Showing 75001 words to 78000 words out of 189984 words

Chapter 26 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15616

kasa yana kissima da tunano sunan da aka kuma daura auren da shi.


RAIHAN fa,ya a kayi hakan ta faru?


Waye yasan sirrin ƁOYAYYIYAR RAIHAN da har ya daura masa aure da ita?wai me ke shirin faruwa?


Abban rabi ma zare ido ya koma yi saboda jin wani auren daga sama ba tare da zato ko tsammani ba.


Na gode Dr Sabo yanzu za mu iya wucewa gida saboda mu tattauna,cewar Abbie kenan ya fada yana duban Dr Sabo dan jin me zai ce ",babu matsala Dr Sabo ya fada suna mai yin musabaha da Liman.


Daga nan gaba daya suka rankaya suka fita daga masallacin,suna mai ci gaba da karbar gaisuwar masu fatan Alkhairi,wanda da yawa mutane basu san komai akan auren ba,bare su fara tunanin wace ce RAIHAN,ko yadda aka yi auren ya zama na mutum biyu.shi dai wazir bin su kawai yake da kallo ,sai dai baka taba gane yanayin da yake ciki,tunda da yawa mutane sun san yadda yanayin sa yake.




Zamewa ya yi ya nufi mota inda securitynsa yake tsaye yana jiransa,sai dai kafin ya saka gangar jikinsa cikin motar,wayar shi na fara sanar da shi a na kiran sa,a hankali ya zaro wayar ya dan duba samanta,sai ya ga sunan abbie,karawa ya yi bayan ya daga,ba gida za ka wuce ba ka wuce can gidan saboda nan ne za mu yi magana a nutse babu hayaniya,",ok ya fada yana karasa shiga motar,gidan su Rahim za mu je",ya fada yana mai kwanciya tare da lumshe idanunsa yana ma rasa irin tunanin da zaiyi.




Suma su Abbu nan suka nufa bayan sun gama sallamar bakin su,shi ma dai Abban rabi kallon su kawai yake bakin sa da jikinsa duk a mace saboda bai san komai akan abin da yayan nasa ya yi ba,wanda alamu duk ya nuna cewa yasan komai kuma dasa hannun sa komai din ya faru...........✍🏽
[12/21, 12:40]: *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page25 ```






A bangaren amarya rabi kuwa,tana can cikin farin ciki,duk da cewa tana jin wani faɗuwar gaba me tsanani tare da bacin rai,sai dai bata kawo komai ba tabarshi akan kawai basu samu yadda suke so akan bincikensu ba ne, sai dai kuma fariincikin aurenta da wazir ya danne wannan takaicin,hakan yasa ta Basar da wannan bacin ran ta cigaba da walwala a matsayin ta na amarya.




Mummunan labarin da ya same ta daga gurin friend dinta maza da suka halarci daurin auren shi ya ruguza duk wani farinciki da walwalarta.


Ko da taji labarin ba ita ka dai aka daura aurenta da wazir ba,zubewa ta yi a take a wajen ta sume.




Cikin shakku innawuro take duban haffiz dan goggo ta Kano,wlh innawuro ba rabi kawai ya aura ba da wata, da kunnena naji amma idan baki yarda ba ki kira su Abbu a waya",dakatar da shi ta yi ranta a matukar bace ta ce" bari kawai duk inda su kayi ina zasu zo nan su same ni?,ta tambaye shi tana zuba masa idanun ta kusan irin na wazir,da sauri ya jinjina kai yana mai tashi daga gurin dan kar bacin ranta ya ɗora akansa,daga ita kuwa bai kara fadawa kowa ba ya shiga sabgar gabansa.




A can sama kuma dakin amarya dakyar kawayenta suka samu ta farfaɗo da taimakon ruwan da suka dinga zuba mata.


