da wannan cakudaddan al'amari ba,jikanta ba zai zauna da mata maza ba", a haka gayyar taron ta watse ba tare da Abbu ya samo kan innawuro ba, Ammi kuwa bata ji komai ba sai son RAIHAN da tsananin tausayinta ta ji kuma zuciyarta ta karbeta da hannu bibbiyu kai ji take ma fa kamar sai yanzu ne ta yi suruka ta hakika.haka shukra da taji tana wani irin dokin zama da RAIHAN a matsayin matar Hmmansu WAZEER, wannan dalilin ne yasa innawuro bata zo dubiyar Abbie da jajanta musu ba,shi kuwa Abbu hatta su salim da Khalid bai bari ba ya sako su gaba dan duba abokinsa kuma surukinsa.
Abban rabi ne zaune a falonshi yau yini guda ya kasa fita, duk abinda yake faruwa a tv yake kalla,zuciyarshi ce kawai ke kaiwa da kawowa da tunanin yadda za ayi yafi dan uwansa,abu na farko da ya fara tsole masa ido shine bataliyar arzikin da Allah ya bashi da daukaka ta hanyar gaskiyar shi dake amfani ta kafafen yada labaranshi,na biyu soyayyar da yake ganin mahaifiyarsu tana nuna masa,na uku ya samu irin matar da yake da burin samu a rayuwarshi, uwa uba yazo ya samu ya'yan da duniya take alfahari da guda daya gashi biyun ma sun dawo za a fara amfana da su wanda idan ya yi sake bai san su kuma irin gudummawar da zasu kawo har a fara jerasu a manyan attijirai ba,duk inda ya kalla sai yaga shine koma baya a cikinsu,Gara ma yaya ita Macece kuma ta yi aurenta, shi fa babu dukiya babu suna sannan babu ya'ya.
Ina ba zai yuwu ba tabbas ba zai yuwu zuciyata da idaniyata ba za su taba lamuntar ganin yaya Chibado cikin dukiya walwala daukaka ba,dan haka duk yadda zanyi sai nayi ko da ace ban samu dukiyarsa ba to na dau alkawarin babu wani cigaba da zai kara samu dole mu dawo daya da shi, dole ya rasa dukiyarsa ko yayansa ko ɗaukakarsa,ba zan iya jurar ganinshi cikin duka wadannan abubuwan ba, WAZER ya ambaci sunan cikin kaunshin murya wazer ɗin na gurin, kana ya cigaba da cewa kaine ka dai yafi cancanta da kabar duniya na san idan har na taba ka tamkar na taba rayuwar zuriyar Chibado ne,da wannan kadai ya isa na tarwatsa farin cikin Chibado tunda na fahimci shine kashin bayansa,karasawa ya yi gaban katon hoton su da suka dauka fuskokinsu cike da fara a,shafa hoton yayi dai dai fuskar Abbu kana ya ci gaba da magana tamkar wani zararre,yaya kayi hakuri ba zan iya juraba ,yadda ka raba Ni da soyayyar mahaifiyata kaima sai na raba ka da soyayyar da guda da yafi soyuwa a zukatan ku daga kai har innawuro,da zan samu yadda nake so to tabbas sai mun dawo dai-dai da kai,ma ana 'ya ɗaya babu dukiya babu daukaka babu 'ya'ya," ya karasa fada yana hadiye wani kullin abu da ko ya hadiye shi ba ya sauka, ya kuma tabbatar da cewa ba zai taba wadawa ba har sai ranar da ya cimma burinsa akan kudurinsa na tarwatsa rayuwar dan uwansa.
___________
Duban Surry yake cike da jin haushi,kafin ya ce", yanzu dai wannan shirin namu ya wargaje akan tarkon da mu kayiwa Raihan ke nan? Shiru Surry ta yi na yan wasu sakanni kafin ta bude baki ta ce", yallabai Ni ina ganin mu saurara tukunna muga abinda zai faru tsakaninsu,kar muyi saurin yanke hukunci tunda kaga yanzu ita rabin ta bisu can asibiti dan ta samo mana rahoton abinda ke faruwa", zuba mata ido ya yi ta cikin facemask dinshi da jajayen idanunshi da suke boye cikin bakin sunglasses,Surry har ta fidda ran maganarshi sai kuma cikin wata irin murya wadda bata isa tantance Muryarsa guda ba,ya ce", shike nan na baku sati guda idan banji abinda nake son ji ba to tabbas zan dau hukunci na gaba", daga haka ya mike daga kujerar da yake zaune ya fice daga gurin cin abincin ba tare da ko waige ya yi ba.
RAIHAN WAZER....
Yana shiga kafin ya rufe kofar itama ta sa kai , a tare suka karasa gadon da Abbie yake kwance tamkar gawa.
