Showing 36001 words to 39000 words out of 189984 words
Chapter 13 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
gani zabin iyaye ce dan haka babu yadda za ayi da Ni" zaro ido jiddo ta yi har da dafe kirji ta ce" au ashe ma matar cushe ce?tuni rabi a ta harzuko ganin haka yasa wazir taka musu burki ta hanyar daka musu tsawa dole suka ja baki suka tsuke,ita dai jiddo dariya ce kawai ke cinta ta yadda ta kunna rabi a kamar wutar karmami,ita kuwa RAIHAN batutuwan da suke tattaunawa sune su ke yi mata ciwo wanda har sai da fuskarta ta bayyana cewa ta kuma shiga damuwa,abin da wazir ya lura da shi ke nan ya yi saurin taka musu burki dan ya fahimci gaba daya RAIHAN bata cikin hankalinta.
A haka suka karasa gidan makokin, suna tsayawa Raihan ta yi saurin fita dan karma ya ce zai tsaida ta dan shi kansa ji take kamar ta yi ta dukan sa ,dukan su haushin su take ji karma rabi a taji labari,babu yadda ya iya haka ya fito suka bi bayan ta.
Wazir ya san cewa raihan bata isa ta zauna a cikin gidan ba a matsayin da take takawa na namiji, sannan kuma babu yadda za ai ya bari ta zo ta zauna cikin maza dan zama na wani dan lokaci,hakan yasa suna fitowa daga gaisuwar cikin gida ya yi sallama da baban halima akan cewa za su je wani dan aiki,jan hannun RAIHAN dake rakube a gefe ya yi suka nufi wajen motar sa,bude mata ya yi ta shiga har lokacin babu walwala a tare da ita,zuwan ta gidan ya dawo mata da sabuwar damuwar da ta binne cikin ranta,tunanin ta ya dawo sabo akan ta yadda zata fara gudanar da aikin cikin sirri kuma ita kaɗai......
Fatima y Adam ✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page11 ```
Jin sassanyan hannun shi ta yi saman nata hannun dake zube kan cinyoyinta,a ya yin da yake kokarin fita daga layin su marigayiya Halima,ajiyar zuciya ta saki a ɓoye ,tare da ɗan duban gefan fuskarsa inda hadaddiyar kasumbarsa take kwance lamban tana ta zuba sheƙi baƙa siɗik da ita,ina alkawarin mu na jiya? Ya tambaye ta dan son kawar mata da tunanin da take ta kokawa da shi,kawar da fuskarta ta yi daga barin kallon nasa tana mai jin wani irin nauyi a kirjinta wanda idan ya tasar mata numfashinta har wani sarkewa yake,bata san taka maiman abinda yasa take jin hakan ba,kawai dai tasan tun dazun da abin ya faru kirjin ta ya yi nauyin numfashinta ya nemi tokarewa,kuma har yanzu bata ji ya sassauta ba,sai ma haɗewa ya kuma yi da tunanin da take ta yi akan sakon camara,hakan yasa abin ya yi mata yawa matuƙa.
