Showing 126001 words to 129000 words out of 189984 words
Chapter 43 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
har sai da ya ƙaraso gida,fita yayi daga motar har ya manta da jaridar sai kuma ya tuna ya dawo ya dauketa. Wani irin bugu ƙirjinshi ya yi ganin hoton Rahim kaninshi a jikin shafin Farko na jaridar,cikin sauri ya shiga karanta rubutun take wani irin duhu ya mamaye ganinshi,da gudu ya ya taka zuwa sashen aunty amarya jikinshi har bari yake cikinshi kuwa juyawa yake kamar zaiyi zawo,da aunty amarya ya ci karo ta fito daga kiching.
Kai Idris lafiya kuwa irin wannan gudun haka? Bai iya bata amsa ba sai mika mata jaridar da yayi yana mata nuni da ta karanta.
Bin rubutun kawai take da kallo tana karantashi da wani irin zafin zuciya idanunta har wani yalo yake yi saboda tsananin tashin hankali,shin ita kuwa me ta yiwa wazer da ta cancanci wannan tozarcin a wajenshi? Babu abinda ya fi bata mamaki ma sai rubutun da ya yi da cewa ta yi haka ne saboda ta samu gado me yawa shi yasa ta boye halittar RAIHAN ta mace ta maidata namiji saboda kishiyoyinta duka maza garesu.
Jagwab haka ta zube a kan kujerar da ta fi kusanci da ita ,wani irin numfashi kawai take fitarwa tamkar wadda ake shirin zare ranta,ita wazer zaiciwa amana,to meye ribarsa na yin hakan",ko dai shima yana da wata boyayyar manufa akansu ne? Mamin Rahim dan Allah ki yi min bayani ki fitar dani daga cikin duhu wallahi duk na rude da wannan labarin ,shin ma wai taya hakan zata faru ? Kuma da gaske ne Rahim Macece kika boyeta ? Idan haka ne taya kika iya yin hakan? Kuma saboda me? Ni dai iya sanina Abbie yana matukar son samun ɗiya mace shi yasa nake ganin kamar da wuya ace Ansamar masa mace amma an ɓoye hakan? Idris ka rabu dani da wannan tambayar abu daya zan iya amsa maka shine ey RAHIM ba namiji ba ne macece kuma ita ce", RAIHAN dan Allah ka rabu dani daga haka",tana gama fadar hakan ta mike ta bar falon wasu hawaye Masu radadi suna gangarowa daga cikin idaniyarta.
Sakalo hamma Idris ya yi yana bin hanyar da ta yi da kallo ji yake tamkar mafarki ne yake yi.sallamar wazer ita ta katse masa dogon nazarin da ya tafi,a hankali ya juya yana kallon Wazer ɗin da kwarjininsa sai ya samu kansa da kasa cewa wazer ɗin komai,bin gefansa kawai ya yi ya fice daga falon zuciyarshi cike da tunani da son jin yadda a kayi hakan ta faru,sai yanzu abubuwa da dama suke dawo masa akan ɗabiun RAIHAN da yadda take acting like male,da wannan tunanin ya nufi bangaren mahaifiyarsa mama murja.
,,,Ɗan bin bayan idiris din da kallo ya yi kafin ya ɗan sauke numfashi,ganin babu kowa a falon yasa ya nufi corridorn dakin RAIHAN,sai dai yana sa hannunsa dan bude kofar yaji Muryar aunty amarya cikin kaushi wadda ke fidda tsananin ɓacin ranta da kuma tashin hankalin abinda fallasar sirrin zai jawo musu,ta ce",,kar ka sake ka shiga inda ɗiya take ka fice ka bamu guri Bama bukatar kara ganin wannan fuskar taka a cikin rayuwarmu,dan haka ina jiran takardar sakin RAIHAN zuwa nan da gobe idan kuma ka shirya ka bani ita yanzu",fuskarshi sam bata sauya ba dan ba kowa ne yake gane manufarsa akan fuskarsa ba,cikin nuna halin ko in kula da maganganun surukartasa ya dago shu'uman idanunsa masu tasiri akan me laifi,cikin kamilalliyyar muryarsa dake nuna ladabinsa ga surukuwarsa ya ce",Mami lafiya dai ko? Wani mugun kallo aunty amarya ta wurga masa Sannan cikin kara jin zafinsa ta ce",Ni za ka tambaya Me ya faru saboda kana son yaudarata kamar yadda ka shammace Ni kayi min yanzu", bata saurari cewar sa ba ta koma falon ta dauko jaridar da hamma Idris ya kawo mata ta wurga masa ita tana cewa duba kaga duk da cewa kafi Ni sanin abinda ka rubuta, wallahi wazer ban taba tunanin za ka iya cin amanar RAIHAN ba dani kaina,"ta faɗa muryarta na fidda sautin kukan da yake cuunkushe a makoshinta ta kasa fitar dashi.
