Showing 162001 words to 165000 words out of 189984 words
Chapter 55 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
gefanshi yana kallon abinda tunda yake a duniya bai taba gani ba sai dai yaji labari tsafi ba,to yau dai gashi ana aikata tsafi agaban idanunshi.
Wata irin zufa ce ta shiga kwararowa Abba yahya tamkar wanda ake jikashi da ruwa,cikin tashin hankali ya shiga neman tsohuwa saboda tazo ta taimakeshi,amma kiran duniya ya yi babu ita babu labarinta,a hankali cikin nutsuwa wazer ya taka zuwa gaban Abbie da yake ta kokarin tashi saboda jikinsa da yake son motsawa,cikin dan gaggawa wazer ya karasa ya dagoshi yana jera masa sannu,ina RAIHAN? Abinda Abbie ya fara tambaya ke nan farkon bude bakinshi,tana gida cikin koshin lafiya", wazer ya yi saurin bashi amsa saboda samun nutsuwarsa,jinjina kai ya yi sannan ya kuma cewa ina his excellency? Abbie ka nutsu in sha Allah za kaji komai shima his excellency ɗin yana nan lafiya", murmushi me ciwo Abbie ya yi yana kallon Dr Sabo da ya bashi amsa sannan ya ce", bana jin his excellency zai zama cikin koshin lafiya saboda hatsarin da Yahya ya jefashi a ciki,nasan ba wanda zai fahimce shi saboda sarkakiyar lamarin", haka ne cewar wazer,Dr Sabo gida kawai zan tafi babu bukatar zamana a nan", Abbie ya kuma fada yana ƙoƙarin tashi,da sauri wazer ya rike shi ya taimaka masa ya mike,Dr Sabo bai hanasu tafiya ba saboda shiima ya fahimci Abbie yana bukatar shiga cikin iyalansa ko dan rage radadin da yake ji a yanzu,ai shi yaga kokarin Abbie dan da wani ne ba zai iya juraba,wata wajen biyar yana kwance ranar farko da ya farka ya tsinci dan uwanshi jini daya a kanshi yana kokarin kasheshi ta hanyar tsafi,dan uwan ma da ya bashi yarda dari bisa dari kai wallahi yayi kokarin yin takwakkaloli,hirar Dr Sabo ke nan a cikin ranshi.
Dr Sabo juyowa ya yi dan su kama Abba yahya amma sai wayam babu shi babu alamunsa ya gudu,Dr Sabo ya fada yana kuma ware idanunsa a Loko da sako na dakin,babu damuwa duk inda yake zamu kamashi cewar wazer da yake sakale da hannun Abbie suna takawa a hankali.
Sai da Dr Sabo yaga fitarsu daga asibitin sannan ya dawo yana kuma tuajjibi da tsarkake Ubangijin talikai.
HAIDAR........
Karaf ya ji an rike hannunsa cikin duhun gurin da baya iya kallon ko abinda ke gabansa,kafin yaji kakkausar Muryar da ta saba yi masa magana duk lokacin da ake son yi masa magana tana,kana kiran wayar nan tamkar ka kira ajalinka ne dan OGA DUDU ba zai Barka ba,daga haka aka fizge wayar tare da fita daga dakin, sai alokacin yasan cewa ashe shigowa akayi tsabar baya cikin hayyacinsa ne yasa baiji motsi ba,in sha Allah na kusa barin gurinnan da numfashina,ya fada yana maida tsatstsaman jikinsa zuwa jikin bangon dakin dan jingina.
Kamar daga sama securitys din gidan suka ga Abbie ya fito daga mota,kafin wazer ya fito tuni sun ƙaraso cikin madaukakin farinciki suna jera masa sannu tare da taya murnar samun lafiyarsa,kafin wani lokaci tuni su mama murja da ahlinsu wadanda suke nan sun hallara a wajen,Hajiya goggo rungume shi ta yi tana kukan farinciki haka masu aikin gidan suka fito suna murna bangonsu ya samu lafiya,baffa Ali kuwa kama hannunshi ya yi suka nufi bangarensa da shi saboda ya fahimci Abbie yana cikin wani mummunan yanayi dan babu farinciki ko daya akan fuskarshi idan ka kula ma zaka ga lokaci lokaci yana share hawaye cikin dabara,baffa Ali ya ce", kowa ya tafi zuwa anjima kan sannan Abbie ya ɗan samu nutsuwa ya huta.
