Showing 153001 words to 156000 words out of 189984 words
Chapter 52 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
ta yi,aoch ya kuma fada sai yanzu ta dago a saɗaɗe kamare tsoran wani abu", haɗa ido su kayi sai ya dan turbine fuska tare da kashe mata ido ɗaya sannan ya nuna mata saitin zuciyarshi da kanshi kafin ya bude baki a hankali ya ce", zaki kashewa Ammi yaro bayan lalata mata shi da kika yi kin samu zuciyarsa kin cinye kin lalataasa tunani baya jin komai sai ke baya ganin komai saike anya ko Raihan ba za ku yi Shari'a da Ammi ba? Idanunta me suka yi raurau dan har ga Allah bata fahimci me ya ke nufi ba,HAMMA yaushe na lalataka?dame na lalataka kuma? Yaushe kuma na cinye zuciyarka? yaushe na lalata tunaninka? Ta karasa fada hawayen da basa yi mata wuyar fita suna gangarowa.
A hankali ya fidda harshensa yasa ya lashe hawayen yana cewa ki yi ta hawayenki Ni kuma bazan fasa shanye kayana ba,bana kusa ne kawai banyarda ki zubda wadannan hawayen ba,dan nasan muddin bana kusa hawayenki bana sangarta ba ne na damuwa ne", rufe idanunta ta yi tana jin ɗumin harshensa da ya dora a kumatunta yana tsotsa kamar wanda ya samu sweet..........✍🏽
Haba wazer ya da haka kayi hakuri mu kai maka ita mana😂
Gaskiya a kyalemu haka kar a haukata mu mu kasa rike kanmu😂
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page57 ```
A hankali take sauke numfashin wahalar da gangar jikinta da zuciyarta da wazer yake yi", bata da yadda ta iya dole ta biyeshi dan taya shi Baccin kamar yadda ya bukata.
______________
A wannan yinin abubuwa da yawa sun faru wanda suka danganci nasarar masu gaskiya da kuma faduwar marasa gaskiya.
A bangaren Dr Sabo ma baiyi da wasa ba wajen binciken wanda ya yi waya da Aunty Amarya,dan haka shima tabangarenshi yana samun cigaba,haka nan Allah ya haɗa kauna tsaftatacciya tsakaninsa da nur da Aunty Amarya shi yasa yake jin zaiyi komai akansu domin yin hakan jihadi ne gareshi.
__________
Tunda aka kaishi magarkama aka aje har yanzu ba a sake waiwayensa ba,kullum jira yake a fito dashi dan yanke masa hukunci akan abinda al'umma take zaton ya aikata amma sai shiru yake ji,gashi an hana kowa ganinsa duk wata kofar da zaiga wani nasa an hanashi wanda shi yasan ko daga ina hakan ta faru,lallai da duniya zata bashi damar fito da ainahin waye Abba yahya to da tabbas tasha mamaki kuma ta koka akan lamarin mutanen duniya,to amma ya ya iya tunda bashi da karfin da zaija da Yahya ya riga yayi amfani dashi wajen gyara sunansa ya rufe ainahin fuskarsa,dan haka ko ya bayyanawa duniya ba lallaine ta yadda ba, sai dai idan yana da hujjojin gani da ido shi kuma a yanzu bashi dasu,Flash din da suke takama dashi yana hannun haidar HAIDAR kuma ya bace,kuma shima baya da wata tantama akan cewa Abba yahya ne ya daukeshi,dan gyara zamansa ya yi a saman dan gadonshi yana jin zuciyarshi na kuna da tafasa akan halinda amininsa yake ciki,a yanzu bashi da wani buri illa ya taimaki nur da Raihan daga hannun azzalumi dan yana da tabbacin wannan lokacin shine daidai lokacin da Abba Yahya yake son cimma burinsa akan RAIHAN da abinda ta mallaka.
