Showing 60001 words to 63000 words out of 189984 words
Chapter 21 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
canja din ta shiga wannan tsarin wanda ya yi matukar bawa sakateria mamaki kai harma da sauran staff din dake saka idanun su akan lamarin da bai shafe su ba,shi kan sa oga kwatakwata wani iri ya ji lokacin da ta fara yin hakan,har yanzu kuma ya kasa sabawa ,duk lokacin da ta yi hakan sai ya ji wani irin abu can kasan zuciyarsa,yanzun ma ɗan jim ya yi kafin ya jinjina kai.
Dubanta sactaria ta yi tare da cewa kana iya shiga,ok thanks" Raihan ta faɗa a nutse babu alamun wata damuwa akan fuskarta.
A nutse ta yi sallama ta shiga,tsayawa ta yi bayan ta gaida shi,sai da ya nuna mata wajen zama sannan ta zauna ,tana mai kame fuskarta kamar yadda shima yake yi a koda yaushe,cikin nutsuwa ta gabatar masa da abinda ya kawota,tana kokarin tashi ya kira sunanta a hankali can cikin ƙasan makoshinsa,yana mai binta da kallon ƙasan ido ta yadda ba zaka taba fahimta ba,sai dai ita da take jin kaifi da tasirin idanun nasa a cikin gangar jiki da zuciya,ba ta amsa ba sai dai ta hakura daga kokarin tashin da take yi,kanta yana kasa,kafin ya ce"wani abu anyi knocked dor,izinin shigowa ya bada ba tare da ya.dainawa Raihan kallon ƙasa idon da yake mata ba,yauwa sir kana da bako a waje,na fada mishi kana tattaunawa amma ya nemi da a barshi ya shiga da alama dai wani babban jami'in ne",ok ce ya shigo", ya bata amsa yana mai tsaida idanun sa kan Raihan da ta tsuke fuska kamar zata yi kuka.
Sallama ya yi cikin nutsuwarsa da kamala ya shigo,miƙewa wazirr ya yi su kayi hannu cikin mutunta wa,nuna mishi wajen zama ya yi kujerar da ke fuskantar Raihan, tashi RAIHAN ta yi tana mika gaisuwa a gare shi,kokarin fita ta fara yi ya kuma dakatar da ita da cewa ban sallame ka ba"juyowa ta yi tana duban shi cike da jin haushin tsaida tan da yake yi,sai dai kuma kamar ma bashi ne ya yi maganar ba,komawa ta yi ta zauna dan kar wannan bakon ya yi musu wata fassarar amma da wlh tafiyar ta za ta yi,mitar da take yi cike da kunkuni kenan,yana jin ta yana kallon ta dan duk wani motsinta a cikin jikin shi yake jin shi.
Gyaran murya HAIDAR YAHYA RINGIM ya yi tare da fara gabatar da kansa a wajen su,ya ɗora da cewa ina so za muyi magana me muhimmanci da kai"ya fada yana ɗan duban Raihan da tayi kamar bata office ɗin,babu matsala zaka iya fadar ko me ye a nan din bani da damuwa da wannan ɗin,wazir ya fada saboda ya fahimci zaman Raihan ne ya saka shi fadin hakan.
Kamar yadda na sanar da kai sunana da kuma aiki na,zan kara maka wani dan takaitaccen bayani dan kafahimci manufata me kyau,a yadda nake ji a bakunan mutane cewa gaskiya ta ce ta kawo Ni wannan matsayi,to na yadda da hakan,sai dai kuma naci na da son tabbatar da gaskiya yasa na dage sai an kawo Ni nan din,dan gaskiya ba Yola a ka so kaini ba,a kwai wani sako da na samu ta hanyar kutsowa da wani kwararren masanin computer ya yi kuma ina tunanin dan jarida ne,cikin shafina,in da na tarar da muhimmin sako wanda shine ya ingizoni zuwa nan din domin kawo taimako ga al ummar wannan jahar,a iya binciken da nayi na samu tabbaci akan duk abin da aka sanar da Ni ta hanyar wannan sako.