Wazer da yake shirin shiga dan duba Raihan ya dakata saboda sakonsu Dady da ya tarar rututu a wayarsa hakan yasa ya dakata da shiga falon ya koma ya fada motarsa yana jin wani irin rashin dadi ga wata irin gajiya da yunwa da suke ta cinshi saboda rashin samun Hutu ko nutsuwa a cikin kwanakinnan idan ka kula ma har wata yar rama ya yi.
Da sauri yaron dake biye da wazer ya kira wayar ABBAN rabi,yana dagawa ya ce", OGA ya fito daga gidan yanzu", ABBAN rabi ya ce", yauwa bari na kira ciska,kashe wayar ya yi ya kira su ciska.ciska yana dagawa ABBAN rabi ya ce", ku bishi da kun samu dama ku harbeshi a ko ina", ok OGA baka da matsala cewar ciska,kashe wayar su kayi tare da jan motar da suke ciki suka bi bayan wazer da yake tafiya kamar mara laka,ta window ya kula da masu binshi hakan yasa ya canja hanya cikin kwarewa da sanin makamar tuƙi.
Dakarfi ciska ya daki abinda ke gabanshi yana cewa shet wannan babban kaine ban taba aikin da aka wahalar dani irin haka ba,gaskiya idan na samu gayennan sai nayi masa kisan wulakanci saboda ya karya min record ", ciska ya fada cike da jin haushi.
Wazer yana ganin ya tsere musu ya dan dafe kanshi cike da gajiya,gidansa ya karasa, komi baiyi ba ya shiga kunna computer tare da yin cineccting din wayar Surry,take abinda ya faru ya shiga maimaita kansa ta hanyar murya,sai kuma ga hotan Bashir da su dady suka ɗauka ya fito baro baro,dan jim ya yi kafin ya furzar da iskar bakinshi, rufe computer ya yi tare da mikewa ,tashin da zaiyi sai ga wannan Flash din ya fado daga jikin kujerar da ya aje shi wancan karon,yanzu ma har zai basar saboda abubuwan dake gabanshi sai kuma ya koma ya zauna tare da daukar Flash din ya jona.
Runtse idanunshi ya yi saboda abinda suka gane mishi,duk da cewa yaga makamancinsa a asibiti ,ba komai ne a ciki ba sai irin barnar da Abba yahya yake ta kashe kananun yara da yanmata da yadda yake sawa ana kamo su ana cire musu wani sassa na bangaren jikinsu da yadda yake sawa yan dabanshi suna tada tarzoma dan kawai a zubda jini,gungun yan sara suka ne dashi sun kai su dari babu abinda yake sasu su yi sai barna da kashe rayuka,ashe ba iya nan ba ne rarraba su yake yi jiha jiha suna sato masa kananan yara yana bawa tsohuwa me jini jininsu dan kawai yana son mulki da kuma uban kudin da Abbie ya tarawa Raihan da shi kansa wanda Abbie yake dasu,karshe wazer kasa ci gaba da gani ya yi saboda muguwar barnar da ake yi,kashewa ya yi yana tunanin ta yadda aka yi aka tara wadannan shaidu duk a guri daya,duk da cewa hadasu a kayi to amma wane dan tsautsayinne ya ke shiga wadannan guraren yana dauka ba tare da an Ganshi ba? Duk da cewa video bai nuna fuskar Abba yahya ba ma ana dai wanda ya haɗa videon baisan waye me wannan barna ba,to amma ya akai yazo wajen shi? RAIHAN ya furta akan labbanshi cikin daukaka mamakinshi tabbas ita ce,da sauri ya mike tare da daukar Flash ,yana kokarin fita ya tuna da karamar wayarshi da yau kaf bai dubata ba,bayan tana daga cikin manyan wayoyin da yake yi na sirri akan aikinshi,duba fuskar wayar ya yi bayan ya kunna haskenta,miss call ya gani da bakuwar nomber,a yanzu baya kin bin nomber ko yaya take dan haka ya shiga kiran nomber amma sai aka ki dagawa,kallon fuskar wayar ya kuma yi sai yaga alamun sako hakan yasa ya yi saurin shiga inbox ya bude sakon.
