Showing 165001 words to 168000 words out of 189984 words

Chapter 56 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15643

nisa,Ki kula da motsin kowa shine abinda ya kamata ki fara yi domin gano mana wannan mugun", Tom shike nan zanyi yadda kika ce", Raihan ta faɗa tana share hawayenta.




Da sauri aunty Amarya ta share hawayenta tare da maida wayar cikin jikinta.




Itama Raihan fita tayi cikin sauri ta nufi bangaren baffa Ali,tunda ta shiga take rarraba ido dan ganin waye baya nan ,kowa yana nan idan ka ɗauke Hamma Idris da Hamma Affan,take tunaninta ya rabu gida biyu,da sassarfa ta nufi kusa da aunty Khadija matar hamma Affan ta zauna.




Tunda ta shigo take jin idanunsa dake yawo akanta,bata san cewa yana falonba amma jin yadda bugun zuciyarta ya sauya da yadda take jin idanunsa ajikinta yasa ta gane cewa yana zaune a falon,sai ta samu kanta da jin nauyin su Abbie da baffa Ali,dan ta tabbata dole su fahimci rashin hakurin wazer akanta,to amma ta wani gefen taji dadin kasancewarshi atare da ita ko dan ta yi sharing din damuwarta da shi,tunda mamin ma shi kadai ta ce", ta sanarwa da damuwarsu duk da cewa tana fushi dashi,satar kallonshi ta yi saiko karaf idanunta cikin nashi,girgiza kai ta shiga yi idanun na cika da ruwan hawayen da bata san ko na meye ba,saboda yadda ya rike kwayar idanunta ya ki bata damar janye nata idon,kallon da yake aika mata wani kallo ne na musamman da yake tahowa da wasu irin sinadarai masu saka gangar jiki da zuciya yin sanyi,yadda jikinta yake mutuwa da wani irin so kauna tausayi da kewa yasa ta fashewa da kukan da kowa saida ya kalleta,hakika ba zata iya jure abinda take ji akan wazer ɗin ba da wannan sakon da yake aika mata shi a yanzu,rasa mafitar ne yasa ta fashewa da kukan,duk da cewa a cikin kukan akwai dalili bayan dalili na kewa da wutar son wazer harda na soyayyar uwar da take jin bata da kamarta a duniya.




Rufe idanunshi ya yi yana jin tamkar ya je ya rungume abarsa yasata acikin jikinshi ya yi mata rarrashin da zaisa ta manta da komai na damuwa,rasa yadda zaiyi yasa shi dauke kansa daga kanta tare da jingina bayanshi a jikin makarin kujerar da yake kai tare da maida narkakkun idanunshi ya lumshesu tamkar me yin Bacci.




Baffa Ali ne yayi gyaran murya sannan ya shiga lallashin Raihan,a zatonshi kukan murnar samun Abbie ne,shi kuma Abbie tausayinta ne ya kamashi da nashi zaton da baiyi kuskure ba na cewa kukan rashin mahaifiyarta take a kusa duk da cewa baisan sunyi waya da mamin ba.


Bayan sunyi addu'a ne baffa Ali ya kuma yin gyaran murya tare da dan muskutawa ya fara da cewa alhamdulillah aka kulli halin dukkan godiya ta tabbata ga Allah me Rahma da jin kai,abinda yasa na ce kowa ya hallara a nan shin..........maganarshi ta katse saboda shigowar HAMMA...




_______________




Cikin hikima ta Ubangiji da taimakon aljanarta Hajiyar agadex tazo har babban kogon da tsohuwa me jini take aikata shirkarta ita da mabiyanta.daji ne me suna daji wanda idan ba wadanda suka ɗebe kayansu daga gaban ma'iki suka fito neman duniya ta wannan hanyar ba babu wanda zaka gani a gurin,to amma saboda suma din ababen tsoro ne shi yasa suke rayuwa a gurin batare da tsoron muggan halittun da suke rayuwa a dajin ba.