To amma da zuwana tun jiya na fara binciken gidan jaridar da ya kamata na fara ziyarta dan kuma samun tabbaci da gaskiyar abin da yake faruwa,kuma alhamdulillah naji dadi saboda duk wanda zan tambaya cewa zaiyi indai gaskiyar batu nake so na tuntubi jaridar chibaɗo daily trues,ko kuma na bibiyi labaran su na chibaɗo fm, da duk sauran tashoshin ku,domin ku din masu nagartane wadanda suka tsaya akan Gaskiya.
Da kamar Raihan ba za ta saurare shi ba,to amma jin bayanansa da kuma fara fuskantar inda suka dosa yasa ta fara bada hankalinta a sauraron bayanan nasa da yake yin su dalla dalla kuma daki daki cike da ilmi.
Ina fata za ku bani dama da kuma lokacin ku domin nima din irin ku ne da nake son tabbatar da gaskiya da san kwanciyar hankalin yan uwana musulmi",shuru ya yi da alamun yana son a tanka mishi, Raihan ce ta yi magana ganin wazir ya kalleta, cikin nutsuwarta da kaifin tunani,ta ce" yallabai yanzu me kake so daga gare mu ko kuma wane taimako kake so mu yi wa wannan himma taka???
Jinjina kai ya yi cike da jin dadin tambayar da Raihan ta yi masa,ya ce" ku yan jarida ne wadan da suke da matukar muhimmanci a cikin rayuwar al'umma har da aikin da hukuma,sau da dama idan wani abu ya faru da ake bukatar dauki kune farkon mutanen da za a fara gani a gurin wanda ko da yan sanda ba su san da batun ba,zasu sani ta hanyar ku,haka.kuma duk batun da ya bullo ta bangaren yan jarida masu gaskiya hukuma tana bashi muhimmanci ko dan kar a yi musu mummunan zato akan aikin su,kuma ta hanyar ku ne kaɗai al umma suke kai kukansu akan wani tauyewa wanda ko da basu da karfin zuciyar tun karar hukuma ku din zaku zame musu jagora,dan wani lokacin da mutum ya tunkari hukuma kai tsaye Gara ya tunkareku , domin tunanin shi yana bashi ta hanyar ku ne kawai zai samu adalci,kamar yadda muke da Baragurmi a cikin hukuma haka kuke da Baragurbi a cikin yan jarida dan kuwa ƙalilan ne masu gaskiya,kamar yadda take akan ko wane aiki a cikin ko wace al'umma,dan haka ina so mu hada karfi da karfe domin bincike akan abin da yake a lullube game da abin da ke faruwa a wannan jihar,domin hakan shine zai kawo kwanciyar hankali a cikin al'umma",
Duk da cewa kalaman Haidar sunyi matukar tasiri a gare su,domin kuwa dama irin su suka jima suna nema,duk da cewa ansha kawo irin sa din amma da an fara bincike ko yana shirin farawa,sai dai ka wayi gari babu mutum an nemeshi an rasa ko kuma a tsinci gawarsa a yashe anyi masa kisan wulakaci.
Fuskantarsa Raihan ta kuma yi sosai tare da cewa shin me ka taka me nene kwarin gwiwarka akan hakan? Idan baka sani ba bari na gaya maka,mutane irin ku basa kaiwa labari a wannan jihar???
