Showing 72001 words to 75000 words out of 189984 words

Chapter 25 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15660

da Hajiya goggo ta kuma shigowa ta yi ta dubata,haka hamma idi da matar shi auntyy Zainab ,kusan a nan din suka raba dare kafin su wuce sashen su.




Chibaɗo's hause........




A nutse ya kammala shirin sa na bacci,kafin ya janyo wayar shi ya danna kiranta.


Zubawa wayar ido ta yi,sai kawai ta ji wasu irin kwalla masu zafi da rad'ad'isun wanke fuskarta,kafin a hankali ta saki shashshekar kukan da ya fara fitowa da wani irin sauti.


Ya Allah ya furta a saman labbansa bayan jin ta daga wayar da biyowar kukannata da yake taba can wani guri ke bantacce daga cikin babbar zuciyarsa, RAIHAN ya furta cikin wani irin yanayi me kashe lakar jiki,jin ya kuma rikita ta yasa kawai ta kashe wayar gaba daya tare da kifa kanta tana ci gaba da fitar da hawayenta masu matukar radadi da taba zuciya.




Shima rufe idanunsa ya yi, yana shuru da dogon tunani.




_______________




Kwana biyu biki sai matsowa yake ,shirye shirye a gidan chibado kamar babu mutuwa,ji suke da bikin ko dan sun jima ba su yi auren ba ne,oho.


A bangaren Raihan kuwa gaba daya ta ajiye zuwa aiki,ta rufe wayarta ,ta ki bari kowa ya ganta, Abbie bai tambaye ta komai ba,aunty amarya kuma tana cikin damuwar da ta fi ta Raihan a cewarta.


Suryy kuwa tun da suka hadu da Raihan din zuwan ta washe garin abin da ya faru,bata kara bari ta ganta ba,saboda haka nan ta ji bata yadda da suryyn ba,ko ba haka ba dama can Raihan bata sakin jiki da ko wane mutum,idan har ba ita ta aminta da hakan ba.


A bangaren Labarin da zasu saki a washe gari kamar yadda suka tsara , hakan bata samu ba,tunda mai gaiyya mai aiki bata zo ba.




Tuni shelar auren AHMED WAZIR CHIBADO ta cika gari saboda masu abu da abin sune,kafafen yada labarai na su da na makotansu,tuni suka samu abin yi, sai dai fatan Allah ya Kaimu jibi juma a musha shagali......✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page24 ```






Haɗuwar tasu sai cikin dare ta kasance,haɗuwar takasance kebantacciya kuma ta sirri,daga ur exsellency sai Abba yahya sai kuma dufuty.


Bayan shuru na wasu yan sakanni baka jin komai sai karar fanka da na urar sanyaya guri.


Abba yahya ne ya fara magana bayan gyatta zamansa da ya yi tare da gyaran murya,ur exsellency ka kiramu kuma daga ji kiran yana da matukar muhimmanci dan haka muna saurareka",jinjina kai dufuty yayi cike da nuna gamsuwa akan maganar da Chip accounter Abba yahya ya yi.cikin nutsuwa ur exsellency ya dube su fuskarsa na nuna alamun damuwa,ya ce"abinda yasa na kira ku shine magana za muyi akan maganar takara da kuma waccan maganar da muka tattauna a dazu,gyara zamansa ya yi yana ci gaba da cewa,ina so muyi sulhu a tsakaninmu akan wanda zai ci gaba da rike kujerar gwamnati,abu na farko shine kunsan cewa ina da damar kara neman kujerar nan a karo na biyu,sai dai kuma ba zan yi hakan ba saboda gaba dayanku na karance ku akan son hawa kujerar nan,to gudun kar mu dannewa juna hakki ko kuma hakan ya kawo matsala a tsakaninmu yasa na ce mu zauna domin yin maslaha akan hakan,me kuke gani mu dai dukanmu a bu guda ne duk wanda ya hau bamu da matsala da haka a cikin mu ukunnan,Ni dai bani da matsala sai dai matsalar da nake hango mana wadda zata dakushe tafiyar mu bai wuce wannan babban al'amari dake faruwa a cikin jahar nan tamu ba,me kuke gani akan hakan?ya tambaye su idanunsa akansu yana mai nazarinsu.