A hankali ya sunkuya ya dauki jaridar yana dubawa cikin nutsuwa,sam babu wani alamun tashin hankali a kan fuskarsa amma da zaka tona zuciyarsa ka gani da mutum yasha mamakin yadda tayi wani irin baƙi saboda tsananin wutar da ta kama a cikinta,taya hakan ta faru idan bai manta ba yau sam bai je office ba,to ya akayi aka fitar da jaridar nan ba tare da saninsa ba? Ya akai aka rubuta ba tare da sa hannunsa ko na RAIHAN ba? Wai meke shirin faruwa ne? Hannu yasa ya shiga murza goshinsa da karfi wannan ita ce ka dai alamar da wanda yasan shi zai san cewa yana cikin tashin hankali da ruɗani.
Murmushin takaici aunty amarya ta yi sannan ta fizge jaridar tana cewa ba ka yi zaton zan iya gani ba ko shi yasa ka aikata hakan? Ko kuma so kake ka nunawa duniya cewa cusa maka RAIHAN aka yi baka sonta?
Wannan kalaman su suka yi tashin fiffike suka shiga kunnuwan RAIHAN da ta tashi dakyar ta yo hanyar fitowa,wani irin dum kirjinta ya yi,bude kofar ta yi a hankali saboda tana son sanin dawa mamin take wannan maganganun.
Gidan gwamnati......
Kifawar Abbie cikin tsananin ciwo ya yi dai-dai da shigowar jami'an tsaro ko wanne da zabgegiyar bindiga fuskar nan babu alamun fara a bare a sa ran tausayawarsu,Ur under arest cewar daya daga cikin jami in wanda da alama shine babba ya fada yana dora tsinin bindigarsa saitin goshin his excellency,cikin tashin hankali Abba yahya ya nufi dan uwansa yana jinjigashi da ambatan sunansa,sai dai kuma da alama Abbie baisan yana yi ba dan a halin yanzu kokuwa yake da numfashinsa da mala' ika a Zara'ilu yake shirin zarewa,dagowa ya yi cikin wani irin fushi ya yi kan his excellency da tuni ya yi sarander shako wuyansa Abba yahya ya yi cikin wata irin shaka yana cewa mugu azzalumi babu abinda abotarka ta amfane mu dashi sai Bala i, wallahi yadda ka kashe dan uwana da sauran al ummar dake a karkashin ka kaima sai ankashe ka kisa irin ta wulakanci,ka she dansa ko bakwai ba ka bari ya yi ba ka kashe uba kai wane irin azzalumi ne mara imani tur da mugun halinka",ya karasa fada yana rushewa da wani irin kukan bakinciki, dakyar jami'an tsaro suka banbare shi daga jikin his excellency da ya ƙi cewa ko mai ,kai hatta da idanunsa a bushe suke zuciyarsa ma dai abushen take,suna kada keyarsa motar anbulas ta shigo har bakin falon,cikin gaggawa suka yayi mi Abbie suka sakashi dan bashi taimakon gaggawa.
His excellency kuwa har aka saka shi a mota idanunsa suna kan Abba yahya,wanda hakan yake dauke da manufofin da shi ka dai ya barwa kansa sani,ai kuwa wannan kallo ya yi tasiri a jiki da zuciyar Abba yahya dan kuwa take ya fara hirji da neman tsari da duk abinda zai shiga gabansa.
