Showing 18001 words to 21000 words out of 189984 words
labarin asalin su da yadda komai ya faru har da yadda sunan ta ya samo asali da irin kaunar da Alhaji nurr mahaifin ta ke wa mace me suna RAIHAN,komai bata bari ba har zuwa ranar da aka haife ta da kuma gundarin dalilin da yasa suka boye ta,shuru raihan ta yi tana sakin ajiyar zuciya, ya yin da kuma daga wani bangaren na zuciyarta yake son saka mata ganin laifin mahaifiyarta,wani kuma sai kokarin ture hakan yake da maye gurbin laifin da matsananciyar kauna da tausayi na mahaifiyarta harma da mahaifinta,nasihun da Dr Sabo ya shiga yi mata da kuma yi mata bayanin alkawarin da suke son ta yi musu, shi ya katse mata tunani,ya ce" RAIHAN ki daure ki ci gaba da zama a matsayin ki na Rahim a idanun duniya ,ke kadai ce yanzu muke da hope din zaki taimaka mana mu cimma gaci,ki duba halin da mahaifiyar ki take ciki da kuma wahalar da tasha akan boyanki,dan Allah ki bamu hadin kai"a hankali ta zame jikin ta daga na Anty amarya tashi tayi tare da barin falon ba tare da ta ce musu komai ba,dakinta ta Wada ta shiga rafsa kuka,kukan da ta rasa na menene ,
Da sauri antyy amarya ta bi bayanta ,amma sai taji kofar a rufe ,gashi safayar nata duka suna dakin tun da yanzu tare suke kwana,kuka anty amarya tasa tana cewa Dr Sabo na shiga uku RAIHAN bata fahimce mu ba,ta rufe dakin bana son damuwar ta kar wani abun ya same ta"ta faɗa tana mai sake rashewa da kukan,Dr Sabo ya ce" a'a amarya kar ki saurin yanke hukunci ki bari ta huce ta fita daga alhinin ƙaddararta,ni nasan cewa RAIHAN zata fahimce ki kuma zata bamu hadin kai ,ki yi hakuri ki bata lokaci,kin san dama dole sai haka ta faru"dor bell din da a ka danna ita ta zaburar da anty amarya,cikin sauri ta shiga goge hawayen ta da kokarin dai-dai ta kanta,zuwa ta yi ta bude kofar ,Hajiya goggo ce ita da jiddo,duban antyy amarya ta yi fuska a hade ta ce" ina Rahim ɗin? Cikin bugun zuciya da in ina antyn amarya ta ce",me ya faru goggo? Ai ke zan tambaya me ya faru ,tun dazu jiddo tazo gurin Rahim amma sai ta samu kun rufe kofa kuna azabtar da shi dan ta ce kukan sa kawai take. Jiyowa"Da sauri Dr Sabo ya mike yana gaida goggo bai saurari amsawarta ba ya shiga bata hakuri da cewa kiyi hakuri goggo
Ba wani abu ake yi masa ba,kin san dai halinsa akan shan magani da allura,wasu ragowar magani ne da Allurai da ba akammala masa ba shine yake ta rigima wai ana damunsa da allura yanzu ma ya gudu dakin yaki budewa"goggo itama ta juya ta zubawa anty amarya ido kafin ta ce"anya babu abin da kike boye mana akan RAHIM? Cikin jan numfashi da karkarwar baki Anty amarya ta ce" babu komai goggo in da da akwai bazan boye miki ba" ƙwafa goggo ta yi tare da nufar dakin Rahim ɗin ta na cewa ,Ni dai ina gargadinki da babbar murya idan ma da wani abu a ranki"taba kofar ta yi ta ji a rufe kiransa su ka fara yi ita da jiddo,amma babu alamun zai bude kofar bare ya kulasu,haka suka gaji suka bar wajen Hajiya goggo sai masifa take akan anty amarya tana takurawa Rahim ,shi dai Dr Sabo tuni ya bawa kafafun shi iska tun kafin Hajiya goggo ta make shi,itama anty amarya
Hakuri kawai take bata duk dan bata so ta zargi komai,a haka ta samu ta bar shashen duk da cewa bakinta bai yi shiru ba.