Wane alkawari? Ta tambaye shi fuskarta babu alamun fara a sai tarin damuwa,huci me zafi ya dan fesar kana cikin nutsuwarsa ya ce"RAIHAN me yasa kike son takurawa zuciyarki? Me yasa kike son sawa kanki ciwo tun da kananun shekarun ki?me yasa kuma kike son fara boye min wani abu da ya shafi rayuwarki da zuciyarki? Kuka ta saka masa kawai saboda shi ka ɗaine hanyar da take jin zata samu sassaucin abin da take ji a ranta,dafe goshinsa ya yi tare da furta ya Allah "a hankali ya samu gefan titi ya tsaya,shuru ya yi yana sauraran kukanta da yake shiga ko wace kafa ta jiki da zuciyar shi,bai tsaida ita ba sai da ta yi me isar ta sannan ta share hawayen ta wanda take jin baza su taba daina zuba ba in dai zata ci gaba da rayuwa da wazir yana kula wasu matan ko kuma su suna kula shi,a yanzu tana jin bata da wata babbar damuwa me illata zuciya da gangar jikin ta sama da wannan, wannan damuwar ita ta hana ta samo mafita a kan batun camarar halima ,da ace babu damuwar wazir chibado tabbas da tuni ta samo mafita akan yadda zata yi ta dauko camarar da ma yadda zata gabatar da duk wani binciken ta cikin sirri,cikin wata irin murya me dauke da sautin da ke kashe gaɓɓan jiki ,ta ce "Ni ban sani ba Hamma wazir,ban san damuwa ta ba,abu daya na sani shine akan ka ne"cikin nutsuwa ya juyo ya fuskance ta tare da cewa me ya faru ki gaya min damuwar ki kawai nake son na sani hakan shine zai bani damar magance miki ita kamar yadda na yi miki alkawari"ya fada yana son shigar da kwayar idanunsa cikin nata,duk da ta ki bashi damar yin hakan, idanunta ta ɗago cike da kwallar da taƙi tsayawa kuma take tahowa da tsantsar damuwar dake dankare cikin ranta, HAMMA WAZIRRRRRR ta fadi sunan ba tare da tasan yadda ta tsinkawa wazir ɗin duk wata laka da jinin da ke gudana cikin jikin shi ba,bai san sanda ya kifa kanshi jikin sitiyari yana fidda wani irin numfashi me huci ba, cikin Muryar da ta kuma ci gaba da ratsa zuciyar shi da juya duniyar shi ta cigaba da cewa, wannan rabi din abin da ta faɗa da gaske ne? Me ta faɗa ya tambaye ta ba tare da ya ɗago kansa ba,ɗan matsowa ta yi daf da shi har ɗumin bakinta me fitar da ƙamshin minty da ya haɗe da ƙamshin kanumfari ya na bugun numfashinsa,cikin yin ƙasa da murya kamar me raɗa ta ce" wai ita zaka aura? Ɗagowa ya yi da sauri har sai da ya dan buge fuskarta dake daf da shi,zuba mata ido ya yi yana kallon yadda take ta kifkifta idanun kamar zata fashe da wani kukan, murmushin da yake da matukar wahala a gurin sa ya sakar mata tare da kama kumatunta yana cewa Kingan ki da rigima ko Raihan,idan ita ta faɗa miki haka to kin ji daga bakina ne?girgiza kanta ta yi dake cikin tafikan hannayen shi,to me yasa hakan zai dame ki bayan kin san me damuwarki ke nufi a wajen mutane uku da kike da muhimmanci a cikin rayuwar su?ƙifkifta idanun ta yi sai ga hawayen sun zabo ta ce"amma ai cewa ta yi iyayen ka sun amince" karya take' ya fada kai tsaye yana kuma share hawayen da suke tuttudowa daga cikin kyakkyawar idaniyar ta.
Kallon shi take yi da dukkan zuciyarta tana jin abin da ya tokare mata kirji na sauka a hankali,kin yadda? Ya tambayeta bayan ya gama share hawayen,ga kuma mamakin sa a yanzun hawayen sun daina zuba ba kamar farko ba da suka ƙi tsayawa,rike hannun shi ta yi cikin marairaice fuska da shagwabar da ta zamar mata jiki ta ce", HAMMA WAZIRRRRRR"ya Allah ya kuma fada yana dan rintse idanun sa,bata kula da yanayin nasa ba ta cigaba da cewa kar ka kuma ɗaukar ta a mota ko Bama tare ka ji? Bazan kuma ba ya fada kamar wani karamin yaro, murmushi ta yi wanda ya bayyana lobawar kumatunta,hannu yasa a gurin yana cewa i like dis face"oya fada min"ta san abin da yake nufi saboda itama abin yana ranta,cikin shagwabar da ta riga ta saba yin ta a ko ina ta ce" jiya bayan mun gama waya ka kwanta ka kuma samu nutsuwa har kayi bacci wanda saura kiris yasa ka makara sallah" ta karasa fada da compidece"zaro ido ya yi kana ya ce" RAIHAN kin fada daidai hakan yana nufin abin da kika fada jiya haka ne" dariyar jin dadi ta yi ,kafin ya ɗora da cewa Nima naji a raina kin yi bacci me dadi kuma kema har kin makara sai da antyy ta zo ta tashe ki"waro manyan idanun ta tayi masu cike da wasu sirrin da suke matukar tasiri a gare shi,ta ce"HAMMA WAZIRRRRRR ka faɗa daidai fa"juyawa ya yi yana murmushi me sanyi wanda yake sanyayawa RAIHAN jiki da ruhi.