Dufuty ne ya fara magana da cewa,tabbas maganarka haka take,amma Ni dai a nawa tunanin da kuma hangen bai kamata ka sauka a kujerar nan ashekarar nan ba tare da kayi tazarce ba,kuma kaine muke da yakinin cewa talakawa zasu kuma zabenka sai dai wannan matsalar da take faruwa wadda ake son jinginata ga tafiyarmu",ko ya kace chip accounter?ya fada yana duban Abba yahya",numfasawa Abba yahya ya yi sannan ya dora da cewa,maganarka haka take dufuty yanzu muna akan cigaban zamanka akan gwamnati ,abinda ya kamata muyi yanzu shine zakulo inda matsalar nan take,muyi kokarin binciko wanda yake aikata wannan mummunan ta asar ko da kuwa acikinmu nan ne,kaga daga nan ne zamu san inda muka dosa",ya karasa maganar yana mai kafe ur exsellency da ido wanda shi kuma sam bai fahimci gugar zanar da Chip accounter yake masa ba,shi dai dufuty yaso ya gane wani abu saboda yanayin kallon da ya fahimci Abba yahya yanayi wa ur exsellency din,bai ɗaice komaiba ya hadiye tunaninsa da mamakin kalaman na Abba yahya a ransa.




Maganarka haka take dan haka za muyi kokarin hakan in sha Allah kuma za muyi nasara", Allah yasa suka fada baki daya.




............




Suryy wai me a ke ciki ne ?


Kin ga fa yau saura kwana biyu daurin auren nan,hankalina ba a kwance yake ba,kina ganin fa yau Even na uku fa ,amma babu wanda wazir ya halatta ,idan na yi wa innawuro magana sai ta ce na yi hakuri wai
da yaya a kayi ya amince da auren ma, gaskiya fa suryy ba zan iya wannan rayuwar da wazir yake so na yi a gidansa ba,a yadda na tsara rayuwar SOYAYYA a gida na ban yi zaton auren zai zo min a haka ba, Kum....Surry ta yi saurin katse ta da cewa kar ki ce ko mai, rubyy kin san dama haka zata faru tunda kika ce kina son Wazir,kuma kar fa ki manta wazir irin mazajen da babu mai gane kan su ne idan ba Macen da suka mutu akan ta ba,ki ƙaddara cewa wazir ba zai taba sonki ba ko ya nuna miki soyayya in dai har da wata a zuciyarsa",suryy kullum haka kike fada amma har yanzu kin kasa gano min abun da ke lullube a zuciyar Wazir,wani kallo sury ta yi mata kana ta yi Murmushin takaici ta ce"wato duk kokarin da nake miki baki gani ba ko,ta yaya zan san wadda ke zuciyar wazir idan har ban bincika ba?




Ganin ran sury ya fara ɓaci ya sa ta sauko,cikin kwantar da murya ta ce" sorry
Ƙawata wlh hankalina ne a tashe, abin da ba za ki gane ba ne ina son Wazir karshen so,son da zan iya yin komai akansa, kuma duk abin da zai yi min zan jure,yanzu dai me ake ciki?




Numfashi suryy ta fesar kana ta dubi rubyy ta ce" idan mun gano yana da wata kafin daurin auren me za ki yi a akan hakan?


Sannan idan ba mu gano ba zaki fasa auren ne ko me kike nufi?


Dan zubawa suryyn ido ta yi kafin ta yatsine fuska ta ce" ,amsar tambayar ki ta biyu shine bazan fasa ba za mu ci gaba da bincike ne har mu gano, kuma ko ina cikin gidan babu abin da za mu fasa kin ga daukar mata ki sai ya fi min sauki tun da ina a matsayin matarsane ba wadda yake shirin aura ba.


Amsarki ta farko kuma,ke ma kanki kin san zan yi ko mai ne akan hakan ko da ya haɗa da kisa ne in dai akan wazir ne ",


Na amsa miki tambayoyinki nima sai ki amsa min nawa,ta faɗa tana gyara zaman gashin da a ka kara mata.




