Showing 99001 words to 102000 words out of 189984 words
Chapter 34 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
mallakinta tayi juyi tare da yin shewa sannan ta fara neman lambar Surry dan ta fesa mata labari.
WAZEER yana tsaye a jikin window office dinsa,idanuwansa ba ko ina suke kallo ba sai kyakkyawan titin da zai kawoka har babban building ɗin nasu na CHIBADO FM,motocine kawai ke kaikawo cikin tsari da bin dokar gwamnaty, sam ba zaka iya tantance halin da zuciyarshi ke ciki ba,dan babu wata alama da ya bari da zai nuna maka ainahinsa.
A hankali yake kokarin janye idanunshi da gangar jikinshi daga jikin dogon ginin office ɗinnashi,kamar ance ya kuma duban wajen sai kuwa yaci karo da Raihan dake fitowa daga motar Hamma Idris,cikin yanayin dake nuna ɓacin rai da damuwa,yana kallo ko sallama bata yiwa Hamma Idris ɗin ba tayi gaba cikin ɗan hanzarin dake nuna akwai abu me muhimmanci dake gabanta.
Furzar da wani zazzafan huci ya yi tare da barin gurin,ayyanawa yake a ransa yasan za ayi haka,wuyarta ace bata ji abinda ya faru ba,amma yasan halin kayansa muddin ta samu labari to tabbas sai ta shigo building ɗin kamar dai yadda ya zata.
RAIHAN dai babu wanda ta kula kai tsaye office ɗinta ta nufa.
Turus ta tsaya tana kallon yadda a kayi kaca_kaca da wurin,an janyo durowowi an wargaza mata duk wasu takardu da suke shirye.
Waye da wannan aikin?
Ta tambayi kanta cike da mamaki,
Dan Murmushi ta saki tana cewa dama nasan za a zo wannan gurin",
A hankali ta karasa jikin window dake saitin kofa ta cusa hannunta jikin labulen ta can sama yadda ba kowa zai kawo da wani abu a gurinba,wani dan karamin abu me kamar kwallo ta dauko,juyashi ta shiga yi tana kallonsa fuskarta ɗauke da Murmushi,bata yi wata wata ba ta juyya ta fita daga office ɗin.
Lifter tabi ta ta karasa office ɗin AHMED WAZEER CHIBAƊO.
______
Suryy na tare da boyayyyan mutuminta kiran ruby ya shigo wayarta,duban ɓoyayyiyar fuskarsa ta yi tana masa nuni da fuskar wayarta.nuni yayi mata da ta daga ta saka a amsa kuwa.
Yadda ya umarceta da yi haka tayi,saiga Muryar ruby ta fito raɗam cikin yanayin dake nuna komai yana tafiya daidai,tace",Surry aikinki na kyau yau dai gani cikin office ɗin CHIBAƊO FM a matsayina na me karbar korafin sirri akan jami'an tsaro ya kika ga wannan lamari?dariya suryy ta yi cike da nata jindadin na ganin cewa duk yadda suka shirya ko mai na tafiya dai-dai,gyara zamanta tayi saman kujerar da take kai sannan ta ce", ruby ki nutsu kiyi abinda ya kai ki karki yi shirmen da zaisa a ganoki dan naga alamun wannan rawar jikin da kike ya soma yin yawa ehem kinutsu ina kuma jaddada miki,yanzu dai ki bani lokaci na tsara abu na gaba zuwa anjima zan kira ki",ruby ta Dan ja numfashi kana tace haba suryy ya kike min kamar ba danni kike komaiba ya za ai nayi abinda WAZEER zai dago jirgina karfa ki manta idan hakan ta faru ba kece a ruwa ba nice a ruwa tsundum kusa da kada,dan haka ki daina min wannan kashedin ina jiran kiranki anjiman",tana gama fadar hakan ta kashe wayarta tana jan tsakin rainin da suryy ta yi mata.
Dariya suryy ta fashe da ita tana cewa yarinya fadi ki kara fada tabbas kece a ruwa,dan ma baki san irin aiyukan da zaki mana ba ke nan.
Menene netx plan ɗinmu oga?gashi dai nasa rubyy ta shiga CHIBAƊO FM da sunan aiki ko meye shirinka akan haka?
