Showing 138001 words to 141000 words out of 189984 words

Chapter 47 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15626

karasawa da ruby gida saboda yadda duk ta firgice kamar me haukan gaske,yau kayan mayen ma hauka ta yi musu dan sha kawai take yi babu lissafi bare tunani,ita dai Surry ta samu ta bar gidan dakyar zuciyarta cike da rashin jin dadin yadda plan dinsu ya rushe,gida ta wuce saboda ta samu nutsuwar yin tunanin abu na gaba duk da tasan cewa oganta zai yi wani abu akai.




Ranar dai gaba daya a cikin asibitin suka yini sai dare suka koma gida,lokacin da su Ammi zasu ta fi ji ta yi kamar ta tafi da Raihan ɗin,to bare kuma oga wazer dan kuwa ba dan idanun baffa Ali da yake jin nauyi ba to da sai ya tafi da Raihan gidansa ko dan ta samu nutsuwar zuciya.




Da yawa zuciyoyi sun dan fara samun salama,wasu sun dauki wani sabon burin wasu kuma suna ci gaba da yakin neman na baya,yayi da wasu suka yada makamansu kamar su mama murja da Mom Hanne ke nan,yadda suka yada makamansu haka suka jawa ƴaƴansu kunne suka fara gyara abinda dama sune suka bata.




Washe gari dakyar RAIHAN ta hakura ta yi shirin fita office saboda rarrashinta da baffa Ali ya yi da kuma IDRES,wazer ne yazo har gida ya dauketa tare da sabbin gerd dinsa.






ABBAN rabi ba karamin haushin wannan abu ya ji ba,da saka innawuro ya yi a gaba yana fada kamar zai a ri baki,a kan me wazer zai kori securitys din da ya kawo masa ya nemi nasa da kansa,dan shi bai san Abbu ne ya kawo su ba,sai da innawuro ta faɗa masa sai kuma duk yasha jinin jikinsa,bai dai kara cewa komai ba amma tabbas ya tsargu.




Rabi dai bata iya komawa aiki ba saboda jinyar zuciyarta da bata gama ba,sannan har lokacin bata samarwa kanta mafita ba,gashi ganin wazer ɗin ma ya yi mata wuya.abin duniya duk ya dame ta,fargabarta bai wuce ace asirinta ya tonu ba,fatanta a yanzu Allah yasa kar wazer ya gano ita ce ta fidda jarida.




Dufuty ya haye kujerar Gwamna a matsayin me rikon kwarya, Abba yahya kuma ya zama mataimakin sa ,ta wani bangaren kuma ɗan takarar gwamnan gobe,yanzu jiran lokaci kawai ake yi.




Yau kwana goma sha biyu da abinda ya faru, Abbie har yanzu yana cikin commer,babban abinda yake damun ahlinsa ke nan shi yasa yanzu gidan ya koma tamkar gidan makoki,babu wanda ya fi RAIHAN shiga halin damuwa saboda ita abin biyu ya haɗe mata,har yanzu idan ta kalli hajiyar agadex sai taji faduwar gaba da tashin hankali saboda abinda taji tana fada ranar da ta fita gadin,gashi ta kasa yi mata maganar,hatta da wazer ta kasa gaya masa,kuma ba komai take tsoro ba sai amsar da zata ji daga hajiyar agadex ɗin bata san manufarta nayin abinda ta yi ba,ita yanzu zata iya cewa ma sam bata yadda da kowa ba a cikin gidannan tunda har zata iya kama kakarta da wannan mummunan laifin.




Yau Sunday hakan yasa Raihan bata fita ko ina ba,tunda ta gama abinda take yi ta gudu bangaren inna maimuna,can ne kawai take zuwa ta samu yar mutawa saboda yadda inna maimuna ke matukar ɗebe mata kewa,




