Showing 156001 words to 159000 words out of 189984 words

Chapter 53 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15630

ba ya yi mishi bayani,take shi kuma salim ya kira wazer ya sanar dashi,shi kam dama wazer kullum a shirye yake dan haka cikin nutsuwa ya ce", dasu su tafi amma suyi komai da takatsantsan,idan suka ga zata ganosu su rabu da ita tunda duk wasu bayanai da kiran da suke shiga wayarta da wayar da take yi duk yana dasu ta hanyar wannan madaukar da kuma canjin wayar da su kayi mata wanda har yanzu bata Ankara ba.




Cikin mintuna goma suka isa gidansu Surry,tana shiga suka figi nafef din da su kara tabbatar mata da cewa su din yanjagaliya ne.




Take wani tunani ya darsu a zuciyar Surry,tunanin da ta yi ne yasa ta yi saurin daukar wayarta ta har zata ogan sai kuma ta fasa,tana gani tunda haduwa zasu yi sa yi maganar ta yadda zai fahimceta,tabbas wadannan matasan zasu taimaka mata gurin sace Raihan", murya saki tana jin wani sanyi a ranta na samun mafita.




Aunty Amarya........




Karka bari ya bace mana pls kaji", in sha Allah bazai nace mana ba,cewar me nafef da yake bin bayan ogan Surry cikin takatsantsan.




Hajiya goggo.........




Suna shiga falon Hajiya goggo ta dubi Raihan tana cewa ina hajiyarki ta agadex", dan hararar kofar HAJIYAR AGADEX din ta yi sannan ta ce", tana bacci har da wani cewa kar a tasheta",zama Hajiya goggo ta yi sannan ta zaunar da Raihan ɗin,cikin nustuwa ta ce", Raihan wani taimako zaki min", taimako kuma? Raihan ta faɗa gabanta na faduwa", ey taimako Hajiya ta faɗa tana zaro takardun da suke nade a kugunta tana warware su a lokaci ɗaya", biro ta ciro a tsakiyar takardun sannan ta mikawa RAIHAN tana cewa wajen da aka bukaci sign kawai zaki dinga bi kina yi min,kin sanni ba wani abu na sani a harkar boko nan ba", take tunanin Raihan ya tsaya duk da cewa bata san nufin wazer akan tasawa duk wadda zata bata takardu ido ba amma tabbas tana hasashen akwai wani abu akasa", karba ta yi tana tuna kashedin wazer akan kar tayi gaddama kuma kar tabi kokkofi akan takardun bare takai ga karanta abinda yake ciki", jinjina kai ta yi kawai ta shiga sa mata hannun,bata dago ba har sai da ta gama tare da mikawa Hajiya goggo takardun", murmushi Hajiya goggo ta yi tana cewa na gode jikallena Allah ya yiwa rayuwar aurenku albarka, Amin Raihan ta faɗa tana bin Hajiya goggo da kallo har ta fita daga cikin falon.




Da sauri ta dauki wayar da wazer ya kira tana karawa a kunne", wacece ita? Abinda ya fara tambaya ke nan" jin a kagauce yake yasa itama ta yi saurin bashi amsa da cewa hajiya goggo ce", runtse idanunshi ya yi kafin ya taune labbanshi da suka bushe sannan dakyar ya ce", da ita maza tashi ki bita sashenta kiga dawa zasu hadu amma kar ki bari ta ganki,amma ina so ki tabbatar min daga ainahin wadda takardun nan suka fito", shike nan ta faɗa tana tashi a lokaci daya jikinta a matukar sanyaye.




Kai tsaye sashen hajiya goggo ta nufa tana gab da karasawa ta hango inna maimuna ta fito daga bayan window falon Aunty Amarya cikin sauri tana yi tana waige da alama bata so wani ya ganta,ganin haka yasa RAIHAN tayi saurin boyewa a bayan bishiyar dabinon dake girke a wajen,bata fito ba har sai da taga inna maimuna ta shiga falon Hajiya goggo,sannan ta fito cikin sanda da yan waige_waige a hankali ta bude falon ta shiga cikin tsananin takatsantsan,babu kowa a falon hakan ya bata damar saurin karasawa corridorn da zai sadaka da dakin Hajiya goggon,rabewa ta yi a jikin kofar tare da kafa kunnenta,bata jin komai bata ganin komai hakan yasa ta canja shawara dan haka cikin sauri ta fita daga falon ta koma ta can bayan dakin daidai jikin window ta tsaya tare da dan zuge glass din,zuciyarta na gudu ta daure ta dan yaye contain din yadda zata iya daukar fuskokinsu dakyau kamar yadda wazer ya umarceta.