Wazer kayi tracking number nan ko kuma kasawa Alh Yahya ido domin duk abinda ke faruwa shine a yanzu haka ina hannunsa dalilin sirrinsa da yake tunanin cewa Ni na bankadosu bayan bai san cewa Raihan ce ta haɗa video nan ba,Ni nawa shine gano shine a cikin video da nayi,ganin bai gano Raihan a cikin case dinba shi yasa naki sanar dashi inda Flash din yake ko kuma wanda na bawa,sanin cewa za a iya kamani shi yasa na yi dabarar yi maka text ina fata zaka taimakamin ka kuma taimaki his excellency ta hanyar watsa wannan abin ta boyayyar jaridarka me suna tree full y trues.........✍🏽
Mu hadu a netx pg dan sanin waye ogan Surry
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page61 ```
......Yana gama karanta sakon ya damƙe wayar a hannunsa tamkar zai rabata biyu,sai da ya dauki kusan sakon goma a haka kafin cikin sauri ya dauki nomber da haidar ya Turo masa sako ya turawa Yusuf tare da yi masa short din sako da cewa yana so a yi tracking nomber nan a ranar nan, yana gamawa aka kwala kiran sallar magriba, dan haka ya koma ya dauro alwala ya fita sallah.
Baiyi gaggawar tashi daga Masallaci ba har sai da aka kira isha ya gabatar da ita cikin jam'i sannan ya baro unguwar gaba daya, zuciyarsa cike da tsoran Allah tare da mamakin abinda mutanen duniya suka zama akan son zuciya.
Duk abinda ke faruwa Raihan bata sani ba,saboda Baccin da take yi,sai dab da magrib hajiyar agadex tazo ta tasheta tana cewa haba Raihan wannan wane irin bacci ne haka? Ku dai yarannan na zamani gaba daya baku da kunya duba dai daga Zuwan mijinki har kin ware kina bacci kamar bake ce me yiwa mutane bore akan bakya sonsa ba fi'ilin banza fi'ilin wofi,shima da nake jira yazo ya sanar dani abinda ake ciki banga idanunsa ba tun ina jiransa har na hakura Ni ma na kama Baccin rashin abinyi,da wannan mitar abakinta ta fita,ita dai Raihan bata tanka mata ba, tashi ta yi ta Wada toilet ta ɗauro alwala ta yi sallah sannan ta fito falon tana raba idanu dan ganin ta inda Mami zata bullo,tunda ta shiga dakinta bata ganta ba ta fito ta shiga dakin hajiyar agadex tana tambayarta Mami bata dawo ba?
Kafin hajiyar agadex ta bata amsa sunji sallamar Abbie da ya kasa jure rashin ganin Raihan da maminta ya gudo bayan ya yi wanka ya yi tsaf dashi kai baka ce shine yake kwance tsawon watanni babu motsi ba.
Ko a mafarki Raihan taji Muryar Abbie dinta sai ta gane shi,dan haka cikin wani irin gudu kamar zata kifa ta fito daga dakin Hajiya tana baza ido dan tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata,aiko da fuskar Abbie ta ci karo yana tsaye a tsakiyar falon fuskarsa akwai walwalar da babu a dazu farkon zuwansa, alhamdulillah abinda Raihan ta faɗa ke nan tare da kankame Abbie tana zubda hawayen farinciki,cikin wata irin kauna mara misaltuwa Abbie ya yi mata masauki a jikinshi yana shafa kanta cikin kaunar da baki ba zai iya fadinta ba,dukkansu babu wanda yake iya magana sai ajiyar zuciya da suke saukewa a tare,tabbas wani farincikin ya wuce gaban a kwantantashi ko a tsaya fadarsa da baki.