Suna zaune a falon kanta na kan cinyar inna maimuna tana mata susar gashi da hakan ke matukar yi mata dadi, Abba yahya ne ya shigo ganin Raihan ɗin yasa shi sakin Murmushi yana cewa Raihan yar gatan mutane da yawa", dariya ta yi tana tashi daga kwancen da take ,gaida shi ta yi ta ɗora da cewa a'a fa Abba karfa ka manta wannan Raihan ɗin har yanzu zagaye take da makiya tunda har yanzu ba a gama gano su ba", inna maimuna ta yi saurin cewa hakane amma in sha Allah suma asirinsu na gab da tonuwa", Abba yahya ya ce in sha Allah kuwa, mikewa ya yi yana cewa bari na shiga ciki", yana wucewa Raihan ta dubi inna maimuna kana ta ce", innata ki tashi kije ki aikin lada kinsan dai Abba daga gidan gwamnati yake dole yana bukatar ki a kusa", rike baki inna maimuna ta yi cike da mamakin Raihan ɗin har zata yi magana sai kuma ta fasa amma fuskarta yalwace take da murmushi, itama raihan din murmushinne akan fuskarta har inna maimuna ta bace mata idanunta na kanta,sai dai kuma a yanzu wani irin kallo take Binta da shi idanunta har sauyawa su kayi,wata ƙil tausayin inna maimuna ne yake dagula mata lissafi kasancewar basu da yawan 'ya'ya shi kuma dayan da Allah ya basu ya zabi duniya a akansu.




Numfashi ta ajiye tana mai daukar wayarta dake nuna haske alamun kira ne ke shigowa.




A hankali ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya bayan jin sassanyan Muryarta da ya yi tana mishi sallama.




Amsawa ya yi yana ƙoƙarin boye sirrin zuciyarshi da a kullum kara bayyana kansa yake,reihann ya fada cikin Muryarshi me zurfi da dadin amo", har tsakar kanta saida ya motsa saboda yadda Muryar tashi ta karbu a duk wata kofa dake jikinta.




A hankali ta amsa tana kallon saitin corridorn da falon Abba yahya yake,me kike yi yanzu?babu ta bashi amsa har yanzu idanunta akan hanyar kamar me son gano wani abu", ok ga nan direba a waje ki fito ki same shi zai kawo ki inda nake", turo karamin bakinta ta yi kana ta ce", Ni kam me za kayi min? Cinye ki zan yi", ya fada yana wani lumshe shanyayyun idanunsa,uhmm ai dama ka saba cinye nin", ta faɗa kasa_kasa dan kar yaji,sai dai kuma ta makaro dan yaji abinda ta ce,amma sai ya basar cikin halin nashi na fuskewa,ki yi sauri yana jiranki" daga haka ya datse kiran, bin wayar da kallo ta yi,kafin ta mike a hankali can kasan ranta tana jin ba zata iya sarayar da bukatar wazer ɗin ba,duk da ta wani gefen tana tunanin amincewar maminta.






Wayar da Abba yahya yake yi ya datse yana kallon inna maimuna dake tsaye tana kallonshi,lafiya naga kin tsaya haka kamar sojiya? Dawa kake waya? Abinda ya fito daga bakinta kenan a maimakon amsa masa tambayarsa,shima kai tsaye ya ce", da ita da danki bashir nake waya ko da wani abu? Babu ta faɗa tana kawar da fuskarta daga kansa zuwa bangaren wata sip dinsa dake dakin ta can kusarwar dake gabas maso yamma,kallon wajen da ta yi yasa shima ya kalla yana cewa maimuna lafiya dai ko? Dan ajiyar numfashi ta yi tana dawo da dubanta kansa sannan ta ce", babu kawai dai jiya ne misalin uku na dare na farka shiga toilet sai na ji kamar magana kasa kasa daga cikin kwabar nan", magana kuma maimuna a'a sai dai idan tsorata kika yi amma ya za ayi kwabar da ake aje kaya ta yi magana,da Allah ki kwantar da hankalin ki naga kwana biyu duk a firgice kike idan kuma da abinda ke damunki ki fada min,ya karasa maganar cikin kwantar da murya", babu wani abu na gaya maka ABBAN Bashir bari na hada maka ruwan wankan", binta da kallo ya yi kawai har ta shige bathroom ɗin.




Lokacin da Raihan ta koma bangarensu bata sami aunty amarya ba,hajiyar agadex ke sanar da ita ta koma asibiti,dan haka sai kawai ta sanar da Hajiyar agadex cewa itama zata bisu yanzu wazer yana jiranta a waje, hajiyar agadex bata hanata ba tunda tasan waye wazer a wajensu baki daya.




