Showing 57001 words to 60000 words out of 189984 words

Chapter 20 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15604

kamar zata cinye shi,zuciyarta na wani ƙara zurfi da maitar sonshi tare kishinsa me tsanani wanda take jinsa har wuyanta,sai ina kuma innawuro ta faɗa tana kallon yadda yake ta faman dauke kai da ƙara kame fuska,wanda yanzu kuma hakan da yake mata duk ya dameta,zan dan fita, aikine ya taso"amma kasan dai abin da ke faruwa a garin dan me zaka fita? Naga dai kai oga kwatakwata ne ba kai ka ke aikin nan ba,idan ma rahoto ne kana zaune za a dauka,to meye ne na sai ka fitan?dole ne dan haka Na da muhimmanci "daga haka ya wuce ta ba tare da ya dubi inda rabi take tana mai kwarkwasa da fadin Allah ya kiyaye ba,nan dai ya bar innawuro da mita kamar zata ari baki.




Yana fita suka yi kicibus da Abban rabi,dakatar da shi yayi bayan ya gaida shi,ya ce" Ahmad ina zaka? Shuru ya yi yana tattara dan abin da zai faɗa,daidai nan Abbu shima ya ƙaraso dan duk labaran abin da ya faru ya baza ko ina tun da tuni yan jarida masu aikin Saida rai suka bazama dauko rahoto,yanzu ko wace gidan Radio da ta television da yanar gizo jaridu da sauran social network abin da zaka ji ke nan kuma ka gani yayin da yan jarida suke ƁOYE suna ɗaukar komai,Abbu ya ce kaima ai kasan inda za shi" to ai naga an riga an haska a gidan tv da radiyo na chibaɗo me kuma zaka je kayi?Abba fitar nawa ya na da muhimmanci" ok gaskiya yaya dole ne Ahmad ya yi hakuri a wannan karon ya karbi securityn nan duk da ya nuna baya so,to amma kasancewar sa tare da su yana da matukar muhimmanci,aikin ku aiki ne me hadari dan haka Ni zan kawo security ko guda biyar ne wadanda zasu na kula da kai"zaiyi magana Abban ya yi saurin katse shi da cewa, bana bukatar cewar ka umarni ne wannan "daga haka ya yi wucewar sa,Abbu ya yi murmushi tare da cewa SOYAYYA ce hakan dan haka sai kayi hakuri idan ya so ni zan lallaba shi ya bar batun biyar din ya kawo ko biyu ne ,tun da gidan ma muna da wadatar su",




Jin jina kai kawai ya yi ya wuce abbun yana sa mishi albarka.




Bai taba tunanin da Raihan a kayi aikin nan ba,sai bayan shigar sa office,da Khalid ya kawo masa bayanan da suka watsa na gidan tv da rediyo,tun da duk kusan ma aikatan daya ne,ƙalilan ne wadan da suke aiki a tv din chibaɗo ba sa aiki a rediyon ko jaridar su ta chibaɗo daily trues ,ma'aikata suka nutsu suka tara masu gaskiya da rikon amana,duk da dai sun san cewa ba ko ina ne ya zama dole sai ka samu yadda kake so ba,dan basu da tabbacin cewa dukan ma'aikatan su masu gaskiya ne,to amma Ahmad wazir da maihaifinsa suna da matukar kula da ma'aikatansu,dan haka ko da kana aikata rashin gaskiya cikin dan lokaci suke gano ka,shi yasa su ka haɗe ma aikatan duk suka zama ɗaya saboda gudun kawo Baragurbi.