Tsayawa ta yi a gefenshi ta inda ta ke iya kallon fuskar Abbie dake rufe hancin shi sakaye cikin abin jan numfashi,a hankali zuciyarta ta fara rauni har idanunta da gangar jikinta suka shaida hakan,saboda yadda idanunta suka fara zubar da ruwan hawaye gangar jikinta kuwa ta fara rawa saboda rausayin halin da Abbie din yake ciki da su kansu ma ahlinsa.
Kukanta ne ya fara karfi kafafunta na son kasa daukarta,tana gab da zubewa kasa ya saka dogayen hannayensa ya tarota ba tare da ya bari gwiwowinta sun sauka kasa ba,gaba dayanta ya yi mata masauki me kyau cikin lafiyayyan ƙirjinsa me fadin dake nuna alamun cikar namiji,samun kanta ta yi da kara narkewa ajikinshi idanunta na ci gaba da tsiyayar ruwan hawaye.dago fuskarta ya yi ya saita da tashi fuskar sannan a hankali ya shiga hura mata iskar bakinshi da ke fitowa da wani irin lafiyayyan ƙamshin banana strawberry,kif_kifta idanun ta shiga yi hawayen na bushewa suna daskarewa a kan kuncinta,ganin yadda take farfari da idanun ya sa shi fidda wani dan asirtaccen murmushi da babu me zarrar ganinshi sai wadda yake rike da mukullin zuciya irin rikewar nan ta har abada wadda bata da karshe.dan kawar da fuskar ta yi tana son basar da abinda yake mata yawo a can kololuwarta ,sai dai kuma hakan ya ki samuwa,dan kuwa dan gidan Ammi jikan innawuro ya yi zarra ya kai can_can kololuwar da bata jin zata iya sarayar da abinda take ji akansa, wannan dalilinne yasa ta kalleshi kallo me cike da sirrinkan da ita kanta bata iya kidayesu da yi musu fassara me sauki,cikin hikimarsa ya sarke idanunnasu yayin da bugun zuciyoyinsu ke tafiya a tare cikin wani irin yanayi me taba ruhi da gangar jiki,hannu ta sa ta taɓa sajenshi da yake matukar kayatar da ita sannan cikin tura karamin bakinta ta ce", Hamma wazer ina son Abbie bana so wani abu ya sameshi", a hankali ya kai tattausar labbanshi jajayen saman nata ya bata wata kyakkyawar sumba kana cikin deep voice dinshi me cike da kamewa ya ce", Nima haka ina son Abbie saboda ya bani wani abu guda me muhimmanci da tsadar da yafi tsada tsada dan haka ina mishi addu'ar samun lafiya ko dan yaga irin da kyakkyawar tsadar da ya bani zata ajiye masa a matsayin sanyin idaniyarsa", sam RAIHAN bata fahimci ko guda daga saurancan da wazer ya yi mata ba,hakan yasa ta kalle shi cike da yarinta ta ce", HAMMA WAZEER me Abbie na ya baka ban sani ba? Za ki sani nan gaba kadan ranar da na fidda irin daga cikin tsadar? Tsaf ya kuma kulle kanta dan haka cikin sakalcinta ta kuma bude baki za ta yi magana amma sai caraf dan gidan Chibado ya cafe harshen da bakin gaba daya idanunshi cikin nata da ta zarosu tana duban inda Abbie ke kwance gadon asibiti.
Wani irin numfashi me tsananin zafi da kuna rabi a ta fesar yayi da ta bude baki kamar zata yi ihu sai kuma ta yi gaggawar dinke bakin da tafukan hannayenta,amma fa ta kasa hana zafafan hawayen da suka fara tsere saman kuncinta zuba, wannan wace irin masifa ce haka? Ji ta yi tana neman zarewa gashi ta kasa matsawa daga jikin window din da take leken su kasancewarsa glass me garaigarai yasa take ganin komai kamar a gabanta.