Dage kafadu suryyn ta yi alamun bata da damuwa da hakan,kafin ta gyara zaman ta , ta ce ",rubyy akwai wani boyayyan sirri da nake shirin bankadowa idan har na tabbatar wanda shine zai kawo karshen binciken mu,ina fata na samu kafin jibi,idan kuma ban samu ba to ina tabbatar miki da cewa ba zai dauki lokaci me tsayi ba,amma fa duk na tabbatar da hakan sai kin kwanta a gadon asibiti idan har bai zama sanadin bugawar zuciyar ki ba.




Cikin tashin hankali rubyy ta bude baki zata yi magana,shukrah auta ta yi sallama tare da turo kofar ta shigo,lafiya? ta tambayi shukrah idanun ta na nuna tsananin tashin hankalin da ta shiga lokaci daya,ey innawuro ce ta ce kizo yanzu tana jiranki a kasa,to gani nan", shukrah ta ce",a'a fa aunty rabi ki ta shi muje kin dai san halin innawuro dan cewa ta yi mu taho tare,ina zuwa ta ce",da suryy tana tashi suka fice daga dakin.


Fitar su bai fi da sakanni hamsin ba,wayar suryy ta fara kara alamun kirane ya shigo mata,ta dan jima tana kallon nomber ganin an yi hiding dinta,sai da aka kuma kira kana,ta daga ba tare da ta yi magana ba.


Jin kuma anyi shuru yasa dole ta fara yin magana, hello wake magana?


Ina fata ina magana da suryy kawar rubyy ne ko?


Ey ita ce",ta faɗa cike da kaguwar jin wanda ke kiran.




Na san duk wani bincike da kike a kan Rahim Muhammad nurr akan sanin alakar dake tsakaninsa da ubangidansa wazir,wanda za a daurawa aure ranar juma'a nan,dan haka ina so ki biyo wannan address ɗin kizo inda nake zan taimakeki da bayanan sa,amma akwai sharaɗin aiki tare da Ni,,,daga haka aka yanke wayar...


Zubawa wayar ido ta yi bayan ta yanke,wani tunani ta yi da yasa ta yi saurin miƙewa.
barin gidan ta yi ba tare da rubyy ta sani ba.


Kai tsaye address ɗin ta bi,ko tsoran kar a cutata mata ba tayi ba,zuciyarta tuni ta tafi akan biyan buƙatarta,wanda ba wai tana yi dan kawar Tata ba ne,a'a kawai tana yi ne dan biyan buƙatar zuciyarta.




A bangaren su shugaban jam'iya kuwa,tun da suka ji an kama mutanensu,hankulansu ya tashi,to amma kira daya suka yi a ka sake su ba tare da sunan ko daya daga cikin su ya fito ba,a cewar su wannan matsalar ba ta bangaren tree full Y trues ba ce,dan haka babu tunanin ma ya san da maganar bare ya yi musu kashedi da barazanar da ke matukar razana su,hakan da ya faru ya sa suka dan saurara da bibiyar Rahim din.




Fuskar suryy cike da farin ciki ta fito daga mahadar ta su,duk da cewa ta yi matukar girgiza da samun bayanan kuma dama ta fara zargin hakan,sai dai tunaninta yadda hakan zai yiwu ne ya sa ta kasa gasgatawa take kuma son Dada zurfafa bincike dan samun tabbaci,sai dai kuma a lokaci daya ta samu yayewar bakin cikin saboda hanyar magance matsalar da ta samu a lokaci daya da abokin aikin nata da ko dan yatsan shi bata gani ba,hakan ya yi mata daidai idan ya so sai ta ji da matsalar rubyy,indai burin ta zai cika za ta iya yi masa ko wane irin aiki yake so,da wannan tunanin ta wuce gida ,daniyar sai anjima ta koma gidan bikin.




AUNTY AMARYA.......




Yanzun ko yaya ta ga wayar ta na haske sai zuciyarta ta buga,zubawa wayar ido ta yi tana tunanin ta dauka ko kar ta dauka,gashi kwana biyu sam bata samun wayar Dr Sabo shi yasa abin ya haɗe ya yi mata yawa,zuciyarta na bugu ta daure ta daga wayar.


Cikin wata irin murya da kullum sai ta ji an sauya ta,a ka ce".