Murmushi Haidar ya yi yana fuskantar Raihan da yake kallo a matsayin namiji a idanun shi,kuma me matukar basira wanda ya yi matukar dacewa da aikin shi,ya ce" meye sunan ka saurayi?kwarin gwiwar ka yana burge ni domin wannan tambayoyin naka cike suke da ilmi wanda yake nuna tsayuwa da jajircewa akan gaskiya" , RAHIM MUHAMMAD NURR, Raihan ta bashi amsa tana kawar da kanta da satar kallon wazir da ya yi tamkar baya wajen,hasali ma kwanciya yayi jikin kujerar
idanun shi a lumshe kamar me bacci,shi Haidar bai damu da wannan ba dan tun kafin ya karaso ya samu bayanin halin sa,duk da cewa ba a ce masa yana da girman kai ba,a halayyar da aka zaiyano masa kaf babu na Allah wadai, miskilancin dai shine,kuma shi bai ga abin damuwa da hakan ba,shi yasa da yaga haka kacokan ya maida hankalin sa kan Raihan ɗin,
Kune kwarin gwiwa ta,da kuma me wannan sako da shi ne asalin komai,a yanzu haka wannan boyayyan dan jarida me suna tree full Y trues ,ya fara suna a can wasu jahohi kamar Kano Kaduna katsina da sauran su,nayi mamaki da baku san labarin sa ba,duk da cewa mu din bamu rufa wata daya da sanin shi ba,ko nace bai rufe wata da bullowar shi ba,kuma.ina kyautata zaton shafinsa zai ci gaba da zagayawa har ya zago cikin Yola da kewayanta,ya boye komai nasa duk irin shaharar ka a sanin computer ba zaka taba gano ainahin sunan sa da duk wasu bayanan sa ba.kalaman sa sune kwarin gwiwata da kuma gaskiyar da nake tafe da ita baban abin kuma dogaro da Allah domin idan har ya kawo karshen abinta sanadin mu to kuwa babu wanda zai mutu a cikin mu har sai mun ida kyakkyawar manufar mu".
Sai a lokacin wazir ya bude lumsassun idanunsa da suka dan sauya kala,ya dubi Haidar kana cikin kamammiyar Muryarshi me cike da nutsuwa ya ce" Haidar baka da matsala in sha Allah muna tare da kai kuma duk abin da muka samu kaine farkon wanda zai ji kiranmu ko kuma ganin sakonmu"',na gode Chibado tun kafin nazo nasan bazaku taba sarayar da kwarin gwiwata ba",sai dai abu daya RAIHAN ta faɗa ba tare da ta dubi dayan su ba,ba ta saurari cewar dayan su ba, wanda dama wazir ba cewar zaiyi ba, ta ce" wannan ya zama sirri a tsakaninmu,kar karka sake ka fito da maitar ka da manufarka ta san gano gaskiya,za muyi komai a cikin sirri,kwantar da kai duk umarnin da na sama da kai su ka baka kabi,dan ina tabbatar maka da cewa ta wannan bangaren za mu yi babbar nasara,saboda kawo yanzu na gama tabbatar cewa da saninsu komai ke faruwa ma ana dai da hadin bakin su".gaba daya shuru su kayi hatta da wazir a yau sai da ya yi matukar mamaki da jinjinawa basirar Raihan,yar baiwa ya fada can kasan makoshin sa,shi kuwa Haidar kasa boye mamakinsa da fariincikinsa ya yi,sai da suka bayyana kan fuskarsa ta asalin bakano, kana ya kara da cewa,Rahim kai din na musamman ne gashi tun ba aje ko ina ba,ka fara aikin da muke son cimmawa, wannan tunanin yayi kyau kuma abin da ka fada gaskiya ne ,a gain dai zanyi yadda ka ce, wannan shine karamin su babban su,sosai zaka iya aikin jami in tsaro",miƙewa wazirr ya yi saboda gundurar sa da maganganun da Haidar yake wa Raihan ɗin su kayi,ranshi ya ji yana ɓaci,an ya ma kuwa zai yadda Raihan ta shiga wannan aikin ? Tun da gashi wannan Haidar din ya fara rawar kafa akanta"wata zuciyar ta ce masa,haba wazir relax mana,kar fa ka manta kai kadai ne kake kallon Raihan a mace...
Haidar ya katse shi ta hanyar mika masa hannu ya ce" shike nan sai na ji ku na kuma gode da karamci,ga nomber ta nan ina fata zan samu ta daya daga cikin ku? Raihan ta san wazir ba bada tasa zai yi ba hakan yasa ta mika masa katin ta,tana cewa gashi nan za ka.iya neman daya daga cikin nombobin nan".....wani kallon kasa kasa wazir ya yi mata ita da katin da ta mikawa Haidar ɗin,ya na kasa hade yawun da ya daskare a bakin sa,godiya Haidar ya yi kana ya yi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da fariincikin haduwa da Rahim.