__________
Akan idanun rabi a suka fito daga office dinsa suka hayo lipter,fuskar nan tashi babu alamun Rahma a gimtse take,sai dai binda ya fara janyo hankalin staff din kansu shine yadda ya ke rike da hannun Raihan ɗin kam tamkar ana damben kwatarta a hannunsa,duk inda suka gifta sai dai kaga ana sadda kai kasa dan babu halin yin kallon kurulla sai dai daga nesa nesan,a haka suka karasa har motarta, securitys ne suka shigo nasa suka biyo bayansu dan kasa barin Raihan ya yi ta tafi ita kadai,haka nan yake jin ba daidai ba tamkar dai wani abu na shirin faruwa.
Wani mugun tsaki rabia ta saki sannan itama ta fito dan tafiya,babu abinda ya kuma bakanta ranta irin yadda aka dinga nunata Allah kadai yasan me mutane suke fada akanta abinda taso ace Raihan akewa sai gashi ita ake yiwa,a fusace taja motar ta fita tana ayyana cewa idan Abbanta bai dauki mataki ba to lallai ita zata dauka, dan dama tuni ta cire Surry daga almarinta duk da dai bawai ta rabu da ita ba ne,dole watarana zata yi mata amfani.
Karfe biyar shine akafi sani da lokacin tashin ma'aikata hakan yasa a daidai wannan lokacin tituna suka cika da ababan hawa kowa kokari yake yaga yakai zuwa muhallinsa dan haka suma wadannan ahli gida biyu suna daga cikin masu hanzari dan komawa ga muhallinsu,
A tare motar Raihan data su Affan suka shigo gidan,wazer ne ke driving dan haka cikin nutsuwa ya samu guri yayi fakin sannan suka fito Dukansu a tare", hannu HAMMA Idris ya mika masa suka yi masabaha haka Affan ma, Raihan ta ce", mun dawo a tare duk da dai mu mun biya wajen Abbie ", ta faɗa tana kallon hamma Idris, Affan ne ya ce", gaskiya ne mu dinma mun dan tsaya ta wani guri Idris ya dan yi uzuri", mika mata key wazer ya yi yana cewa zan shigo anjima ina son magana da mami", jinjina kai ta yi tana karbar key ɗin ,maimakon ya bata sai ya haɗa da hannunta ya riƙe dan duban gefansa ya yi yaga su Affan sunyi gaba hakan yasa ya karasa janyota jikinsa alokaci daya yana bata kyakkyawar sumba a tausasan labbanta da suka yi ja saboda tsotsan da suka sha a gurinsa ", good night ya fada yana sakinta tare da ja baya har ya juya dan fita cikin nutsatstsen takunsa,kasancewar motocinsa suna waje basu shigo ba yasa dole sai ya yi tafiya me dan tsayi.kasa tafiya tayi tana kallonsa har sai da yazo bakin kofa sannan ya dakata tare da juyowa alama ya yi mata da ta shiga gida,cikin sanyin jiki ta juya tana jin idanunsa a jikinta har ta shige ƙatuwar kofar glass din sashensu.
A hankali ya ɗan sauke numfashi kafin ya fita daga gidan yana dagawa securitys din gidan hannu.
Da misalin karfe tara na daren ranar, innawuro ce zaune kan kujerarta ta mulki sai Abbu da abban rabi da yake ta cika yana batsewa,dan a kwanakinnan sosai yake kasa boye mummunan halinsa da hassadarsa akan dan uwannashi,sai kuma Ammi da OGA kwata kwata Ahmad wazer,da matarshi rabia Mustapha Chibado,bayansu ba a bawa Kowa umarnin zama ba hatta su Khalid hayewarsu su kayi sama inda dakunansu yake.