Ina zamu je HAMMA WAZIRRRRRR? Gidan gwamnati ya bata amsa yana daukar titin da zai sa da shi da gidan gwamna, HAMMA WAZIRRRRRR me zamu yi a gidan gwamna?mai makon ya bata amsa sai kawai ya jefo mata tasa tambayar,me yasa kika iya fadar sunana kamar ke kadai kika iya fadar shi a duniya?zaro ido ta yi cike da mamaki ta ce"kai Hamma Ahmad da gaske kake?"numfashi ya furzar ba tare da ya ce da ita komai ba,itama shurun ta yi tunda ta fuskanci ya gaji da maganar,shi kuma a ranshi ba wai haka bane kawai dai ya fuskanci idan ya ci gaba da biye mata tana fadar sunayen shi da irin salon da ya tabbatar bata san tana yi ba,hakan zai iya sawa ya kasa nutsuwar yin tuki saboda halin da hakan ke jefa shi wanda ya kasa gane dalili,duk da cewa kuwa yana jin Gajiyar surutun da yake yi ,dan a tsawon rayuwar shi bai taba doguwar magana da mutum ba kamar yadda yake yi da Raihan.
Da haka su ka karaso gidan gwamnati,duk da cewa gwamnan ya san da zuwan wazir din,hakan bai hana su fuskantar Matsala ba,amma tun da Hussaini p,a din sa ya karaso shike nan suka samu sa ida daga binciken da ake ta faman yi musu.
Yauwa ku zauna nan da mintina goma insha Allah za ku shiga,inji p,a Hussaini,jin jina kai kawai wazir ya yi tare da duban Raihan da ta coge guri daya karamin bakinta a cune saboda haushin abin da aka yi musu wanda kuma ta riga ta san dole sai hakan ta faru,to su anyi musu da sauki ma tun da gwamna da kansa shi ya neme su,cikin yin ƙasa da murya sosai wazir ya ce" zauna mana" zama ta yi tana ci gaba da hararar hadadden falon tamkar shi yayi mata laifin ,cikin kunkuni ta ce" Ni ban san me yasa ka sa mu zuwa nan ba,idan magana zai yi damu ya same mu a inda muke mana"dan zaro idanu wazir ya yi kafin ya ce"Raihan gwamna ne fa"ƙwafa ta yi tare da cewa nifa ina jin banda a poster bam taba ganin mutumin nan ba,duk da cewa aminin Abbie ne kasan lokaci lokaci yana yi min aika shima fa bai taba ganina ba, ta faɗa a hankali idanunta akan katon hotamshi da na shugaban kasa,,bai ce mata komai ba kawai ya maida kanshi ya jinginar tare da lumshe lumsassun idanunsa,ji yake kansa har wani sarawa yake saboda yawan magana da hayaniyar da ya shiga kwanaki biyun nan.
Itama RAIHANN shuru ta yi tana saka abubuwa masu yawa cikin karamar kwakwalwar ta me kaifin basira.
Cikin mintuna goma kuwa sai ga p,a Hussaini ya fito tare da yi musu iso.
Cikin kamilalliyar Muryar sa ya yi sallama Raihan na biye da shi a baya a matsayin RAHIM,cikin fara'a mayalwaciya gwamna ya amsa tare da nuna musu kujeru guda biyu dake gaban sa suna kallon juna,cikin nutsuwa suka zauna,ya yin da Raihan ta kuma kama kanta saboda ba a gaban wazir take ba,wanda shi ka dai ne a waje idan tana tare da shi take mantawa da cewa ita din namiji ce.
