Showing 9001 words to 12000 words out of 189984 words
dan sauke farali,dan babu zancan zuwa Masallaci a gurin sa tunda auntyn bata bari,da dai Abbin shi na nan ne yasan dole zasu tafi tare.
Yana idarwa yayi azkar dinsa na marece tare da karanta wasu ayoyi daga cikin suratul Mu'uminin,daga nan ya tashi ya dauko jakarshi ta makaranta,zama yayi dirshen cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a kan kyakkyawar fuskarsa, ribom ya fara ɗaukowa daga nan sai sarƙa da zobe awarwaro,kai duk wasu abu na sha'awa na adon mata haka ya cika gaban sa da su,ya fara wasan sa cikin nishadi da walwala.
Innalillahiwa'inna ilaihi raji'un,abun da ya zaburar dashi ke nan ,ya kuma yanke masa nishaɗin da ya tsunduma a sanadin wasan da yake da abin da suke matuƙar burge shi a rayuwa,da sauri ya mike jikin shi babu inda baya rawa saboda tsoran ganin yanayin antyn nashi,wadda ke ta rafsa salati da inna lillahi kamar wadda taga wani mugun abin tsoran,wani irin kallon tashin hankali take bin Rahim da shi kamar zata haɗiye shi ɗanye,gadon shi ya haye tare da ƙudundune kan shi cikin tattausan dovet,yana mai rufe idanun shi da kunnuwan shi dan gujewa tsawar auntyn shi da kuma hargitsewar fuskarta,sai dai abin da Rahim bai sani ba shine yau ran maman shi ya ɓaci fiye da kullum zuciyarta ta shiga fargaba fiye da na kullum,dan haka hukuncin da take jin zata yi masa ya zarta na tsawa,da muzurai,dan a ganinta ya raina hukuncin tsawar shi yasa kullum yake ƙirƙirar sabuwar fitinar da zata iya yin sanadiyar karar da guntun farincikinta.
Da wani irin ɓacin rai ta karasa bakin gadon,ba tare da tunanin komai ba,ta janyo shi daga cikin bargon tare da dauke shi da wani irin mahaukacin mari,wanda ya ji saukarsa babu zato,ya kuma yi masa shigar da har sai da jin sa da ganin sa suka dauke,ba tare da ta kula da halin da yake ciki ba,ta shiga banbami da masifar baya jin maganar ta,a hankali kunnen shi ya dawo daidai sai dai kuma idanun sunƙi dawowa daidai,sosai yake ganin duhu saboda jinin da ya taru a gefen idanun nasa,kuka ya saka me karfi yana kiran Abbin shi,cikin siririyar muryar da ake yawan kira masa ita da muryar mata,ya ce"aunty idanuna bana ganin komai zafi suke min a ciki kika buge ni"cak ta dakata daga niyar kwashe tarkacen kayan wasan nasa,ɗagowa ta yi zuciyarta na wani irin bugu ,kafin ta watsar da kayan da ta fara diba ta nufo gun tilon yar da take jin zata iya bada rayuwarta dan fansar rayuwarta, za kuma ta iya mutuwa a duk lokacin da aka ce yau babu RAIHAN din a duniya,Wanda hakanne yasa take yin duk wani abu domin tsira da rayuwar tilon yar tata.
Kama shi tayi cikin tashin hankali tana kiran sunan sa, RAHIM bude idanun mu gani me ya same ka a idon?ta tambaye shi cikin son kwarara kanta,aunty bana gani ido na ya rufe"innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa tare da sunkutar shi,su kayi waje tana mai kiran sale driver domin bata jin zata iya tuki a cikin wannan yanayin na tashin hankali da take ciki.
Suna tafiya tana kiran Dr Sabo da kyar ta samu kiran ya shiga,yana dagawa ta sanar da shi cewa ga su nan ita da Rahim yayi kokarin shirya musu ganin likitan ido,amsa mata yayi ba tare da ya tambaye ta dalili ba,tunda dai yasan nan din zasu karaso.