Cikin nuna girma na amsa sunan uwa me faɗa aji da kuma fada gurin diyoyinta, innawuro ta fara magana, Mustapha Inaso ka maimaita abinda ka fada min dazun saboda inason duka nan suji laifin dansu akan yarka kamar yadda ka fada", ta faɗa idanunta akan ABBAN rabi da lokaci daya duk ya dabarbarce kai kace bashi ne yake wannan kumfar bakin dazu ba,dan muskutawa ya kuma yi a karo na wajen hudu tare da dan goge goshinsa da gumin rashin gaskiya ke tsatstsafo masa,shiru na kusan mintuna uku kafin innawuro cikin kufula ta kuma cewa kaifa muke sauraro Mustapha ", um ey dama rabi ce dazun ta kirani take kuka akan rashin adalcin da wazer yake mata sannan suna mata rashin dacewa shida matarsa a can gidan jarida,kullum sai sun sata kuka bakincikin hakan yasa ta kirani ta faɗa min,gashi kuma ta ce", gidan ma ba ya dawowa wataran ma ba ya kwana,GASHI KUMA BAYA BIYAN HAKKIN AURENTA DA YA RATAYA AIANSA.....ɗuf falon ya yi baka jin karar komai sai ta fanka da a,c,Ammi kam kasa kallon kowa ta yi a wajen shi kansa abbu bakaramin kunyar maganar nan yaji ba.
Innawuro ce ta kore shirun da ɗan sauke numfashi sannan ta dubi wazer tana cewa, kaji abinda matarka ta fadawa ubanta akanka me zaka ce game da hakan shin gaskiya ta faɗa? .
A hankali ya dago kansa dake kashingide tun dazun, kai idan ba lura ka yi Bama sai kayi zaton baya falon,bude idanunsa ya yi sosai akan rabi a dake rakube a gefe idanunta tarwai akansa babu alamun karaya ko jin nauyi a tare da ita,ji ya yi yana rasa abin cewa yo haka kawai ma ya rasa abin fada bare kuma irin wannan lamari me zafi haka,maida dubanshi kan innawuro ya yi kana a hankali ya bude bakinshi da yayi masa nauyi ya ce", innawuro bansan daga ina wannan maganar ta fito ba dan haka bani da abin cewa", idan kuma.kuka ce lallai sai na ce ɗin to tabbas abinda zan fada akanta ba zaiwa kowa dadi ba har ita ɗin ", daga haka ya mike yana wa Amminshi sai da safe,ko kallon inda ABBAN rabi yake sake da baki baiyi ba.
To ke rabi kinji abinda ya fada kuma kinsan halinsa baya zama dan ya yi maganar shirme,cewar innawuro tana duban ABBAN rabin", aiko cikin fushi ya mike yana cewa tashi mu tafi rabi wallahi wazer zaisan Ni yayiwa wannan cin fuskar ko da yake ba laifinsa ba ne daurin kugu ya samu shi yasa yake abinda yaga dama a gida da wajen aiki hatta inda ba zuwa yake ba zuba iko yake a gurin, wallahi wannan laifin na yaya ne innawuro haka kawai ya zauna yaro karami yana juyashi tamkar shine ɗan ba uba ba,to Ni 'yata ba zata zauna ta yi zaman boranci ba dan haka duk ranar da aka isa dashi yazo ya tafi da ita", daga haka fuu yaja hannun rabi suka fita daga falon.
Abbu zaiyi magana innawuro ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu,sannan ta ce", tashi kaja matarka ku koma bangarenku Allah ya yi muku albarka shi kuma Allah ya ganar dashi", Amin ya Allah abbu ya fada yana tashi ɗan bin umarnin mahaifiyar tasu.
Innawuro ta jima tana saka da warwara akan ABBAN rabi,tabbas ta fahimci akwai wani abu tsakanin Abbu da Mustapha sai dai amma tafi danganta matsalar daga ɓangaren ABBAN rabi,shi yasa bata dakatar da wazer ba ta barshi saboda tunda taga ya yi haka to lallai akwai wani abu akasa,amma in sha Allah ba zata zama sakaryar uwa ba koma meye zata gano tunda dukansu babu wanda bata san halinsa ba ciki da bai.
______&&
DUDU
Sosai dare ya tsala tunda wannan lokacin zamu iya kiransa da tsakiyar dare,kwance suke shida baturiyar matarsa,bacci take sosai yayin da shi kuma yake ta duban agogo daga gani dai a kage yake,saura mintuna biyu lokacin da tsohuwa me jini zata zuke jininta ya yi, amatukar kage yake saboda wannan aikin shine mataki na karshe da zai kai dan cimma mafarkansa.saura minti ɗaya.