Daki ta Wada ta danyi represh din kanta tare da zura doguwar a bayar da a yanzu tunda ta fara shigar mata shigarta ke nan saboda tun a baya shigar doguwar riga ko wace iri ce tana burgeta.




Tunda ta fito daga gate din farko take yan kalle kalle,har yanzu jin kanta take wata da ban,duk lokacin da ta yi shigar mata ta kanji alfahari da hakan kuma duk ta fito sai ta rude saboda yadda mutane ke kallonta kamar wata sabuwar halitta ta daban.yanzun ma tunda ta fito daga gate din security ke satar kallonta haka bayan fitowarta yan tsirarun mutanen da suke kaikawo a anguwar suke kallonta ba ko kunyar kallon dan ko ta kama mutum yana kallonnata baya dainawa,Tom inda sabo ta saba da hakan yanzu, tun daga ranar da ta fara fitowa a zahirin siffar ta ta cikakkiyar budurwa me tsananin kyawu.




Ko a wajen aiki bata tsira ba da yawa mutane son mu amala suke da ita, dan kuwa kallonta suke a wata diya da Allah ya bawa baiwa ta musamman,hatta yan koren rabi a yanzu basa iya kallon RAIHAN su dauke ido, sactariya kuwa bata iya haɗa ido da Raihan saboda kunya da nadamar abinda ta rinka yi mata,ita kuwa Raihan bata cewa karkarinta gaisuwa dan kuwa ita kadai wazer ya bata damar yi da abokan aikinta sai kuma abinda ya shafi aiki",tsaf a cikin kwanakinnan take kiyayewa saboda ta lura da take takensa so yake ya hanata aikin gaba ɗaya.




Da wannan tunanin suka ƙaraso gidannasa da a yanzu ta gama haddaceshi saboda zuwan da ta dan yiyyi.




___________






Zaune take bakin gadon da yake kallon Abbie,kallonsa take cike da tausayawa da karayar zuciya gani take kamar ba zai farka ba,idan ta tuna hakan ji take kamar zata yi hauka saboda tashin hankali,a hankali ta sa hannu ta share hawayen da suka gangaro mata kan kunci,wayarta ce ta yi ƙarar kira,duban wayar ta yi kamar ba zata daga ba sai kuma ta sa hannu ta danna ok tare da kara wayar a kunnenta,kafin cikin nustuwa ta yi sallama........






Cikin gaggawa Abba yahya ya gama shiryawa ya fito ,inna maimuna ya samu ta gama jera masa abinci,dubansa ta yi tare da cewa ina kuma zaka baka ci abincin ba? Bar abincin nan maimuna kira na samu daga gwamna me rikon kwarya,jin jina kai ta yi tana cewa shike nan Allah ya dawo da kai lafiya", Amin ya Allah ya fada yana karasa daura agogonsa.






Aunty Amarya




Tsugunne bata kare miki ba hajiya ramla akwai wani abu a ƁOYE Sannan akwai lauje cikin naɗi game da abinda ya faru a kwanakin nan,na baki satar amsa kyauta dan haka ki zuba ido kiga abinda zai faru,Ni masoyin ku ne dan haka kar ki shakku a kan dukkan abinda na fada mik....ji ta yi kamar an kwace wayar tare da kai duka me karfin da yasa ta runtse idanunta,ƙirjinta kuwa babu abinda yake sai duka,me wannan mutumin yake fada haka? Kuma waye shi? Meye a lakarsu da shi? Sannan me ye lauje cikin danin da yake fada? Akan wa laujen yake? maganar gwamna da mijinta ko maganar bayyana sirrin RAIHAN? Dafe kanta ta yi da yake matukar sara mata hakan ya sa ta mike da sauri ta fita daga dakin, kai tsaye office din Dr Sabo ta nufa dan warware masa wannan sabon tashin hankalin da ya kuma Kunno musu.






WAZER.......