Tun da RAIHAN ta kulle kanta a daki take kukan yadda kaddarar ta tazo, wannan wace irin rayuwa ce? Take tambayar kanta,ke nan haka zan ci gaba da boye kaina?me yasa tun baya ba su gaya min ba?yanzu ne suka ga ya fi da cewa da su sanar dake tun da ko ba su gaya miki ba,dole zaki gane saboda alamun balaga da su ka fara bayyana a jikin ki,da kuma ilmin da kika yi wanda ba dan kuruciya ba tun baya ya kamata ace kin gane ba tare da an gaya miki ba,wani bangare na zuciyar ta ya bata wannan amsar, murmushi ne ya suɓuce a, kan kyakkyawar fuskarta,a hankali ta tashi ta nufi jikin badubin dakin,zubawa kanta idanu ta yi tana mai tsarkake buwayar Ubangiji da kuma ƙara kaɗaita shi akan yadda yayi mata baiwa ta zamowa mace kuma ya bawa mahaifiyarta da Dr Sabo fikira da basirar ɓoye ta a matsayin mace da bayyana ta zuwa namiji.
Take ta shiga kai kawo a dakin da tunanin umarnin Anty amarya,idanun ta ne suka kuma cikowa da kwalla tana jin jina yadda zata iya ci gaba da boye kanta tun da ta san dole tabi umarnin aunty amarya a matsayin ta na me son kare rayuwarta da taimakon Ubangiji,tabbas ta yiwa aunty amarya uzuri akan abin da ta yi ,to amma ita ta yaya zata fara fuskantar sabuwar rayuwarta a matsayin namiji?share kwallar ta yi tare da karasawa bakin ƙatuwar sif din kayanta,budewa ta yi tare zubawa sutturunta ido,yar ajiyar zuciya ta saki saboda yadda ta ga kaf kayanta manyan kayan sanyi ne masu wando da hula,mara sa nauyin basu da yawa,rufewa ta yi tare da aiyyana cewa haka nan zata ci gaba da saka su tana boye jikinta dan tsira da rayuwarta da kuma cika alkawarin Anty amarya har ma da son samar da nutsuwa ga mahaifiyarta abar kaunarta.
Antyy amarya ta rasa sukuni da nutsuwa ,tun da RAIHAN ta kulle kanta,ko da me aikin su ta dawo daga aika , anan bakin dakin RAIHAN ta samu Anty amarya nazarya da kaiwa da kawowa,ko da larai ta tambaye ta cewa tayi Rahim ne baya jin dadi shine ya rufe kofar dan kar ya sha magani kamar dai yadda suka sanar da Hajiya goggo.da wannan amsa ta kawar da tunanin larai.
Ranar dai yinin damuwa aunty amarya ta yi,wanda hakan da raihan ta sani ne yasa ,ta fito daga dakin domin samawa Anty amarya nutsuwa,ai kuwa da sauri antyy amarya ta janyo ta jikinta ba tare da ta ce mata komai ba ta jata suka shige ɗakin RAIHAN ɗin,haba RAIHAN ya zaki min haka ?dan Allah ki yi hakuri ki fahimce Ni kar ki min kallon muguwar uwa wadda bata son farincikin ƴaƴanta "da sauri raihan ta tare antyy amarya da cewa ,haba mamy dan Allah ki daina bani hakuri,Ni ce zan baki hakuri ba na gudu daki dan in bata miki ba,kawai na gudu ne saboda na samu nutsuwa da kuma yin tunani akan sabuwar rayuwar da zan fara na ɓoye kaina tun da yanzu da akwai banbanci da ban sani ba yanzu kuwa na sani dan haka dole nayi tunani a kan hakan"rungume RAIHAN antyy amarya ta yi tana sa mata albarka da fatan rayuwa me kyau a nan gaba.
Dalilin hirar da A Wazir chibado ya yi da Alhaji Ibrahim mangal ya sa ta kuma janyowa jam'iyyar su farinjini gurin jama a,harma da abokan adawa wanda suma suka dinga zazzage rigar su suna juyowa jam'iyyar su Alhaji Garba,kafin kace me zan tuka sun fara yaɗuwa masu kyau da marasa kyau.