Sai da motar yansandan ta wuce shima ya yi saurin shiga tashi ya bi bayan motar asibiti.
Abba yahya ba karamin mamaki ya yi ba ganin lokaci kadan yan jarida sun fara yayata wannan labarin saboda da ya fito yaga garin duk a harmutse,shi kansa da kyar ya samu ya kufcewa tambayoyin yan jarida,sai da ya samu kanshi ne ya kula da wani me dan sahu yana binshi, da da farko baiyi zaton shi suke bi ba sai da ya ga yazo har gab da asibitin basu daina binshi ba sannan ya tabbatar shi din suke bi,ganin haka kawai sai ya shammacesu ya juya kan motar kan kace me tuni ya bace ko kyallinshi basa gani.
Wani irin bugu ya kaiwa sitiyarin dan sahun yana cewa shet ya gano mu,na kusa da shi ya ce", oga ina ga dole sai mun bi a hankali dan na ga alama shima yana da wayo", na bayan yace ai Ni ban ga amfanin kamashi ba,tunda hajjaju cewa ta yi kar mu bari yayi nasarar kubutar da Muhammad nuur domin hakan yana daga cikin babban kuskuren da za muyi",dayan yace",yanzu dai mu bari mu yi magana da hajjaju sai musan abinda ya dace muyi", gamsuwar da su kayi da hakan yasa suka ja mashin ɗinsu suka wuce inda su kafi wayo.
Sai da ya tabbatar sun tafi Sannan ya fito daga maboyarsa ya nufi asibitin zuciyarshi cike da sakesaken wanda yasa a biyo shi.
Can babban headquarters suka kai his excellency kafin kace meye kobo manya sun san da maganar ,cikin kankanin lokaci aka fara tafka muhawara tsakanin talakawa da masu kuɗi harma da masu mulkin.
RAIHAN WAZER......
Aunty amarya ta ci gaba da cewa Wazer baka kyauta min ba sam baka kyauta min ba,ka zubda mutuncinka da kimarka da nake gani a idona", a hankali cikin wata irin murya ya bude baki ya ce", Please Mami ki saurareni wallahi ban san waye yayi wannan aikin ba,hasalima yau banje office ba ki tsaya mu fahimci juna kar muyi abinda za muzo muna da nasani", wani banzan kallo ta yi masa sannan cikin takaicin kalamansa ta ce", haba wazer da na sani kuma na nawa ai nice a cikin nadama da danasani dumu_dumu,dan haka ka zo ka fice bana bukatar ganinka kuma kamar yadda na gaya maka ina sauraren takardar sakin RAIHAN,wani irin runtse ido ya yi a karo na farko da damuwarshi ta bayyana saman fuskarshi,tunda suka fara magana maganar sakin RAIHAN shine abu mafi tsananin ɗaci da ya fuskanta.
Tuni ƙafafun RAIHAN suka fara rawa wani irin juwa na ɗibarta, wai wane irin mafarki ne take tayi yau marasa dadi, har yanzu abinda ta gani ta kuma ji da kunnenta ya kasa guguwa ya kasa barinta sukuni ko runtse ido ta yi sai taga fuskar matar da ta gani dazun me shirin ganin bayan Abbanta Yahya,kai Bama iya Abbanta ba har ita, dan kuwa tabbas ta gane ita ce me son kasheta tun tana cikin mahaifiyarta,to bata gama da wancan ba ta kuma riskar wani.
Dakyar ta iya bude baki cikin dan karamin sauti ta ce", Mami meke faruwa?
