Showing 180001 words to 183000 words out of 189984 words

Chapter 61 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15652

da yaji kamar numfashinsa zai tsaya,ji yayi kamar ya ce", a hakura da bikin haka saboda yasan ko yau babu maza hotunanta zasu yi yawo a social media a matsayinsu na sanannu,ji yayi duk ranshi ya ɓaci bashi da damar dakatar da matan da suka ziyarci bikin ɗorawa a social media,rufe idanunsa ya yi yana hasaso yawan mutanen da zasu ganta maza da mata,anya ko zai iya bari a karasa bikinnan wannan kwalliyar fa shi kadai ya dace da ya gani", me makon ganin hoto ya faranta masa sai ya zamana ya wuni da ɓacin rai,duk tsokanarsa da Yusuf ke yi bai tanka ba,shi ko Yusuf bai damu ba dan yasan halinsa,damuwarshi yanzu bai wuce ya bashi fuskar yiwa ƙaramar kanwarsu shukra magana ba,dan Allah ya gani yarinyar ta tafi dashi matuka.






A haka daga ango har amarya suka dinga ɓacin rai har zuwa yau asabar da za ayi dinner daga nan ango ya wuce da matarsa washe gari kuma sai yan uwa na nesa suje ganin gida.






Ƙin tsayawa ta yi a yi mata kwalliya sai da Auntyy Khadija ta je ta gayawa hajiyar agadex,,hajiyar agadex tana shigowa dakin da ake shiryatan ta yi mata dakuwa tana cewa yau dai naga baƙin rannan da kike zai kare tunda yau zamu mikaki gun wanda kikewa,ko kinyi zaton ban san abinda kikewa ba?,fadin haka da hajiyar agadex ta yi kuma duk sai ta ji kunya babu shiri ta tsaya aka tsantsara mata kwalliyar da ita kanta saida taji tsoran kanta,Masha Allah tabarakalla haka me kwalliyar take ta faɗa tun kafin ta kammala shirya RAIHAN ɗin..




Babban hol din dake cikin gidan gwamnati yayi tsit kai ba ka ce mutanene wadanda suka haura dubu ba aciki,tun bayan sanar da shigowar ango da amarya gurin yayi tsit saboda karramawa ta musamman ga ango da amarya.






Motar da aka dauko RAIHAN daban motar da aka dauko wazer daban,dan haka har yanzu basu ga juna ba.




Bude motar escort din ango su kayi ango ya fito,waww abinda zan iya cewa kenan,hakika ba zan iya kwatanta muku irin kyau da wazer ya yi ba,to kyaune ya hadu da kwalliya da aji da kuma kasaita dan haka kuwa sai abinda aka gani.




Har bakin motar da Raihan ke ciki a hakimce suka rakashi daga nan suka ja baya su da EXCO din amarya suka yi nasu comber din suna tsimayin fitowar amarya,




A hankali ya duka bayan ya bude murfin bangaren da take Sannan ya dan zura kansa,take yaji numfashinsa na sarkewa saboda wani azababban kamshi me sanyi da sanyaya zuciya kafin idanunshi su yi arba da abincin da aka hanashi gani bare tabawa tsawon kwanaki goma,jan numfashinsa ya yi a nutse sanann ya furzar dashi,a hankali ya mika dogayen hannayensa da suka ji adon agogo samfurin alben me tsananin walwalin gold da sheki ya kamo nata da suke kawace da adon jan lalle da baki da bangle din gold da zobuna,dukkansu ji su kayi numfashinsu na kokuwa saboda yadda zuciyoyinsu suka amsa da wani irin kewa bege shauki me ban mamaki,duk da cewa ita Raihan har yanzu ta kasa dago kanta ta kalli kyakkyawar fuskarshi dake sheki da haske tamkar wata,duk yadda take jin kewarsa da begensa sai taji sam yanzu bata iya kallonsa saboda wata irin kunya wadda ke hade da wani irin shauki ta baibayeta,(tabbas kai budurci gidan miji koda irin na su Raihan ne da aka daura aure yana da muhimmanci, yanzu da wazer ya amshi budurcin Raihan da wannan shaukin ko da zai jishi ba wani cancan ba,kuma ita ma ba zata kai masa wannan nagartacciyar kunyar da aka san ɗiyan Hausa Fulani da ita ba.shi kuma Wazer ba zai ji irin kewar da yake ji a yanzu ba,saboda ya riga ya samu wani bangare na farincikin aure ko na ce abinda ake yin aure dominsa daga gare ki,ki sani cewa duk SOYAYYA da mijinki yake miki ko zai miki muddin babu wannan budurcin wallahi kin zama sorry ,ey akwai son ba babu ba,amma akwai jin haushi me tsanani wanda zai iya rinjayar wannan son,kuma tsautsayi kadan zai iya giftawa ya yi miki gori duk daren dadewa ko akanki ko akan yayanki,dan haka ina kira garemu ke da baki auren fari ba,ki rike darajarki da mutuncinki har zuwa gidan mijinki,idan ba haka ba akwai nadama,ba iya budurwa ba har zawaran duka ina kira gareku Allah yasa mu dace).