Wani shegen Murmushin da ba a gani ya yi , sannan cikin Muryarshi da kullum take sauyawa baka taba cewa ga Muryarshi guda ba duk yadda ka jima da shi kuma kake da shi,ya ce suryy aikinki ya yi kyau,ke dai ba burinki wazer ya rasa su duka biyun ba kema kuma daga nan sai ki kutsa cikin rayuwarsa ba? Jin jina kai tayi cike da bashi tabbaci akan tambayar da yayi mata,woldon ya fada yana duba fuskar wayarshi sannan ya dago ya dubi suryy ya ci gaba da cewa,asirin Raihan zai tonu ne ta wajen Ruby", zuba mishi ido suryy ta yi cike da son ƙarin bayani, fahimtar hakan da ya yi ne yasa shi jinjina kanshi yana mai ci gaba da cewa duniya zata san cewa RAHIM ba namiji ba ne macece,kuma ba kowa ne zai fidda wannan labarin ba sai rubyy matar WAZEER,za musata ta fidda labarin ta wata sigar daban yadda za mu jawo hankalin mutane kan Raihan wata ƙil ma hakan ya jawo mata bakin jini domin idan aka hau teburin malamai lallai sun tafka kuskure kuma malamai zasu kalubalance su akan wannan abu da su kayi".
Cikin zakuwa suryy ta ce", to meye amfanin hakan agaremu?
Dariya yayi yana mai jingina bayanshi da kujerar da yake kai zaune, sannan ya ce", sury me yasa kanki baya ja ne a wasu lokutan? Kaima kace a wasu lokutan dan haka bani haske",
Suryy duk duniya waye bare da yasan sirrin Raihan da mahaifiyarta? WAZEER ne", ta bashi amsa kai tsaye kuma cike da zakuwa,yauwa idan har wannan labarin ya fita kuma daga jaridar CHIBADO daily trues me kike ganin zai faru? Wa Raihan da mahaifiyarta zasu zarga? Idan mahaifiyar Raihan ta tsani WAZEER me kike gani zai faru?bare kuma idan Raihan da kanta tayiwa WAZEER tsana mafi muni ita da mahaifiyarta to ya kike ganin wasan zai kasance?
Bari na tuna miki daya daga cikin halayyar da Raihan tafi tsana tsana mafi muni,cin amana da yaudara, sannan abinda tafi ƙauna ƙauna mafi ƙololuwar daraja itace mahaifiyarta duk abinda take yi tana yi ne don farin cikin mahaifiyarta bawai dan tana tsoron mutuwa ba,to tayaya kike ganin tsanar zata kasance saboda ta kasance ninki biyu",?
Baki sake suryy take kallon fuskar da bata ganin ainahinta,wani mutum guda da take ganin cewa makircinsa da sharrinsa ya fi na mata dari,da ta rasa abin cewa kawai sai ta kama hannunsa ta ƙanƙamr cike da wani irin farin ciki kai kace ta samu wazer dinne ta gama.
Sai da ya bata dama ta gama fariincikin sannan ya magani da cewa,yanzu kin fahimci ribar tamu?na fahimta oga to amma idan mun kawar da Raihan daga rayuwar WAZEER to ita kuma Ruby fa?tafa hannayensa ya yi cike da jin dadin tambayar da tayi masa yace", wannan tambayar nake jira domin nafison duk abinda zan fada ya zamana cewa an tambayeni hakan na kara kawo min dabaru cikin ko wane shiri da zan gabatar.
Cike da burgewa Surry take kallonshi saboda yanzu ji take haɗuwa dashi ya zame mata babbar riba,yayi mata amfani yayi mata rana ranar da baza ta taba mantawa da ita ba,fahimtar abinda take saƙawa ya sa shi ci gaba da cewa,"WAZEER ya iya ɓoye abinda ke zuciyarshi,dan haka har yanzu bamu da tabbacin cewa yana son Raihan ko baya sonta,abinda dai muka sani shine ya ɗauketa da matuƙar muhimmanci ta wani ɓangaren kallon ahlinsa yake mata, sannan bincike na ya tabbatar min da cewa WAZEER yayiwa amarya mahaifiyar Raihan alƙawari akan cewa ba zai taba sanar da kowa wannan sirrin ba,ya ɗau amanar Raihan da hannu biyu,shin ya kika ga abun zai kasance idan yasan cewa matarsa rabi itace ta fitar da wannan sirrin ? Dama bata cikin ransa fit zata kuma fita zaiyi mata tsana me muni akan yanzu, wazer yana da taurin kai sannan mutum ne me tsayawa akan magana guda idan yace ya rabu da rabi har abada to har abadan yake nufi.