Suna zuwa babu ɓata lokaci ya kai su office din Dr salamon,ganin yadda duk aunty amarya ta ruɗe yasa Dr Sabo ya ce" plz amarya ki nutsu ki yi mana bayanin da zamu fahimta domin yin solven din matsalar"duban shi ta yi cikin hawaye ta fara bashi labarin abinda ya faru,jinjina kai kawai yayi tunda shi yasan musabbabin komai,da sauri Dr salamon ya shiga aikin sa,ai ko cikin kankanin lokaci ya gano matsalar ,duban Dr Sabo ya yi bayan ya gama binciken sa ya ce"marin da tayi masa ne ya kawo taruwar jini a gefen idon wanda hakan ne yayi affecting din ganin sa ,amma dai ba wata babbar matsala ba ce,dan a halin yanzu ma idanun sun buɗe sai dai magunguna da za a bashi da kuma kiyaye wata matsala da zata kara shafar idanun"ajiyar zuciya me karfi aunty amarya ta sake tana mai rungume Rahim ,ta ce" sorry my son ba zan kuma ba kasan ban taba dukan ka ba ko da tsintsiya ne wannan ma tsautsayi ne"yanzu ka na ganin komai? Ta tambaye shi tana shafa lallausar sumar kansa da ta fara yawa,jinjina kai yayi tare da kara lafewa ajikinta,Godiya ta yiwa Dr Sabo daga nan taja hannun Rahim suka wuce permacy,suna zuwa aka hada magungunan aka basu.
Ko a mota ci gaba tayi da rarrashin sa,tare da yi masa nasiha akan ya dinga jin maganar ta,a haka suka zo gida,bangaren Hajiya goggo suka nufa,nan fa ta shiga tarairayar Rahim da nuna masa gata,hakan yasa Anty amarya zama a bangaren saboda baza ta iya tafiya ta bar Rahim ba,kuma bazata iya daukewa Hajiya goggo dan farincikin da ta samu na ganin Rahim din ba,hakan yasa sai wajen sha biyu na dare su kabar sashen,a lokacin ma tuni Rahim yayi bacci.
Kwanaki na ja suna zama sati ,sati na komawa watanni watanni na komawa shekaru,abun dadi da akasin sa na faruwa,burukan mutane wasu na raguwa wasu na karuwa,ana haihuwa ana mutuwa,to kamar haka ne ya faru akan Rahim rayuwa na gangarawa halittun shi na canjawa kalubalen rayuwar shi na karuwa, kullum yanzu sai ya duba kan shi a madubi ya karewa matashiyar halittar sa kallo,yayin da zuciyar shi take da ɗa cika da ɗimbin mamaki na yadda Allah ya halicce shi a sunan namiji halittun shi kuma kaf irin na mata,sosai abin yake bashi tsoro dan a yanzu yana matakin shiga shekaru goma sha biyar,ya gama secondary school tare da saukar alkur ani da kuma litattafan addini, kamar su hadisi piqhu sira bulugu akbari ishmawi da dai sauran littafan addini,saboda Rahim hazikine a kowanne bangare shi yasa ya samu karatu wanda ya fi shekarun sa yawa,tun da ya gama secondary school aunty amarya ta tare gaba ta tare baya bata barin sa fita ko ina sai tare da ita,bata barin kowa yazo wajen sa ko a cikin gidan na su ba ko ina yake zuwa ba sai tare da ita, wannan rayuwa da yake ta kunci ya sa babu walwala a tare da shi bai san wani abu wai shi farinciki ba,saboda an riga an gina rayuwar shi da kaɗaici,duk da gatan da yake samu ta bangaren iyayen shi da kakannin hakan bai sa ya rage kadai ci ba,a gurin baffa Ali ne kawai yake dan yin walwala duk da shima baffan fama yake da jinyar da ta tarar da tsufa,Abbin shima kullum burinsa ya ga farin ciki da walwalar RAHIM,haka inna maimuna da Abba yahya wanda shike kula da duk lamarin su na cikin gidan tun da Abbin ba zama ya fi ya yi ba.