Hajiyar agadex kanta da ta fito ruwan hawaye take matsewa daga idanunta dan su abin yazo musu a bazata daga ita har Raihan ɗin. A hankali ya janyeta daga jikinshi tare da kama hannunta suka zauna akan kujera,itama hajiyar sai ta zauna tana kallon Abbie cike da son karin bayani,fuskantar hakan da ya yi ne yasa shi murmushi sannan ya ce", Hajiya mun sameku lafiya? ya a kaji da wannan tashin hankali? Alhamdulillah Nura ko mai ya wuce tunda Allah ya baka lafiya ya tasheka ba tare da iyawar masu iyawa ba,ya nufe ka da bude ido dan ya nuna shi din ishashshene me yi a sanda yaso,lallai Allah alhakimune babu abinda zamu ce sai godiya gareshi", ta karasa maganar tana goge ragowar hawayenta, jinjina kai Abbie ya yi sannan ya dan kalli Raihan yana cewa ina maminki take banji motsintaba? Da sauri RAIHAN ta kalleshi tana mai fiddo manyan idanunta da suka nuna tashin hankali a lokaci ɗaya,sannan ta ce", Abbie tun wajen la asar Mani ta fita cikin damuwa ta ce min wajenka zata zo kuma har yanzun bata dawo ba," shiru ya yi yana son tuna lokacin da ya farka,lallai lokacin da ya farka babu ramla a asibiti dan da tana nan Abba yanzu ba zai samu damar shiga ba duk da cewa yana takama da tsafinsa ne a lokacin", idan haka ne ramla ba taje asibiti ba ke nan", wannan tunanin da ya yi yasa kirjinshi dukan tara tara, Allah yasa ramla bata shiga komar Yahaya ba dan lokacin da suka fito ya gudu idan haka ne ke nan har yanzu wasan baizo karshe ba, innalillahi wainna'ilaihi raji'un ya furta can kasan ransa saboda baya so Raihan ta fahimci wani abu dake faruwa bare har ta tayar da hankalinta.
Cikin dabara ya dubi Hajiyar AGADEX yayi mata alamar cewa dakwai matsala,take ta gane abinda yake nufi dan haka cikin saurin danne Tata damuwar ta ce da Raihan ", Kinga Raihan na manta ban gaya miki ba maminki can AGADEX ta tafi zata karbowa Abbie dinki wani magani to gashi cikin ikon Allah ma kafin yasha maganin sauki yazo daga rabbil alamina,dan haka ina tunanin bata samu jirgi bane shi yasa ta bari sai gobe", cikin gamsuwa da maganar hajiyar Raihan ta gyada kanta tana cewa amma me ye na boye min din? Kar ki damu da wannan kinji auta cewar Abbie yana kallonta cikin tausayawa,shike nan Abbie ta faɗa tana barin falon.
Shiru su kayi bayan barinta falon kafin Abbie ya ɗan numfasa cikin damuwa ya ce Hajiya yanzu ta ina zamu fara neman ramla dan na tabbata cewa Yahya ne ya dauketa,Nima haka nake tunani cewar Hajiya,mikewa ta yi tana cewa Nura ka kwantar da hankalinka ramla zata dawo tashi ka koma wajen iyalanka in sha Allah zan yi wani abu", bai Musa bata ba ya tashi ya bar dakine,sai da ta tabbatar ya tafi Sannan ta tashi ta koma dakinta,tsaf ta gama shiri cikin dogon hijab sannan ta kuma fitowa kai tsaye ta dau hanyar barin gidan,aljanarta ce a tare da ita dan haka ita tale haska mata kogon tsafin su tsohuwa me jini,bakinta dauke da karatun bakara sura me tarwatsa rundunar aljannu,zuciyarta cike da son tarwatsa wadannan mutanen mushrikai makiya Allah in sha Allah yau sai na kawo karshen ku da izinin Allah ta faɗa a fili tana ci gaba da tafiya me nisa ba tare da gajiya ko gazawa ba.
Wazer kai tsaye gidan Alh Muhammad nur ya taho,duk da cewa dare ya dan fara yi to amma be ji zai iya zama a gida ba tare da yasan yadda Raihan ta yi ta haɗa wadannan videos din ba dan shi har yanzu mamakin hakan yake,bai taba tunanin cewa kwazo da jarumtar matartashi ya kai haka ba.