Lokacin da ya tabbatar Raihan ta ziyarci gurin nan, ba karamin bacin rai ya shiga ba,duk da bashi da dalilin hana ta tunda aikin ta ne,shi kan shi bai san me yasa yake jin bacin rai me tsanani ba a duk lokacin da Raihan ta fita irin wannan aikin da yasan cewa za agauraya da maza, abu na biyu kuma shine yadda al'amarin na yau ya kasance dole a kawai bukatar su yi taka tsantsan da rayukansu,amma Raihan ko tsoro bataji ba ta fita,wato dai mu'amala da cudanya da maza yasa ta koyi dakiya da rashin tsoro,sam baya ganin fargaba ko sarewa a cikin al'amarin Raihan,to amma idan ita bata jin tsoro ai su da ta zame musu tsokar jiki,suna jin tsoran faruwar wani abu da ita,abu na uku shine tsallake bikin gidan su da ta yi ta fita aikin lada domin Raihan ba dan wani abu take aiki ba face taimako da neman kusanci ga Ubangiji,numfashi ya dan ja kana ya fesar yana neman hanyar ganinta,duk da yasan cewa yanzu da baya ba daya ba ne,wata irin rayuwa suke yi yanzu kamar ta makiyan da suka shahara wajen kin juna,to wai duk me ya kawo hakan? Ya tambayi kanshi wanda shi kansa bai san amsar ba,kuma bai san adadin sau nawa yakewa kansa wannan tambaya a rana ba.


Wayar office dinta ya nema kai tsaye,sai dai kuma yaji daga bakin abu Huraira cewar ai tana gama gabatar da rahotanni ta wuce gida saboda yanayin garin da kuma bata sanar da kowa da cewar ta fito ba,Nima wasu rubutu na zo dauka office din,ok"abin da wazir ya iya cewa da Abu Huraira dake ta ƙwaro bayanai ba,abinka da dan jarida.




_________________




Oga komai ya kammala munyi duk yadda ka sa mu,yauwa dage,aikinku na kyau naji dadi da ba ku bari yan sanda sun kama ku ba,duk da cewa suma din sai da muka bi ta kansu sannan muka gabatar da al'amarin ,kuma hakan yayi daidai tunda sun cika alkawari da ba suzo gun ba har sai da mai afkuwa ta afku"mutumin da yake sanye da wata doguwar bakar riga me hula wadda ta rufe mishi fuskar shi gaba daya ,ya fada yana mai ci gaba da yin dariyar sa cikin shakewar murya.....






Dr Senate ya yi wata irin zabura zufa na karyo mishi ya ce"garin yaya kuka bari aka kashe yaran mu,me yasa duk sanda irin haka zata faru kuke yin sakaci da rayuwar ku ne?shugaban jam'iya ya ce"to me ye na tashin hankalin tunda dai su sun tsira ba shike nan ba,karfa ka manta daukar su muke yi suna mana aiki kuma sun riga sun san cewa aikin na Saida raine amma suka karba suke yi,to kuma mu meye na mu ,aikin kawai idan an kashe wasu mu samo wasu shi ke nan kawai, Alh sale ya yi wata shegiyar dariya yana kallon su kafin ya ce" gaskiya shugaba ba Allah a ranka,amma fa maganar ka tana kan hanya dan haka ku kuje sai mun nemi ku"haka zugar yan daban suka.wuce su ka fita bayan suna ji da ganin cin mutuncin da akayi musu da maganganun da idan suna da hankali sun ishe su komawa ga Allah (wanda yayi nisa baya jin kira)....