A bangaren inna maimuna kuwa tana shiga falon bata ga Hajiya goggo ba sai kawai ta wuce bedroom dinta,anan ta sameta ta fito daga bathroom,kallonta hajiya goggo ta yi a dan mamakance tana share ruwan fuskarta da alama alwala ta ɗauro,maimuna kece a tsakiyar ranarnan haka? Goggo ta faɗa tana zama a kan kujerar dakin,dan muskutawa inna maimuna ta yi sannan cikin fara a ta ce", ey wlh zuwa nayi na karbi takardun saboda da sassafe zan fita dasu na kaiwa yayana na can kusurwa,haka ne", Hajiya goggo ta faɗa tana janyo takardun sannan ta ɗora da cewa amma maimuna ban yadda da hujjarki ta ƙin bawa Raihan takardunnan ta sa hannu ba zanso kiyi min bayanin da zan gamsu,sannan ki fada min su din takardun na meye? Kuma daga ina suka fito? Da sauri inna maimuna ta karɓe takardun tana cewa Hajiya zanyi miki bayanin komai idan na kai takardun na dawo amma fa karki tada hankalinki dan ba wani abu ba ne",daga haka ta mike da takardun a hannunta ta fito daga dakin ta bar Hajiya goggo sake da baki.




Sai kuma ta dan tabe baki tana cewa haka kawai dan wani sanabe ki kawo min shirgin takardu waike kunya kike ji kicewa Raihan baki iya sign ba,dan Allah na bata tunda tasan Ni banyi boko ba kuma Ni kakarta ce akwai wasa tsakaninmu",ta karasa fada da kuma mele baki tana jin abun wani banbarakwai kai sai yanzu take ji kamar tayi sakarci wai surukarta ta aike ta duk yadda take da jajircewa akan surukanta kai duk yadda akai da akwai abinda maimuna take boyewa dan yaran yanzu ba abin yarda ba ne.




*RAIHAN* ......




Tana gama daukar komai ta janye jikinta saboda ganin inna maimuna ta fito,ba ta fito ba saida ta tabbatar da cewa inna maimuna ta kai ga sashenta,sannan ta yi saurin komawa bangarensu,tana shiga daki ta turawa wazer video dan ita kanta ta kagu tasan abinda yake faruwa.




Yana kashingide amma baisan sanda ya tashi zaune ba,a nutse ya gama kallon video kafin ya saki wani kasaitaccen murmushin gefen baki, send ya yiwa Yusuf,shima yusuf din yana gani ya kira shi ,wazer yana dagawa Yusuf ya ce", wazer na sarawa zurfin tunaninka anya kuwa kai din ba aljan bane? Murmushin ya kuma saki yana sauraren Yusuf da ya cigaba da cewa,kaga shegiyar mata wato tayi hasashen wani zai iya bibiyarta ta hanyar Raihan ɗin shi yasa ta canja tunani ta kaiwa Hajiya goggo takardun kaga koda zata kasance akwai me bibiyarta ke nan Hajiya goggo ce zata zama suspect dinsa", wannan shine abinda nayi tunani na kasa yadda cewa Hajiya goggo ce", cewar wazer kenan ", ajiyar zuciya Yusuf yayi sanan ya ce", amma kaga nifa harna yadda wallahi", cikin dan gajiyawa da maganar wazer ya ce",ba zai yuwuba Yusuf sam ba zai yiwu ba,da zai iya cutar uwarsa dan uwa zai iya cutar dan uwansa komai shakuwar dake tsakaninsu,amma banda uwan Yusuf soyayyar da uwa takewa danta dabance son da uwa takewa danta dan bayayi mata kwatankwacinsa,dan haka ka cire wannan aranka Hajiya goggo ba zata taba cutarwa Abbie ba har fa da kokarin kisa tun anan lissafin zai canja indai har ita ce ta haifeshi ko da kuwa shidin yakasance ba mutumin kirki ba ne.