Wazer ji ya yi tamkar yaja matarshi su koma gida saboda baya jin zai iya jurar kallon daruruwan mutanen da zasu samu kallon fuskarta da gangar jikinta,wata kila ma wani zai iya raya cewa inama wannan matarshi ce", runtse idanunshi ya yi tare da hannunta dake cikin nashi,kasa barin wajen ya yi har sai da Yusuf ya matso ya sanar dashi su fa ake jira,dole ba dan yaso ba sai dan kar ya bar iyayensu da jin kunyar manyan mutanen da suka samu halartar wajen.




Daga kafarshi yayi sannan itama ta daga,yadda zuciyarshi ke bugawar azabar kishi haka Raihan da har yanzu bata ga kwalliyarsa kanta yana kasa Tata ke bugawar yawan yanmatan da zasu gane mata shi,tasan cewa Wazer ko bai kwalliya ba shi din me kyaune kuma me aji ne dan haka bata da bukatar yin la'akari da kwalliyarsa.




Wani irin taku ne suke yin shi me cike da aji da kasaita wanda yakasance tamkar umarnin yinsa a ke basu,kamshinsa da nata kuwa tuni ya buge ko wane kamshi dake wajen.




Cikin girmamawa duka mutanen dake gurin suka mike ba tare da ambasu umarni ba, yayin da wani irin sassanyan sautin kida ke tashi a wajen cikin slow.




Cikin takunnan da suke yinsa ɗai-ɗai tamkar suna saman gajimare suka isa mazauninsu,basu zauna ba sai da wazer ya daga hannunsa dake sarke da na RAIHAN yayi wavin din yan uwa da abokan arziki alamun Barka da zuwa,suma daga musu suka yi sanann wazer da Raihan suka fara zama kafin sauran mutanen suka zauna a lokaci daya suna sakin tafi taf raf raf,,,,,idan na ce muku katarwa to karshen kayatuwa nake nufi,ba kida a kayi a wajen ba,manyan mutanene suka dinga yiwa amarya da ango kyauta dangin ango na yiwa amarya dangin amarya na yiwa ango abun burgewa daga karshe a kayi wa azi me ratsa zuciya aka rufe da karatun Alqur'ani da a marya ta rera wanda ya sa mutane da yawa zubar da hawaye saboda kushu'i da aka samu a cikin karatun alhamdulillah Masha Allah abinda mutane suke fada ke nan,da haka taro ya watse ango da Amarya basu bar gurin ba suna mazauninsu duk wanda zai tafi zai karaso su gaisa su yi hoto har kowa ya watse ya rage saura abokan ango dana amarya da sune karshen tafiya tare da ango da amarya saboda jagoranci da za suyi musu zuwa gidansu rakiya.






Kai tsaye main Hause suka wuce saboda sai ya fara Kaita wajensu Ammi da innawuro kafin su wuce can gidansa da ya tanadeshi domin farincikinsa Raihan.




Duk wannan budurin da akayi akan idanun Rabia da take gani a acikin tashar Chibado da ake haskawa live,ganin yadda numfashinta yake neman barin kirjinta yasa mamanta ta kashe tv sannan ta karaso tana rarrashinta da kwantar mata da hankali.