Lokacin da RAIHAN ta dawo gida tuni ,aunty amarya da innar agases(innar aunty amarya) da inna maimuna sun fahimci bata nan,innar agases din ce ta dinga bawa aunty amarya da inna maimuna baki ita da matar yaya giɗe ,wato yayan ta wanda tuni ya bar gadin da yake yi a Niger abbie ya sai musu gida babba kuma wadatacce, a garin yamai suka koma,bayan yayi yayi da su akan su dawo Yola sunki,innar agases ta ce",to ke kam banda abinki ramle,Rahim fa namiji ne kuma matashi to me yasa har kullum kike masa kallon yaro karami ko kuma mace ,tun da su ne kawai idan ba a gansu na tsawon awa ɗaya zuwa biyu ba za A damu, wannan kalma da ta ji daga bakin innar ta shi yasa ta daure ta kawar da tashin hankalin ta,itama inna maimuna sai ya zamana hakurin ake bata dan kowa yasan cewa itama bata da juriya akan al'amarin Rahim,baki suka ci gaba da basu har zuwa lokacin da Raihan din ta shigo falon cikin nutsuwa da sallama a bakin ta,wata boyayyar ajiyar zuciya aunty amarya ta yi tana kallon Raihan din da yar hararar da bata kai zuci ba,ta ce" Rahim wane irin abu ne haka ? Ya za ai ka fita a na wannan abun baka sanar da mu ba? Zuwa Raihan din ta yi ta rungume ta tana cewa sorry mamina,bazan kuma ba"innar agases ta ce" ja iri ka ce haka mana tun da ka daga mana hankali da wata zuciyar ka ta marasa tsoro"karasawa Raihan ta yi ta rungume inna maimuna tana cewa sorry sweetie na tayar muku da hankali bayan ƙara ba,shafa kansa inna mainuna ta yi tana cewa Rahim ka tayar mana da hankali dan Allah kar ka kuma yin irin wannan gangancin",jinjina kai ta yi daidai nan zubaida babbar yar giɗe take bawa innar agadex amsa da cewa " to ke inna idan namiji bai zama jan gwarzo ba me kike so ya zama? tsam Raihan ta mike ta nufi hanyar dakin ta,dan duk za ayi irin wannan maganar da ta shafa banbancin jinsi bata yadda ta zauna a gurin,da wani irin boyayyan kallo me cike da damuwa da tausayawa aunty tabi Raihan din da shi..




Dinner dai an fasa ta ,kawo amaren ma dan an tabbatar da tsaron jami ai ne kuma gari ya lafa tamkar babu abin da ya faru,dab da magriba a ka shiga da amare dakunan su bayan kowacce an mika ta gurin surikanta,da yawan baki sai gobe zasu koma yan Kano da yan niyame,harma da wasu garuruwan.




Aunty amarya ce tsaye a gaban tafkekiyar wardrobe dinta tana dauko kayan bacci,kasancewar yau abbie ba a wajen ta yake ba,dan haka yana can bangaren sa,tana gama saka kayan ta feshe jikin ta da turare,so take ta je dakin RAIHAN su kwana tare dan kwana biyu ta yi kewar zama da ita,wayarta ta dauka zata fita sai kuma taga alamun shigowar sako,murmushi ta yi dan a zaton ta sakon abbie ne wanda ya saba turo mata duk dare kamar haka In dai ba girkin ta ba ne,ko da kuwa ya zo sunyi sallama,tunanin hakan yasa ta samu gefan gado ta zauna,dan bai kamata taje dakin RAIHAN ta karanta ba,




Duk abin da kike boyewa na sani duk wani sirrin ki a tafin hannuna yake, ina muku fatan alkhairi ke da yarinyar ki RAIHAN..................✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page19 ```






Wani irin bugu kirjin ta ya yi sai wani mahaukacin jiri da ya kamata,wanda ba dan a zaune take ba, tabbas zata iya yin mummunar faduwa,gumine ya shiga yanko mata ta ko wace kafa dake jikinta,tashin hankali babu kalar wanda bata shiga ba ,sakon kuwa ta karanta shi har sau ba a dadi karshe ya zauna a harshen ta da ƙwaƙwalwar ta daram,waye wannan ko wacece wannan?


Ya akayi ya san sirrin da take ta boyonsa tsayin shekaru?


Shin ɗaga hankalinta zata yi ko Allah zata godewa da ya fara haska mata hanyar da take ta nema tsawan shekaru goma sha bakwai?


A iya saninta bayan ita wazir da Raihan sai uwa uba Dr Sabo babu wanda yasan wannan sirrin,shi Dr Sabo ma baya ƙasar yau wajen wata biyar zuwa shida ke nan.


To ko Raihan din ce ta fada wa wani bayan wazir?