Kurdawa ta yi har cikin kogon da idan ba kaima irinsu ba ne to baka isa ganin gurin ba,to dake Allah ya kawo karshensu shi yasa ya bawa aljanar hajiyar agadex ikon zuwa gurin take kuma ganin komai ba tare da wani shamaki ba,duk da kasancewarta aljana sai da firgita da ganin irin barnar da ake yi wajen da irin mutanen da suke rayuwa a wajen,manyan mutanene wadanda baka taba tsammata za su aikata wannan mummunar aikin ba take gani a gurin kowanne da nashi kalar aikin tsafin,ita dai bata bar karanta Alkur'ani ba wanda take karanta shi da wani irin kushu'i ta yadda tsikar jikin me sauraro zata na tashi me imani,mara imani kuwa sai dai ya dagargaje.




A wannan lokacin Abba yahya yana gurfane gaban tsohuwa wadda ya maidata Ubangijinsa roko yake yi da banbadanci akan a sake masa aiki me karfi wanda zai rufe bakin duk wanda yasan yana aikata wannan barna,ko kuma duka su mutu cikin biyu yana so ayi daya babu wanda yake so a kyale harda hajiyar agadex da yake kiranta shuumar tsohuwa me gani har hanji.cikin muryarta mara daɗi da fitar da bakin hayaki ta ce", SHUDA tabbas a yanzu tsoran ci gaba da mu'amala muke da kai saboda abinda zaka iya jawo mana dan tabbas muka ci gaba da shiga cikin lamuranka to muma sai mun zama tarihi dan haka kayi gaggawar barin gurin nan, idan kana son taimako yanzu sai dai danka DUDU ya taimaka maka tunda shi har yanzu da sauran shan ruwansa a tare da m....kafin ta rufe bakinta sai ga hajiyar agadex tsakiyarsu tamkar an jefota,bakinta dauke da adduoi masu zafi.........✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page62 ```




....Idris,da kallo ya fara bin mutanen falon kafin ya ƙaraso kusa da Abbie cikin shauki irin na kaunar dake tsakanin *ɗa* da mahaifi, cikin farinci Abbie ya tarbeshi cikin nasa farincikin yana cewa dan albarka ina ka shiga ne? Tun da na dawo nake tambayarka domin ina son saka duka yarana cikin idaniyata", zama hamma Idris yayi a kasan kafafun Abbie sannan ya ce", Abbie na danyi nisa da gari ne,ashe ban sani ba ana nan ana farinciki babu Ni gida ya haɗu ", ai kam dai to ina shi Affan din yake na dauka ma kuna tare cewar Hajiya goggo ke nan,girgiza kai hamma Idris ya yi tare da cewa Bama tare da Affan sai dai idan shima wani uzurinne ya rikeshi", to Masha Allah baffa Ali ya fada yana ɗan zagaye falon da idanunsa sai kuma ya tsaida idanunsa a kan Raihan kafin cikin mamaki ya ce", raihana ina maminki take ne tun dazun nake zuba idanun ganin shigowarta amma hallau shiru? Tsit falon ya yi kowa na sauraron amsar da Raihan zata bada,hatta da wazer sai da ya bude idanunsa da suke a rufe ya zuba su kan Raihan ɗin da tambayar ta zo mata a bazata, yanzu me zata ce da su? Ta tabbata shi kansa Abbie yana bukatar wannan amsa tunda ita tasan cewa abinda ya fada mata akan rashin dawowar mamin ya fada ne kawai dan ya kwantar mata da hankali,Dagowa ta yi zata yi magana sai sautin babureshin din wayarta ya katseta,maida idanunta ta yi kan wayar kafin cikin sauri da rawar jiki ta daga kiran tare da sawa a amsa kuwa domin ba zata iya jura ita ka dai ba dole ta take maganar Mami na cewar kar ta bari kowa ya sani dan tana da tabbacin sune suka kira dan neman kudin fansa.