________


Innawuro dakanta ta fito tarbar RAIHAN iyalanta zagaye da ita suna take mata baya,da kanta tayi Bismillah sannan ta riko hannun Raihan ɗin ta fito da ita,wata yar uwar innawuro ta sanya budu kafin nan suka rankaya su kayi cikin katon falon innawuro,ta ciki suka bi suka wuce zuwa babban falon Abbu inda suke tare da Ammi.




Zaunar da ita innawuro ta yi a gaban Abbu da Ammi sannan itama ta samu guri ta zauna.




RAIHAN kanta yana sunkuye ta fara gaida surukannata,amsawa su kayi suna mai sa mata albarka,daga nan kowa ya bar falon sai su isu,Yusuf ne ya shigo da wazer kamar yadda Abbu ya umarceshi da ya rakoshi.




Bayan nasiha me ratsa zuciya da suka gabatar wa yaran nasu,daga karshe innawuro ta kuma fito da Raihan har cikin sabuwar motar da Abbie ya bata wadda suka zo a ciki, Allah ya yi muku albarka ta fada sannan ta ɗora mata kyaututtukan da bata san ko meye ba a cinyarta,na gode innawuro Allah ya saka da alheri ya bamu ikon binku sau da kafa..........✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page68 ```


Ameen innawuro ta amsa tana rufo kofar bangaren da RAIHAN ɗin take,komawa ta yi wajen wazer kasancewar driver ne yanzu zai tukasu,dan haka ta dawo bangaren da yake shima ta yi masa sai da safe,tana shirin tafiya taji ya riko hannunta tare da saka mata wata yar karamar takarda,duban takardar ta yi sannan ta dubeshi dan son jin karin bayani,basarwa yayi sannan ya daga fatar bakinshi a hankali ya ce", ta jikarki ce ki bata tunda dama ke kika hada", zuba mishi ido ta yi tana masa kallon anya abinda kayi ka kyauta kuwa? Kamar ya san abinda take tunani dan haka ya kuma yin kasa da murya sannan ya ce", bazan iya ba innawuro akwai wahala rike mata biyu,sannan Allah dakanshi cewa yayi ku yi daya idan har ba za kuyi adalci ba,to Ni kam ba zan yi ba Allah ya gani kuma ya sani", daga haka ya koma cikin motar tare da rufewa wanda hakan shi ya bawa driver damar jan motar a hankali cikin nutsuwa ya fita daga tafkeken gate din da securitys suka wangale shi.






Ajiyar zuciya innawuro ta saki tare da kara kallon takardar tana jin jikiinta na yin sanyi,tabbas abinda wazer ya fada gaskiya ne,to amma ya za ta yi da rabi a? Bata so taga kamar dan ubanta yayi wannan halin an wareta ko kuma taga kamar ba a sonta kamar yadda take gani a baya,to amma babu yadda ta iya rabi a da ubanta su suka jawowa kansu,tana shiga falon ta bawa Abbie takardar bai tambayeta ba ya shiga budewa,(Ni Ahmad wazer Chibado na saki Rabia Mustapha saki daya bisa dalilan da ba zan iya fadarsu ba amma daya daga ciki shine ba zan iya adalci ba) Wani irin sanyi Ammi ta ji dan kuwa yanzu gaba daya ta tsinke da almarinta itama zata iya kashe wazer ɗin tunda halin ubanta ta yi ", Abbu kuwa komai bai iya cewa ba sai innawuro da ya mikawa takardar sannan ya iya cewa Allah yasa haka shi yafi alkhairi dashi da ita", Amin suka amsa gaba daya.




___________




A hankali motar take tafiya saboda umarnin da aka bawa matukinta da yaja a hankali saboda zinariyar dake cikinta,ba kajin komai amotar sai sassanyan ƙamshinsu da ya haɗe guri daya ya kuma bada wani kamshin na musamman,sai kuma na urar dumama guri da ta cika motar da dumi me dadi wanda ba zai cutar da mutum ba,kasancewar mun fara shiga cikin yanayin sanyi wanda ya taho da karfinsa a lokaci ɗaya.