Tafi sury ta kuma yi masa cike da gamsuwa da duk abinda ya zana,oga baka ganin cewa idan ya gano gaskiya zai iya zuwa ya warwarewa Raihan da mahaifiyarta ? Idan suka yadda fa kaga dai Raihan ta dawo ke nan", tabe baki ya yi kana yace", ba zamu bari hakan ta faru ba,zamu bi duk wasu hanyoyi na ganin cewa shiima ya samu Raihan da wani laifi wanda zai hana shi zuwa garesu dan warware musu gaskiya, sannan ba alokaci daya za muyi wannan ba,idan labarin ya fita sai mun tabbatar da cewa komai ya cakuɗe kamar yadda muke so sannan mu tonawa rabi asiri ta yadda wazer zai kamata da laifin redhand",.
Ok na gane oga zanyi komai cikin takatsantsan har mu cimma gaci,amma inaga wannan aikin kamar nawane Ni kadai shin meye kudurinka akan Raihan? Wani duba ya yi mata kafin ya nuna mata yatsa ya ce",ki tsaya matsayinki kar ki ƙara min wannan tambayar wannan sirrina ne ", ganin yadda yayi lokaci daya sai hakan ya ɗan bawa suryy tsoro babu shiri ta mika wuya tare da bada hakuri.......
RAIHAN tana kokarin shiga office ɗin tana ci gaba da gwada wayar asp Haidar,ta rasa me yasa yau kusan kwana shida ke nan tana gwada kiranshi amma ta kasa samunsa,sai yanzu hankalinta ya fara tashi saboda tun ranar da ta kira shi suka tattauna ya tabbatar mata da cewa yana da wasu manyan bayanai akan mutanen da bata taba zato ko tsammata ba,shi yasa ta dauki video ta bashi akan ya haɗa da bayanan wajensa idan lokaci yayi sai su fitar baki ɗaya,ta tuna tun ranar basu kara yin waya ba kuma ko a chat bata ganinsa.
Cikin wannan tunanin ta shiga office din,zuba mata ido wazer ya yi ganin kamar bata cikin hankalinta,sauke wayar tayi tare da aje numfashin damuwa idanunwanta cike da kwallar tunanin da yake zuwa mata akan Haidar ta ce",Hamma wazeer dan Allah kira wayar Haidar ko kai zaka.iya samunsa",bai ce mata komai ba ya dauki waya ya shiga neman Haidar ɗin sai dai shima bai samu ba yadda ake ce mata akashe take shima haka aka gaya masa.
Wayyo Allah Hamma shima sun kashe shi kuma sun boye shi,kamar yadda suka yiwa halima", ganin yadda duk ta birkice yasa shi tashi cikin natsuwa ya ƙaraso inda take tsaye tana yarfa hannu idanu cike da ƙwallah,gaya min me yake faruwa? Me kike boye min?.
Cikin kamekame ta sanar dashi maganar videon da yadda akayi ta bawa Haidar ɗin.zuba mata ido ya yi fuskarnan kamar hadarin gabas,cikin fitar maganar shi daidai ya kira sunanta", Raihan",cike da tsoro take kallon fuskarshi dan kuwa tasan tayi babban laifi,kin iya boye min irin wannan abun dama? Yarfa hannu ta ci gaba da yi kana cikin tsoro ta ce", Ni tsoro nake ji kar suyi maka wani abu",gashi sunyiwa Haidar ya fada yana watsa mata kallonnan nasa me firgita me laifi,kuka tafashe dashi me ciwo wanda dan dole yasa shi sassauta kallon tuhumar da yake mata,ganin taƙi yin shiru yasa shi takawa daf da ita ya kamo hannunta,baiyi kasa a gwiwa ba a hankali ya janyota cikin faffaɗan kirjinsa domin baki ba zai wadatar dashi wajen rashin ta ba............✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page35 ```
Abba yahya bai sanar da inna maimuna abinda ke faruwa ba,wanka ya shiga yayi ya saka doguwar jallabiya sannan ya fito falon.