A lokacin ne aka tsaida Alhaji Ibrahim mangal matsayin defity gomner, wanda da bashi aka so bawa ba, Alh garba so ya yi Aminin shi Alhaji Muhammad nuurr ya karbi matemakin,to amma sam ya nuna baida ra ayin siyasa,hakan ya sa ya ce a bawa Alhaji Ibrahim mangal,shi kuma Alh Garba ba dan komai yaso Aminin shi ya karba ba sai dan yadda ya tsaya masa da dukiyarsa wajen takarar,kuma har yanzu yana kanyi tunda ba wai anyi zaben ba ne,to amma ganin baya so dole tasa ya rabu da shi,daga karshe ma har karar sa ya kai gurin Abba yahya da Baffa,to su ma dai ba su goyi bayan shigar sa siyasa ba,amma sunyi na'am da ya ci gaba da bada gudummawar da yake badawa,da wannan aka kashe maganar.
.......A bangaren A.Wazir kuwa ,sam shi bai da damuwa da hakan,hasali ma tun da aka yi hirar ya ture batun su ya manta su a babin sa,wanda bai san su a wajen su ba Haka ba ne,ya zamar musu tamkar wani linzamin da zai kai su ga nasarar abin da suke hari,hakan ya sa suke ta kulle kulle a tsakanin su duk akan A Wazir.
A bangare daya kuma ya sakawa jam'iyyar adawar su Alhaji Garba tsananin tsanar sa,saboda suna ganin shi ne ya bawa alhaji Garba damar samun nasara akan su,duk da cewa ba ayi zaben ba,kamar su Alhaji ribodo da Alhaji sale me shanu,to shi dai A wazir duk bai san suna yi ba,daga wadan da ya yiwa dalilin nasarar da shi ma bai san ya yi ba,da wadan da ya yiwa dalilin faduwar da shi ma bai san ya yi ba.to bari dai mu bi su a hankali muji yadda abin zai kaya.
A sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakanin RAIHAN da A Wazir,duk da cewa ba su taba ganin juna ba, kuma Raihan na hakuri da halin miskilancin sa,sosai ta fahimci cewa shugaban din gwani ne wajen miskilanci da rashin son hayaniya.
Abangaren A wazir kuwa shi dai yasan yana grmama yaron da ya dauke shi tamkar yaya,haka kuma yana jin sa a rai da zuciyarsa,duk miskilanci irin na A Wazir bai cika yin sa wajen Rahim da aikin sa ba,a cikin ƙanƙanin lokaci kowa na gidan su ya san da zaman Rahim duk da cewa ba fitowa fili ya yi ya bada labarin sa ba,ta yadda kawai su ka gane shi ta yanayin yadda yake amsa wayar Rahim,ba wani abu yake nunawa kan fuskar sa ba kawai dai yadda baya ignoring din coll Dinsa ta hakan ne suka san shi din mai muhimmaci ne a rayuwar A.wazir,baram ma innawuro da har so take taga Rahim domin taga wane irin kwarjini ne da shi haka da yayi tasiri a rayuwar jikanta A Wazir.
Lokaci daya Abbie yaji maganar karatun Rahim daga bakin aunty amarya,kintsaye ta sanar da shi ta amince ya nemawa Rahim din makaranta a kasar da yaga ta da ce da irin karatunta,sosai ya ji mamakin saukowar ta lokaci daya akarankanta kuma,bai zurfafa tunani ba ya shiga neman karantu har ya da ce da samu a kasar syprus,ba su gayawa Rahim ba sunyi niyar yi masa ba zata ne dan hakan ya faranta masa.
Lokaci daya RAIHAN ta ji zancen tafiyarta makaranta har kasar syprus,amma duk da yadda take son karatun jarida sai da hankalinta ya tashi ba dan komai ba saboda A Wazir,wanda har yanzu bayan gani na farko da ta yi masa a tv bata kuma ganin sa ba a zahiri ba ko a tv ,sai dai muryarsa da ta hadda ce a ƙwaƙwalwa da zuciyarta,shi kansa A Wazir sai da yaji wani irin sanyin jiki da na zuciya lokacin da abokin shi Rahim yake sanar da shi,(kar ku manta cewa a idon duniya RAIHAN namiji ce )ganin yadda Rahim ya damu sai yayi ƙoƙarin bashi karfin gwiwa tare da nasiha, da haka ya samu ya dawowa da Rahim ɗin farincikin sa na samun cikar burin sa na san zama ɗan jarida me gaskiya.