Tashi Ta yi zata fice,amma sai ji ta yi ya janyo hannun ta da dan karfi,wanda hakan yasa su kayi kusanci da juna har tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa....................✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page20 ```
"Zuba mata lumsassun idanunsa da suke karya lakar jikinta ya yi,yana son su haɗa ido amma sai ta rufe idanun ,hakan kuma sai ya bashi damar tsurawa kyakkyawar fuskarta ido,zuciyar shi na wani irin sanyi wanda yake shiga har cikin bargon shi,hannuwanta da ya haɗa ya rike take ta kokarin kwacewa saboda yadda jikin ta ya fara rawa zuciyarta na ƙoƙarin karyewa ,saboda a kallon da yake mata take fuskanta da kuma jin yadda abin yake damun shi,jan hannun ya yi hakan yasa suka kuma yin kusanci sosai, ɗauke numfashi ta yi tana kokawa da abin da ke tokare kirjinta da numfashinta,can kasan makoshinsa ta ji dakakkiyar Muryarsa wadda ke cike da wani irin amo me tsayawa a kwanya,ya ce"meye laifi na Ni?
Da sauri ta bude idanun ta ta kalli fuskarshi wadda ke a kame kamar ba shi ya yi maganar cikin mutuwar jiki da Jigatuwar ruhi ba,kasa magana ta yi saboda fuskantar kamar ma ya raina mata wayo,wato ma ya manta shine ya fara kuma shi ya koya mata,amma yake tambayar meye laifin sa,bata da abin ce masa dan haka kawai ta kawar da kanta gefe dan bazata yadda da abinda yake son yi din ba,wato na son ta kalli cikin idanun sa,har yanzu kallon ta yake wanda hakan yasa take mamaki shi ko gajiya ba yayi ya yi ta kallo duk da cewa ta daɗe da sanin cewa ba dabi'ar shi ba ce,hasali ma ko namiji ɗan uwanshi bai tsayawa ya yi masa kallo fiye da biyu,duk sanda ake masa magana ko yake yi,zaka sameshine kansa a jingine idanun sa a lumshe idan a zaune yake,idan yana tsaye ne zaka ga yana duban wani gurin dan sai ka zaci ma baya tare da kaine,sai dai ba haka bane kawai ɗabi ar kallo ce bai da ita ,kuma shima bai so a cika kallon sa,shiyasa yake matukar jin haushin rabi a saboda kallonsa da take kamar zata cinyeshi ko kunya bata da shi a matsayinta na mace,baramma idan ya hada ta da Raihan wadda bata iya kallon cikin idanun sa,ita da take cudanya da maza kuma a matsayin da take da shi na namiji.
Tura karamin bakinta tayi ,cikin ƙunƙuni take cewa yanzuma haka yake kallon yan iskan yanmatan da suke son shi mune yake nuna mana baya iya kallon mutum,sarai yaji me ta ce,amma sai ta fuske da cewa na baki iznin bashi nomber ki ne? Tambayar rainin hankali"ta faɗa ƙasa ƙasa,a fili kuma ta ce"ai naga kai ba bashi naka za kayi ba,kuma shi din yana da muhimmanci "yaushe kika san muhimmancin shi?
Ya kuma jeho mata wata tambayar da take daukar su na tsantsar rainin wayo,idanuntane suka kawo ruwa, ta kasa ce masa komai sai hawaye, knocked dor din da akayi shi ya taimaketa daga tarkon da wazir yake danawa zuciya da gangar jikinta,sakin hannunta ya yi ,tayi saurin gyara fuskarta , Sannan ta nufi kofar,daidai nan ya bada izinin shigowa cikin kamammiyar Muryar shi da tsarewar gira,karo su ka ci da sakatarea ,ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce ta gefanta, kai tsaye ta fice daga office din.
Chibado's Hausa
Kuka take wa innawuro kamar ranta zai fita, innawuro kuwa saka mata ido kawai ta yi,sai da ta yi me isarta,kana ta ja numfashi me dumi ta fesar,cikin shakurarriyar murya ta ce" yanzu innawuro kina kallon abun da hamma wazir yake min ya dace ?.