A hankali jeniper ta bude idamunta wanda ita kawai ji tayi kamar an ce ta farka,a can kasan makoshinta ta fara ambatan sunan alhakimu, wanda ji ta yi kawai ta ambata duk da bata kasance musulma ba,kafin a hankali ta bude idanunta gaba daya akan bayan mijinta da ta Ganshi tsirara haihuwar uwarsa yana tsugunne yana karanta wasu ɗalasumai da ko a Yaren Chaina bata taɓa cin karo da makamantansu ba,sai kawai ta koma ta yi luf ,duk da yadda kirjinta ke bugawa kamar zuciyarta zata fito,amma hakanan ta daure tana so taga abinda Bashir din ke son yi.
Wani irin bakin hayaki me tsananin kauni ne ya turnuke dakin kafin cikin kankanin lokaci tsohuwa ta bayyana,fuskarnan Tata kamar kayi amai saboda kyama,wangamemen bakinta ta bude wanda ke fitar da wani irin wari wanda ke gairaye da bakin hayaki ta ce", DUDU wannan matakin shine matakinka na ƙarshe daga wannymatar taka ka gama bamu jinin nasara sai kuma jinin musulmi,kamar yadda ka sani mu muke hasko maka matar da zaka aura wadda jininta zai mana amfani,to a wannan karonma haka za muyi kuma ba tun yau ba mun nuna maka matar da muke so ka aura a musulmai kuma ka ganta,dan haka muna karbar wannan jinin gobe zaka fita domin farauto waccen yarinyar, saboda ita dama wannan ba wani abu za ayi wa gawarta ba tunda ba musulma ba ce", jinjina kai kawai Bashir yake yana sauraron bayanan tsohuwa.
Jeniper kuwa tuni zuciyarta ta buga da yin wannan mummunan ganin tun kafin su shanye jininta ta ce ga garinku nan.
Kai tsaye tsohuwa ta yi kan jeniper dan tsotse jininta amma sai cak ta dakata tana kallon jeniper da jajayen kwalakwalan idanunta,kafin cikin muryarta mara daɗi ta ce", DUDU wannan aikin ya lalace dan wannan ta riga ta mutu jininta babu abinda zaiyi mana dan haka sauranka jinin mace biyu aikinka ya dawo baya",runtse ido ya yi yana jin wani irin mugun takaici kafin cikin neman rangwame ya ce", me jini shin bazan samu wata hanyar kawo kowa ba dole sai ta wannan hanyar? Babu hali DUDU dole duk macen da zaka bamu sai ka sadu da ita,alfarma daya kawai jini zaiyi ma shine zaka iya kawo jinin matar da ka sadu da ita ko ba ta hanyar aure ba,ma'ana dai ba sai ka aureta ba,amma wannan sai daga karshe sai bayan ka auri waccan yarinyar da muka zaba maka idan yaso wancan aikin sai ya zama shine na karshe", daga haka ta bace daga dakin,shi kuma Bashir ya fasa kukan mutuwar matarsa.
Washe gari rasa yadda za ayi da gawar jeniper a kayi daga karshe dai Bashir ya ce", ya tuna tana da yar uwa a nan ,dan haka ya kirasu suka zo suka dauki gawar.daga nan Bashir ya fara laluben neman suryy.
A yau dinne da takansance weak end ranar Hutu ga daukacin ma aikata,dan haka Raihan tana gida babu inda ta fita,asibiti ne wazer kuma ya ce ta bari sai yazo za su je,saboda yana son zama da Aunty Amarya jiya bai samu dawowa ba sakamakon kiran innawuro.
___________
Mikawa Yusuf takardun ya yi yana cewa ka tabbaida cewa ka bata su a yau", Ni kuma nasan cewa dole a cikin kwana biyu nan na Hutu zata yi kokarin bawa Raihan yusuf kafin kwana biyu nake so nasan wacece wannan matar," wazer ya fada fuskarshi tana a yadda take kullum cikin gizago da nuna rashin son wasa", in sha Allah yau zan bata su dan yanzu haka ma Ni take jira dan na gaya mata mu hadu zan bata takardun",hannu suka yi da juna kafin Yusuf ya fice daga motar wadda ke cikin gidansa na ,g,r,a hore fillo.