Tabbas maganarka dutse wazer wallahi har ka sa na kuma jin tsananin son Hajiyata lallai iyayenmu abin alfaharinmu ne Allah Ubangiji ya kara musu lafiya ya kuma saka musu da gidan aljanna Amin ya rabbil alamin 🙏", wazer ya fada yana ɗorawa da cewa Yusuf zamu hadu mu tattauna yanzu ina jiran sauran bayanan da su Salim zasu kawo game da dayan dan ta addan shi kuma kowa za mu gani? Allahu a'alamu cewar Yusuf daga nan suka yi sallama kowa ransa cike da mamakin halin dan Adam ,ko acikin mutanen da suke hasashe babu inna maimuna a ciki lallai matar nan ta san takan munafurci da iya taku,cewar yusuf da yake magana shi kadai bayan kammala wayarsu.




BASHIR




Share zufar da ta gangaro masa ya yi bayan ya gama zagaye garin bai samu Surry ba,samun gefen hanya ya yi ya faka,sannan ya fito ya jingina jikin motar yana kallon cikin hotel din da yake fuskantarsa.




Daidai lokacin motar ogan Surry ta ƙaraso cikin sauri securitys suka bude masa gate,saurin shigewa ya yi saboda ganin Bashir a gurin,sosai yake cikin mamakin ganin Bashir din, Allah yasa dai tsayuwarshi a gurin bai danganci zuwansa ba. abinda ya ayyana a ransa kenan,yana samun guri danyin fakin.




Gaban aunty Amarya ne ya fadi ganin Bashir dake tsaye jikin motarsa yana ɗan kalle kalle,gaba daya sai tunaninta ya nemi tsayawa cak,gabanta ya shiga faduwa,me ya kawo Bashir nan?ko dai shine na cikin motar? Kai bashi ba ne? Ai tana ganin sanda motar ta shiga hotel din dan haka bashi ba ne,sai dai idan shima da abinda ya kawoshi ko kuma tare suke da na cikin motar, wannan tunanin da ta yi ne yasa ta umarci me nafef din da ya sauketa ya tafi,dan ita dole ta yi dabara wajen shiga hotel ɗin saboda kar Bashir ya ganta.




_________




Hajiyar agadex ce ta shigo dakin Raihan tana cewa ke taso maza me gyaran jikin da na dauko tazo yau din nan za a fara gyara min ke dan ba zan yi sake rana tsaka a zo ace in fito dake za a kaiki ba," tura baki Raihan ta yi sannan ta ce", Hajiya wane irin gyaran jiki? Gyaran jiki irin na amaren da za akai gidan miji", au na manta ma ashe ke rabuwa za ku yi da zarar nur ya farka amma dai duk da haka za ayi miki saboda sabon mijin da zaki aura", ta karasa fada tana kamo hannun Raihan ɗin,da sauri RAIHAN ta fincike hannunta kafin cikin zubo da hawaye ta ce", Hajiya dama ana aure biyu? Tsayawa hajiyar ta yi daga kokarin kamata da take yi sannan cikin hade fuska ta ce", ai shi wannan din raba shi za ayi tunda dama haka mukayi dak.....kafin hajiyar agadex ta karasa RAIHAN ta saki kukanta me karfi harda shura kafa, sakin baki hajiyar agadex tayi tana kallon abinda ya isheta,tafa hannuwa ta shiga yi tare da cewa yo kaji iskancin banza ina ji ke kika ce bakya sonshi,mu kuma muka bi abinda kike so muka ce idan komai ya daidaita sai a raba auren kowa ya auri wanda yake so,sallamar wazer cikin deep voice dinshi ce ta dakatar da hajiyar agadex daga magana", yauwa tunda kazo sai ayi a gabanka wata ƙilma yanzu zaka rubuta mata takardar kowa ya huta", dan zaro manyan idonshi da ako da yaushe suke a lumshe ya yi yana furta ya Salam akan labbanshi idanunshi akan Raihan da yake jin kukanta a tsakiyar kansa", me ya farune? Ya tambayi Hajiya ba tare da ya dauke kallonshi daga kan Raihan ba,kora mishi bayani Hajiyar agadex ta yi daga karshe ta ce", shine kuma zata zo tana kukan sakarci saboda na fadi
gaskiya ", kawar da kanshi ya yi yana dan fidda karamin murmushin dake kan labbanshi,au baza ka ce komai ba ko kana so kace min ba haka a kayi ba? Haka akayi Hajiya amma yanzu ki yi hakuri idan ta ce tana sona ba sai an raba auren ba tunda dama dan ta ce bataso ne", Tom shike nan hakan ya yi bari na fita na barku abinda ake ciki sai kasanar dani dan da zancen tarewa nake yi to amma tuna wannan sharadi yasa na daina maganar", ta karasa maganar tana fita tare da sakin dariyarta da take ta kannewa tun dazun.