Ki bawa yaro na auren 'yarki,in dai kuna son taci gaba da rayuwa,kuma cikin kwana uku tak nake bukatar hakan,shima saboda na bawa zuciya da kwakwalwarki dama ne,idan kuma ba haka ba to wlh sai na kashe RAIHAN.....ƙit aka kashe wayar.




Wata irin zufa ce ta tsananin tashin hankali ta shiga keto mata,innalillahi bakin ta ke iya furtawa kawai,cikin kankanin lokaci idanunta suka kada kanta ya shiga wani irin sarawa kamar ana buga adda,jikinta kuwa babu inda baya yin rawa,tunaninta neman gushewa yake,yadda ta jike da gumi kaika ce shaya ta shiga,wani kiran ne ya sake shigo mata,wata irin zabura ta yi tana duban wayar da dukkan idanunta da zuciyarta da ke neman bugawa,dishi dishin da take gani yasa ta kasa fahimtar wanda ya kuma yin kiran,hannunta na rawa ta danna tare da rintse idanunta,tana shirin jin abin da zasu kuma bukata.




Amma kuma sai ta ji sabanin Muryar da ta tsammaci ji ,Dr Sabo ta faɗa cikin rawar murya,kawai sai ta saka wani irin kuka me ban tausayi kamar zata hadiye zuciyarta,cikin kukan take cewa Dr Sabo ina cikin tashin hankali za su raba Ni da farinciki na,wlh ina son RAIHAN ba zan iya rabuwa da ita ba,idan har kaddarata ita ce ta rabuwa da Raihan,ina rokon Allah ya canja min ita ko Ni na mutu ita ta rayu,amma ba zan iya jurewa ba,ya isa haka ramla yanzu me ya faru?


Da kyar ta nutsu ta yi masa bayanin abinda ke faruwa ba ta boye masa komai ba,tun da shine abokin cin mushenta.


Ya jima yana shuru dan har ta yi zaton ya sauka daga kan layi sai kuma ta ji ya ce",amarya ki nutsu in sha Allah babu abin da zai faru akwai mafita ki kwantar da hankalinki,bana so ki tashi hankalinki har Raihan ta san abin da ke faruwa ta dalilin damuwarki,ki zuba idon ganina gobe in sha Allah,dan abinda yasa na kira ki kenan,sosai ya kwantar mata da hankali har sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan su kayi sallama,ta kuma kashe wayar ta gaba daya.




.............




Abba yahya Sai da ya gama cin abinci ya nutsu tukunna , sannan ya fuskanci inna maimuna,gyara zamanta ta yi itama tana fuskantarsa saboda ta fahimci akwai magana a bakinsa.


Kin san kuwa yau me ya faru?ya tambayeta da alamar shima abin yana taba shi tare da saka shi cikin mamaki,girgiza kai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba,a nan ya zaiyane mata duk tattaunawar da su kayi da ur exsellency,kai me ka fahimta a nan? Inna maimuna ta tambayeshi, murmushi ya yi tare da cewa,da muka nuna cewa yaci gaba da jagorantar jahar mu,bai yi musu ba, sannan bai nuna min komai akan gugar zanar da nayi mashi ba,Ni dai na fassara hakan da tsananin kwarewa a makirci,zan ci gaba da bibiyarsa har sai na gano duk wani shirinsa da makircinsa akan dan uwana da kuma jahata",na baka goyan baya a kan hakan..




RAIHAN......




Sai wajen karfe goma na daren ta kunna wayarta,dai dai lokacin da take zama kusa da Abbie,jikin ta duk a sanyaye,fitowar ta ma daga dakin bai fi sau biyu ba tunda abin ya faru,yanzun ma daurewa ta yi saboda tasan auntyyn daurewa kawai take yi bata kula ta ba,sai dai bata san cewa itama auntyyn damuwa ce ke neman kwantar da ita ba.