Aiko ba ta ida tunanin da take yi ba,wata murya me karfi ta fara magana da cewa muna magana da Raihan Muhammad nur ne? Ey nice ta faɗa cike da gwarin gwiwar da wazer yake bata daga cikin idanunsa,dariya mutumin ya yi kafin ya dora da cewa maminki tana hannunmu idan kin yadda da sharadinmu zamu baki ita lafiya ba tare da ko sauro ya cije ta ba,idan kuma kika sabawa sharadinmu da abinda muke so to tabbas zaki tsinci gawar maminki a kwalbati", me kuke so ta faɗa cikin rashin tsoro? Yauwa yar gari nasan kina son maminki ba za ki so ta mutu a banza ba dan haka bukatarmu a gareki shine ki tattaro kudi kimanin biliyan hamsin ki kawo mana mu kuma za mu sake mahaifiyarki,sharadinmu kuma shine....karasa masa ta yi da cewa babu 'yan sanda cikin lamarin idan kuma na samar da jami'an tsaro zaku kashe mamina kalas ba shi ne abinda zaka fada ba? Dariya yayi sosai sannan ya ce yauwa yarinya me wayo da basira na sara miki wannan shine abinda zan sanar dake dan haka ina jiranki gobe da misalin ƙarfe shida na asuba,zan turo miki address din inda zaki aje mana kudin," idan na baku kudin mahaifiyata fa? Idan kika aje ki tafi zaki samu mahaifiyarki a kofar gidanku ko a cikin motar da kikazo da ita ko a wani guri da zaki iya ganinta", shike nan zamu yi kokarin hada kudin a darennan in sha Allah ", da haka suka kashe wayar.




Falon ya jima shiru kowa da irin kalar nashi tashin hankalin,yanzu me ye abinyi kudin za mu basu ke nan? Cewar baffa Ali fuskarshi na nuna alhinin jarabtar da suke ciki,girgiza kai hamma Idris ya yi Sannan cikin zuciyarshi da ba ko yaushe take tasiri ba ya ce", baffa ba za a basu kudin nan ba duk da cewa akwaisu amma ba za a basu ba," a nutse wazer ya dago daga jinginen da yake tun dazun sannan ya dubi Abbie da ya kasa cewa komai baya ga da hadiyar yawun bakinciki da yake yi,dan rissinar da kanshi ya yi cikin girmamawa ya ce",baffa maganarka akan hanya take kudin za a basu kuma ayi yadda suke so kar a sanarwa da jam'i an tsaro saboda gujuwa abinda zai faru da mami", Hajiya goggo ta ce", kwarai kuwa nima dai abinda na gani ke nan tunda dai akwai kudinnan," a nan dai kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa kafin daga bisani baffa Ali ya nemi da su yi shiru dan a tsaida magana.




Shiru duk su kayi bayan tsawon yan mintuna da basu wuce biyar ba,baffa Ali ya ja numfashi sanann ya ce da Abbie kaje ka shirya kudin za ayi yadda suke so", shi dai Hamma Idris fuskarshi ta nuna rashin gamsuwa da wannan shawarar kawai dai dan an rinjayeshine.




Cikin mutuwar jiki Abbie ya amsawa baffa tare da mikewa dan barin falon,sallamar hamma Affan ce ta sasu kallon kofar baki dayansu,ganin Abbie yasa shi rungumeshi cikin tsananin farin ciki har da yan hawayensa shidinma Abbie sai da ya yi hawayen da dama suna hanyar fita daga haka ya saki Affan ya fita daga falon yana ci gaba da share guntayen hawayen da baya so su gani,da sauri Affan ya karasa gurin baffa Ali yana cewa meke faruwa ne baffa? Kama hannunshi baffa Ali ya yi ya zaunar dashi a gefansa sannan cikin hikima ta yadda zai fahimta ya sanar dashi abinda ke faruwa da kuma irin shawarar da kowanne ya kawo", gaskiya ne baffa shawarar da kuka yanke ita ce shawara Gara a basu sannan abi sharadan da suka bayar saboda gujuwa abinda zai faru",




Wani irin kallo Raihan take masa tun shigowarsa zuciyarta bata gama gasgata mata abinda take tunani ba sai da taji lafazin bakinsa,lallai kuwa indai har Affan shine ya yi garkuwa da mami to wallahi ba zata yafe ba,a hankali ta saki siririn kukan da yake ta cin ranta kamar ana yakushin zuciyarta,dan gaba daya ji take kamar ba ita ba damuwa ta yi mata rufdugu ta ko ina ji take bata jin dadin rayuwar saboda halinda Mami ke ciki da kuma tarin kaddarorinsu.