Raihan ta so yin sallama da A Wazir ta hanyar haduwa ido da ido,sai dai hakan bai yiwu ba,babu yadda ta iya haka ta ta fi tare da rakiyar antyn ta da innar ta maimuna zuwa kasar syprus.
Karatu Raihan ta shiga yi ka in da na in ,saboda tana son ta fita da kyakkyawan sakamako, ta kuma fita a iya shekaru biyun da zata yi ba tare da ta samu matsalar da zata sa ta kuma maimaitawa ba,lokaci lokaci suna waya da A Wazir yana kara mata karfin gwiwa da wayar mata da kai akan duk abin da bata gane ba,sosai kuwa take gane karatun nasa,wanda yawanci shi yake mata karin bayani akan darussan nasu.
Yayin da kuma a tacan bangaren yan siyasa su Alhaji Garba me fata da Alh Ibrahim mangal,ba karamin ci gaba su ka samu sakamakon tallata siyasar su a gidan rediyon CHIBADO FM ba,sosai mutane suke ganin mutuncin Alhaji Garba me fata,tare da girmama shi, ba komai ne yasa A Wazir ya bada himma wajen sawa a tallata siyasar ta Alhaji Garba me fata ba sai dan ganin irin yadda yake da son talakawa da kuma irin yadda yaga yana da burin tallafawa marayu da matasa, ba A Wazir ka dai ba,hatta da jama a sun shaida cewa Alhaji Garba me fata ya cancanta da su zabe shi a matsayin gwamnan su,kuma Alhaji Ibrahim mangal ya cancanta da ya zama matemakinsa,saboda kyakkyawan halayyar shi,dan haka duk inda ka duba a cikin jahar ta Adamawa postan shi ne ,sosai ya samu karɓuwa a wajen talakawa.
Anyi zabe lafiya kuma Alhaji Garba me fata ya samu nasarar lashe zaben wannan shekarar,sai fatan Allah ya taya shi riko.
Takanas Alhaji Muhammad nurr da Abba yahya da Baffa suka je yi masa Barka da samun nasara,a lokacin ne kuma ya yiwa Abba yahya tayin matsayin chip accounter idan yana da ra ayin siyasa,dan jim ya yi yana duban Abbie da Baffa,ganin hakan yasa Baffa cewa,idan har kana da ra ayi mu ma su yi maka addu'a ne",shima Abbie kallon sa ya yi cike da bada kwarin gwiwa,hakan yasa ya karba tare da godiya me yawa,gwamna Alhaji Garba ya ce",ai mune da godiya ba zan iya manta alherin Muhammad nuurr a gare Ni ba,duk matsayin da na kai shine sanadi dan haka nine zan ci gaba da kokarin kyautata masa tare da addu'ar gamawa lafiya.
Wannan shine sanadin shigar Abba yahya siyasa tare da matsayi me girma.
A daidai lokacin kuma Raihan take cin shekara daya da fara karatu a kasar syprus.
Raihan bata samu matsala wajen boye kanta ba ,saboda tana zaune ne a ƙasar da kowa yake har kar gaban sa,dan dama yawanci kayanta irin na su ne,tunda su kullum cikin sanyi suke.
........sosai Dr Sabo yake son taimakawa aunty amarya da yarta,dan haka ta wani bangaren za mu iya cewa ya fara nasa yunkurin na son gano me ke a ƙasa.