Kuka ta sa tana mai duban Surry cike da neman karin bayani tare da kallon tuhuma,fahimtar hakan da sury ta yi yasa ta yi saurin girgiza kanta,tana karawa da cewa wlh rubyy ban san komai ba,Ni kaina daga sama naji zancan da matukar mamaki ya nemi tafiyar da numfashina,duk wahalar da nake yi ban samu amsar ko mai ba sai lokacin da bashi da amfani,ta yaya aka yi wazir ya shammace mu?


Wai shin ma wacece RAIHAN?


Me yasa a duk bincike na ban taba cin karo da komai sunan ta acikin rayuwar wazir ba?


Anya kuwa wannan al'amarin babu wani boyayyan abu a cikin sa?


Tunawa da wani abu da ta yi wanda ya yi daidai da tuna sunan da ta ambata na Raihan yasa ta wata irin zabura ,idanun ta gaba daya a waje numfashin ta har wani sama yake yi.


Kar dai mutumin nan yaudara ta ya yi? Ta faɗa tana mai figar jakarta,ko duban gaban ta bata yi ta fice daga dakin ba tare da ta saurari rabi dake tsimayin jin ta bakinta ba.




Kai tsaye gidan abbie suka wuce,babu mai cewa komai har suka karaso,sai dai dukan su da akwai abin da yake damun su.


A falon baffa suka yada zango inda suka sami wazir a can din yana jiran karasowar su,kamar ko da yaushe babu komai akan fuskarsa komai ya boye shi can kasan zuciyarsa, ba za ka taba gane cewa yana cike da dinbin mamaki ba,ba za ka gane cewa ya shiga rudani ba,yadda ya saba boye komai yau din ma ya boye abin shi,dan haka dukkan su babu wanda ya fuskanci halin da yake ciki.




Zama su kayi tare da gabatar da addu'a,daga nan baffa ya dubi Dr Sabo ya ce ",Dr muna sauraron ka".




Aunty amarya na kokarin shiga kiching wayar ta ta hau ruri kamar dama jira ake ta bude wayar,cikin dan kwarin gwiwar da take samu daga Dr Sabo ta daga ba tare da ta ce komai ba,dole zaki yi shiru saboda kin san munfincin da kika hada,to ki sani cewa ba tsira kika yi ba, sannan kuma ba ki tseratar da Raihan daga tarkona ba,auren da kika yi mata yana daga cikin makullin bude tashin hankali da wahala a gareku,dan haka ki jira yi sakamakon da zai biyo baya",ba tare da ya jira yi cewarta ba ya katse wayar.




Sakaro aunty amarya ta yi tana mai zurfafa tunani,kallon wayar take kamar ita ce zata bata amsar tambayar ta.




A falon baffa kuwa bayan su isu babu wanda suka kuma nema cikin zaman nasu,kaf Dr Sabo ya kwashe abin da ya faru tun daga haihuwar Raihan har zuwa yau ya sanar da su baffa,dukkan su labarin ya zo musu a ba zata , ya kuma dimautasu,sai dai daga abbie abun ba haka ba ne,dan ga dukkan alamu ya san komai.




Abbie ne ya gyara zaman sa tare da yin gyaran murya ya ɗora da cewa,baffa abin da yasa ban sanar da kai ko yaya ba, shine nima nayi hakanne domin na bawa ramla mamaki na kuma nuna mata kuskuren abun da ta aikata ba tare da tunani ko shawarar mu ba,kai kuma nasan idan na sanar da kai zaka ce sai an zauna da ita an fada mata komai."


Tun wane lokaci ne kai kasan da maganar?baffa ya tambayi Abbie fuskarshi cike da mamakin da ya kasa barinsa.