Wazer da baisan me ke faruwa ba ya sa hannunshi ya tallafi keyar Raihan yana kuma yi mata brosh da harshensa tawunsa yana zagaye ko ina na cikin bakinta,taba kofar dakin da akayi ne ya bawa RAIHAN damar son kwace kanta,amma sai wazer bai bata damar hakan ba hasalima shi kunnuwansa ba ji masa alamun shigowar da ake yi ba,da kyar RAIHAN ta samu ta kwace bakinta daga nashi amma ta kasa kwace jikinta da yake rike da shi kamar ance za a raba shi da ita,ɗan kallon idanunshi da suke a lumshe ta yi sannan cikin rada ta ce da shi HAMMA WAZEER za a shigo fa ina ga su baffa ne", ko gezau baiyi ba saima hannunsa da ya shiga yawo da shi a sassan jikinta,doke hannunshi ta yi za ta kuma yin magana amma sai maganar ta tsaya cak dalilin shigowar su Abbu da Ammi da kannanshi su salim sai kuma Abba yahya da yayi musu jagorar shigowa duba Abbie ɗin,wani irin kakkauran miyau Raihan ta haɗiya na tsananin kunya da tsoro,rasa yadda za ta yi da abin kunya yasa ta fashewa da kukan da ya fahimci sam baya yi mata wahala, a hankali ya bude idanunsa da suke a lumshe dan dubanta ya yi sannan ya maida kallonsa kan su Abbie da su kayi kamar basu gansu ba,fahimtar abinda yasa ta kukanne yasa shi ɗan zame ta daga jikinshi ya rike Duka hannayenta kanta a kasa tana faman murza idanun da suka ki tsayawa da ruwan hawaye,ji ta yi kawai yaja ta ba tare da tasan inda ya nufa da ita ba ta bishi,hannunta ya cire daga nashi ya saka a na Ammi odanunshi akan Ammi din da ta ki kallonshi,yasan wacece mahaifiyarshi sarai yasan abinda ya hanata kallonshi,ɗan murmushin da ba ko da yaushe aka cika ganinshi a kan fuskarsa ba ya yi kafin a hankali cikin sautin Muryarshi me tafiya da wata irin Hausa irin ta Fulanin da suka ji boko turanci ya zauna a bakinsu ya ce", Ammi ga RAIHAN", jin haka yasa RAIHAN saurin dago da kanta aiko ta ci karo da fuskar kyakkyawar mace me cike da kwarjini irin na danta tana yi mata kallon da zamu iya kiranshi kallon kauna ta fisabillihi da yadda da jin cewar ey lallai nayi suruka. Sosai Ammi ta damƙe hannun Raihan tana mata murmushi,ganin raihidin ta rasa sukunin sakewa da kunyar da wazer ɗin ya bata yasa Ammin janta jikinta tana cewa ya dai Raihan duk kukan rashin Abbie ne? Girgiza kai Raihan ta yi kafin cikin dan son sakewa ta ce", ina wuni Ammi? Lafiya kalau Raihan ya me jikin kuma? Alhamdulillah ta faɗa tana satar kallon Wazer da take jin idanunshi na yawo a jikinta, Ammi ta ce", ki yi hakuri kinji Raihan ko mai yana wucewa kamar ba a yi ba, kuma duk abinda kikaga ya faru da bawa to haka Allah ya tsara masa babu tsimi babu dabara abinda Allah ya zanawa mutum sai ya faru in sha Allah zai samu sauki kinji", a wannan karon sosai ta kalli Ammin kafin cikin jin wani kwarin gwiwa ta rungumeta tana ji kamar maminta ta rungume.
Haka Abbu ta yiwa Raihan nasiha da rarrashi cike da nuna kulawa da kauna,shukra da kananan wazer duka babu wanda aka bari a baya wajen nuna tattalinshi da kauna akan Raihan ɗin,sosai Raihan taji kaunar wannan ahli masu tsananin mutunci karamci sanin ya kamata da uwa uba ilmin addini wanda komai za su yi sai sun saka Allah da manzo a ciki", wani irin sanyi zuciyarta da gangar jikinta su kayi, saboda yadda a cikin mintuna ta ga tsagwaran ƙauna daga ɓangaren wazer ɗinta, dole ne wazer ya kasance na musamman domin alhlinsa ma na musamman dinne.
Duk suka fita daga dakin Raihan na tsakiyar umma rumana da shukra da suke ji kamar su tafi da ita gidansu tun yanzu.
Rabi da a na mutuwa a dawo to zamu iya cewa ta mutu sau kusan dari ta dawo,a wannan karon ta kasa yin sambatun sai zare ido da take yi tana jin zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito,tunda take gaisuwar mutunci ma bata taba samu daga shukra da rumana ba amma wai sune suke neman maida Raihan cikinsu saboda kauna,Ammi da bata taba kama hannunta ko da sunan fada ba bare har ta samu runguma ,amma yau Raihan makiyiyarta wadda ake kira da kishiyarta ita ce rungume jikin Ammi tana bata kulawa kamar ƙwan da ba ason fashewarsa,tafiya kawai take bata san in da take jefa kafafunta ba,duniyar ce kawai ke juya mata kamar katantanwa.
Surry da tun ɗazu take zagayen neman inda zata ga ruby ta hangota kamar zata kifa bata san inda take cilla kafarta ba,da ace motoci na yawo a harabar gurin tabbas babu abinda zai hana wata motar yin awan gaba da ita,da sauri ta janyo ta tare da jefata cikin motarta da sauri suryn ta shiga mazaunin direba ta figi motar da gudu suka bar harabar asibitin.
Haba ruby wai so kike ki tona mana asiri ne? Ke me yasa baki daukar abu ta yadda zai yi miki sauki? Wannan zafafawar da babu abinda zata yi mana saima aikin danasani da za ta yi mana", ihun da Ruby ta saka ne ya firgita sury har ta nemi sakin sityarin motar,amma dake Allah bai tsara musu mutuwa a lokacin ba sai ta yi saurin taka burki a gefan Titin tana maida numfashin firgici da tashin hankalin da ta shiga,idanunta akan ruby da ko gezau bata yi ba........✍🏽
Pg51
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
A tsorace Surry ta iya