A hankali yake juya dan karamin Flash din dake hannunsa,tunanin ta yadda a kayi ya shigo cikin kayansa yake yi danshi dai bai san na meye ba,gyara zamansa ya yi tare da janyo laptop dinshi dan saka plash din yaga me yake ciki yasan dole ta wannan hanyar zai gane na waye,sallamar da Raihan ta yi cikin sassanyar Muryarta ne ya dakatar da shi daga abinda yake shirin yi,aje plash din ya yi a gefansa yana Binta da kallon da take jinsa yana matukar tasiri a dukkan gabobin dake jikinta.




Mika mata hannu ya yi alamun ta ƙaraso amma sai ta noke ta samu waje daga can gefe ta zauna tana sunkuyar da kanta, ganin haka ya sa ya dubi jikinsa,sai a lokacin ya tuna shigar dake jikinsa,babu riga a jikinsa daga shi sai dan shot boxer iya cinyarsa,maida kansa ya yi ya kwantar saman kujerar yana ci gaba da bata wasu irin kallo da take rasa inda zata saka ranta dan takura.a sace ta dago dan kallon shi sai a kayi katari idanunsu suka sarke,kokarin kwace kwayar idonta take yi amma hakan ya gagara sosai ya sarke nata cikin nasa,bata Ankara ba sai jin numfashinsa ta yi a gefanta har jikinta na gugar nashi, dan muskutawa ta yi cike da rashin sabon hakan,hannunta ya kama a hankali ya shiga murza yan yatsunta,kafin cikin gizagon shi fuskarshi kadaran kadaran ya ce ", ina aikin da na sa ki? Du ban shi ta yi kafin kawar da kai tana cewa Ni sam ban ganewa wannan aikin da ka sani yi ba, ai ba so nake ki gane ba", ya fada yana juyo da ita suna fuskantar juna", musayar numfashi suka fara yi,cikin sauri ta rufe idanunta tana cewa dan Allah hamma wazir ka sa kayanka ban iya zama kana a haka", mutum ma ko kunya baya ji ta karasa fada kasa kasa.mikewa ya yi kamar zai bar wajen sai kuma ya dawo a hankali ya sunkuya ya dauketa gaba dayanta yana cewa muje ki fada min me kika fara ganowa akan aikin da na baki idan kuma ba ki yi ba ton sai na cinye wannan dan bakin tsiwar drama queen kawai", harba kafafunta ta fara cike da yarinta tana cewa dan Allah kar ka cinye min baki dame zanci abinci idan ka cinye,ba Gara ga kaci kayan dadi ba kuma ma ai Mayu ne suke cin naman mutum", dan ware idanunshi ya yi a kanta daidai lokacin suna kawowa cikin hadaddiyar bedroom dinsa da take tashin wani irin kamshin sa da ya gama kame komai nasa,a jiyeta ya yi yana lalubo idanunta dan mayar mata da martanin maganarta,bai samu kallon tsakiyar idanunnata ba hakan yasa ya janyota zuwa naked jikin nashi da take gudu yana cewa babu wani kayan dadi da ya wuce wanda ke tare dake sannan maita ai kowa ma maye ne akan kayanshi dan haka ki fadi abinda kike so ko me za ki yi yau sai na cinye ki gaba dayan ki", wayyo Allah Mami Abbie ta faɗa idanunta na cika da ruwan hawaye saboda bata san wani irin cinyewa zai yi mata ba dan haka ta ji tsoro sosai ɓaram ma da ta ji yana wani irin shafa jikinta da take tafiya da sulbin doguwar abayar dake jikinta .........✍🏽