Yana yin fakin ya fito ya nufi inda yaga Abbie tsaye shida Bashir da shima bai jima da dawowa ba,a maze yake duk da cewa ya shiga tsananin shock da ganin Abbie sai bai nuna ba ya shiga nuna farin cikinsa anan Abbie yake tambayarsa yaushe ya dawo yake sanar dashi bai jima ba dan ko sati baiyi da dawowa ba matarshi ma shekaran jiya ta rasu,,sosai Abbie ya jajanta masa daga nan ya umarce shi da su wuce sashen baffa Ali saboda yana son ganinsu gaba daya gidan,bai Musa ba ya bishi a nan ne su ka ci karo da wazer,janyo hannunsa Abbie yayi yana cewa zo muje kai dinma ka zama ɗan gida kome za ai ya kamata ayi da kai itama Raihan ɗin yanzu zata fito", hakan yasa wazer ya bisu suka rankaya gaba daya zuwa part din baffa Ali.
RAIHAN dai bata fito ba dan gaba daya hankalinta ya koma kan maminta,waya ta dauka ta kirata akaro na kusan biyar yanzuma tana ringing ba a daga ba wanda hakan shi ya tayarwa da Raihan hankali.
A daidai wannan lokacin Aunty Amarya na kulle jikin kujerar da suka daureta masu gadinta suna can daga waje,sam babu wanda ya lura da wayar Aunty Amarya dake yashe daga can gefe inda ta fadi lokacin da suke kokarin kulleta,tana kallon wayar sai dai babu halin dauka dabara ce ta fado mata,hakan yasa cikin sauri ta tura kafarta dake daf da wayar cikin dabara ta dinga janyo wayar tana yi tana kallon kofa,cikin ikon Allah wayar tazo daf da ita sai dai kuma yadda zata yi ta dauki wayar ne tashin hankali,tana kallo wayar ta mutu Raihan ta kuma kira,da sauri ta hade hannunta ta fara kici kicin kunce daurin,idan Allah zai kawo maka mafita tofa zai kawo maka ne ta inda baka taba zata ba dan daga baya dakanka idan kayi tunanin hanyar sai ka shiga al'ajabi da mamakin yadda akai hakan ta faru,itama Aunty Amarya haka ne ya faru da ita dan kuwa cikin ikon Allah sai gashi ta kunce daurinnan tas,take ta yi hamdala ta godewa Allah sannan ta yi azamar daukar wayar wadda ta sake katsewa a karo mara kirguwa,kiran RAIHAN ta fara yi.
Raihan da ta gaji da kiran mamin ta aje wayar cikin sarewa da tsananin damuwa, har zata fita daga dakin ta ji wayar na ringing,da gudu ta koma ta dauki wayar hannunta da muryarta duka rawa suke gurin daga wayar da kiran sunan maminta,Mami kina ina? me ya same ki ? Me ya faru kika ki daga wayar? Cikin yin kasa da murya aunty Amarya ta ce", Raihan ina cikin hadari amma ina so ki kwantar da hankalinki kar ki sanar da kowa sai wazer, Raihan daya daga cikin butulayen gidannan yayi garkuwa da Ni ,take ta sanar da Raihan manufarsa ta saceta,ta ɗora da cewa nasan dole zai kira dan haka ki shiru ki kwantar da hankalinki nasan wazer ba zai taba barin ko waye ba.cikin kuka Raihan ta ce", Mami ina cikin farin cikin tashin kafadun Abbie ke kuma kika fada wannan hadarin ke nan har yanzu ba zan samu cikakken farinciki ba? Wane Abbie din kike fada? Mami Abbie mijinki Allah ya tasheshi cikin ikonsa da buwayarsa a yanzu haka yana falon baffa Ali ya ce", yana son ganin kowa da kowa," alhamdulillah ala kulli halin RAIHAN bani da wata damuwa in sha Allah za muyi galaba akan makiyanmu,yanzu ki tashi ki je ,ina so ki kula da wanda baya gurin ko wanda zai shigo yanzu saboda shi wanda ya sace nin yanzu ya taho gidan dan haka nasan zuwa yanzu bai ƙaraso ba saboda gurin yana da