Sai da kowa ya fita sannan ya mike cikin nutsuwarsa da kamewar dake sa ba a iya gane ainahinsa,kama hannunta ya yi ya mikar da ita sannan ya yiwa baffa da Hajiya goggo sallama suka fita yana rike da hannunta.




Suna fitowa ya shigar da ita jikinshi yana ɗan shafa fuskarta saboda ya tare hawayen da suke zuba a kasa,hamma wazer me yasa haka take faruwa dani? Me yasa saini duk me ya jawo hakan ne? Kudine sanadi ko to zan hakura da komai da nake dashi ko zan samu na zauna lafiya nida iyayena da ahlina gaba ɗaya", ta karasa maganar cikin kara fashewa da kuka.




Kar kiyi saɓo RAIHAN Allah yana jarabtar bayinsa talaka ko me kudi me lafiya ko nakashashshe,ba sai masu kuɗi Ubangiji ke jarabta ba kuma ba sai talaka Ubangiji ke jarabta ba, jarabta tana daga cikin wani yanke na imani dan haka kar ki fushi komai zai wuce,yanzu muntafi can gida inason ki samu nutsuwa ko yaya ne umm", rungumeshi ta kuma yi tana cewa na gode da tunatarwa",




Da kansa ya sakata a mota sannan ya koma mazaunin direba ya shiga yaja suka bar gidan.




A hanya ya kira Salim ,yana dagawa ya ce ", ina Dady? Gashi muna tare", Salim ya fada yana sauraron abinda wazer zaice", ok har yanzu ba ku fitar da ainahin Muryar ba", Dady ne ya amsa a wannan gabar yana cewa sir kashim ya fitar da ainahin Muryar wanda Surry ke waya dashi a halin yanzu ma Turo maka muke kokarinyi sai dai muna kokonto dan ganin kamar dare ya yi", no Dady ka Turan kawai", ok sir dady ya fada yana ɗorawa da cewa sir ya batun abu Huraira ? Dan dafe kai wazer ya yi tare da cewa yana ina? Salim ya ce", yana can dakin ajiya", to ku barshi a wajen zuwa gobe in sha Allah zanzo idan banzo ba kuma kuje ku fara matsashi ya fada mana wanda ya turoshi da kuma inda suka kai khalil", ok sir suka faɗa a tare", na gode ya fada yana kashe wayar", kallon RAIHAN da duka hankalinta yake kansa ya yi sananan ya maida hankali kan tukuinsa yana cewa ya dai da wani abu ne? Hamma kana boyen abubuwa da yawa da suke faruwa akaina dan Allah ka fada min wani abu ko naji sanyi kuna barina a duhu sosai",in sha Allah zan sanar dake abinda ya kamata ki sani kar ki damu ya fada yana shafa fuskarta,jinina kai ta yi tare da lumshe idanunta.




__________




Shet ya fada bayan gama wayarsa da ciska,lallai wannan yaron dan baiwane ba kowa ne yake tsalleke tarkona ba amma shi duk sanda na nada masa tarko sai ya tsallake,cizon yatsa ya yi idanunshi sunyi jajur saboda tsananin bakinciki, wallahi ba zan Barka ba wazer dole sai nayi nasara akanka,ya fada zuciyarshi cike da bakincikin da yake ji zai kasheshi.