Baffa na dan jima da sani dan zan iya cewa tun lokacin da Dr Sabo ya bar kasar nan,kuma bani na nema ba shi da kansa ya ga dacewar na sani din ba kuma tare da ya sanar da ramla din ba,dan duk lokacin da ya yi mata maganar ya kamata a sanar dani bata bari ,tsoro ne yake shiga ranta acewarta idan na sani hakan zai bawa makiyanmu kofar sanin RAHIM ba namiji ba ne.shi yasa ko da ya sanar da Ni ban yi wani yunkuri a gaban idanun ta ba,sai dai abin da ba ta sani ba ina biye da ita duk abin da yake faruwa na sani,ko da ban sani ba Dr Sabo yana sanar da Ni kamar dai abinda ya faru na shekaran jiya,ina zaune Dr Sabo ya turo min duk abin da ya faru tsakanin lamra da wannan me yi mata barazana ɗin,da farko mun so muyi bincike dan kama mutumin ,to sai kuma muka fahimci cewa abun ba karami bane dan kuwa ya toshe duk wata hanya da za abincike shi, Sannan bamu da wata hujja ta gano shi din waye.




A lokacin da nake zaga babban office Dina na kamfanin audigar Raihan,a nan na hango katin daurin auren wazir a kuma take a wajen mafita ta zo min ,ban yi kasa a gwiwa ba na nemi a minina Alhaji chibaɗo babu mata lokaci ko noke noke na sanar da shi abin da ke faruwa ta yadda zai fahimta,sannan nazo da kaina nasanar maka a yadda muka tsara abun a gurguje kafin mu yi zama irin wannan,,shi ne dalilin da yasa muka hada aurensu duka biyun da rabi da Raihan,kuma shi wazir yasan komai hakan ba zai sashi ya razana ko daga hankali ba. Shi kuma Mustafha mun sa shi cikin lamarin ne saboda shine uban rabi ,dan haka muna so a ci gaba da rufa batun nan har zuwa wani lokaci tunda har yanzu bayan mu din babu wanda yasan wacece RAIHAN.




Baffa ne ya tari mfashinsa da cewa, meye hujjar ka ta mu cigaba da rufe wannan al'amari?Dr Sabo ne ya amsa masa da cewa baffa muna so ne mu yi bincike a nutse mu fara gano wannan mutumin da yakewa amarya waya,mun tabbatar da cewa idan muka kama shi za mu iya samun ragowar wadan da suke tare da shi,dan abin da ya yi ya nuna mana cewa yana da hannu a wancan lamarin na farkon haihuwar Raihan da ake son kashe ta,kuma muna ci gaba da bincike akan nos din da lamra ta ji a na bawa wannan aikin.idan kuma har muka bari maganar nan ta fita zasu yi kokarin kufce mana ne ko da kuwa suna kusa da mu",jinjina kai baffa da abbu su kai cike da gamsuwa,Abban rabi ya ce",insha Allah wannan ba matsala ba ce,kuma babu wanda zai ji wannan maganar ,muna fata Allah ya bamu nasara akan makiyan mu,da Amin suka amsa baki daya.




Abba yahya ya gabatar da addu'a tare da fatan samun nasara akan makiyansu na fili da na boye.


Wazir dai yana zaune kamar wani status,har yanzu bai ce komai ba kuma babu wata alama da ta bayyana akan fuskar shi,baya ga sassaucin da take yi idan yana gaban iyayen shi,abbu ne ya dube shi cikin natsuwa da son karantar ko kadan ne daga abin da yake binne a zuciyar shi wanda yasan cewa da kamar wuya.ya ce"ya dai wazirin gida baka ce komai ba?cikin biyayyarshi da Ako da yaushe ke karawa iyayen nasa kaunarsa ya ce"babu damuwa Abbu Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi ",Amin ya rabbil alamin suka hada baki wajen amsawa,Abba yahya ne ya dan numfasa tare da cewa, sai dai kuma abu daya da nake tunanin yadda za ayi da shi ,shine ta yaya za a boyewa mahaifiyarsa da kuma kakarsa,tun da nasan cewa a yanzu haka tuni labari ya kai musu cewa da mutum biyu aka daura auren?