Gaba daya juyawa su kayi suna kallonta,da sauri wazer ya sunkuya zai dauki jaridar gudun kar RAIHAN ta gani tunda a yanzu ya fahimci bata san komai akan jaridar ba,sai dai kafin ya kai nashi hannun Mami ta riga shi,bata yi wata wata ba ta mikawa RAIHAN tana cewa duba kiga cin amanar da wazer ya yi mana........✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page47 ```
.......karbar jaridar ta yi jikinta da zuciyarta na wani irin harbawa,a hankali ta dubi wazer da ya zuba mata ido fuskarshi a cunkushe, shi kadai yasan irin tashin hankalin da yake ciki,shi bai ma taba sanin akwai abinda zai dugunzuma rayuwarsa da farin cikinshi ba sai yau da mami ke bashi umarnin sakin RAIHAN,da sauri ta kawar da kanta tana maidawa kan jaridar,da fuskarta ta fara cin karo kafin ta fara bin rubutun daki_daki tana karantawa,gaba dayansu sun zuba mata ido har da hajiyar agadex da ta fito daga daki saboda jin yar hayaniya,itama raihan din dago kanta tayi daga karanta jaridar bayan rubutu na karshe da ta karanta,a kan wazer ta sauke idanunta da suke neman rufewa babu abinda take gani sai jiri,aunty Amarya ce ta karɓe jaridar tana cewa Kinga Ni da idanunki dai ba kage a kayi masa ba,domin babu yadda za ayi a fitar da labari ko jarida ba tare da saninsaba,kin ga kuwa ko da ace ba shi ya wallafar da jaridar ba to tabbas da saninsa bare ma kuma babu wani ja shine ya shammace mu ya ya yaudaremu", hajiyar agadex ce ta kula gaba daya RAIHAN bata cikin hankalinta saboda yadda ta kafe a gurin kamar status,sai kuma ta tafi luuu zata fadi cikin zafin nama wazer da ya fi kusanci da ita ya tarota ta fado saman kirjinsa,da sauri su kayi kanta suna kiran sunanta,wazer bai sauraresu ba ya nufi dakinta tana dauke a hannun shi,kafin su aunty amarya su shiga tuni ya rufo dakin kuma babu wanda ya isa budeshi ta waje,cikin wani irin takaici aunty Amarya taja birki tana yaba tsarin ido irin na WAZER ɗin,kafin cikin kwafa ta ce", ko me za kayi sai ka sakar min yarinya butulu kawai a baka amana saboda an yarda da kai shine daga karshe zaka watsa mana kasa a ido",
Hajiyar agadex ce ta kama hannunta suka nufi falon tana cewa zo ki gaya min meke faruwa danni har yanzu Ban gane kan zancen naku ba", a tare su ka zauna mai makon ta yi mata bayani sai kawai ta fashe da wani mahaukacin kuka me tsanani wanda duk wanda ya jishi zai tabbatar tun daga can kasan zuciya yake fitowa,sam hajiyar agadex bata hanata ba, barinta ta yi tayi me isarta dan kanta ta yi shiru , Sannan ta karantawa hajiyar abinda jaridar ta kunsa,shiru hajiyar agadex ta yi na yan sakanni kafin ta dan nisa ta ce", lamra abinda nake so dake ki nutsu mu yi bincike akan wannan lamarin kar idanuwanmu su rufe mu kasa ganin gaskiya,abinda nake nufi shine kar ki saurin yankewa wannan yaron hukunci mu tsaya muyi tunani da kyakkyawar zuciya kuma mu saka lura cikin lamarin , Sannan ki daina zafafawa kanki, wannan abin da duk aka bi shi a sannu ba wani abin tada hankali ba ne,kasancewar ita kanta RAIHAN tashin hankalinki ne yasa ta cikin wannan ɗimuwar amma sam wannan bai kai tashin hankalin da yake kokarin tunkaromu ba", yadda aunty Amarya ta zuba mata ido cike da mamaki a kalmar ta ta karshe ne yasa ta anka da cewa ta yi subul da baka.kafin ta nemi abin kare kanta aunty Amarya ta jeho mata tambaya da cewa", Hajiya akwai wani abu ne? Me yake faruwa? Meye zai samemu da har zaifi wannan tashin hankali a gurina? Cikin son kawar da maganar hajiyar agadex ta ce", a'a ramla ba haka nake nufi ba dan Allah ki kwantar da hankalinki kar ki jefa kanki cikin wata matsalar daban.