Haka ta bangaren aunty amarya ma,sai dai duk abin da aunty amarya zata yi masa dan faranta masa hakan baya burge shi ,saboda ya riƙe ta a matsayin wadda ta yanke farinciki da walwalarsa ta hanyar raba shi da mutane masu muhimmanci a rayuwarsa,Abbin shi ya sha tambayar shi damuwar shi da musabbabin juyawar yanayin shi,to amma baya jin zai iya kai korafin auntyn nashi wanda yasan hakan zai iya jawo matsala babba tsakanin iyayen nashi,duk kuwa da cewa ta wani bangaren yana mai jin haushin auntyn a kan yadda ta ke juya rayuwar shi,sai dai so da yawa yana tunani irin na manya kuma da ilmi na sanin darajar iyaye baram ma mahaifiya,dan haka yake kokarin kawo tunanin cewa lallai akwai wani babban dalilin da yasa auntyn take abin da take yin.duk dan kawar da rikon da yake jin zuciyar shi na son yi mata wanda yasan hakan bai da ce ba a matsayin ta na mahaifiyar shi.
Haka kuma kulawar da yake samu daga wajen inna maimuna da Abba yahya yana rage masa kadaici,dan sosai suke kulawa da shi wanda hakan ya ke jawo kace nace tsakanin kishiyoyin aunty amarya dan gani suke kawai tsabagen munafunci ne da neman wajen zama a gurin Alh Muhammad nuurr yasa suke yin hakan,duk da cewa har yanzu babu wanda yasan ba Uba daya suke ba.
.........✍🏽
typing
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page4 ```
Abu daya ne yake sawa kaga walwalar Rahim da dariya harma siririyar wushiryar shi ta bayyana ,shine sauraron daddaɗar Muryar matashin saurayin nan me gabatar da shirin labarin masoya a tashar nan da tayi ƙaurin suna take kuma kan tashe wato CHIBAƊO FM,a duniya babu abinda Rahim ke kauna sama da sauraron labarin masoya daga Muryar AHMAD WAZIR CHIBAƊO,lokacin gabatar da shirin yana gabatowa zai janyo tap din shi ya yi joinin gidan Radion ya fara zaman jiran cikkar lokacin,ya yadda ya jira amma bai yadda ya wuce shi ba,aunty amarya dai wannan karon bata hana Rahim farincikin shi ba,sai ma dadi da hakan yayi mata,harma da kanta take zama tana taya shi jin shirin dan kawai ta kawata farincikin nasa,ai kuwa hakan ba karamin dadi yake wa Rahim ba,dan haka cikin kaso dari na damuwar sa kaso tamanin ya gushe saboda samuwar shirin labarin masoya daga Muryar matashi Ahmad wazir chibado.
A hankali aunty amarya ta karaso kusa da Rahim din hannun ta dauke da wasu tablet sai ruwa a cop din tangaran me garai_garai,ajiye littafin dake hannun shi yayi yana ya mutsa fuska saboda yasan me auntyn tazo bashi,zama tayi a kusa da shi tana cewa meye kake wani haɗe rai sai kasha maganin nan idan ba haka ba yau na hana jin shirin labarin masoya" kuma ko ka kaje bangaren goggo ko inna maimuna su ma ba za su Barka ba tun da suna so ka samu lafiya",da sauri ya bude bakin ta watsa masa maganin tare da kafa masa kofin a bakinsa ,haɗiyewa yayi badan ransa na so ba, cikin sanyin sa da ya riga ya zamar masa jiki ya ce da auntyn Please aunty wannan maganin da kike bani na miye? Na mutuwa ne ta bashi amsa tana haɗe fuska tare da barin wajen dan kar ma tambayar tayi tsaurin da zata janyo tayiwa Rahim din faɗa,(azahirin gaskiya ba ko wane magani take bawa RAIHAN ba illa maganin tsaida jinin al'ada saboda duk wannan yana daga cikin tashin hankalin ta saboda shine abu na farko da RAIHAN zata fara yi ta gama tabbatarwa Ita din fa macece ba namiji ba)bin auntyn yayi da kallo yana dan tura baki irin na shi bai ji dadin nan ba,ko ta bani ba zan kuma hadiyewa ba tunda Ni dai na san lafiya ta kalau".