Dan jim su kayi kafin, Abban rabi ya ce"wannan ai ba wani abu ba ne,karfa ka manta cewa mu ne ka dai muka san da Raihan ,dan haka ba sai mun sanar da su kan zancan ba,kawai dai wazir ya kawo matar da yake so an hada an aura masa duka biyun ",baffa ya ce" kuna ganin hakan ya yi dan bana so daga baya wata fitina ta bullo",Abbu ya ce"in sha Allah babu abin da zai faru in dai muna tare da addu'ar ku",addu a kam ai anayin ta sai dai kawai Allah ya cigaba da dafa mana ya kuma shiga tsakaninmu da makiyanmu,"Amin baffa suka amsa,daga nan su kayi sallama dan tafiya ,shi wazir ma kafin su mike shi ya riga su fita ba tare da ya bari sun fahimci abin da ya kumshe a zuciyar sa game da auren nasa da Raihan ba.




CHIBADO's HAUSE........




Kallo kawai innawuro ke bin su da shi bayan sun gama bata labarin da take jin shi kamar tatsuniya,shi kuwa gogan naku ko binsu sashen abbu bai yi ba,dake a can suka kira innawuro saboda nan ne babu jama a.Abban rabi ne ya kuma duban rabin da suka kira ta itama dan fita hakkinta a matsayinta na uwargidan da a kayiwa amaryar bazata,kuka take kamar ranta zai fita ji take tamkar ta sokawa kowa na wajen wuka,kai ita fa ji take zata iya halaka kanta ta kuma halaka wadda ake kira mata a matsayin amaryar wazir,cikin fada me kama da tsawa Abbanta ya ce",Malama ki mana shuru kan ki faraune ko kuma ƙarau?Ni sai nake ga ma kamar wazir din shi ya cancanci ban hakuri saboda bake yake so ba amma ya hakura ya yi mana biyayya,to me yasa mu kuma ba za mu kyautata masa da bashi abin da yake so ba?wannan ma ai shirmen banza ne. Ya kare maganar da jan tsaki yana hararar ta.




Abbu ne ya yi masa magana akan ya rabu da ita ai abinda aka yi mata akwai ciwo dan ta fitar da abin da ke ranta ba aibu ba ne.




Innawuro baki ce komai ba?ya maida hankalinsa kan tsohuwarshi,wani banzan kallo ta yi masa kafin ta bude baki cikin takaicinsu da ya kasa barinta ,ta ce" to me kuke so na ce? Tun da ku iyayensa kun yanke hukunci da abinda kuke ganin ya fi ai Ni bani da ta cewa,amma ku sani cewa Ni sam ban yarda da wannan auren ba,saboda ban san wacece ba ,ban kuma san yar gidan wacece ba,dan haka ba zan yarda akawo min wadda ban san ya tarbiyyar ta yake ba ehe kunji da kyau.kallon juna su kayi kafin kamar hadin baki su ka fara bata hakuri,amma ko gezau innawuro ba ta yi ba,sai ma umartar su da ta yi su ta shi su bata guri kar ta faffalla musu mari agaban yarsu.babu yadda suka so haka suka tashi sumi sumi suka bar falon.ita kuma rabi abin da innawuro ta yi shi ne ya dan sama mata nutsuwa ita ma ta ta shi ta fita zuciyar ta na saka mata mugayen nufi akan ko ma wace aka aura ma wazir din,tunda dama nemanta suke ido rufe ,ita ce ta hana zuciyar wazir ta so kowa,kai ita fa gani take yi ma kamar karya ne ba wazir ne yake sonta ba,wata manakisar dai ake son shirya mata.(harda baban naki hhh).




Suryy...........




Cikin kankanin lokaci ta isa inda tasan zata iya ganin sa,tun da har yanzu bata san takamaiman matsugunin shi ba,zuciyarta da idaniyarta kukan zuci kawai suke yi,fatan ta kawai ta yi ido hudu da shi ta ji dalilin yaudararta da yayi,yanzu ne take ganin wautarta haka kawai bata san mutum ba ta dauki yarda da amana ta ba shi kaico da makauniyar zuciyarta,ashe ita ta yiwa kanta ramin da zata faɗa,ta jima a gurin tana jiransa kafin ta hango shi cikin shigarsa da ta fahimci kullum ita yake yi,har yau bata san fuskarsa ba,bata da hujjar da zata neme shi idan ya bace mata saboda bata taba sanin kamanninshi ba,hannun da yasa ya kifta idanun ta da shi ne ya sa ta dawo tunaninta wanda bata Ankara ba har ya samu mazauni yana fuskantarta da boyayyan fuskarshi sai idanun shi kawai da take gani su ma din ba ainahin su ba ne ta ke gani.