Cikin girmamawa suka gaisa da gwamnan jihar Adamawa,kafin gwamna ya dan yi gyaran murya, sannan ya fara da cewa, Ahmad wazir hakika nayi matukar farinciki da amsa gayyatata da kayi ,duk da cewa baka san dalili ko kuma makasudin kiran ba,dan haka ina matukar godiya da hakan,sai dai kuma ban sani ba ko za mu iya tattaunawa kai tsaye, ya fada yana duban gefan da Raihan take idanun ta a kasa,shima wazir duban Raihan din ya yi kafin ya dan lumshe idanunsa yana cewa babu damuwa zamu iya tattaunawa in dai akan abinda ya shafi aiki ne ko kuma sirrin da ya kasance nawa ne,amma in dai kana ganin sirrin ka ne wannan bani da ta cewa" ya karasa fada yana mai bude dukan idaniyar shi da zuciyar shi akan Raihan da har yanzu bata ɗago kanta ba,duk da yadda take jin idanun wazir din akan ta,numfashi gwamna ya dan ja,tare da cewa shi ke nan,tun da ka yadda da shi babu damuwa.
Kai tsaye ya ɗora da cewa,wazir ba komai ne yasa na kira ka ba,illa magana akan abubuwan da suke faruwa wanda kuma har yanzu mun kasa kawo karshen abun,ba komai ne ya kuma tayar min da hankali ba,illa kisan yar jarida halima,kuma kowa yasan cewa ina da kakkarfar dangantaka da gidan jaridar ku,hakan yasa na kara jin tsoron kar a dinga bin ku daya bayan daya ana kashewa saboda kawai kuna da kyakkyawar mu'amala da Ni,wanda sai a yanzu Nima na fara zargin daga inda wannan taadi yake fitowa,duk da cewa har yau ana kan bincike kuma akan wadan da muke tunanin,to amma Ni abin da na gani shine ina so bincike ya bi ta kan kowa ko Allah zai sa mu da ce,idan nace kowa kuwa to ina nufin har Ni" gaba daya su ka ɗago suka kalle shi duk da cewa ba wai sun iya duban shi ne kai tsaye ba,gane mamakin da suka shiga ne yasa shi jin jina kanshi fuskar shi dauke da wani irin yanayi na matukar jimami,ya ce"wazir hakan shine kadai mafita kuma shine zai fidda Ni daga idanun masu jingina Ni da laifin nan,dan haka daga yau na baku dama kai da staff din ka kuyi bincike me kyau a kaina da duk wanda yake tare da Ni defity ne shugaban jam'iya Alh Yahya duka ban dauke kowa ba,dan Allah Ahmad ka taimaka mana wannan shawarar ba yawa ba ce Ni ka dai shawara ce daga babban Aminina Alh Muhammad nuurr shi yasa na dauke ta da matukar muhimmanci ", Raihan bata yi mamakin ambatar sunan mahaifinta da gwamnan ya yi ba,dan mutane da yawa sun san shaƙuwa da alaƙa me girma dake tsakanin su,mutane basu kara tabbatar da haka ba sai da Abbie din ta ya kuma yin ruwa da tsayi ya tabbatar da hawansa kan kujerar Gwamna,so mutane da yawa sun san cewa gwamna da bazar Alh Muhammad nuurr yake taka rawa.