Tana fita ya taka a hankali ya isa inda Raihan ɗin ke kwance a ruf da ciki tana fama da hawayenta na shawagaba,a hankali ya bi bayanta cikin wani irin shauki dake tasowa tun daga can kololuwarsa,bai sakar mata nauyinsa ba amma gaba dayan jikinsa ya haɗe da bayanta har tana jin tudun jikinsa a nata,runtse idanunta ta yi tana sauke wani irin numfashi dake gauraye da wata irin kauna mara algus,cikin Muryarshi dake kara narkar da ita cikin duniyarsa ya ce", meye na kuka keda kika ce bakya so yanzu kuma ana ƙoƙarin yi miki gata na rabaki da abinda bakyaso ai ina ga sai tsallen murna tunda an rabaki da abinda bakyaso ko? Bata san lokacin da ta yi wata irin juyowa ba saiga dan Ammi akasa yar Mami a samansa dukan ƙirjinshi ta fara yi tana ci gaba da kukanta cikin kukan ba tare da ta saurara da dukan da take mai ba ta ce",Ni bansan meye ƙi ba in dai akanka ne,ko kai dinma ai basona kake ba", rike hannunta ya yi yana son ganin fuskarta da taki bari ya kalla sannan cikin yanayin da take sake jefa shi na shaukin ƙaunarta mara ƙarshe ya ce", Raihan na fi kowa sonki in kika cire Mami da Abbie su dinma fa ba su fini sonki ba", Raihan ina miki kaunar ƙauna wadda harshe ba zai iya fadinta ba,ban san me zance akan sonki ba Raihan i love You ya karasa fada yana hure idanunta da tunda ya fara tsakura mata son da yake mata ta kafeshi da su,kasa cewa komai ta yi sai kawai ta kankame shi tana bin fuskarsa da sumba a ko wane loko da kusurwa na fuskarsa.




Aunty Amarya......




Tana cikin tunanin ta yadda za ai ta shiga hotel din,sai ga adaidaitar su Surry ta tsaya a gaban motar Bashir,Bashir dake dan kalle kalle ya yi kyakkyawan gani saboda Surry da ya gani tana fitowa daga adaidaitan hakan yasa gaba daya hankalinsa ya koma kanta wannan shine ya bawa Aunty Amarya damar shigewa hotel din ba tare da Bashir ya ganta ba.....✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page59 ``


Uch innawuro Raihan zata cinye miki jika wazer ya fada yana lumshe idanunsa saboda yadda yake jin ɗumin bakin Raihan a duk sassan fuskarshi,hakan ba karamin tasiri yake yi a jiki zuciya da ruhinshi ba,duka ta shiga kai masa tana hawayen sakalci daga karshe ya rike hannayenta ya haɗe ta da jikinshi ya shiga aika mata da sabbin darussan da yake son ta fara dauka kafin a kai masa ita inda zai karbi ladar Koyarwarsa.


Aunty Amarya......