A bangaren gwamnati kuwa ,za mu iya cewa talakawa na jin dadin mulkin Alhaji Garba me fata tare da matemakin sa Alh Ibrahim mangal, yana musu aiki daidai gwargwado,sai dai kuma akwai babbar matsalar da aka kasa gane ta ina take bullowa,daga mutanen gari har zuwa kan gwamnati yanzu gaba daya hankalin su na kan son gano inda matsalar take,mutane suna yawan mutuwa ta hanyar shan magani , sai yawan mutuwar da yara ƙanana suke yi ta hanyar yawaitar fyaɗe,sai daba ta hanyar zubda jinin al'umma,dan haka nan suke tada fituna dan kawai suyi ta kashewa jini na zuba kamar an yanka rago,hankalin mutane a ta she yake da wannan al'amari ,da yawan mutane yanzu sun fara jin tsoron fita ,baram ma da zarar magriba ta yi,saboda kusan kullum sai an samu gawarwaki sama da biyar na kananun yara,gaba daya yanzu iyaye basu da sakewa saboda wannan babbar matsalar da ta Kunno Kai wadda ta zamar musu kamar annoba,gaba daya gwamna bashi da kwanciyar hankali saboda tashin hankalin da talakawan sa suke ciki,kuma wani karin abin mamakin shine, ba iya yaran talakawa ake dauka ba hatta da ya'yan masu hannu da shunin dauka ake wasu idan suka bata sai dai aga gawar su,wasu kuwa ko gawar ta su ba a gani,to yanzu dai akan binciken da gwamnati da hukuma su ke kai ke nan,harma da yan jarida, da duk wani ma aikacin bincike.
Yanzu fa gaba daya gari ya dau dumi ,duk gidan rediyon da ka kunna batun da zaka ji ana yi ke nan kafin a saka ko wane shiri,tabbas talakawa suna jin dadin mulkin Alhaji Garba me fata,sai dai kuma rashin kwanciyar hankali ya hana su samun jin dadin yadda ya kamata,wasu daga cikin abokan adawa sun fara korafi a gidajen rediyo kan cewa , wannan abin da yake faruwa ya kamata a binciki gwamnati ,saboda sai da suka hau mulki wannan abun ya fara faruwa,to da yawan mutane basu gamsu da wannan yarfe ba,kowa dai yasan yadda siyasa take, wannan batu da ya fito sai ya sa mutane suka fara dogon tunani,take zance ya juya kan cewa abokan adawa ne suke aikata wannan fasadi dan kawai su ɓata gwamnatin dake ci,ai kuwa abokan adawa sun jawa kansu,kan kace meye an shiga ce ce kuce a Media,har ma jami an tsaro sun fara bincike wasu daga cikin manya wadan da zargin su ya fi yawa,to bari mu tafi muga a inda gizo ke sakar.
Jin yadda abin yake son taba kimar gwamnati ne yasa Alhaji Muhammad nurr,zama da gwamna dan tattaunawa akan batun.
Duk da cewa Alhaji Muhammad nurr ba dan siyasa ba ne,to amma dole abin da yake faruwa ya shafe shi tun da ya shafi Aminin sa da kuma dan uwansa da a yanzu yake cikin siyasa dumu_dumu.
Shi din me kishin talakawa ne kuma me tausayi,sai dai kuma sam bashi da sha'awar siyasa,shine dalilin da yasa ya bawa Aminin shi tallafi da kwarin gwiwa ganin cewa shi yana da sha'awar siyasa,sunan Alhaji Muhammad nurr bai taba fitowa a jerin yan siyasa ba,sai dai a jerin manyan masu kudin da suke tallafawa talakawa da marayu kai da duk wani aikin lada,dan haka yanzu ma ba wai dan kar sunan sa ya ɓaci ba ko kuma sunan Aminin shi da yayan shi ya ɓaci ba,a'a kawai tsabar tausayi da alhinin halin da al'umma suke ciki ne,duk da cewa ba za ku ce baya tsoran wani abu da zaisa mutuncin su ya tabu ba.
Wannan ne yasa shi neman zaman tattaunawar da gaggawa dan ganin ko yana da hanyar taimakawa al'umma da suke cikin halin ƙaƙaniƙayi .
Cikin fuskar damuwa Alhaji Ibrahim mangal ya dubi Abba yahya ya ce",nifa ina ga kamar dan uwanka shima ya fara zargin da ake mana na cewa muna da sa hannu akan al'amarin da yake faruwa",wani duba gwamnan Adamawa Alh Garba ya yi masa kafin cikin takaicin maganar sa ya ce",tur da wannan kalami naka,ko da yake na maka uzuri akan baka san yadda nake da Muhammad nurr ba,amma dai shi yahya ai kasan cewa dan uwansa