Girgiza kai aunty Amarya ta shigayi tana cewa a'a Hajiya dan Allah ki fada min ina ji ajikina akwai wani abu daban bayan wannan,saboda tun jiya nake jin zuciyata da gangar jikina ba daidaiba", haba ramla ki nutsu mana nace miki babu wani abu dagata hajiyar ta yi tana ci gaba da cewa muje ki samu ki dan kwanta nutsuwarki ta dawo", kuka Aunty Amarya ta kuma fashewa da shi tana cewa haba Hajiya ina naga ta bacci muna cikin wannan tashin hankalin na tabbata yanzu zaki yan jarida sun cika kofar gidannan shin me zance musu ta ya zan gyara abinda aka riga aka batashi? Cewa da su kayi na sauya RAIHAN a matsayin Rahim saboda gadon namiji ya fi na mace,taya kike ganin zan goge wannan? Ɗan jim hajiyar agadex ta yi kafin ta ce", ai sai kin fita duk zasu yi miki wannan tambayar ko? To babu inda zaki muje ki kwanta ko mutanen gidannan babu wanda zai ganki", ta gamsu da maganar Hajiya hakan yasa ta bita jikinta a sanyaya ga wani irin zazzaɓi da ya kamata farat daya.
Ko da hamma Idris ya shiga bangarensu kasa yin komai ya yi,hatta matarsa kasa yin magana ya yi da ita, damuwa tasa ya kasa rike wannan babban almaraiin hakan yasa ya fita zuwa bangaren mamansa murja.
RAIHAN WAZER.........
A hankali ya kwantar da ita saman lafiyayyan gadonta da yasha wani hadadden bedsheet, dan karamin Fringe ɗin ta dake dakin ya nufa ya ciro bottle water,cikin nutsuwa ya dawo ya zauna saitin kanta ya bude kwalbar ruwan ya ɗan zuba a tafin hannunta sannan ya shafa mata a fuskarta sai da ya yi haka sai biyu,kana taja wani dogon numfashi tare da bude idanunta da suke kallon dishi_dishi,sai da ta samu minti ɗaya kafin ganinta ya dawo dai-dai,zuba mishi ido ta yi tana son tuna abinda ya faru saboda gani take kamar mafarki ta yi,bude bakinta ta yi a hankali saboda ta gasgata ba mafarki take ba,ta ce", da gaske ne komai da na ji na gani ya faru? Ta tambayeshi zuciyarta na tafiya da sauri saboda fargabar amsar da zai bata ,jinjina mata kai ya yi kafin ya ce", haka ne amma ban san komai ba ban san ya akai hakan ta faru ba", wata irin zabura ta yi ta tashi zaune idanuta cike fal da ruwan masifa ta ce", Hamma wazer karkace komai domin ba yadda zanyi ba,idan har ba kai ba ne me yasa zanje har office dinka amma kace baka bukatar ganina baka bukatar ganin kowa saboda kana ganawa da matarka rabi,akan idona rabi ta fito daga office din tana ce min wai mun dame ku", ta karasa faɗa hawaye na zuraro mata dan ita kadai tasan irin zafin da take ji akan hakan,lumshe idanunsa ya yi sannan ya kuma bude su akanta kafin cikin taushin murya da ke nuna lallashi ya ce", da ita plss RAIHAN yau banje office ba ban san me ya faru a wajenba,ko mai da ya faru shirine so plz kar ki bari yardar dake tsakaninmu ta rushe domin abinda wanda ya yi hakan yake bukata ke nan", harara ta watsa masa kafin cikin turo karamin bakinta ta ce", to idan wancan shirine shifa wannan na jaridar ai dai mu munsan cewa kaine kawai kasan wani abu da ya shafi wannan sirrin namu dan haka kaine ka fitar", bani ba ne RAIHAN", ya fada cikin sallamawa da wata irin karaya,wani iri ta ji ajikinta da yadda ya yi ɗin, hakan yasa ta kawar da kanta dan kaucewa kallonshi me kashe dukkan wata laka dake aiki a jikinta,kara matsawa ya yi jikinta yana kama hannunta dake ta faman murzawa ya cigaba da murza yatsun a hankali yana mai ci gaba da yi mata kallon har hanji, sannan cikin kamewa ya ce", kin yarda ba zan ci amana ba? Shiru ta yi tana tunanin to idan ba shi ba ne waye? Kafin ta dawo daga dan tunanin da ta tafi sai jinta