Duk fuskar wanda ka kalla a zahiri za kaga farincikine kwance a kanta,kasancewar yau suna tare baki dayan su family guda su Affan ne kawai ba sa nan,amma hatta da Baffa Ali da Abba yahya da inna maimuna duk suna gurin,duk da cewa dama a sashen su a kayi wannan haɗuwar wadda ta kasance suna yin ta duk bayan wata uku,ba dan komai ba sai dan zumunci da kuma jin matsalar kowa daga cikin su sai kuma hirar da take gudana a tsakanin su duk dan kara son karfafa zumunci da hadin kai da Baffa Ali
Yake so ya karu a zuriyar tasa.
A bangaren aunty Amarya kuwa wannan zama sam baya yi mata dad'i hasali ma fargabar zuwan sa take yi,a ganinta wata rana za a iya Ankara da sirrin da take faman ɓoyewa tsawan shekaru goma sha biyar ,sai dai ta wani bangaren zaman yana mata amfani ta wajen son gano maƙiyansu a cikin fuskokin da suke zagaye da su,duk kuwa da cewa har yau din bata gano komai ba,kuma hakan shi yake kara cusa mata wata irin fargaba,tunanin ta har tsawon wani lokaci zata kai tana ɓoyan RAIHAN?bayan kuma ita ta sani Dr ya sani sanin mutanen shi kadai ne hanyar bude sirrin RAIHAN, shin RAIHAN zata yi ta zama a matsayin Rahim ne? Ko kuwa zata hakura da rayuwar RAIHAN ta bangakada sirrin ɓoye?,su kuma makiya su farma rayuwar RAIHAN,daga karshe kuma ita ce da asarar ,tunda har yau bata kuma yin ko ɓatan wata ba bare saran samun wani ɗan,wanda kuma bata jin koda ta haifi wasu yaran zata iya hakura ta fansar da rayuwar RAIHAN sanyin idaniyarta,wata ƙwayar halitta da take jin tana mata son da bata yiwa kanta da rayuwarta,share zufar da ta fara tsatstsafo mata tayi tana jin kamar zata yi aman zuciyarta saboda tashin hankali da rudani.
Maganar Abban Bashir ce ta dawo da ita daga zuzzurfan tunanin tashin hankalin da rayuwar su take ciki,gyaran murya ya yi tare da fara wa da addu'a kamar yadda suka saba,bayan sun shafa sai ya fara jin damuwar kowanne,shi kuma Abbie yana rubutawa,idan wata kuma matsalar bata shafi kudi bace sai su tattauna har a samo mafita dan gyarata,daga nan kuma a ka ci abinci ,sai kuma zaman hira wanda shine aunty amarya bata so,a ƙage take da ta bar wajen saboda yadda kanta ya dau zafi dan anzo lokacin da ya kamata ta nemowa kanta mafita tun kan abin ya zama daga neman gira.
Da kyar ta iya daidaita kanta a ka kammala hirar,amma fa duk tunanin ta ba ya gun ,Dan ba abinda ta fahimta bare ta rike akan abinda aka tattauna,jan hannun Rahim dake jingine jikin Abban Bashir tayi suka wuce sashen ta tare da rakiyar Abbie ,kasancewar girkin momy ne yau.
****
WAZIRI CHIBADO HOUSE
A hankali kuma cikin nutsuwarsa wadda take haɗe da tsananin kamewarsa,wanda shine yake ƙara fidda zahirin kyau da haibarsa tare da tsananin kwarjinin sa,yake saukowa daga saman Benen da yake ɓarin hagu ta cikin hamshaƙin main falon nasu,a hankali ya sunkuya daga gefen hamshaƙiyar matar da take zaune cikin wadatacciyar kujerar da tafi kowacce girma da kyau a cikin saitin kujerum falon,tare da kai mata sumbata a gefen fuskar Tata,a lokaci daya kuma yana gaida ta cikin yaran fillanci,murmushi ne ya ƙawata kyakkyawar fuskarta wadda take kama da tasa tamkar an tsaga kara,kamo hannun sa tayi tana cewa zo nan wazirin gida yau a gabana zaka yi karin kumallo saboda na gaji da ganin kana fita da yunwa bayan idan ka fita ɓaɓatu kake yi kana karawa kanka yunwa"Ni wallahi har mamakin ka nake ta yadda kake iya zaro zance bayan kuma ba haka ɗabi ar ka take ba"a hankali ya kai hannu ya shafa tattausar suman kansa wadda take kwance lamban ta ainahin Fulani tana ta sheƙi,kafin ya samu damar tanka mata tuni ta daga murya tare da kwala kiran lantana,cikin ƙananan lokaci lantana ta bayyana da abinda ta tabbata shine makasudin kiran,tana cewa gani Hajiya inna wuro,ran wazirin gida ya daɗe" cikin kamewar shi ya ce" yauwa lantana ya aiki? Alhamdulillah sai godiya"ta faɗa tana jera kwandunan da ta fito da su daga kiching.