Ki duba dai ki gani tun da aka yi maganar auren nan bai kalli inda nake ba bare nasa ran zai saurareni mu tsara rayuwar mu da yadda shirin bikin zai kasance,Ni gaskiya wannan abun yana damuna kawai kiyii mishi magana"',wani kallon banza innawuro ta wurgawa rabi kafin ta bude baki cikin gatsali ta ce"to uwa ta,ai idan ba uwar da ta haifeni ba,babu uban da ya isa ya sani a gaba da bani umarni,ke idan ba sakarya ba,kina fa kallon da yadda ya amince za ayi auren amma shine kike son mu daga masa hankali yadda zai yi kaura ya bar ƙasar da maganar auren gaba daya ko? To bari kiji na gaya miki Ni na gama nawa aikin sauran aikin ya rage naki ,ai ke macece idan kina da dabaru da salo na kwatar soyayya sai ki gwada,shawara daya zan baki shine ki fara karantar halin wazirin gida dan naga har yanzu baki san ko waye shi ba,idan baki fara sanin halinsa ba to tabbas zaki ci wuyar zama da shi",daga haka ta ci gaba da kallon ta hankali kwance ba tare da ta kara duban inda rabin ke zaune tana sharar hawaye ba.
Ta shi ta yi ta nufi dakinta,tana mai lalubo wayar ta,kira daya a ka daga wayar da wata iriyar shewa a lokaci daya wadda ta kira tana cewa shegiyar duniya yau ke nan kin tuna daNi a duniya ko?ajiyar zuciya rabia ta ja ,kana cikin yar damuwar da take ciki ta ce" suryy dan Allah ina zan same ki ina bukatar shawarar ki a wannan gabar saboda kaina gaba daya ya kulle,matsalar wazir ta fara toshe min numfashi wata kila sonsa ne zai zama ajalinna",suryy ta kuma yin wata shewa irin ta yan duniya, Sannan ta ce" ruby ai na dauka yanzu bakya bukata ta a rayuwarki,saboda tun da kika koma wannan gidan fita ta gareki sannan kika daina hulda damu kawayen ki waike kinzo gidan mutunci kar a ganki da kawayen banza asirinki ya tonu to ai dai naga duk inda tuwo yake sunansa tuwo",ta karasa maganar cikin dan bacin rai.
Dan Allah suryy ki yi hakuri mu bar maganar nan,yanzu ki gaya min inda kike",bazan fada ba sai dai Inzo gidan,dan jim rabi a ta yi kafin ta ce" to amma dan Allah suryy kiyi shigar mutumci bana so a gano boyayyan halina a gidan nan,kin san cewa badda kaman da nayi ne yasa har naja ra'ayin karkarmu ta amince da maganar auren nan",to shike nan in dai wannan ne kar ki damu dogon hijab zan saka har kasa,indai zaki barni na shigo gidan chibado's family"shi ke nan sai kinzo,daga haka suka yanke wayar rabi a ta fara kirga sakanni zuwa mintuna na zuwan kawarta suryy.
RAIHAN na fitowa daga office din Ahmad wazir,su ka ci karo da abu Huraira a hanyar sauka, yauwa kai nake nema dama,tun dazu naji dadi da baka tafi gida ba,ɗan duban shi Raihan ta yi a wani yanayi wanda wazir ya jefa zuciyar ta a ciki,lafiya dai ko? Ta tambaye shi tana dan basarwa dan kar ya gano damuwarta,labari ne me zafi akan su Alh sale da Dr sanate",dan jim ta yi kamar me tunani,sai kuma ta ce"wlh abu Huraira na gaji gida zan tafi idan Allah ya kaimu ma tattauna idan kuma na hau online sai mu yi magana "ok to ka huta lafiya"sallama su kayi. Raihan ta gangara ta dauki mashin ɗinta ta yi gida.
Chibado's hause
Sai da rabi ta yi waya da security na gidan sannan su ka bar suryy ta shiga,a falo suka hadu tana