___________




Cikin bakinciki hajiyar agadex ta nuna shuda Abba Yahya da yatsanta tana cewa kai dai ka cika tabbatacce la anannan Allah, Allah Ubangiji ya yi mana tsari da irinku masu bakar zuciya zuciyar kafurci zuciyar shaidan wallahi Yahya kayi asarar rayuwa duniya da lahira kuma in sha Allah sai ka girbi abinda ka shuka dan Allah baya barin azzalumi da zalunci butulu kawai",juyowa ta yi kan tsohuwa tana cewa ke kuma tsohuwar najadu tsinanniya wadda Allah ya tsinewa in sha Allah yau karshen barnarki yazo", ke dakata tsohuwa ta faɗa tana nuna hajiyar agadex da sandar tsafinta,sai dai kuma ga dimbin mamakin tsohuwa taga babu abinda sandar ta yi hasalima sai gani su kayi sandar na narkewa tamkar ana narka roba da wuta,cikin tsananin razana tsohuwa ta yi kan gunkinsu da suke bawa jini a karo na biyu danyin Abinda ya dace tun kafin hajiyar agadex tayi nasara akansu,tsayawa ta yi can saboda ganin shima gunkin yana rushewa yana zubewa a wajen tamkar ba ayi shi ba,da wani irin tsoron da ya kama dukan mabiyanta da suka hallara lokaci daya a gurin suke kallon hajiyar agadex dake tsaye kyam bakinta dauke da addu o'in kariya daga sihiri wanda Annabi ya umarcemu da mudinga yi a sa'ilin da muka ga wata masifa ta tunkaromu.




Kamar abun almara sai ga ginin kogonnan ya fara rushewa yana zubowa a hankali tamkar wanda ake sa hannu ana baroshi,cikin tsananin tashin hankali da firgici wanda basu taba shigarsa ba tun bayan kafa kungiyar suka fara darewa kowa yana neman gurin tsira daga cikinsu har da Abba yahya da ya fara kokarin yin takansa,cikin wani irin zafin nama hajiyar agadex ta cafko shi take ta samu igiyar da suke amfani da ita wajen tsafinsu ta daureshi katamau sannan ta jashi suka fice daga kogon,tamkar jira kogon yake ta fita wuta ta fara kama duk wani abu dake wajen hadda mutanen da basu riga sun fita ba.




Ita kanta tsohuwa neman hanyar tsira ta fara yi sai dai ina duk da haka sai da wuta ta fara kama wasu bangare na jikinta,dakyar ta samu ta fita tsakiyar dajin, tunaninta tunda wuta bata cinyeta gaba daya ba ta tsira ,to amma ina ashe tsugune bata kare mata ba,dan kuwa bayan ta samu wutar jikinta ta mutu dakyar ta fara tafiya dan canja sheka,katsaham ta ji wani abu me nauyi ya nannadeta dubawarnan da zata yi ta ci karo da wata narkekiyar mesa,ta fasa kai tana razanata da mugun dafinta,tsohuwa bata taɓa tunanin akwai abinda zai bata tsoro ba sai yau da ta gamu da gamonta abinda take takama dashi kuma babu,bude baki tayi zata fasa ihu sai caraf mesarnan ta cijeta akan harshe ,tsohuwa tana jin haka tasan cewa mesar ta shirya azabtar da ita ne kawai.


_____________




Hajiyar agadex tana zuwa bakin gate din gidan ta kwankwasa, securitys suna ganinta suka bude mata kofa,bakinsu ne ya mutu lokacin da suka yi arba da Abba yahya dake rike a hannunta tana jansa kamar kayan wanki,alamu ta yi musu da suyi shiru hakan yasa suka maida bakinsu suka kulle,wani tsohon daki dake can boyquaters ta ce su bude mata, aiko cikin hanzari suka bude mata,suna kallo ta jefa Abba yahya a ciki ta kulle ta bar gurin da key din a hannunta.




____________




Tunda aka gama taron ya dawo bangarensu yake sunturi da da leken ta inda zaiga inna maimuna ko abbansa,duk sakan sai ya duba a gogo,to me yake faruwa ne? Ya tambayi kanshi a karo mara adadi,wayarshi ya kuma dagawa ya kira inna maimuna shiru dai har yanzu,sai ya koma kan abbansa shima kuma layin yana shiga a wannan karon sai dai ba a dauka ba,tsaki ya yi yana zama saman kujera dabar,shi rashin ABBAN bai esameshi kamar innarsa ba,take wata dabara tazo mai,hakan yasa ya tashi da sauri ya nufi dakin abbansa.




Wannan kofar da babu wanda yasan da ita sai shi da Abba yahya ya bude,shiga yi ya duba ko abban yana ciki saboda lokuta da dama tsohuwa na sasu yin aikin tsafi na kwanaki a dakin wani lokaci har kwana biyu yana yi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login