Inna wuro da kanta ta zuba masa kayan karin tasa ka shi a gaba har sai da ta tabbatar ta gamsu da irin cin da yayi,tun. Da dama ba wai cin abincin ne ba ya yi ba,kawai dai ba zai zauna ya ci ba ne,kullum cikin sauri yake ,kuma idan ya fita ba ci yake ba saboda baya iya cin abincin waje indai ba ya yadda da ingancin sa ba kuma ya zamar masa dole ba.
Yana gamawa ya mike tare da goge bakin shi da tisue,kana cikin nutsuwarsa din ya ce"inna wuro zan shiga wajen su Abba daga nan zan wuce office" to wazir Allah ya taimaka ya bada sa a, Allah ya kare min kai a duk inda kake"cikin jin dadin addu ar da kakar shi ke mishi a kullum ya amsa kyakkyawar fuskarsa na bayyana ƙaunar da yake yi mata,har ya fita cikin takun shi na cikakkun maza masu kwarjini da haiba tana bin shi da kallon ƙauna me tarin yawa wadda bata ɓoyuwa ko da taso ɓoyewar,numfashi taja tare da kiran lantana ta kwashe kwanukan ita kuma ta kuma maida kai ta kashingida idanun ta akan gidan tv tashar chibado FM.
Cikin dan gaggawar da ta nuna a tare da shi ya gaida ,Ammi da Abbu na shi ,cikin kaunar da suke nuna masa suka amsa ,kafin haihuwar kannen shi ta biyo baya,ba tare da ya dubi kowannen su ba ya masa yana mai kokarin ficewa daga falon,Ammi ta ce" Allah ya sa dai wannan shegen saurin naka ya Barka ka karya a nutse? Abbu ya ce" ke ma kin san innawuro ba zata bar shi haka ba" da wannan amsar da abbu ya bawa Ammi ya samu ya kufce ya fita daga falon cikin kakkarfan takun shi me cike da wata izzar nutsuwa.
Alhaji WAZIR CHIBADO bafulatanin Yola ne cikakke,dan boko ne ko nace tsohon dan jarida ,wanda yayi suna a cikin jahar ta Yola,hakan ne ma yasa ya bude katafaren gidan tv da rediyo wadan da suka yi suna a cikin birnin Yola da Adamawa,harma da wasu jahohin ,mahaifin sa chibado ya dade da rasuwa kuma su uku kawai iyayen su suka haifa,daga yayar su inna batula sai shi sai kanin sa Mustapha, mahaifiyar sa me suna innawuro,ita kadai ta rage musu,a yanzu haka kuma suna tare a tamfatsetsen gidan sa,matar sa ɗaya Hajiya Binta wadda suke kira da Ammi,sai ya'yan su biyar ,bababban shine Ahmad wazir chibado,sai kalil wazir chibado sai umma rumana wazir chibado,sai kuma Nasiru WAZIR CHIBADO,da kuma auta me sunan innawuro wato Khadijah suna ce da ita shukrah,
Kowannen su yayi karatun boko da addini me kyau da na garta,sun samu tarbiyya da soyayya daga gurin iyayen su,anyi auren umma rumana ba da jimawa ba ita da babban dan kawun su,safiyulla,kkhalil yana Amurika bai karasa karatunsa ba, Nasiru ne yazo hutu wanda yake kasar ƙatar wajen yayan Ammin su a wajen sa yake nasa karatun,auta kuma yanzu take shirin shiga jami a ,an zama yanmata, Ahmad kuwa dawowarsa ke nan,daga syprus a can ya yi karatun sa na jarida dake shekara uku ne sai ya ɗora da