Haduwarta su bata wuce yan mintuna ba,dan Yusuf bata takardun kawai ya bata tare da cewa yana so duk yadda za ta yi ta yi Raihan tasa hannu a takardun nan tunda kwana biyu tana Hutu, cike da kwarin gwiwa ta bashi amsa daga nan su kayi sallama.
_____________
Cikin sauri Aunty Amarya ta fito daga dakinta tana zura hijab alamun dai sun nuna fita zata yi, Raihan da taga tana neman fita bata ce mata komai ba,yasa ta yi saurin cewa Mami ina zaki ne haka kamar ba babu shirin fita akanki yau? Ba tare da ta kalli Raihan ɗin ba ta bata amsa da cewa asibiti zani yanzu zan dawo",a daidai lokacin ta karasa saka hijab din har da karin facemask ta fice da sauri", ɗan jim Raihan ta yi sai kuma ta mike ɗan bin bayan aunty Amarya wadda suka hadu da hajiya goggo a waje ta ce mata asibiti zata je ta dawo", dan haka haniya goggo ta nufi falon kai tsaye anan suka yi kicibus da Raihan zata bi maminta,
Kamo hannunta hajiya goggo ta yi tana cewa dawo ina zaki bita yarinya kin girma amma baki san kin girma ba,dawo nan wani dan aiki nake so kiyi min", Hajiya goggo ta faɗa tana jan hannun RAIHAN..
A daidaita Aunty Amarya ta tara ta nuna masa motar mutumin da ta ji yana waya a bayan gadin ,a lokacin tana gadin din,bata bari ya ganta ba shi yasa har ya gama wayar akan tsarin da ya yiwa yaransa na sace Raihan bai ganta ba,itama bata ga fuskarsa ba kawai dai ta gane muryarsa wadda ya fara yi mata waya da ita ya shaida mata cewa yasan sirrinta na boye RAIHAN.
Shi yasa ta dawo cikin gida ta kofar kiching ta dauko hijab ɗan bin bayansa,so take ta ga waye ,haka nan take jin wani irin kwarin gwiwa,dan haka take fatan kawo karshen zaluncin daya daga cikin makiyansu.......✍🏽
Tofa wai ya take nake ne?
Me Hajiya goggo ke nufi da dakatar da Raihan?
Shin Bashir zai samu nasarar auren sury?
To ya batun Abba yahya ne?
In sha Allah a pg na gaba za ayi walkiya muga fuskokin wasu...
Da kuna yin comments da yanzu mun gama
Da yanzu babu wannan gantalewar😂
Walle Nima na gaji🙄
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page58 ```
A bangaren Bashir kuwa suna mika gawar jeniper ya shiga gari bulayin inda zai hadu da sury ba dan yasan zai gantan ba,sai dan kawai yasan duk wannan yana daga cikin aikin tsohuwa shigo da suryn cikin rayuwarsa.
___________
OGA yana fitowa ya daga waya ya kira Surry ta same shi inda suke haduwa", cikin sauri ta karasa fita dan dama tana shirin fitowa ne ya kira ta,duk a kwanakinnan bata da mutsuwa saboda tunanin ta yadda zasu sace Raihan,wayar da su kayi dashi ne a safiyar yau akan su hadu dan tsara hanyar da zasu saceta yasa ta ɗan samu nutsuwa tasan zai taimaka mata duk da cewa ita ta dauki wannan alhakin.
Motarta babu mai dan haka ta saka kiran masu nafef dinta akaro na farko tun bayan haduwarsu da karbar lambar.
Da sauri Dady ya daga wayar yana cewa ranki shi dade hajjaju", tare da naka ta faɗa tana ɗorawa da cewa dan Allah ina son zanje wani guri idan kana kusa kazo ka ɗaukeni", babu damuwa turo min address din gun", ok ta faɗa tana kashe wayar,da sauri Dady ya tashi ya fito daga office dan kiran Salim", dan dama su ba kasafai suka fiya yin Hutu ba,kicibus sukayi da Salim din hakan yasa bai tsaya bata lokaci