Can gefe RAIHAN ta matse jikinta kanta kasa tana jin wani irin kewar gida wanda yasa ta zubar da hawaye,daga nan ta fara kuka kasa kasa kamar me tsoran ajita,bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba ita dai kawai ta tsinci tattausan hannunsa saman kafadarta kafin a hankali ya janyota gaba dayanta ya manneta da jikinshi,alokaci daya suka saki ajiyar zuciya,lumshe idanunsa ya yi ya bude su fes akanta yana kallon daurin kanta da yake ganin zai iya damunta, wannan tunanin da ya yi ne yasashi zame dankwalin daga kanta take sassalkan gashinta baki me sheki ya bayyana yana zuba wani ubansu ƙamshin da yasa wazer dora fuskarshi akannata yana shakar kamshin da yake ji bai taba jin irinsu ba,tamkar wani maye haka ya shiga bin kanta zuwa wuyanta yana shinshinawa har ma yana neman manta inda suke.




Itama Raihan ɗin tun bayan jinta da tayi manne da faffadan ƙirjinsa kukanta ya tsaya ba tare da ya yi mata rarrashin baka ba,wanda dama shi bai iya shi ba sai dai yayi shi a aikace.




Tsayawar da motar ta yi shi ya ankarar da wazer inda suke,dakyar ya iya dago kansa dake wuyan Raihan tun dazun sannan a hankali ya bude baki ya ce," da driver isah ina sakon da Yusuf ya baka?cikin sauri isah dake karasa kashe motar ya ce", suna nan gaba yallabai",




"Ok ka shiga dasu ciki",


An gama yallabai",




Daga haka ya fita daga motar bayan ya dauki manyan ledojin da suke gaban me zaman banza.


Shiru wazer yaki fita har sai da Raihan ta dago da kanta ta kalli fuskarsa ta cikin dan hasken da ya haska cikin motar ,sarai ya gane me take so tace amma sai ya basar,bai ce komai ba har sai da isah ya dawo ya bashi key ɗin motar yayi masa ihsani ya kuma tabbatar securitys sun bude masa gate ya tafi Sannan ya daga Raihan ɗin cak suka fito tana hannunshi tamkar wata jaririya,a haka ya nufi cikin gidan da ita.




Idan na ce zan tsaya fasalta muku haduwar wannan gida lallai kuwa zan gundureku dan haka ku ƙiyastashi a ranku da karshen haduwa,sai dai muce Masha Allah Allah ya bamu wanda ya fishi a nan da kuma aljanna",




Bai tsaya da ita a falon ba kai tsaye ya haye up stairs da ita ,ya shige da ita hadadden dakinta da yake ta zuba kamshinta da yake manne da komai nata,a hankali cikin nutsuwa ya kwantar da ita,a yanayin yadda ta tafi luuu yasashi dan kallon fuskarta da take ta sheki,dan murmushi ne ya subce masa ganin wai har ta yi bacci,kyaleta ya yi bai tasheta ba har sai da ya kammala shirinsa tsaf sannan yazo ya zauna a gefanta ya shiga dan tafin fuskarta cikin wata irin lallabawa da tarairaya kamar kwai,aiko a hankali ta shiga bude idanunta da suka dan fara canja launi saboda bacci,mirgiinawa ta yi zata ci gaba da baccinta yayi saurin rikota tare da tayar da ita zaune.




Fuska ta kwabe tana shirin sakin kuka alamun ya takura mata, langabar da kanshi gefe ya yi sannan a hankali ya ce", sorry freety yanzu ba lokacin bacci ba ne", to lokacin me ye? Ta faɗa tana kokarin zamewa dan kara kwanciya,shima yayi saurin kuma tarota yana cewa lokacin yin ibada ne sallah za mu yi kici abinci", na koshi kuma nayi sallah", a'a hibban wannan sallar ta godiya ga Allah ce da ya kawo mana duka karshen makiyanmu ba tare da tsuminmu ko dabararmu ba", dan shiru ta yi bata ce komai ba sai murza idanunta da take yi tana so ta dan wartsake.