Duban ta Abbie ya yi cikin kulawa da wani yanayi na tausayi da ke shimfide saman fuskarsa,ya ce" Rahim ya dai ko har yanzu jikin ne? Murmushi ta yi wanda ya nuna sanyinta a fili,kana ta ce"Abbie jikina ne kawai a mace",ai kai naga baka gajiya da zaman daki kamar wata mace,kai dan irin abokan nan ma duk baka da su,dole ne ka dinga kadaici,numfashi ta dan fesar a ranta tana cewa anzo gun dama irin wannan maganganun da Abbie yake yawan yi ne yasa take kauracewa zama da su a falon,bata samu damar cewa ko mai ba wayarta ta shiga ringing wanda hakan ya yi mata dad'i,tsam ta mike ta nufi hanyar dakinta tare da kokarin duba fuskar wayar dan ganin me kiran.




Zuba wa fuskar wayar ido ta yi,kafin a hankali kamar me ciwon hannu tasa hannu ta danna ok,shuru na kusan minti ɗaya ,kafin ya aje miskilancin nashi ya furzar da wani dan huci, sannan cikin kamammiyar Muryar sa me cike da tarin nutsuwa ya ce", lafiyar ki fa?runtse idanun ta ta yi cike da takaicin sa, wannan wace irin tambaya ce",me yasa kika koyi wannan abun?ya kuma jeho mata tambayar da sam bata fuskance ta ba.


Da kyar ta bude baki ta ce"me ke nan?


Shuru ana miki magana",ashe ba dadi ta faɗa kasa kasa,ƙit ta ji ya kashe wayar,tabe baki ta yi tana hararar wayar kamar ita ce tayi mata laifin.




_______________




Wai Rahim ba zai fito mu tafi daurin auren ba ne?Abbie da ya fito a shirye sai kamshi yake ya yi kyau sosai ya fada yana duba a gogon da ke daure a hannun sa, RAHIM ba shi da lafiya auntyy amarya ta faɗa tana basarwa da mika mishi key din mota,dan jim ya yi kafin ya dubi Hamma idi dake shigowa ya ce" ,mu wuce kawai sai mun dawo,hamma idi ya ce",ina Rahim din? Baya jin dadi ba zai samu zuwa ba",zaiyi magana Abbie ya tare shi da cewa muje muna makara,yaya da Baffa na jiranmu,dole Hamma idi ya hadiye abinda zai faɗa ya juya suka fita aunty amarya na yi musu Allah ya kiyaye.


Ajiyar zuciya ta sauke tana mai duban hanyar dakin RAIHAN ɗin,kafin ta nufi dakin.


A kwance ta same ta, da alama dai ko tashi ba ta yi ba,tun sallaar asuba,karasawa ta yi ta shiga taba ta, Raihan lafiya dai har yanzu baki ta shi ba?ga shi sallar walha ba,,a hankali ta bude idanunta da su ka yi mata nauyi kamar an danne su da bulo,bata ce komai ba sai maida kanta da ta yi ta kuma rufewa,taba jikinta aunty amarya ta yi sai ta ji alamun zazzaɓi,ajiyar zuciyar damuwa ta dan sauke kafin ta juya ta fita daga dakin.




Sai da aka gabatar da sallar juma a,kafin a fara daure dauren auren da ake da su ranar,sai da aka daura aure uku kafin a zo kansu,mamaki ne ya rufe wazir lokacin da yaga harda baffa a daurin auren,tunda yasan yana fama da ciwon kafa ba ko ina yake zuwa ba,bai gama da wannan mamakin ba yaga baba buzu duk da cewa bai sansu ba amma kallo daya zakayi musu kasan cewa jinin Raihan ne,daga shi har kawun Raihan ɗin,sai wani mutum da shima yake jerin su,wanda bai san fuskarsa ba,amma tunanin shi ya bashi a cikin abokan Abbu yake. kawar da tunaninshi ya yi da komawa kan tunanin abinda yake cin ransa,babu yadda za ayi ka gane wani abu akan fuskar sa farinciki ko sabanin haka.




Daurin aurensa da rabi Mustafa chibaɗo aka fara gabatarwa,kafin ya ji wani abin da yasa ya kasa boye razanarsa da mamakin sa,duk da cewa tsananin jan ajinsa da kamewarsa ya biye kaso dari na razanar da mamakinnasa,da sauri ya dubi Abbie dake gefansa,sai dai kuma ya kasa cewa komai sai kawai ya maida kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login