(Alhji Garba shi kadai yasan muhimmancin Alh Muhammad nuurr, Alh Muhammad nuurr ya yadda da Alh garba wanda har ya kai ga bashi amanar dukiyar Raihan yake juyawa,babu wanda yasan wannan sirrin sai lauyan Alh Muhammad nuurr da kuma mahaifinsa da yakasance baya iya zartar da komai ba tare da ya sanar masa ba,kuma duk fadin duniya babu wanda yasan wani abu akan Raihan sai Alh Garba)
Nasan zaka ce me yasa,ban sanar da wadan da alhakin binciken yake hannun sa ba,to ba komai ne yasa na yi hakan ba,sai dan cewa suma ba za a rasa munafukai a cikin su ba,koma na ce dukkan su munafukai me ƙaɗan daga cikin su ne masu amana,amma kai wazir na yadda da kai,nasan ba za a taba hada baki da kai a cuci al umma da jihar ka ba,kuma kai ne ka dai za kayi aiki cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba, wannan shine amfanin kiran ka da na yi,kuma shine babban taimakon da yan jarida suke wa kasa da al'umma,saboda su din kai tsaye suke taimakawa hukuma wajen zakulo me laifi ba tare da an yi wata ciwa ciwa ko san zuciya ba,duk da cewa ko wane aiki a kwai me gaskiya da kuma makamancin hakan,dan haka ina mai kuma jaddada maka cewa na baka wuka da Nama kayi duk abin da ya kamata,babu wanda yasan za mu yi wannan zaman bare kuma sanin abin da zamu tattauna daga waje sai iya mu hudun nan ,dan ko p,a Hussaini bai san akan me na kira ku ba"ya kare maganar shi da zubawa wazir din Ido, don gane yadda maganar shi ta karbu wajensa,tun da yasan ba lallai ne wazir din ya tsaya ya yi masa bayanin da zai gamsu ba,ilai kuwa ,wazir sauke numfashi ya yi kana cikin nutsuwarsa ya ce"na gode ranka ya dade ,kuma zan yi duk abin da ya kamata insha Allah,fatan nasara ya fada yana miƙewa tsaye,mika masa hannu gwamna ya yi fuskar shi dauke da murmushi su kayi musabaha maida hannun shi kan Raihan ya yi yana cewa na gode ina fata ba za ku bani kunya ba"wani kallo wazirrrrrr ya bi hannun gwamna da shi kafin ya maida kan Raihan da yaga tana kokarin zaro hannun ta saboda rashin ta kamaiman mafitar kaucewa yin hannu da gwamnan,hannun yana gab da isa wazir ya saki wani wahalallan tari wanda shi kansa bai san ta yaya a kai ya fito ba,dan shi dai yasan ba ƙirƙirar sa ya yi ba,haka nan yaji tahowar kwarewar tamkar wanda ya ci wani abu,aiko da sauri Raihan ta janye hannun ta wanda dama kiris take jira,ruwan dake gaban su ta dauka ta mika masa tana faman yi masa sannu,shima gwamna sannu ya yi masa,ruwan ya karba ya kwankwada sosai,da sauri yaja hannun RAIHAN suka nufi kofa ba tare da ya kuma bi ta kan Alh Garba ba.
........
Suna shiga mota yaja wata doguwar ajiyar zuciya,Hamma Ahmad wai me ya faru? Kasa ce mata komai ya yi saboda ita kanta haushin ta yake ji wato da haka bata faru ba mikawa wannan katon hannu za ta yi da sunan sallama,dafe goshin sa ya yi saboda wani abu da ya tuna wato laushiin tafin hannun RAIHAN,ji ya yi jikin shi ya dauki rawa,saboda duk da cewa ba su yi hannun ba haka nan yake jin faduwar gaba da ta shin hankali,sai ya shiga tunanin yanzu haka ma duk mazan da suke tare a bokanan aikin ta ta hanyar masabaha suke gaisawa,Hamma wazir wai me ya faru ne? Ta kuma tambayar shi,banza ya yi mata tare da figar motar kamar zasu tashi sama,shuru ta yi zuciyar ta na wani irin nauyi,bata san meye dalilin bacin ran wazir ba,amma tana da tabbacin cewa ba ita ba ce ba,sai dai idan gwamna ne ta fada tare da kwarin gwiwa,da haka su ka isa gidan su,bai shiga ba bai kuma kalleta ba,murya a cushe fuskar nan babu kame kai ba ka ce sun taba maganar arziki da Raihan ba,ya ce"fita"wani irin tsoron shi ne ya kamata da sauri ta fita daga motar jikin ta har rawa yake,figar motar ya kuma yi kamar zai take mata kafafu,