Samun inna maimuna yayi zaune hannunta rike da waya fuskarta cike da damuwa kamarma dai kuka taci saboda yadda idanunta suka yi jawur dasu kamar an bada musu barkonon tsohuwa,zama yayi gefanta yana yi mata duban tambaya,ganin yadda ta bawa banza ajiyarshi yasa shi magantuwa da cewa maimuna meke damunki ne haka?cikin fusatar da bai taba ganinta da shi ba ta ce", haba Abban Bashir wane irin uba kake so ka zama wanda bai damu da rayuwar iyalanshi ba,yau kwana na uku ina neman wayar Bashir amma bana samu kuma kai banga alamun damuwar haka a tare da kai ba,karfa ka manta kaine kasa yaron nan yaki dawowa mahaifarsa akan kana son hukunta shi akan kuskuren da yayi wanda bai wuce kan kowa ba,"au kuskure ma kike kiran wannan bakar halaiyyar tasa dashi,har kin manta halayyar dannaki ko? Zata yi magana ya dakatar da ita.
Dakata maimuna wannan fadan naki na rashin daliline,me yasa lokacin da na dauki matakin kika bada goyan baya,ke yanzu ba abun kunyarmu ba ne ace yaron nan ya tafi tare da yan uwansa kowa ya dawo da abinda aka tura shi nema banda shi,me yasa ya biyewa shashashan abokai har ya fadi jarrabawa idan bance ya zauna ya maimaita ba ya kike so nayi?
Sassauta murya ta yi kana ta ce", nasan Bashir yayi laifi amma da mun sani ba mu boyewa Nura ba,kaga fa daga karshe ce mana ya yi yayi aure kuma nasan cewa wannan yarinyar da ya Turo mana baza ta kasance me tarbiya ba,kuma be kamata kayi fushin zuciya dashi irin haka ba,duk lalacewar naka ai naka ne."yanzu me kike so nayi? Idan banyi masa haka ba ya kike so nayi ?wai ko anya maimuna kinsan irin manyan taasar da danƙi yake yi a can? Shiru tayi ranta sam babu dad'i,dan nisawa tayi tare da cewa abban Bashir kayi hakuri dani amma duk laifin Bashir Ni uwa ce babu ta yadda zanyi na cireshi a raina kamar yadda kai kayi, sannan ina neman alfarma dan Allah ka barni naje na dubo lafiyarsa a karo na farko dai kayi min wannan alfarma",shi kadai gareni Banason wani abu ya sameshi",
Tashi Abba yahya yayi ba tare da yace mata komai ba,binsa ta yi da kallo ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a maleshiya.
_____________
Dawowarsa ke nan daga campanin auduga na Raihan wanda karkashin kulawarsa yake hannun babban dan ur exsellency wato Yusuf,sosai yaji dadin halartar Company saboda lissafin da aka fitar wanda aka ware ribar da aka samu a ka ware kudin albashin ma aikata da na zakka da dai sauran duk abinda ya kamata comfani ta yi a shekara,dadin da Abbie ya ji shine irin ribar da aka samu a wannan shekarar kamar wanda ake zubin dashinta kullum.
Kai tsaye sashen Baffansa ya nufa a nan ya samu Abba yahya,bayan sun gaisa Baffa ya dubi Abbie ya ce", Muhammad da alama yau kana cikin farin ciki bani nasha",dariya Abba ya yi yana cewa haba Baffa kaima kasan babu wani abu da zai samu Nura wala na alkhairi ko akasinsa da zai sameshi bai sanar da mu ba ko ba haka ba Nura? Ya fada fuskarshi cike da annurin da tasamu bayan ganin farincikin dan uwannashi.
Dariya Abbie ya yi ya ce, wannan haka yake yaya daga nan ya gyara zamansa ya sanar dasu komai harma da na sauran companies din dan wannan shine na karshe a fidda lissafin,masha Allah alhamdulillah suke ta maimaitawa bayan jin wannan daddaɗan labarin,fuska cike da walwala zuciya fari kal suka gabatar da addu'a daga nan suka fita sallar la'asar.