Kai Raihan ba zata yi haka ba,tabbas a kwai wani abu da yake a ƁOYE wanda bata sani ba,cikin ƙwarin gwiwar da ta fara samu dalilin tunanin da ta yi,ta janyo wayarta , ta yiwa Dr Sabo powordin saƙon tare da yi mishi bayanin da zai fahimta,dan ji ta yi ba zata iya yin maganar a cikin gidan nan ba ma, gani take kamar mugun yana tare da su kuma yana bibiyar su,shi yasa taki yi masa waya kai tsaye,ta danyi nisa a tunanin waye? Wacece ?ya a kayi? Sakon Dr Sabo ya shigo wanda shine ya kara sama mata yar nutsuwa,a sakon nashi ya nuna mata ne ta kwantar da hankalin ta wannan kamar wata hanya ce ta bude a gare su dan sanin abin da suka dade suna son sani din, sannan RAIHAN macece mai kamar maza wadda Allah ya bata baiwa mai tarin yawa,ita ma ta kawo karfin da ta ko ina ba zata bari a cuce ta ba sai dai idan Allah ya tsara hakan cikin littafin kaddarar ta da kuma raunin da aka san ko wace mace tana dashi, wannan abin da mu kayi na ƁOYE raihan mun sani ta wani bangaren mun yi daidai ta wani bangaren kuma munyi kuskure,amma abin da nake gani Allah ya riga ya tsara hakanne dan ya rubuto raihan sai tana matsayin namiji ne zata koyi abubuwa masu tarin yawa,kamar tarin ilmin ta na boko da na addini,da kuma aikin ta na taimakon al'umma, wan da nake ji a jiki na cewa al umma masu tarin yawa zasu samu taimako da tsira da ga sanadin ta na kadan daga cikin baiwar ilmi da Allah ya bata,zasu amfana da ita ta fannoni da dama wanda da ace tana a matsayin mace baza a bata damar yin hakan ba,ba kuma za a bata kwarin gwiwa akan kudirin ta ba,dan haka ki kwantar da hankalin ki,ki nutsu ki sa ido da zuciya gurin fuskantar al'amarin da yake da akwai kuma yake tunkaro mu domin kuwa yanzu na tabbata cewa kakwai babban yaƙi a gabanmu,Nima na kusa karasa cos din in sha Allah zan dawo very soon.




Wadan nan kalamai ba karamin tasiri su kayi a gangar jiki da zuciyar Aunty amarya ba,dan haka kawai sai ta goge duka sakon da wanda aka turo mata da wanda ta yiwa Dr da reply din da ya dawo mata da shi.




Kai tsaye ta sawa zuciyarta cewa yanzu haka ma bugar ciki ne makiyansu zasu mata saboda sun rasa yadda zasu yi,sai dai kuma basu san cewa da wannan dama zata yi amfani dan tona asirin su ba,da wannan tunanin ta bude dakin Raihan da key din hannun ta ,ta shiga,samun Raihan din ta yi tuni har ta yi bacci saboda yar gajiyar da take tare da ita,kwanciya ta yi tare da kara tofa musu addu'a, ta rufe idanun ta da san kawar da komai ta fuskanci abin da ya kamata ta fuskanta.




Washe gari kowa ya watse aka bar gidan, amare na bangaren su da mazajen su,dan haka gidan ya koma ya yi shiru ,ga jiddo da ma kwana biyu bata gidan taje hutu kamar yadda ta saba zuwarma mamanta,to ko da aka gama bikin binsu ta kuma yi daniyar kara kwana biyu zuwa uku sannan ta dawo.




Kamar yadda Abban rabi ya ce"hakan ya yi ,dan kuwa a cikin kwana biyu ya samo kosassun security guda uku,daya shi zai dinga tuka wazir duk inda zashi,ko da wadan can ba sa tare shi dai ya zama aikin sa ko da yaushe yana tare da Wazir,to haka dai wazir ya karba ba dan yaso ba.




Sosai a kwana kin nan ake wata Irin rigima ta rashin imani,tuni gari ya kuma rikicewa,hankalin talakawa da abin ya shafa ya kuma tashi,cikin kankanin lokaci,gwamnatin da ake alfahari da ita me taimako da san talakawa,ta juye ta koma wata iri talakawa sai zaginta suke,meye amfanin baɗi babu rai abinda suke fada ke nan,kowa dai da abin da yake fada.