Sorry ya fada cikin wata irin lallabawa da son yin calming dinta duk dan kar ta damu.




Bude idonta ta yi sosai akan shi kafin cikin sakalcinta ta ce", to amma muna yin Sallah zanyi bacci ko?




Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya iya furta komai ba,tura karamin bakinta ta yi tare da kwabe fuskar kafin ta ce", ai baka amsa ba Ni kam sai ka amsa min da baki sanann zan Yadda", na amince zaki bacci", ya fada a hankali yana ci gaba da kallon fuskarta da baya gajiya da kallah,bai bari ta kuma yin wata maganar ba ya dauketa cak yana farawa da zame mata hadaddiyar rigar dinner dinta,har ta fara wurga kafafu akan ya barta zata yi da kanta amma yadda ya haɗe fuskarnan ya dawo asalin wazer dinsa yasa ta yi gum.




Tana ji tana gani yau dinma ya sabeta tas ya kuma danota cikin katon showel yazo ya shiryata cikin wata hadaddiyar rigar bacci wadda tasa ta jin kunyar da bata shirya mata ba,hijab ya saka mata sannan ya nuna mata wajen sallar da aka kebance shi kamar fadar Sarkin Makka.




salloli su kayi wadanda Raihan bata san adadinsu ba,sai da yaga Raihan na neman kwanciya kana ya hakura su kayi zaman addu'a,sosai ya yi mata addu'a tare da yi mata tambayoyi akan addininta daga karshe yasa ta rera masa karatun Alkur'ani ayoyi goma daga cikin suratul kahfhi cikin zazzakar muryarta wanda yaji tamkar kar ta daina,amma ba yadda ya iya haka suka shafa,a hankali ya kamata yazame mata hijab din ya maidashi muhallinsa,kunya ce ta kuma kamata ta shiga rufe jikiinta da yake duk a waje,shi kam Wazer ko ajikinsa sai ma fita da ya yi ya dauko kazar da ya tsaya ya yayyankata kananu ya kuma zubo madara a Glass cup guda biyu ya kawo ya dire yana ɗan yatsina fuska saboda yayi aikin da bai saba yi ba.




Zuwa yayi ya janye bargon da ta shige yana cewa baki yi dayan aikin ba zaki kwanta,bude idanunta da suke cike da bacci ta yi ta dan kalleshi sannan ta juya ta kalli abinda ya shigo dashi din,kamata ya yi ya dagata ta tashi zaune,janyo dan teburin da ya aje madarar ya yi gabansu ita kuma ya janyota jikinsa yayi mata makari da kirjinsa,a hankali ya shiga bata tsokar naman kazar tana ci cikin nutsuwa shi kuma yana karewa dan karamin bakinta da yake taunar cikin salon da bata san tana yinsa ba kallo,ganin yana kallonta yasa ta bata fuska sanann ta dauki kazar da hannunta tayi hanyar bakinshi da ita,bai Musa mata baya bude bakin amma memakon ta sa masa sai kawai tayi kwana da ita ta jefa a bakinta tana masa gwalo da cewa punishment din kallon da kake min kana neman sani kwarewa.




Au haka ne? Ya tambayeta yana ƙoƙarin saka mata wani naman abakinta", dage mai gira ta yi, murmushi kawai yayi yana cewa azuciyarshi ki yi komai kike so yanzu lokacinkine,kafin nan da wasu mintuna nawa lokacin ya fara.




Madarar ya bata tasha sannan ya danci kadan shima yasha madarar kana yajata suka je su ka kuma yin brush.


Yana kallon hammar da take tayi akai akai sai da ya ce hmm azuciyarshi.




Kwanciya ta kuma yi tana jan tattausar duvet dinta daya ke ta zuba kamshi me sanyin dad'i,gefanta ya kwanta yana shigewa cikin jikinta tare da sakala hannunshi ya zagaye cikinta a hankali kuma ya burkitota ta dawo suna fuskantar juna,kifkifta idanunta ta shiga yi dan tsoro ya fara shigarta,yatsanshi ya saka saman idanunta yana zagaye idanunta in a emotional way sannan a hankali ya bude bakinshi ya ce ",

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login