Sosai Raihan ta sawa ranta lallai sai ta gano abunda ke boye dan kuwa ɓatan Haidar ba karamin girgizata yayi ba,tuni suka saka sanarwar ɓatansa a kafafen sadarwarsu,kanka ce wannan gari ya dau dumi,tuni jam'i an tsaro suka fara aikinsu wasu dan Allah suke yi wasu na musu barazana wasu kuma an siye su da kudi,kai wasu ma aje aikin sukeyi dan ganinsu da su aikata ba daidai ba Gara su hakura da aikin.
Ur exsellency da kansa ya nemi yin hira a gidan tv CHIBADO kuma yace yana so a nuna live kai tsaye ga masu kallo,cikin kankanin lokaci a ka shirya zaman su abu Huraira tuni suka bada sanarwa.raihan tare da wazeer su zasu jagoranci shirin.
Da misalin ƙarfe biyar aka fara haska tattaunawar.
RAIHAN cikin shigarta ta basaja wadda duk kokkofinka baza ka iya gano sirrin matantakanta ba,cikin gyara zama da yin gyaran murya irin dai yadda aka san yawancin maza nayi,ta ce", ur exsellency muna yi maka Barka da zuwa a madadin ɗaukacin al'ummar dake cikin wannan gida da kuma masu kallonmu a daidai wannan lokaci,amsawa ya yi cikin daddakonsa,kana Raihan ta ɗora da cewa ur exsellency za mu so jin abinda ke bakinka damu da masu kallo akan abubuwan da suke faruwa a cikin jahar nan",
Dan gyara zama ya yi fuskarshi na nuna alhinin abinda yake faruwa ya ce", Assalamu alaikum jama'ata ,hakika na nemi magana ne domin kawai na baku hakuri akan dukkan abinda ke faruwa daku da mu baki daya,duk da cewa nasan hakan ba zai rage muku ko kadan daga cikin zaluncin da ake yi muku ba,amma duk da haka dole na baku hakuri da kuma sanar da ku cewa lallai za izinin Allah za mu kawo karshen rikicin da ke faruwa zamu yi kokari da jikinmu da aljiihunmu muga cewa mun samar da zaman lafiya a jiharmu ,hakika muna jin raɗadi akan abinda ke samun jama armu,to amma kuyi hakuri domin duk abinda kuka ga ya yanke sai da izinin Allah,dan haka ina rokon ku da ku ci gaba da addu'a kamar yadda muma muka sa ake yi babu dare babu rana akan Allah ya tona mana asirin duk wanda suke kawo fitina da kashe rayukanmu a banza asiri,in sha Allah Allah zai tona musu asiri, na gode", muma muna godiya ur exsellency.
A hankali wazer ya maida dubansa kan ur exsellency,kana cikin mafamarshin nan me janyo hankalin yan mata kanshi,ya ce",ur exsellency muna godiya wannan karramawa,juya kyakkyawar fuskarshi kan abun haskawa ya yi yana ci gaba da cewa to masu sauraron mu, kun dai ji ta bakin ur exsellency saura kuma zamu saurari ra ayoyinku wanda aka baku lokacin yin tambaya ga ur exsellency za ku iya Turo sakonninku ta wannan lambar 0805443.....sai kuma kira ta wannan lambar kamar haka 0912626.......muna sauraronku......
RAIHAN dai ganin wannan yanga ta wazeer abun ya bata bata rai dan ita kadai take harare harare tare da dan ƙunkuni ta yadda babu wanda zai fahimta.sai dai shi ogannata tsaf yake ganinta ta cikin glasses din da ya kara kawata kyakkyawar fuskarshi.
Cikin sauri Raihan ta dauki kiran da ya fara shigowa ,hello salamu alaikum,amsawa ta yi ta ɗora da tambayar wanda ke magana, sunana .....ya bata amsa daga nan ya yiwa ur exsellency Barka da zuwa da fatan komawa gida lafiya.
Ajiyewa yayi daga nan ta amsa sakon message,wanda yake cewa Salam sunana Hashim Yusuf,tambaya ta anan shin ur exsellency ya tabbatar da cewa babu sa hannun gwamnaty cikin wannan al'amari dake faruwa da talakawa?.
Murmushi ur exsellency ya yi kana ya ce ", bani da sani akan gaibu Allah shine yasan gaibu dan haka ba zan baka tabbaci akan abinda Nima nake