52




ƁOYAYYIYAR RAIHAN






Girgiza kanta ta fara yi saboda yadda take jin tsigar jikinta na wani tashi da abinda yake matan,mutsu_mutsun kwace kanta ta fara yi dan kaucewa abinda ke shirin faruwa wanda sam bata shirya masa ba,rike ta wazer ya yi sosai yana wani shigar da idaunsa ciki tamkar wanda yake jin bacci,cikin rawar murya ta ce", umm um zanje hospital Mami na can tana jira na", wannan aikin da za ki yi yafi na Mami lada", ya fada yana sauke zip din rigarta kasa ba tare data sani ba,bata san sanda tasa hannunta ta zagaye shi ba tana cewa dan Allah dan Allah ka bari", waro idanunta waje ta yi jin rigarta na yin kasa,wata irin kara ta ƙwallah tare da hade jikinta da nashi da yake naked ta wani irin kamkameshi,kasancewar ya sake jikinshi kawai sai suka faɗa saman tattausar shimfidar gadonshi tana samanshi yana ƙasa,sosai Raihan ta fashe da kukan tsoratar da ta yi,shi ko wazer wani miskilin murmushine ya kwace masa yayin da tuni kwakwalwarshi ta fara aikin manta a duniyar da yake ciki sakamakon jin tudun breath din ta a ƙirjinshi, Raihan kuwa tashin hankalin da ta shiga ba kadan bane saboda tasan ba bra a jikinta doguwar rigar kawai ta zura ta fito bata taba tunanin za a kai matakin da wazer zai cire mata riga ba.




Dago ta ya shiga kokarin yi amma kam ta manne shi tana faman zubar hawayen sangarta,ash ya fada yana ɗan rintse idanunsa, da sauri ta dago kanta dan ganin abinda ya sashi yin wannan dan ihun,tana dagowa ya nuna mata ƙirjinta da girar shi,duka ta shiga kai masa tana kananun kukanta,hakan ya bashi damar kara kusanta ta da shi tare da dago kanta ya shiga lashe hawayen da yayi dama_dama a saman fuskarta a hankali har ya gangaro bakinta wanda baiyi wata_wata ba ya shiga bata zazzafan kissess din da yasa ta hadiye kukanta ba da shiri ba,ta kuma manta da cewar babu kaya jikinta.




Cikin wata irin kwarewar da baisan yana da ita ba ya shiga juyata da bata wani irin zazzafan romance da ya kusa zauta karamar ƙwaƙwalwarta,shinshina take yi yana shakar kamshinta ji yake tamkar ya maida kansa jikinta saboda yadda kamshinta yake gigitashi lasar wuyanta yake zuwa ƙirjinta yana sakar mata wani dan Marayan nishi wanda yake sata jin sanyi har ciki bargonta.....




Aunty Amarya.....


Kuka sosai take yi tana bawa Dr Sabo labarin abinda mutumin ya ce mata babu ko batan wasali saboda yadda abin ya zauna mata tamkar karatu,bai hana ta kukan ba sai da ya bata lokaci ta Gama dan kanta ta share hawayenta sannan cikin nutsuwa ya ce", ramla ki yi hakuri in sha Allah komai zai zo karshe kuma ina so ki rike wannan kar ki sanar Da kowa dan yanzu ba kowa za mu saki jiki da shi ba,shi kansa gidannan naku yana bukatar saka idanu,shi yasa nake so ki kwantar da hankalinki dan mu samu damar bincike a nutse,shi mutumin da nomber ya kira ki ko ya boyeta? Mika masa wayar ta yi dan ita bata da lakar iya dubawa.karba ya yi ya duba jim kadan ya dago ya kalleta kana ya ce", nomber ce dan haka zansa a yi tracking nomber in sha Allah za mu gano duk wani mugu da ke tare da mu,jin jina kai ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba....ta shi ta yi ta fito daga office din tana jin kwarin gwiwa duk da cewa har yanzu tsoran bai sake ta ba,tsoran rasa Raihan da mijinta,




Tana bude kofar ta yi mummunan gani,ganin da yasa jinta da ganinta suka fara gushewa,matar da ba ta gane ko wacece ba ta gani kan Abbie tana danna masa filo da iya karfinta burinta kawai Abbie ya karasa inda ba a dawowa,karar da aunty Amarya ta saki ne ya sa matar sakin filon da sauri ta juyo kasancewar facemask dake fuskarta shi yasa Aunty Amarya bata shaida ko wace ce ba, duk da yadda jikin Aunty Amarya ke bari hakan bai hanata kokarin kama matar ba, sai dai ina tuni matar ta angije Aunty Amarya ta fice a sukwane,duk da yadda Aunty Amarya ta yi matukar buguwa hakan bai hanata ci gaba da kokarin tashi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login