Hankalin Gwamna ya matukar tashi,dan ya tabbata yan adawa ne suke wadan nan abubuwan duk dan sun san za a iya ra taya laifin akan gwamnatinsa,duk da cewa yana ƙoƙari gurin tabbatar da tsaro ,amma abin kamar ana kara iza wutar sa.


Abu na biyu kullum talakawa su kasa kunne suna jira suga an kamo yan ta'addan ,amma kullum shuru kake ji sai ma wasu rigingimun da suke kuma ta shi,daga a tsinci gawar yaro an cire ido,sai atsinci gawar tsohuwa babu jini ko digo a jikinta,asibitocin ma idan anje babu ingantattun magunguna,ala cuta dai aka magani ta ko ina ba dad'i,




Yan jaridu ne kullum suke kokarin yaɗa abubuwan da suke faruwa saboda jawo hankalin al'umma da jami ai ,dan duk a yi maganin matsalar amma ko an samu jajirtaccen jami'i me gaskiya da ya fara bincike ko ya ce"zaiyi sai a neme shi a rasa ko kuma a tsinci gawarsa.


_________________




A hankali ya fito daga motar bayan dauko shi daga filin jirgi,sabon mataimakin Kwamishinan yan sanda HAIDAR YAHYA RINGIM,,,




Nutsatstsan mutum me aiki da gaskiya matashi dan kimanin shekaru talatin da shida,me mata daya da yara uku,kwazon shi da himmar shi harma da gaskiyar shi su suka.kaishi kan wannan babban matsayi a cikin kananun shekarun da yake da su,baizo da kowa na shi ba,amma yace idan yaga yanayin aikin zai koma ya taho da iyalin shi,kai tsaye gidan da aka bashi driver ya kaishi domin ya samu ya huta,kafin gobe ya shiga office.




Yallabai kana ganin babu abin da ya kamata muyi akan barnar da ake yi din?kamar me kake so kayi? Kwamishinan yan sanda ya gyara wayar dake kunnen sa ya cigaba da cewa, ina so ka bamu dama mu samu wasu daga cikin mutanen ku mu kama,saboda idanun talakawa yana kanmu harma da sauran al'ummar jihar nan,kasan duk abin da yan jarida suka sani bamu da halin boye shi,dan ko mu mun boye su ba za su yi shiru akan hakan ba,ko da sauran jaridun sun bi tsarin mu sun bar maganar,kasan wannan CHIBADO's din ba zasu bari ba,suna da matukar ƙarfi wanda yasa dole duk rahotonnin,da suka fara bullowa daga gare su musan abin yi akai,su ka dai suke rubuta bayanan gaskiya wanda kuma suke janyo hankalin al'umma da manyan kasa kanmu,shi yasa nake so mu yi wani abu akan hakan",


Daga can bangaren cikin wata murya wadda ke nuni da isar da me Muryar ke da ita ,aka ce za ka iya yin hakan amma ba mutanen mu zaku kama ba,kuyi abin da ya dace kawai,amma dai karka sake matsalar ta shafe mu",ok sir za a kiyaye" yana sauke wayar aka bude kofar office din aka shigo ,da sauri HAIDAR ya yi solute din Kwamishina,daga nan su kayi gaisuwa ta mutunci da nuna sanin juna,Kwamishina ya ce" ina maka Barka da zuwa tare da taya ka murnar samun wannan babban matsayi, Allah ya bamu ikon tsayawa akan gaskiya,cikin jin dadi HAIDAR ya amsa,daga nan ya yi masa sallama ya wuce office din sa.






Ko da RAIHAN ta je office ba ta nemi zuwa office din oga ba,duk da cewa akwai aikin da zata gabatar masa,ba ita ta nufi office din ba har sai da ta tashi daga aiki,sallama su kayi da abu Huraira ya wuce ita kuma ta nufi office ɗin oga.




Gefe taja ta tsaya tana jiran sakataria ta yi mata iso,kamar yadda ake yiwa kowa,tun bayan da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login