Cikin bacin rai ta fara magana kamar zata yi masa duka saboda tsananin haushi da bakin ciki da takaici mai dimbin yawa da ya tokare kashin zuciyarta take ji har bata iya hadiyar miyau da sakin numfashi yarda ya kamata.


Me yasa kayi min haka?
Me ye shirinka akai na?
Meye dalilinka na yin amfani da Ni wajen cikar burinka?
Sannan kuma kai din waye kuma Me yasa ka haɗa auren wazir da Raihan a maimakon maganar da mu kayi da kai akan zaka sa a baka auren ta?.


Shuru ta yi tare da zuba masa idanun ta ko Allah zaisa ta gano kamanninsa,sai dai ina hakan ya zama abu me wuya a gare ta,miƙewa ya yi tsaye hannayen shi goye,zagaya ta ya shiga yi sai ka ce wani me aikin sihiri,sai da ya yi hakan sau wajen uku kafin ya dakata ya kuma zuba mata jajayen idanun shi dake tsorata mutum me imani.


Ke ba ki isa na yaudareki ba,ke baki isa na janyo hankalinki ta wata sigar ba,sannan kuma baki isa nayi miki dabara ba,idan ina bukatar ki kai tsaye zan janyo ki cikin aiki na ko kina so ko bakyaso kuma dole ki yi abin da nake so,dan haka ki sawa ranki cewa sai ki na tare da Ni zaki samu nasara akan abinda kike so,saboda nine tsanin nasarar baki daya", Surry samun kanta ta yi da kasa musanta mishi sai ma wani girma da kima da ya yi mata,haka kuma ta ji maganar sa ta yi mugun tasiri da samun mazauni a zuciyarta na cewa sai da shi din zata yi nasara.




Muhammad nurr hause.........




Aunty amarya kulle kanta ta yi a daki ita kadai,ko wayar Dr Sabo ta kasa kira dan a wannan karon kanta ya gama kullewa gaba daya,harma ta fara tunanin ko dai wannan mutumin ba mutum ba ne,idan kuwa mutum ne to ba karamin shu'umi ba ne,kanta ta dafe da yake wani irin sarawa saboda tsananin tashin hankali da shiga rudani,koda Abbie ya shigo ya taba kofar bedroom dinta ya ji a kulle bai kara kokarin san shiga ba,dan yasan tana cikin matsalar da yake ganin kamar ita ta jawa kanta.


Abu daya ne yasa Abbie ke yi mata uzuri shine SOYAYYA,tabbas yasan cewa son da take yiwa RAIHAN shine tsanin da yaja ta har ta aikata abin da take ganin shi zai kubutar da Raihan ɗin. Ya mata uzuri akan haka saboda yana kwatanta hakan da kansa da irin son da yakewa Raihan tun kafin yasan zai dameta a rayuwarsa.




Amma kuma abunda ya dan bashi mamaki shine ko lokacin da ta haifi Raihan a matsayin namiji,sai ya ji gaba daya soyayyar Raihan ta koma kan yaron,yana boyewa ne kawai saboda gudun haddasa fitina cikin iyalan sa,baya son ya kuma yin kuskuren da ya yi a baya,saboda ko mai da yake faruwa a yanzu shine sila duk da yasan cewa yana kan daidai kuma bai take hakkin kowa ba, sune dai suka kasa fahimtarsa saboda dukiyar Raihan ta samu kyakkyawan hannu kuma Allah ya yi mata albarkar da ta yi bunkasar da shi kansa yake mamaki wani lokacin,a ganinsa suma da tasu ta yi albarkar da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login