Ƙirjinta na dukan tara tara ta shiga laluben inda zata Ganshi sai dai bat yayi mata batan dabo,ke Hajiya me kike nema ne?cikin razana aunty Amarya ta juya tana kallon me maganar,ganinshi da uniform yasa ta gane cewa security ne dan haka ta yi saurin saita kanta tare da hadiyar kakkauran miyan da yake kin tafiya zuwa makoshinta,budar baki ta yi ta ce", ban taba shigowa ba Ni bakuwa ce shi yasa nake neman hanyar da zata kaini reseption", ok biyo Ni ya fada yana yin gaba,takun da aunty Amarya zata yi sai ji ta yi an toshe bakinta da handkichip ba a yi wata wata ba aka janyeta daga gurin, security dai sai juyowa ya yi yaga wayam cikin sauri yabar gurin yana kiran gexos domin shi a tsammaninsa gamo ya yi.




Cikin yabawa da aikin yaronnasa yasa suka saka Aunty Amarya a mota ba tare da kowa ya Ganshi ba,kasancewar hotel din manya ne ba kowa ke kama shi ba shi yasa ko da yaushe zaka same shi tsit,kuma bai yi hakan ba sai da ya shirya dan sai da ya fara hada baki da staff din da alhakin cc camara ke hannunshi shi yasa ya yi aikin cikin kankanin lokaci.




Surry dake kokarin fita daga nafef ta dakata saboda tareata hanyar da Bashir ya yi,bude baki ta yi zata fara zazzaga masa rashin mutumci amma sai ta ji tamkar an shake mata wuya ga wani irin tsoran Bashir da ya shigeta farad daya dan haka sai kawai ta hadiye kalaman da take shirin yi tare da komawa kalar tausayi sannan cikin tausasa harshe ta ce", plz bawan Allah dan bani hanya wallahi sauri nake yi", wani kallon raini ya yi mata kafin ya ce", fito ki biyo Ni saboda bukatar dake tare dani akanki tafi uzurin da kike dashi", yana gama fadar haka ya saki karfen nafef din ya yi gaba zuwa gurin motarsa, cikin mutuwar da jikinta yake kuma yi ta fita daga nafef din ta bi bayanshi, su kuwa su Dady tsayawa su kayi suna kallon abun mamaki saboda su dai a iya fahimtarsu basu ga wata alama dake nuna cewar Surry tasan wannan mutumin ba,cikin dabara Salim ya dauki hoton fuskar Bashir saboda su nunawa Wazer wata ƙil yasan ko shi din waye.




Daidai lokacin da Surry ke bude gaban motar Bashir zata shiga,a daidai lokacin ne kuma oganta ya sako hancin motarsa dan fitowa daga cikin hotel ɗin,karaf idanunsa suka sauka akan Surry da Bashir,wani irin kallo ya bisu dashi zuciyarshi na masa mugun tunani akan Surry,wata irin kwafa ya yi tare da kallon gefan da yaronsa yake yana cewa ina so ka fita ka bi su kaga duk inda zasu daga karshe ka kawo min bayanai akan alaƙar dake tsakaninsu", ok OGA yaron ya fada yana saurin fita daga motar da gudu ya figi motar baka ganin komai sai ƙurar gurin da ya bari.






Inna maimuna Yusuf....




Cikin kebabban gurin da suka saba haduwa suke zaune suna fuskantar juna,kowanne fuskarsa cikin walwala wanda hakan yake nuna cewa suna cikin farin ciki,mika mata hannu Yusuf ya yi dan ta bashi takardun amma sai ta yi biris dashi shi kuma bai janye hannunsa ba ya tsaya yana son ganin gudun ruwanta wanda dama hakan suke fata domin ta shiga tarkon da suka dana mata,fuskarta ce ta sauya daga murmushi zuwa fusata kana ta ce", banzo dasu ba, shima hade fuskar ya yi sannan ya ce", saboda me? Saboda hakan shine tsarina", ta bashi amsa babu alamun wasa a tare da ita", murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce", to me kike nufi da hakan? Cin amana ko me? Ka bawa kanka amsa ta faɗa tana mikewa sannan cikin tsare shi da idanu ta ce", Yusuf kana tunanin da zan saida raina a banza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login